Page 15
by @zainab221
NI DA GIDANA
Zainab ilyas mazawaje
Best brilliant intelligent writer.... 🖋️
Page 15
Saboda Momi ta kula ban fiye zuwa wurinta na karɓi abun buƙatar da tace ba, ta sake kirana washe gari. Na durƙushe a gabanta kamar mai neman gafara.
Sai da ta shari lokaci kafin ta waiwayeni tana kallon wayarta, da latse latse kamar ba ita ta kirani ba, kamar yarda ta saba yimin, sai can a daƙile ta waigeni.
"Um, kina sane da cewa nace kome kike bukata ki na girki da bukatun yau da kullum kizo wurina, domin Faiz ni yake ba kudi duk sati na bukatun gidan nan, har kayan a binci da komai".
Nace.
"Momi, ai ba sai na karb'a ba, tun da ina da kayan garata da aka kawo ni ita, da komai na girki."
Ta zabgomin wani kallo na baki isa ba.
"Na Sani d'iyar tajiri, 'yar na gada. To, hak'k'in mune ciyar dake. Babu ruwan mu, da wanda aka kawo daga gidan tsoho. namu za'kiyi amfani dashi."
Ni kam mamaki ya kamani ma, na menene a bin zafin a ciki. Ai duk domin a amfana dashi aka kawo garar.
Na sanyaya murya nace.
"Allah ya huci zuciya, Momi, ayi a fuwa, tuba nake. Zan rink'a karb'a.Duk da haka komai na aikin gidan nike yi. Wanke wanke Shara, wanke band'akuna da kayan k"amshi. Amma fa banyi fari ba, bata hanani ba dai. Khairat girki ne nata. Muhibbat Sai taga dama take sa mata hannu, kuma Momi bata yi musu gyara ba.
Daga nan damuwa ta soma samun gurbi a Zuciyata. Gani da yalwar kud'i, ga Kayan binci a store, da a ka kawomin komai a kwai, amma wai kullum Sai naje wurin Momi karb'ar komai, kuma idan naje, Sai an min wulak'anci kafin a bani, musamman idan Khalifa da Muhibbat, suna wurin. Habaici, da zambo da tsaki, nafi shansu ma.
Gaba d'aya Momi ta canza min. K'iyayya muraran ta fito min da ita. Ko kirana tayi, ban ji ba, ko na kuskure wani a bu, to zagine. Banza ,shashasha, sauna, d'iyar matsiyata, wannan sunaye nane,da Momi ta rad'amin daga baya. Sam bata Kiran Sunana ma. Kullum a mai laifi nake,da nayi da banyi ba, Sai an k'irk'irar min.
Khalifa da Muhibbat sun fi takuramin. Bani da 'yancin fitowa tsakar gida Sai habaici, harara da tsaki. Amma Khalifa idan shi kad'ai ne, kulani ne kawai bayayi, sai harara da tsaki, sai dai idan Muhibbat tana kusa, ya samu 'yar uwa Sai suyi min taron gayya. Khairat idan tana kusa, a fuska zanga ta nuna damuwa sosai a kan a binda suke min.
To sai dai bata da yarda zata yi da su, sun girmeta. A Kwai Sanda tayi magana a kan bai dace ba a binda suke, suka hayayyak'o mata. Khalifa ma saura k'iris ya kai mata duka Muhibbat ta Kare.
Yace mata a gabana.
"Wallahi, kika sake yi mana shishshigi jikinki Sai ya fad'a Miki.
Kuma Sai na fad'awa Momi, zagon k'asa kike mana."
Tun daga lokacin, Sai take jan jiki, da taga sun soma yi min iya shege.
Sunan da suke kirana da shi, wai 'Yar jiran k'ofa. A bin nufi, ni Salima nake yiwa gadon wuri, kafin tazo. Wato bani da wani amfani face kula da muhalli suke nufi. Jin sunan ya zamemin jiki, domin suma shi suka rad'amin ko kirana za'suyi, bayan na Momi da nake ji da shi kuma.
Duk da naga gabar suke dani ta sosai, ni har gaishesu nake, idan basu kulani ba, amma babu sauk'i wai ciwon Arne. Ko sallama nayi musu basa amsawa ma.
Rannan Khalifa ya biyo Muhibbat a guje suna wasan banza, ni kuma zan wuce rik'e da fulas da kofunan tea biyu na glass, na fito daga kichean zanje na wanke su, Muhibbat da gayya ta bangajeni da k'arfi na kife, fulas ya fashe da kofuna, ni kuma bakina ya d'an fashe na k'ume da garu, kafin na kife amma Muhibbat ko ta d'aga kai ta dubeni ballantana tace sannu.
A gaban Momi, aka yi, domin ta lek'o ta Sama tana yiwa Khalifa magana, amma bata yi magana ba, kuma ko sannu. Hak'urin dai da nayi ban tanka
saboda naga kullum k'ara d'aukar zafi a ke yi dani. Ta yiyu, so a ke na tanka a yi b'atacciya. Domin ko washe gari da naje gaishe da Momi, bayan ta amsa da k'yar, na mik'e Sai Muhibbat da take kusa da ita taja tsaki tace. "Aikin banza, isar ba'a isa ba. Mace Sai nacin jarraba, ba'a sonki, amma kin manne."
Ban d'aga kai na dubeta ba, na fito. Momi naji.
Sati na biyu Kenan da aure na da Ancle Fa'iz. Ji nayi komai yayi min zafi. Baki d'aya naji gwara nayi komawa ta makaranta, duk da hutun da na dauka da saura kwana biyar ya cika.
Babu wani a bu da yake d'ebemin kewa a gidan. Ga kuma damuwar wulak'ancin da a ke yimin. Ni kuma bazan iya fad'awa kowa ba nawa, ballantana Ancle Fa'iz da dangin sa ne kemin. Nasan bai Sani ba, tun da komai Sai bayanan a ke min, duk da ba wani sona yake ba, ballantana nace suna shakkar ya Sani ya d'au mataki, Sai dai kawai sun San shi mai zafi ne da baya d'aukar wargi ko wani iri, ko yaga anyi wani a bu da bai da ce ba, batare da ya taka zazzafan burki ba.
Sam hutun ma da na d'auka na aure ma nayi da na Sani, domin bai min rana ba, Sam. Sannan babbar damuwa ta kawu Sulaiman yak'i zuwa ballantana naji sanyi. Domin ganin sa da hirar sa mai kwantar min da hankali, kan mantar dani damuwa ta, da maraici na.
Ancle Fa'iz ya kasa bani lokaci, ko yaya da zan jarraba salo ma na soma jan hankalin sa gareni, ko da daga hira ma gajeriya a bin ya faskara. Kullum cikin uzuri yake, idan na nemi hakan. Banyi zaton zai yi tsaurin samuwa haka ba gareni.
Amma kuma duk Sanda zai fita, ya kan ce me nake so ya sayo min, nace babu komai.Abinda nake son ya gaza.Komai ya sayo d'aurina dabam. Kuma komai ya sayowa su Khairat sai ya sayo min. Wannan ya, tabbatar min rukuni guda ya a jiye mu.
Randa na hak'k'ak'e zan fad'a masa komawata makaranta, ranar ya shigo da robar madarar roba biyu a hannunsa, ya mik'omin d'aya. Daga tsaye bai zauna ba, Sai yace.
"Bari naje na nemi Ado coach d'in mu, naji ance yanzu yazo bana nan, ba domin shiba kwanciya zan yi na gaji".
Ban yi mamakin gajiyar da yake yawan cewa yayi ba, saboda nasan Boll ya buga, ko training. Amma uzurin sa na kullum da baya yankewa, shi yafi ban mamaki.
Har ya juya, Sai ya dawo yace min.
"Ki rink'a rufe k'ofarki da daddare Sumayya. Naga har na kwanta a bud'e take, me yasa?".
Nayi masa wani salon kallo nace. "Bacci ne, yake kwasheni ban Sani ba."
Yace"Yace "Saboda me?".
Nace.
"Saboda bani da a bokin hira"
Ya gyad'a kai."Kin raina a bokan hirar takine. Gaki da book's na gani, ga kayan kallo ai sun isheki."
Nasan jahiltar manufata yayi, yana sane. Nace cikin narai narai da ido.
"Wad'an nan ba'a bokan hira bane face d'ebe kewa. My Ancle kaifa kace na rink'a kallonka kamar Ancle Sulaiman, amma Sam baka bani lokaci irin nasa. Baka hira dani irin sa. Anya za'ka maye gurbinsa?
Kullum Sai kace kana da uzuri. Na Shiga d'an Kukan shagwab'a kamar na gaske. Ni Wallahi bazan iya wannan rayuwar ba. Kullum ni kad'ai kamar mayya.Karabani da Ancle d'in dake yi min hira yana sani dariya da wasan nishad'i, kai kuma kak'i hira dani. Ni gida zan tafi yau ma".
Yarda nayi zaton zai d'an lallasheni ko yaya, ai sai ya bud'emin wuta.
"Maza maza tashi, ki tafi, karki bari k'uda ma ya rigaki. Ni zaki fad'awa wai damuwar sulaiman gareki? to duk Soyayyar da yake miki ai bazai iya aurenki ba, Kenan no reason da zaki rink'ayin wani prouding a kan'sa har da wata tutiya.
Kuma tun da haka ne me yasa baki zauna can ba, yayi ta sangartaki yana shagwab'aki da soyayya, karki auri kowa, tun da, Soyayyarsa da kulawarsa ita kad'ai ke gamsar dake."
Na yarda Ancle Fa'iz ya iya yanka maganganun ramuwa na cusa haushi, idan aka yi masa kan kara shi kuma na itace yake yi.
Raina kam ya b'aci da jin furutan'sa. Kenan babu inda zanji San yi a gidan. Da sauri na mik'e na Shiga d'aki na janyo gyale na da takalmi da jaka. Na fito. bada niyyar fita na fito ba, jarrabawa zan yi naga zai barnin na tafi, kuma idan ya barnin ficewar zanyi, domin zuciyata wani irin suya kawai takeyi.
Yana nan zaune in da na barshi. Ya bini da kallo, Yayin da na yafa gyalen, nasa takalmi, nayi kamar banganshi ba, nazo zan fita. Wata tsawa ya dakamin har Sai da jikina ya d'au rawa. Bana ko kokwanto su momi sunji, kuma nasan ransu zai yi fari tas.
Ya nunani da yatsa.
"Wallahi, kika tsallake tudun k'ofar nan kika fice Sai kin raina kanki." Nayi tsuru tsuru dani, kamar wacce ta yiwa sarki k'arya. Sai kuma na dawo turus na zube kan kujera na Shiga rera kuka na rufe fuskata da gyale Ina ta sheshsheka, a zahiri rantsewa za'ayi na gaskiya ne, amma a bad'ini na k'arya ne.
Ina k'yallaro shi, dai jijjiga kai yake, yana Jan kwafa da ina Kukan, tabbas naga 'Yar damuwa a tare da shi, naji yace.
"Haka siddan Ina zaman zamana na jawa kaina d'aukakkiya.
Jin furucinsa, Sai na k'ara sautin Kukan sosai. Ya dubeni yaja tsaki, tsam Sai naga ya mik'e yace.
"Kyayi ke kad'ai ."
Yasa kai ya fice. Yana fita na tashi na Shiga d'aki nasa kayan bacci. Kyakykyawar riga ce silk mai k'aramin hannu doguwa, nasa da hular bacci mai kyau. Na kishingid'a bada niyyar bacci ba tukun. Damuwar da naga Ancle ya d'an Shiga sanadin Kukan da nake yi da yake zaton gaskene ta farantamin. Da wannan na soma fahimtar wani sirri nasa da zan iya cin nasara a kan sa wani lokacin. Sam bayason a na yi masa kuka musamman na wata damuwa haka na fuskanta.
Ban sa rai da zai sake waiwayata ba a daren, Sai jin sallamarsa nayi a falo yana Kiran Sunana.
"Sumayya! Sumayya!!.
Naki amsawa ku ma nak'i fitowa, domin so nake ya shigo d'akin.
Kuka ma naci gaba dayi kamar dama can aikin kukan nake yi.
Babu shiri ya fad'o d'akin. Da alamu shirin baccin yayi Shima. Riga ce ta bacci yasa da dogon wando pure cotton mai taushi, irin kayan. Sunyi masa kyau ainun. gaskiya Sai da ya tsaya a kaina na sakanni yana kallona Kawai, Sannan ya tsuguna a gabana, murya k'asa k'asa yace.
"Wai Sumayya menene damuwarki? haka kawai kina neman ki d'agamin hankali. Me kike so ne?".
Cikin shagwab'abb'iyar murya nace. "Bakaine kace bazan tafi gida ba."
Ya kuwa sake k'uluwa yace.
"Bazakije gidan ba na hana,kuma ko me za'kiyi. Ke ko kunyama ba kyaji k'atuwar budurwa kamarki ki rink'a acting irin na yara, k'anana, har kina kuka saboda sangarta ko? Ko da yake goyon kakace dole kiyi. Ga Sulaiman kuma ya sangartaki. To Any way ni bazan d'auki sakarci ba wallahi, tun wuri ki Shiga taitayinki."
Nayi dib! Ko uhum ban sake cewa ba, face mitsitstsike idanu.
Shiru ya ratsa wurin na mintoci, Sai Iskar sama dake motsi tana wulwulawa tana bada iska madaidaiciya mai dad'I, sakamakon d'an yanayin zafi da ya shigo a tsukin.
Ko tausayina yaji, Sai kuma ya tausasa murya Maimakon kausasawa da fari.
"Sumayya, ni banga a binda zai sa ki rink'a damun kanki ba. Da a ce tun farko na munafunceki, to shine za'ki damu kanki, idan kika ga wani sauyi. Amma haka siddan ki rink'ayimin tuhumar da gangan? Me na yi miki? Kullum fa Sai na tambayi me kike so, menene damuwarki, amma duk ban fita ba. Kinsan manufar auren mu, kin a mince, to me yasa zaki rink'ayi min bore bayan anyi?.
Naga shiru ba mafita bace, gwara na fad'amasa burina ko zanyi sa'a ya a min ce daga nan k'ofar farko ta bud'e.
"Ancle nifa buk'atata ka rink'a yagar min lokaci, muna hira ko yaya, na samu mai debemin kewa. Su khairat da kake cewa muyi hira basu da lokaci kullum suna kan hanyar makaranta, Boko da islamiyya. Dare kuma Kowacce d'akinta take Shiga, saurin bacci ne dasu. Momi kuma kunyarta nake ji, bana iya sakin jiki muyi hira sosai."
Nayi dace yace. "To, zan jarraba yarda kike so, amma fa ni ba ko yaushe nake son hira ba, karki zamemin BBC, uwar watso kanun labarai".
Dariya furucinsa ya bani, har nayi ta fito fili a hankali, saboda yanayin da ya furta. Shima sai naga yayi 'yar dariyar.
"Ke dai 'yar tawaye ce rigimammiya, mai fuska biyu kuma. Kin rikita mutane da kuka, kuma kin dawo kina yimin dariya ko? Warki ne ni dai dai k'ugun kowa."
Yanayin da muke ciki, da yanayin lokacin, ya sanyayamin zuciya sosai. Naso mukasance daren ranar da faranta ran juna irin na ma'aurata, koda iya hira, amma Ina!.Mikewa Ancle yayi. Nikuma na tuno da a binda nake son ce masa.
Nace"Am, Ancle"
Ya juyo a hankali. "Ina jinki Sumayya."
Nace. "Gobe
nakeson komawa makaranta. Yace"Sai yanzu za'ki fad'amin?"
Nace"To, na bari, Sai Jibi? ".
Yace. "No, kije goben, tunda kin niyyaci hakan.
Daga nan yayi min Sai da safe ya fita. Inajinsa ya b'amemin k'ofar sosai.
Na kuwa kasa bacci. Da nayi juyi, Sai na hango Ancle Sanda ya tsuguna gabana, ya zubamin kyawawan Idanuwan nan nasa masu hasken blue masu kashe gab'b'ai, yanamin surutai a hankali. Gaba d'aya kasa dai daita nutsuwata nayi a lokacin. Komai nasa mai ruruta wutar k'auna ce,
ga ma'abocin kallonsa. Nasan shi a lokacin babu komai a ransa, burinsa ya shawo kaina Kawai.
Wasa farin girki
Muje zuwa
Zainab ilyas mazawaje