Page 1
by @zainab221
NI DA GIDANA
BY
Zainab ilyas mazawaje
Best brilliant intelligent writter....
Baa yarda a juya wannan littafiba ta kowacce irin siga ba tare da izinin marubuciyar ba
๐น๐น๐น๐น๐น๐น๐น๐น
Page 1
๐ป Labarin rayuwa ta d'auke yake da amsoshin tambayoyin wasu mataye,haka zalika d'auke yake da warwarar matsalolin wasu mataye. Kuma yana d'auke da mafita ga dubban matayen aure da suka shiga takun kumin Ina mafita ga damuwar su.
Sumayyya, duk ke wad'an nan furutai ga manyan a minan'ta biyu Laila da Aliya da suka sata a gaba, suka zuba mata idanu, game da tambayoyin da suke ta yi mata a kan rayuwar'ta. Ta dubesu tayi murmushi.
โNi ba 'yar kowa bace, ni 'yar talaka ce lis. Kuma ni ba kyakykyawa bace, amma na auri mijin da ko a mafarki, ban tab'a zaton zan aureshi ba. Na Shiga daula ta arzik'i nayi ninkaya a ciki da Sai d'ai, d'ai kun mata a duniya ke rabautar irin sa. Na mallaki kadarori da dukiya da ni kaina bazan zayyano su cikin sauk'i ba. Kuma shaida ne, da zaku labarta kowa wacece sumayya.
Taja dogon numfashi ta d'ora.
Duk da wannan jin dad'in duniyar da daula da sa'ar miji na kerewa sa'a da na rabauta, Ina tare da wani tabo na mikin ciwo a zuciya ta da ya kasa warke wa da a ka jarrabeni da shi, da Sai Jifa Jifa yake motsamin yayi ta d'an zugi idan na tuno jarraba ta, a rayuwa. Babu kuma Wanda yake fahimtar wannan damuwa tawa, sai Mijina da muka zama han'ta da jini.wannan ita ce mummunar kaddarata da nafi jin ciwonta fiye da kowacce.
Laila ta dafa kafad'ar sumayya Sannan tace.
"Sumy, yanzu nan har kina da Wata damuwa ko
matsala a rayuwa da bata kau ba?. Zato na ai kin gama shan kwana."
Aliya ta karb'a.
"Wallahi yarda kika zama a bar Sha'awa ga mata a ko'Ina babu wanda zai yarda kina da Wata damuwa ko yaya a rayuwa sumayya.
"Idan kuka fad'i haka, kun jahilci sanin ita kan'ta rayuwar. Babu yarda za'a yi a ce wai mutum burin sa a rayuwa ya cika d'ari bisa d'ari, ko bashi da matsala ko d'aya, dole ubangiji yatab'a shi, ta wani b'angaren ko a hanashi ta wani fannin. Cikakken musulmi, zai ce yayi imani, Sannan a ce wai ubangijin'sa bazai jarrabi imanin sa ba? impossible."
"Gaskiya ne, dole ne Kam." A cewar Aliya.
Laila ta muskuta, ta k'ara matsawa dab da Sumayya, tayi d'an duba kad'an cikin katafaren falon da samun irin sa zai wahalar a zamanin nan.
"Sumayya, don Allah ki daure ki bamu labarin rayuwar nan taki domin na tabbatar a Kwai a bubuwa da yawa da mata zasu amfana da shi, domin ke d'in nasan bata wasa bace, Sai dai a d'au co's a wurin'ki a komai, tun da ga mai gida ma duk kin mallake, kullum tunanin'sa yana gareki."
"Tabbas, tun da daga zaman mu a nan, ya kiraki a waya ya kai sau biyar." Inji Aliya.
Sumayya tayi 'yar dariya tace.
"Bazan ce ba haka ba ne a minai na, sai dai nayi k'ok'arin mai da tunanin Ku can baya, domin Kusan gwagwar mayar da sumayya tasha kafin ta samu wannan matsayin wurin Mijinta da wurin dangin'sa, har ma da ku da duk wad'an da nake burgesu da basu Sha'awa. Duk Wacce zata iya kwaikwayo na wurin juriya da Hak'uri da dangin sa da dogaro ga Allah, da iya tafiyar da miji da juriyar irin d'abi'un sa duk hutsancin'sa, to tabbas zata iya dace da irin rayuwar Sumayya ko ba duka ba.
Sai dai matsalar dole idan Ina baku labarin za'a zo wurin da zan yi ta kuka, k'arshe ma na sare na kasa ci gaba. Saboda haka domin komai yazo min da sauk'i zan rubuta muku a rubuce kawai.
Ta dan ja fasali, kafin tace.
Na yarda Ku yad'a shi ma, ko ya zama littafi, domin na tabbatar 'yan uwa na mata zasu k'a ru da yawa ma. Ku bani Sati biyu, saboda kunsan Mijina yanzu bai fiye yin nisa ba sosai, kuma yana d'an jimawa bai yi tafiya ba ynz.,kunga kuwa Sai ya fita zan samu dama ko?.
"Wallahi da gaskiyar'ki . Mu dai godiya muke sosai, muna jira ."
Cike da zumud'i Laila ta fad'a.ita ma Aliya jinjina tayi mata.
"Allah yaja da ran gimbiyar mata, Allah ya k'aro twin's biyu bayan su Abalkhair. "
Murmushi Kawai tayi. Saboda sun jima suna yi mata nacin labarin rayuwar'ta saboda ta zamewa kowa kamar abar shaawa da kwatance.
Amma fa ga Wanda ya San'ta ko ya gan'ta ko labarin'ta da ya shahara ya riski Mutum.
Bayan Sati biyu kuwa Sumayya ta cika alk'awari ta basu rubutaccen labarin'ta.
_______________________
jigon al'amarin kaddara
Had'uwa ta da Fa'iz Bukar, daga nan k'addarar ta soma.
__ Ajin ya kaure da hayaniya saboda rashin malami,dama kuma al'adar 'yan a jin na mune surutun, koma da malamin, saboda sunci sunan mun gagara.
Ni da nake monita na tashi na duba time table, domin naga wani malamine da mu a lokacin,naga English teachear ne, wato malamin turanci.
Na nik'e na nufi taff room in da mu kaci karo da malam Abba class teacher d'in mu. Na rusuna nace.
"Sir, babu malami a ajin, Sai hayaniya kuma suke sunk'i yin shiru."
"Wani malami ne daku bai shigo ba?". Yace.
Nace "English teachear ne sir, kuma anyi masa transfer,sabon malamin da a kace yau zai soma zuwa kuma bai zo ba."
Da sauri yace.
"Ai kuwa yazo. Malam Fa'iz sunan sa, yana ma staff room suna ganawa da princepal na baro su.muje na nuna miki shi, ki fad'a masa period d'in sa ta Shiga, bai Sani ba ne."
Ban da shi malamai uku ne a staff room d'in biyu maza, Sai malama wasila dake aikin sa hannu a test a gefe guda.
Yana gefe d'aya shi kad'ai a zaune yana duba wani text book. Dole da ka Shiga, shi zai fara d'auke maka idanu, saboda farar fatar'sa irin haka ta shuwa a rab. Matashin saurayi ne da duk cikin malaman babu mai k'asa da shekarun sa, sai dai sama.
Ni dai Ina yin tozali da shi, na Shiga mamakin sake had'uwa ta da shi a karo na biyu a rayuwa ta, kuma zai zomin a matsayin malami. Ko da yake had'uwa ta da shi d'in ma ta farko, ba wani a bu ya Shiga tsakani na da shi ba, face wayata da na tab'a yarwa ya tsinta ya kawo min.
Tsawon Wata tara Kenan.
Amma a bin mamaki nunawa yayi kamar bai tab'a gane ni ba, da ya d'ago kai muka had'a idanu. Sai da ya wani ja a ji, cikin jin kai, Sannan yace da k'yar.
"Kece monita"Yace.
Na gyad'a kai.
"Yes, sir".
Har ya mik'e nayi ni kuma gaba, ya kirani yace.
"O K. Jeki, gani nan zuwa.'" Ya koma yayi Zaman'sa kuma bansan dalili ba.
Ban jima kuma da Shiga ba, Sai gashi ya shigo. Duk da an ga shigowar'sa ba'a saurara da hayaniya ba, kuma duk kuma da jarabar kallon da a ka bishi da shi, kamar bak'on halitta.
A haka ya soma gabatar da kan'sa cikin harshen turanci. Ya dakataYace
"Keep Quiet. I said keep Quiet. "Amma ba'a rage Surutu ba. Ai sai ya daka Mana Wata irin tsawa da dank'ara mana zagi, ya zarce da.
"Ku wad'an ne irin jakai ne ku, a na cewa Kuyi shiru baza Ku yi ba?"
Ai kuwa sai tsit ka ke ji , saboda dalilai biyu. Farko tsorata, na biyu babu wani malami da ya tab'a zagin mu, saboda ji da mu da malamai suke, koma me muka yi.
Amma shi wannan daga zuwa har ya fara yi Mana lugude? Saboda Surutu Kawai ma?.
Tabbas da a lamu zai fita zakka. Domin da jin kai da tsare gida ma ya shigo class d'in. Shiru yayi kuma yana ta harare harare da nufin yaga wata tayi ko uhum! yaci zarafin'ta, haka na karance shi. Babu Wacce kuwa ta kuma yin ko tari.
Yayi sanyi kad'an ya soma magana cikin harshen Hausa kuma.
"My name is fa'iz Bukar. Ba wasa ne ya kawo ni nan ba. Kuma bazan d'auki ko wani irin iskanci na d'aliba ba. Kuyi k'ok'arin Sani na kafin ku fad'a tarko na, shine maslaha a gareku. Bana son wasa, ko kusa cikin darasina.
Bana kuma shiri da dak'ik'ai da jakai da basu San me ya kawo su makaran ta ba. Dole ne ni a iya darasina in dai na karantar. Idan yarinya bata fahimta ba, to ta tambaya,bayan wannan bata da uzuri kuma na cewa bata iya ba.Duk wacce tayi sake ta fad'o tarko na, to ta Shiga uku,
ni bansan kalmar hakuri ba, ballantana tayi ceton ta. Ba wasa ne ya kawoni ba, na sake jaddadawa."
Ya nuna ni da pen.
"Ke monita lallai ki kula da hak'k'in aikin ki, ko kuma ki kwana a ciki. Duk mai Surutu Ina writing ki rubutamin sunan'ta. Kuma kiyi copy na time table ki kawo min anjima.
"Sit down" .
Yace, batare da ya kalleni ba, cikin jin isa.
Na zauna.
Note yayi mana muka kwafa. Yayi dogon bayani da turanci, yace duk wacce bata gane ba, tayi tambaya. Amma shiru kake ji. Iya tsiya da fad'in rai yasa wad'an da basu gane ba ma suka yi shiru.
Ko a jikin'sa. Yace Kowacce taje tayi bita kafin ya dawo.
Yana fita a ka rud'e da sowa. Yasha zagi, a d'abi'ar cin mutunci da ya soma da shi. Ya kuma Sha zuga da yabawa a b'angaren halitta. Ba'atab'a Samun malami mai kyau da a ji irin sa ba, bama iya cikin makaranta ba. Da ganin sa kaga half cast. Wato ruwa biyu.
Yabar a bin fad'a Kam da k'orafi. Saboda baki d'ayan makarantar, babu a jin da malamai ke tarairaya kuma a ke ji da su irin mu. Bawai ga k'ok'ari ba, Sai dalilai biyu. ''ya'yan masu kud'i su suka cike fiye da rabin a jin. Sannan babu a jin da ya kai shi tsula tsula kuma kyawawan 'yan mata gagara gasa, daga kan farare zuwa bak'ake. Idan Mutum ya zagaye a jujuwan d'alibai ko'ina
Mutum zai rantse tsince kyawawan 'yan mata a kayi na makarantar a ka zube a a jin mu.
Shi yasa yawancin malamai suna da wad'anda suke so cikin class d'in mu, dalilin da yasa kenan saisuyi ta tsiya ba'a yin komai na hukunci.
Amma duk da haka a Kwai d'alibai tsirari a cikin a jin 'ya'yan talakawa, kuma wad'an da baza'a ce musu kyawawa ba, kuma baza'a kushe ba. Wato irin mu, har dani.
Ni kad'aice ban tofa komai ba, a kan sabon teachear d'in namu. Wato Fa'izu Bukar.
Takun'sa ni ya burgeni sosai, saboda ta hakan na tabbatar zai yi maganin tsagerun d'alibai masu kuma nuna isar sunfi k'arfin komai. Kuma dole Zai kawo gyara da zakkarar da shagalallun d'alibai da dak'ik'ai. Saboda babu Wata alama ma da ya nuna na wata yarinya ta isheshi kallo ballantana a ce ya k'yasa da har zata samu damar kawo masa lalata.
Fari ne sosai, da ganin Sama kasan cikin iyayen'sa a Kwai sirki.
Bayan farin fatar sa a goge take, irin gogewar da ba'a cika samu ba cikin Hausa Fulani.
A gefunan fuskar sa a Kwai k'asumba da ta d'an feso, dake nunin yana da baiwarta askewa yake.
Idanuwan'sa madaidaita ne, masu launin shud'i, irin idanun nan da idan haske yayi haske yake dan ba da launin shudi.
Yana da dogon hanci sosai, da madaidaiciyar hab'a da k'asumbar sa ta zagayo ta kewaye ta, tayi masa wani irin kyau da ta dace da tsari da ita kanta siffar halittar tasa.
Babu a binda yafi komai yi masa kyau, irin turuwar girar sa bak'a da gashin kan'sa da suka d'ai sun isa bada shaidar irin jinsin da ya cakud'u da shi, ga Wanda yayi musu farin Sani. Wato (Shuwa).
Madaidai cine a tsawo. Yana da diri irin Wanda mata suka fiso.mai cikar b'araza da gab'b'ai ,da fad'in k'irji. Bashi da rama Sam. Kuma bashi da k'iba sosai. Idanuwa bazasu tab'a k'osawa ba da kallon'sa, musamman mace. Kome take nema ga namiji, na dai surar kyau, to dole ta taka burki, idan tazo kan Fa'izu Bukar. Sai dai fa idan tana k'yamatar namiji mara sakin fuska, mai jin kai da wulak'anci, tofa baza ta iya da shi ba Sai dai hak'uri.
Cinnaka ba Sani babu sabo, ko kuma mai kyawun dan maciji.
Kirarin da naji d'alibai ke yi masa kenan, wasu lokatan.
Amma Sai da ya d'an jima a makarantar yaci wadan nan kirarin sunayen.
domin lokacin ne kowace d'aliba tasan wanene Fa'izu Bukar, domin halayen sa sun bayyana a sarari sosai.
Alkalamin...... โ๏ธ
Zainab mazawaje