Page 17
by @zainab221
NI DA GIDANA
Zainab ilyas mazawaje
Best brilliant intelligent writer...✍️
Page 17
Ranar litinin sai yamma Lis sannan
na isa gida. Sai naji na sarara a raina a kanda, na samu nutsuwa.
Sanda na dawo daga makaranta, Kichean nake shiga na dafa a binda ya samu, nayi shigewata d'aki, idan ba alwala ba bana sake fitowa. Amma duk a binda na dafa, ina kaiwa Momi. Bata tsinkamin, amma sai na a jiye gefe. Bansan yaya take da shi ba. A lokacin babbar damuwata na samu kulawa koyaya daga Mijina, kar abin yayi min yawa wai shege da hauka.
Cikin nasara na soma samun kuwa.
Domin Ancle yana d'an zama a falo na fiye da da, muyi 'yar hira kad'an, da sai dai mu zauna kawai muyi jugum jugum, ko shi naga yana ta chat a waya, kuma nasan da Salima ne, sai yayi kamar ma ya manta da ni a wurin. Da abin yana da muna daga baya sai na dai na sawa kaina damuwar, domin naga ba mafita bace.
Ancle baya jimawa dai sosai ma a falona idan ba wani kallo na kunna da yake so ba. Kuma bai fiya yi min hira ba, Sai dai ni. idan kuma na cika jan shi da hira, Sai yayi min shiru, nayi ta zuba kamar kun nan niyar rediyo baya tagamin. Idan hirar ma tayi tsayi, Sai kawai naga ya tashi ya fice.
Hakan na nufin na dameshi da Surutu kenan.
Da na fuskanceshi, sai nake binsa da salon halinsa. Da naga yayi shiru ya daina tayani, ko bani amsa, Sai nima nayi shiru. A hankali a hankali na soma sanin Ancle Fa'iz. Me yake so, menene bayaso. Kuma hakuri da kwantar da kai yasa na soma fahimtar.
Ancle yana da wani irin hali da raayoyi da ya bam bamta da na wasu mazan, baison turare mai tashi, sai mai sanyi can kasa, baison turaren wuta na daki sam, ko za asa sai dan kadan sosai da baaji sai sama sama, haka ma air freshner nunawa yayi baiso ta yi yawa sai kadan.
Sannan baya son k'unshin zamani da ake yayi, yanzun. Bansani ba, Sai bayan nasa an zo har gida an rangad'amin.hannu da k'afa, marun da bak'i na fulawoyi, yayi kyau ya zanu. Amma yana arba dashi yace.
"Wannan ai b'ata jiki ne,menene a bin Sha'awa game da wannan shirmen."
Nace"Kwalliya cefa ta mata Ancle."
Yace"b'ata kwalliya dai, Ina a bin burgewa a ciki?".
To kwalliyar fuska ma ta mata, baya so Ancle Fa'iz. Ranar wata lahadi banje makaranta ba, bayan kwalliya ta situru nasha make up.powder eye liner, da eye shadow ,lipstic da white lips da jagira tsararriya, da tasha shape. Wallahi kuma nayi kyau har ga Allah. Amma Ancle yana shigowa da ya kalli fuskata ai sai naga ya kwashe da dariya. Dariya sosai da ban tab'a ganin yayi ba. Zatona daga can wurin su Momi ya taho da a bar'sa, ai sai na ta yashi, ina yi ina tambayar ba'asi.
Abin gwanin bandariya wai yaro ya tsinci hak'ori.
Yace"Kema dariyar kikewa yi wa kan ki?".
Nayi harr da ido, Nace.
"Kamar yayafa?'".
Ya sake duban fuskata, ya tintsire da dariya.
"Kinga fuskarki kuwa? Sai kace wata sabuwar aljana?".
Tabbas furucin'sa ya sosa min rai, amma na daure zuciya ban nuna ba, ko furtawa ba.
Cikin salo ma na kamar shagwab'a nace.
"Kai Ancle, me fuskata tayi?".
Yace"Kin cikata da shafe shafe da yawa. Ga na fuska, gana ido gana leb'e gana gira, gana zagayen ido. Is too much, Sumayya. Don Allah karki sake yi."
Tun daga lokacin kuwa ban sake yi ba. Iya kacina powder kad'an, kwalli. Sai white lips idan tayi hali. Domin ragowar basa burgeshi, baya so. A bubuwa da yawa basa burge Ancle Fa'iz.
Lokacin da ka Tak'ark'are Sai kayi masa bajinta, to lokacin zai kushe. Shi yasa daga baya na sanyawa Zuciyata salama, bana fushi sam idan nayi abu ya kushe bana fushi, sai dai nayi k'ok'arin gyarawa irin yadda ya nuna yana so, ko bana so kuwa.
A cikin 'yar hira dana ke Samun albarkacin ta a tsukin, nake bincikar sa irin ra'ayoyin sa da a binda yake so da wanda baya so. Ya kan fad'a min, wani zubin. Wani lokacin kuma ya bijire yace wai menene dalilin da nake damunsa da tambayoyi da bincike?.
Nan saduda na rabu jdashi, na tara gaba kuma. Har lokacin babu ka lamun somi somin Sona dana fuskanta daga gareshi.
Har lokacin girkin Momi kawai yake cI. Cikin hikima nake yi masa magiya nace ya rink'a ragomin, nima ina Sha'awar girkin Momi. To wani zubin ma nan falona yakan zo da shi yaci, saboda naci na. Nima daga nan Sai na turo masa nawa da magiya nace yasa albarka. To dai nawan ma kushewa yake a gabana. Ya kance gishiri ya zarta. Ko kuma magi. Ya dai ficewa na cika attaruhu. To Sai na rage sa attaruhu, na rage magin ma da gishiri, nayi iya iya wata wurin kyautata komai. To amma me.? ya daina k'orafin, amma ba yabo.
Na lura girkin Momi kawai ya fiso. Kuma naci, na yaba Kam. Yabon gwani tilas. Momi ta iya girki sosai kuwa. nafi zaton fannin girki ma ta karanta.
Na dai zamewa Ancle Faiz dan kadafi, na manne na nace, cikin shiga al'a muransa, duk furucin da zai jefamin mara dadi ba na yin fushi ko zuciya, zuciyar tuni ta horu da haka har ta bushe.
Ni keyin zaraf cikin al'amuran sa, kafin ya buk'aci a bu nayi. Sam. baya so na yi masa d'awainiyar komai. Rufe dakin sa yake yi da mukulli idan zai fita. Idan yana ciki, kuma bayaso nace zan Shiga ballantana nayi masa gyara ko Shara kamar yarda na k'wallafa rai, Sai ya hanani fir!.
Baisani ba rannan na zari d'aya daga cikin 'ya'yan mukullin sa da yake jikin key holder na b'oye.
Da yamma Lis, na taso daga makaranta da wuri saboda lacture ta ranar gajeriya ce na bud'e d'akin nasa. Gaban su Muhibbat da Khairat suna hira, suka bini da kallo. Gyara nayi masa sosai. Dakin a share yake tas, amma a kwai 'yar k'ura jikin sib da wardrobe. Na k'alk'ale komai . Na cire zanin gadon nasa masa sabo gau, nawa duk da nasan ma baiyi wani datti ba, saboda ba laifi Ancle yana da tsafta. Haka ma labule na cire nasa masa nawa sabbi masu kyau, domin biyu aka yi min. Nasan ma mai kyau ne, amma nawa sabone ful, domin kala biyu ne dani masu tsada. Zanin gado kuma kala uku. Na tsara masa Kayan cikin kwabar sa, na jera, saboda yana yawan hautsinawa ya barsu garin binciken kaya. Nayi masa gyaran da bazai rinka hautsina komai ba, komai dalla dalla. Na ware under's d'insa da singlet da gajerun wanduna, har da Kayan boll da babu wanki na kai d'akina na a jiye da niyyar gobe na wanke.
Na fesa masa air freshner Sama Sama, kar yayi min k'orafin turare ya hau masa kai. Shi yasa ma ban k'ara da turaren wuta ba. Dakin nasa yayi kyau sosai kamar ba shi ba. Da yake falon ma babu tarkace, kujera guda ce sai TV dake jikin bango da risiba.
Wata laptop d'in Ancle na gani madaidaiciya ta d'au hankalina na bud'e.
Tabbas da nasan me zan yi tozali da shi, da ban bud'e ba. Hoton Salima ne da Ancle Fa'iz ya cika fuskar laptop d'in. Suna jikin juna, Salima ta kwanto a jikinsa ya tallafota da hannayensa ya mannata gam a jikinsa. Tamkar mata da Miji. Abin ya d'aure min kai, dama Ancle Fa'iz zai iya haka? Ko kuwa soyayyarce duk ta zautar da shi, ya biyewa hud'ubar shaid'an?. Sai da na daure zuciya na sake kallon hoton. Su duka murmushi suke yi a hoton. Sai da nayi tasbihi ga mahaliccin surorin'su. Ita da shi d'in babu kanwar lasa wurin kyau. Sun dace da juna Kam in dai wurin duba ne.idan kuwa suka tashi haihuwa,wad'anne irin kyawawan yara za'su haifa. Za'a Sha kallo.
Ko shakka Ancle Fa'iz yana son Salima sosai. Kusan duk wani abu nasa mai muhimmanci hotonta ne a kai. Wayoyin sa biyu ne banason gani ma, Saboda duk hoton
Salima ne. Da dai da key holder dinsa na d'aki hoton Salima ne, k'arami a ciki anyi masa siffar zuciya. Lallai Ina da gagarimin aiki a gabana, tun da ko makami na yak'i daya ban mallakaba, na satar zuciyar mijin da muka kusa tarayya da Salima.
Ko ince ni zaman wucin gadi nake yi a wurin Ancle, waadi nake jira.
Tayi min fintin kau Salima na k'wace Miji tuni. Tun da familyn sa ma duk mayak'anta ne na fagen daga. Gashi kullum kuma k'ara zarmewa nake cikin Soyayyar Ancle Fa'iz. Shi yasa kullum kishin sa ma k'aruwa yake a raina, duk da bai a jiyeni a rukunin mata ba ma. Ba domin na tabbatar Sai mun d'ebi 'yan kallo da shi ba, da Sai na rotsa laptop d'in nan. To laifi kan laifi ma zanyi. Na shigo masa muhalli bai Sani ba, kuma nayi masa tsadadden ta'adi. Nan ma cewa zai yi lek'en a Siri ya kaini. Wannan hoton, ko ba'ace ba, nasan yana ji dashi.
Da na fito daga d'akin Ina rufe komai, Momi da Muhibbat na gani daga saman bene sun kafa min idanu, nayi kamar bangan su ba. Nasan Muhibbat ta kai mata tsurku.
Fuskar'sa d'auke da alamomin Mamaki ya shigomin. Hannun sa ya dafe kujera yana daga tsaye ya ce.
"Wa ki ka ga ya shigar min d'akina?"
Kamar da gaske na dake
"Anya an Shiga d'akinka kuwa yau Ancle? Wani a bune ya faru?".
Yaja dogon numfashi.
"Tabbas an Shiga an jima, domin komai na d'akin ya canza. An canzamin tsarin komai na wurin. Wanene mai wannan aiki, ko nace wacece?".
Na kanne cikin b'oye dariyar dake son k'wacemin.
"Ta'adi a kayi maka Ancle?".
Yace. "Gyara a kayi, tun da wurin ya k'ara haskaka yayi kyau".
Naji dad'i sosai na yabon da yayi. Ancle Fa'iz kafin ya yaba abu a ya'ra.
Saboda Jan zare, na zolayeshi da cewa.
"Ancle, Ina Jifa aljanun cikin d'akinka ke sonka, suka yi maka gyara."
Yayi min k'uri da idanu, har Sai da naji wani abu mai hargitsa yanayi kafin ya nisa tukun yace.
"In dai haka ne, to kece shugabar aljanun, ke kika jagorance su."
Dariya nasa ta burgewa. Wato ya fahimci ni nayi masa dai gyaran.
"Ina kika samu mukullin d'akina? Yace.
Nace.
"Jikin mukullayenka na cira."
Nayi zaton zai min fad'a, amma Sai naji yayi shiru.Na fahimci yaji dad'in gyaran da nayi masa a fuska. Duk da kullum nunawa yake yi baya so nayi.
Tamkar kaska haka na Mak'alewa Ancle Fa'iz, saboda ya rage kyarata da yawan yi min fada,a kan da. Domin takai ko bai shigo d'akina ba, ni zan bishi nasa d'akin, bana kuma shayi, ko fargabar mutanen gidan. Tuni na soma yin sabo da shan zagi, harara, habaici da zund'e. Shi yasa idan ma anyi min, bana d'aukar'su a bak'on al'amari da zai yi ta damuna. Wannan yasa zuciya ta ma ta kangare ta bushe, domin idanuna sun rufe da Soyayyar Ancle da bin hanyoyin da zan janyo ra'ayin'sa gareni. Duk da Shima Ancle Fa'iz d'in ina shan wuyar sarrafashi wurin shishshige masan da nake yi. Yakan nunamin ma k'arara cewa na ta kuramasa, wani lokacin, amma Sai na shanye.
Bayan Ancle Fa'iz ya sauko daga saman Momi, ya sameni zaune a d'akin'sa Ina dakon'sa.
Ya samu wuri ya zauna, ya fara da cire hular kan'sa. Nayi zaraf na d'auka, nasa a kaina na dubeshi nace.
"Ancle tayi min kyau?".
Ya jefeni da kallo d'aya na gefen ido yace.
"Ke namiji ce da hula za'ta yi miki kyau?".
Sai na cire daga kaina nasa masa a kan'sa. Ya cire ya ajiye. Na sake d'auka na rik'e nace.
"Wallahi hula ba k'aramin kyau take yi Maka ba, my Ancle."
Yace. "Ko?".
Na sake saka masa a kan'sa, ya kuwa cire da sauri yace.
"Wai yaya haka ne, ina cirewa kina samin?".
Nace. "To, ni nafi son ganin ka da hular, kafi kyau Allah".
Wannan Karon wani murmushi naga yayi Maimakon hasala da nafi zato, yace.
"Sumayya, kina fa takuramin, kina fa sani surutun da ban shirya ba, Allah kina ma cin darajar maraicinki ne nake sassauta miki, domin ina tausayinki wani lokacin, amma a kiyayi dai zuwa rafi kullum, wataran sai an fasa tulu".
"Nayi murmushi. "In dai bukatar da a kaje na debo ruwan ya samu to ai ba damuwa, Ancle kasan ranar biyan bukata rai ma ba a bakin komai yake ba".
Ya dan daga min bakar girar sa gami da dan fito da ido. "I see".
Iya a binda yace kenan, da alamu ya dan shiga duhu da furucina, ko kuma ya fahimta ya maze, saboda na fahimci yana da saurin karantar mutum sosai, amma sai ya waske yayi kamar baisan me kake ciki ba, ni kuwa da gayya na furta.
Kwana biyu na sake samun Ancle a daki ya na bubbude sababbin wasu unders da ya sayo daga leda ya na dubawa, bai dago kai ba gareni duk da ya amsa sallama ta. Na zauna gefen sa kan kafet din dakin, shi kuma yana gefen gado.
"Sannu da aiki my Ancle".
Nace ina murmushi.
Yace " Yauwa sannunki".
Na mika hannu zan amshi singilet din dake hannun sa, ya janye.
"Ancle gani fa zanyi".
Yace "Ahaka ba kina gani ba, look karfa kizo ki matsamin, bana son takura".
Na sake yin murmushi.
"Ni ba takura maka zanyi ba Ancle, kawo to na ninnin ke nasa maka a ward robe".
" Barshi nayi".
Nace "Kai my Ancle bai kyau tu ba ina zaune kayi aiki ba gaskiya kawo please".
Yace " Hmmm!! " Kawai.
Kamar bazai bani ba sai ya miko min kayan duka ya mike yana mai fadin.
Yarinyar nan duk kin bi, kin hanani sakat? nasan idan ban baki ba baza ki barni ba, bansan wa kika gada ba wurin kafiya a dangi".
Nayi 'yar dariya nace.
"A dai laluba za a samu, domin ruwa baya tsami banza"
"Bulala kawai Allah zan a jiye kusa dani. Surutun da ki
ke Sani banyi niyya ba, yayi yawa fa".
Nace "Barewa fa a dawa ance da d'anta take wasa Ancle Fa'iz. Kaman ta bani da kowa Sai kai? Kaine uwa, kaine uba, kaine Kawu, kaine Yayana kaine....."
Ya da katar dani da hannu.
"Ya isa !. Ke kin fiye Surutu, Sai kace aku kuturu."
In da sabo na saba da irin wad'an nan lafazai nasa. Kuma a hakan muke ci gaba da hirar bana fushi kamar kullum.
Ranar dai na ganshi cikin walwala dai, Bansan dalilin ba. Ya nutsu ya soma cemin.
"Ki ta yani murna, na samu shigowar wasu kud'ad'e masu yawa na wasu wasanni da muka yi a state uku, Sai jiya aka turomin nawa cikin a count. Ban tab'a Samun kud'i masu yawa a wasa ba irin wannan. Nayi kasafin su ma. Na wari wanda zan ba Momi da Baba, na wari Wanda zan Sai mota, da wanda zan sake jefawa a harkar ginina da yake taci min kudi, da na samu da ya handame".
Naji dad'i sosai da na samu matsayin da ya fad'amin sirrin ci gaban'sa. Na kuma yi ta surfamasa godiya da addu'a na kyautar kud'in da zai ba iyayen'sa, Sai a zaci nawa iyayen zai bawa.
"Wallahi ka kyauta Ancle Fa'iz, musamman alkhairi na kyautatawa ga iyaye yafi kowanne. Allah ya saka da alkhairi, ya k'ara bud'i"
Ya gyara zama daga kishin gid'ar da yayi gefena da nake ninke masa kaya.
"Kema za'a baki Lada na ganin ido, kamar 'yar dubu goma, tayi?".
Nayi masa murmushi
"Wanda za'a ba kyauta har yana da zab'i? aiko naira goma ka bani godiya zan yi tayi, ballantana har dubu goma Ancle?".
Ya kanne ido guda cikin dubana yace.
"Na lura, kina da Yakanah! Saboda haka bari a k'ara miki dubu goma su zama twenty thausand. Godiya nayi ta surfawa da addu'a."
Yace. "Ya isa haka Sumayya, Sai kace kyautar rai na baki?".
"Ancle wai kuwa wacece Anti Husna da naji su Khairat suna yawan fad'e?".
Yace"k'Anwar Momi ce, ita ce autar su.
"To, Ancle Jamil fa?".
Yace. "Yayan Momi ne"
Na sake cewa "Maman fahad fa?"
Cikin nuna 'yar k'osawa yace.
"K'anwar Babar Momi ce, Kenan uwa take a wurin Momi. Na gaji Sumayya, tashi Kije ki kwanta, bacci zanyi karfe goma na dare ta gota, ina son yin sammako".
Nace"Abin har da kora my Ancle?".
Yace"Wanzami dama ba yason jarfa, ni me yasa jiya kika koroni daga d'akinki?".
Cikin 'yar dariya nace. "Au, daga kayi bacci na tasheka nace kaje ka Mik'e a gado?".
Yayi doguwar hamma kafin yace. "Wannan a bu duk mai sauki ne, idan baki son tafiya, nan d'akin yayi miki, Sai na kawo miki guzurin filo, ba Shike nan ba?"
Na kuwa ce "Kawo min".
Sai kuwa naga ya tashi, ya na kokarin jawo filon, nan nasan da gaske yake. Kafin ya dauko kuwa na mike da sauri na fice, in da nace masa
" Sai da safe Ancle".
A tsukin cikin wata hudu da aure na da Ancle Fa'iz, a bubuwa sun soma zuwa min yarda nake so. A lokacin ne kuma na sake shiga tsangwama da takura da fitintunu a cikin gidan, saboda sun fuskanci muna d'an d'asawa da Mijina, yana nunamin kulawa fiye da da.
Kwana ne kawai Ancle bayayi a d'akina, amma har a binci tare muke ci, idan ya shigo d'akina. Kuma ni na gadar masa da hakan, domin ko shi kad'ai ya soma ci, Sai na zo na sashi a gaba,nima na soma ci, muci gaba da ci tare. Ko a bincin Momi ne kuwa, domin naci na yasa kullum Sai yaci nawa. Shi yasa baya cika cikin'sa ma da a bincin Momi, saboda yasan nawa d'an k'a'ida yana jiran'sa.
Wulak'anci da cin mutunci muraran a ka Shiga yi min a gidan, da kare ma ba zai ci ba.
Duk wani laifi idan a kayi a gidan, Momi ni take cewa. Babban a bin takaici har Sata a ka kallafamin. A zatona babu wani abu da ake sacewa, domin a d'oramin laifin sata ne kawai. sai Momi yau tace an sace mata a bu kaza, gobe ma haka, kuma tace nice ware, nice lallai zan d'auka, domin cikin 'ya'yan ta babu b'arawo. Momi ta kirani cikin 'ya,'yan ta, ban da Ancle, taci min mutunci a matsayin ni b'arauniya nayi mata Sata. Khalifa ma da Muhibbat su zageni son ran'su. Khairat ce Kawai bata tofawa, zanga ta b'ata rai sosai. Na lura bayan kirkinta, hak'uri ne da ita ainun.
Muhibbat ta matsamin lamba sosai a tsukin. Idan nayi wanki, nayi shanya ta zubar a k'as. Da yake Ina wanke ma na Ancle marasa nauyi, amma bata zubar da na yayan'ta. Kunji son zuciya. Ni ke sharar gidan, amma randa Muhibbat ta so tsiya, Sai ta fizge tsintsiyar daga hannu na, ta share ko'Ina. Sharar idan ta kwashe Sai ta watso falona. Na rink'a dauriya, Saboda Kawai bana so K'orafi ya fara b'ulla daga bakina wurin Ancle ko wani nawa. Sannan Zuciyata tayi nisa a son Ancle Fa'iz, banason a binda zai haifar da sa'in sa tsakanina da kowa nasa . Zaman aure na mutu ka raba na k'uduri yi da shi, iya yina.
Komai nawa na Kayan kichean, ni da Muhibbat muke amfana, musamman idan tayi bak'in k'awayen'ta, komai na kichean d'ina za'tayi facaka da shi. Filet filet da kofuna na k'arau ta yi amfani da su, ta zubemin a waje babu wankewa, ta kuma fasa na fasawa da gayya, duk dai Sai an cuzgunamin nayi magana, an zagi ubana. To, ni kuma Sai nayi lub, kamar banji ciwo ba. Kayan kichean d'ina duk ta farfashe k'arau d'in, ban dai tanka ba, na k'yale. Sun Sani a kwana sosai Muhibbat da Khalifa. Wulak'anci salo salo, zagi da Habaici. Hannune kawai basa sawa su dakeni. Sau d'aya nayi wa muhibbat magana da ta fasamun fulas d'in shayi, da shi kad'ai ya ragemin, ta kuma kwashemin drink's na Friedge da nake tanada saboda Ancle.da tayi bak'i.
A binda ya fito daga bakin'ta shine.
"Ai naga, ba' daga gidan uba, akazo da drink's ba, yayan mu ya saya, aikin banza shishshigi babu kwarjini, diyar matsiyata ke har wani kaya ne ma dake na kichean da zakiyi fariya a kai, kuma komai na ci ko sha ai yayan mu ke sayowa ba daga gidan tsoho a ka kawo ba".
Raina ya sosu, tamkar na fallamata mari, amma na daure zuciya, saboda ubana da baya raye da ta tsomo a ciki".
Tabbas yayanta na sayo komai, amma wanda duk ta kwashe ni na Saya. Kawu Sulaiman yana aiko min da kud'i a kai a kai, kuma yawanci, wurin yiwa Yayan su d'awainiyar sa kai na, suke tafiya. Sauk'inta bana yini a gidan,saboda makaranta, ba domin haka ba, a bin yawa zai min, wai shege da hauka.
Ranar a sabar bani da lacture, banje school ba. A kayi dace nayi bak'i kuma.'yan uwan ummata da suke uba d'aya, baba Maryam, da baba Hasana. Tare na had'a mana a binci mukaci, Sai yaran su, dana ware musu a faranti guda.
Ancle Fa'iz ne ya shigo da a zahar da ba sabon'sa ba. Ina hangen sa ta taga, saman Momi ya haye rik'e da poly bag k'arama, irin ta take a way.
Muna hira da bak'ina ya shigo falon da sallama, baisan da bak'in ba, Sai da ya shigo. Bayan sun gaisa, na gabatar masa da su suka gaisa a mutunce kuwa. Sai yace nazo yana son ganina dama tsintsiya ce a hannuna, zan share a bincin da yaran suka watsar, sai baba Maryam tace naje Kiran mijina ta share. Nabi bayan Ancle
Yana tsaye a d'akin nasa ya rungume hannu a k'irji, ya jingina da bango, kamar wani a bu yana damunsa na fuskanta.
Nace "Ancle yau ka dawo da wuri Amma "
Fuskar'sa babu walwala yace "Eh!" Yayi shiru. Sai daga baya Yaci gaba.
"Momi ta dawo dani,saboda waya tayi min wai na taho mata da take a way yunwa take ji. Nace mata yanzu Momi a binci Sai ya gagareki a gidan bayan da a kwai komai? Saboda bana son dawowa, Ina kan wani a bu mai muhimmanci, amma Sai da na barshi, saboda tace min su Khairat dama ke dafa binci su bata, kuma duk sun tafi unguwa tun safe . Kuma gashi likita yace lallai Sai taci a binci sosai kafin tasha magungunan ta, na larurar rashin lafiyar da take ciki."
Nan na dubeshi nace.
"Dama Momi bata da lafiya?".
Ya dubeni galala. "Wace irin tambaya kike min? Waye baisan MomI bata da lafiya ba, kwana biyu? duk da tace kikan jima bakije kin gaisheta bama, amma ai za'kiga ta fad'a kwana biyu".
Wannan abu ya Sosa min rai, shi yasa kika ga na kasa juriyar a jiyewa zuwa wani lokaci. Domin da nace Momi tayi miki magana ki bata a binci, tun da kina gida, Sai tace bata buk'atar a bincin ki, tun da baki damu da ita ba. Tunda ta kwanta jiyya baki tab'a yi mata sannu da jiki ba, ba kya gaishe ta ma. Kuma da kina bata a binci, kika daina, Sai dai kiba almajiri. A binda ciwo a ce Momina ta rasa a binci a gidan nan Sai da na dawo, amma ga bak'inan su sunci, har sun zubar".
Tun da nazo gidan raina baitab'a b'aci ba irin ranar. Duk a binda suke yi min, ni banyi k'orafi ba Sai Sai su? Kuma gashi ya Shiga cikin su, ya yarda tun da yake tuhumata.
Na had'iyi yawu da k'yar .
"Nifa ban fahimci zargin nan da ake so a lik'amin ba. Sam ni bansan Momi bata da lafiya ba. Waya fad'amin? Kuma Ina gaisheta, ni banga alamun wani rashin lafiya ba. A binci Ina bata ta dai naci tace bataso, to yaya zan yi.
Na sake daukar zafi saboda na fuskanci Ancle yana bayan su, yarda ya daure fuska yana yimin wani kallo a sangarce.
Kuma a binci ma ai cewa a kayi nayi iya cikina, nifa a ka ware. Kuma ai ba'a bani umarnin ma bawa Momi a binci ba, iya kaina a kace na dinga dafawa, ina dalilin da zaa dawo a na zargina kuma. Ni fa nasa kaina nake bawa Momi a binci".
Take naga ya fusata ga rashin zato na.
"Har wani alfahari kike na wai ke kika sa kanki kika ga damar bawa Momi a binci? Sai da kika ga dama? to kiga kuma hagu. Kar ki sake bawa Momina a binci, umarni na baki Shima. Ki dafa iya cikin ki na sake fad'a. Ki Sani, ko zan iya hak'uri a kan wani a bu, banda a tab'amin uwa. ko wanene bai isa ba wallahi."
Take zuciya tazo min iya wuya. A fusace nace.
"Girkin ma ai ba dole bane. Domin iya cikina zan wahala? nama daina dafa komai, kome na samu ya fad'o bakina ya wadatar. Kuma Allah shine Sha'hidi a kan kome nene gaskiya. K'arya ta shekara k'arya. Gaskiya na makwafinta".
Ina fad'in haka na mik'e nayi ficewata.
Na fusatashi sosai na gani kan fuskar sa, amma Sai naga ya gaza cemin komai, face bina da kallon Mamaki, har na fice.Tun daga ranar na rufe kichean ruf, ko ruwan tea bana dafawa. Sam bana karyawa da safe, ko ina gida. Abinci Sai a bu mai ruwa ruwa,Sai ciye ciye Sama Sama. Amma banacin gaskiya a bincin kirki a cikina. Ga damuwa da na d'orawa zuciyata. Kuma na d'au fushi da Ancle Fa'iz ko falonsa bana zuwa. Da safe yana shigowa wurina Bayan sallar a suba. Bayan na gaisheshi, bana sake ko kallon sa ballantana na tsinka masa. Shima ganin babu fuska, Sai ya ajiyemin kud'in da yake bani, batare da sake kulani ba. To dai banga ya d'au fushi kamar ni ba, yarda na fuskanta. Komai ya sayo zai kawomin nawa d'aki ya a jiye. baya cewa komai, Sai ya fita.
Ni kaina banyi zaton Ina da zuciya ba, Sai da aka kaini bango. Dama wasu sunce, mai hak'uri bai iya fushi ba.
Ba iya Ancle Fa'iz ba na d'au fushi da shi ba, duk gidan ne. Ji nayi an kai ni gargarar da bazan kuma d'aukar raini da wulak'anci ba. Momi Kawai zan iya d'agawa k'afa, albarkacin Ancle Fa'iz da kuma darajar haihuwa, tun da ta haifeni. Amma ita kan'ta Momi taga canji a wurina. Kullum zan je na gaisheta, Amma fuskata babu walwala, da rawar jiki na biyayya da nake yi mata. Domin da kullum naje gaishe ta, Sai na tambayi ko da wani aiki da zan yi mata. Bayan fa Kusan aikin gidan gaba d'aya da na kallafawa kaina, kamar mai aikatau.
Momi ta ban Mamaki da tace wai bana zuwa gaishe ta, da bata a binci, da dubiyar rashin lafiyar da ban San da ita ba. Gaba d'aya zuciya ta ta karkata wurin yarda da cewa Momi yak'i take yiwa Salima bayan idonta.
Domin Khairat ce ta sameni rannan da babu kowa a gidan bayan sallar magariba, tazo d'akina tace min.
"Matar Yaya, wallahI ki k'ara rik'e mijinki da kyau, domin Kusan kullum Sai Salima ta yiwa Momi waya. Rannan hands free Momi ta manta tasa, naji Salima tana yiwa Momi magiya kamar zata yi kuka, Wai tana bala'in Son Yayan mu, shi yasa baza ta iya zama da kishiya ba, Wai Momi ta taimaka mata. Saboda Salimar ta cewa Yaya, ya sakeki tun da saboda ya sameta ya aureki, kuma tun da Momin ta ta sauko ma tace ko yaushe yazo a yi aure. Amma Sai Yaya yace mata babu ruwanta da zancen auren sa dake, tayi gefe da shi. Kawai tasa himma a kan tsara musu zaman farin ciki da Soyayyar da za'su shimfid'a, kafin isowar auren. Ita burin Salima fa Kawai Yaya ya sakeki kafin auren ta da shi. Shi kuma yak'i bata amsar yiyuwar hakan. Momi hak'uri ta bata dai, tace tabar komai a hannun'ta zatasan yarda za'ta b'ullowa komai, saboda yanzu binsa take yi a sannu, saboda har yau bai gama hucewa ba, da a binda maman'ta tayi masa. Kuma Khairat ta ce min, taji Momi tana fad'awa Ancle Fa'iz wai ya d'auki matakin plannig, wato tsarin iyali a auren ku, saboda batason ya haihu da ke kafin zuwan Salima. In so samu ne ma ya sallameki yanzu, tun da kwalliya ta biya kud'in sabulu. Amma Sai cewa Momi yayi. Momi nasan a binda nake yi nima name ya kamata nayi a lokacin kuma da ya dace, kusamin ido".
Momi bataja musu da shi ba, duk da bata fahimce shi sosai ba. Haka za'lika nima ban fahimta ba. Amma fatana kar burin su ya cika a kanki Anti Sumayya. Wallahi ni nafisonki da Anti Salima."
Wani irin k'aunar Khairat ya k'ara mamayeni. Rungumeta Kawai nayi, nace ."Khairat Ina k'aunarki, fiye da kowa a gidan nan. Allah ya ganar da su gaskiya, su san ni ba a bokiyar hamayya bace, face masoyiya ga Ancle, mai son sa da son ci gaban'sa, da su baki d'aya. Ta kuwa ce.
"Amin".
Murmushi nayi, da a ke gudun, na samu ciki na haihu da Ancle, to duk Ina tunanin su ya tafi? Ko jituwar da suka ga munayi da shi a tsukun, suna zaton komai yana tafiya na aure tsakanina da shi? da sun San komai nasan Momi bazata yi a sarar yawun bakin'ta ba.
Tun da Khairat ta fad'amin maganganun nan, suke tayi min yawo a rai. Tabbas k'wace goriba hannun kuturu bazai yi wuya ba. Za'su iya iya rabani da Ancle Fa'iz nan da nan, tun da ko tubalin ginin dasa sabo da k'auna da shak'uwar da nake fad'i tashin yi kullum, bai yi nisa ba, ballantana yayi k'warin da Sai anyi gwagwagwa da shi, kafin a rushe. Shi yasa wata zuciyar ke min shelar cewa, Kawai na shafawa kaina lafiya da Ancle, na saddak'ar, nasa rai da isowar cikar wa'adin auren mu, na rungumi k'addarar shiryawa zaman zawarci, da tunkarar sabon wani auren da bazan tab'a so ba, Sai dai nayi a larura.
Saboda manyan matsaloli ne masu wuyar warwaruwa ke ta tunkaro ni cikin aurena da Ancle Fa'iz. Ko ga na Momi Kawai ya isa na sare. Saboda naga k'iyayyar mai zafi ce, tunda har ba'ason had'a jini dani. Lallai Khairat, tana k'aunata sosai, tun da ta iya fad'amin sirrin mahaifiyarta.
Na tara bokiti bakin fanfo zan debi ruwa
zan Shiga band'aki nayi wanka, saboda wani zafi da ake surfawa, Muhibbat ta taho da sauri da nufin angijeni tayi saurin shigewa saboda neman fitina, bayan ta baro wani band'akin a bayanta. Batasan a yarda nake ji da tsiya ba, kowa ya tunkaroni a lokacin karawa za' muyi. Shi yasa banyi jinkirin angijeta ba,iya k'arfina, Sai gata a k'asa wanwar .
Ta kuwa Mik'e da masifa za'ta soma aunamin zagi, yarda ta saba. Nace cikin d'aga murya.
"Ahir. yarinya. Karki d'auki kawaicina a matsayin gazawa. Kuma karki d'auki hak'uri na a matsayin tsoro. Idan har ke kin cika d'iya ta halas, to ki kai ga jikina, domin fad'a na baki na matsorata ne."
Sautin murya ta da yayi Sama, a she Momi taji yo, Sai ta fito, haka Khairat, suka zubo Mana idanu daga saman bene.
Muhibbat tayi min wani matsiyacin kallo, cike da mamakin yarda na rikide tashi guda, don duk iskancin da take min sunkuyar da kai nake yi na wuce.
Tace cikin tafa hannu.
"Samun wuri, Wai d'an wake a hotel. ke bora, kuma 'yar tsaron k'ofa, har kina da bakin magana? har da fiffik'a?
to ba za ta kaimu da nisa ba, zakisan matsayin ki idan kin manta. Bari yaya ya dawo."
Na sake hada idanu da Momi sai kuwa na sake daga murya a fusace.
"Yazo din, me ya isa yayi min, datse min numfashi, ko duka na zai yi, don bazan daku ba wallahi, iko daya ne dai cal zai iyayi kololuwa, shine ya sakeni, kuma na shirya tsab, tun da ba autan maza ba ne. Gari da yawa ai maye baya cin kansa".
Wasa farin girki, har yanzu ba a shiga farfajiya na rigin gimu da manufofi da soyayya da daɗin wannan littafi ba.mai son sanin komai to ya ci gaba da bibiyata.👌🏻
Zainab ilyas mazawaje