CHAPTER 2
Game bukatar document din sa ko kuma PDF sai ya siya 500 ne ga lambar account dina sai ya turamin da receipt din ta Whatsapp ***
Number account dina
9115902627
Abubakar Ishaku
Opay Bank
Thanks ๐ ๐
CHAPTER 2
Bayan kowa ya watse daga wajen, sai Hafeez ya nufi gida cikin kwarin guiwa, sannan ya na Allah Allah dare yayi badon komai ba, sai don ya sake yin arba da 'yan matan biyu, wannan shine burin sa na duniya a halin yanzu, bai gushe ba yana cikin tafiya har ya iso kofar gidan su, nan take kuwa ya kunna kai izuwa cikin gidan da shigowar sa cikin farfajiyar gidan kuwa, sai ya yi arba da mahaifiyar sa wato Maryam ta na tsaye cikin tashin hankali, tana jiran dawowar sa daga tsinannan yawon da ya zame masa jiki, a kullum kwanan duniya, bashi da wani aiki da ya wuce yawo. Koda ganin Maryam din sai Hafeez ya ce mata. "Lafiya kuwa Umma na ganki a cikin damuwa irin wannan?" Maryam ta dube shi cikin karayar zuciya idanuwan ta suna zubar da kwalla, sannan ta ce masa.
"Ina fa lafiya Hafeez naji labarin cewa a daren jiya kayi arba da wadannan 'yan matan guda biyu, sannan kuma kace sai ka kara neman su a daren yau ma, to ta yaya hankali na bazai tashi ba alhalin kai kadai ka rage min a duniya, daman kasan kai kadai na haifa kuma dalilin mahaifin ka na guji iyaye na, sai kuma gashi bayan haihuwar ka shima mahaifin naka sai ya mutu ya bar ni. A halin yanzu kai kadai ne wanda ya rage min a wannan duniyar, to in ka mutu kai ma tayaya kake ganin zan iya ci gaba da rayuwa bayan bani da kowa a duniya? Na roke ka dana da ka janye abun da kake kokarin aikatawa, domin kuwa ina ji a jiki na cewar za'a iya samun wata babbar matsala wacce magance ta ba karamin wahala bane, domin na sha yin mafarkin hakan akan wadannan 'yan matan da kake kokarin sai ka yi musu magana."
Lokacin da Maryam ta zo dai-dai nan a zancen ta, sai Hafeez ya kamu da matukar tausayin ta amma kuma sai yaji matukar mamaki ya turnike shi, shin ta yaya akayi labari ya riski mahaifiyar ta sa? Amsar da ya kasa baiwa kansa kenan, nan take sai ya dube ta cikin sanyin jiki yace mata. "Umma kada ki damu ki yi sani cewar da yaddan Allah babu wani abu da zai same ni in na hadu da 'yan matan, ta yu ma wata dama ce da zan samu a rayuwata ta zaman duniya baki daya, saboda haka ina bukatar addu'ar ki ne kawai a gare ni ina fatan dai bazaki ki goyan bayan abun da nake son in aikata ba." Yayin da Maryam ta ji hakan daga bakin Hafeez, sai tayi ajiyar zuciya cikin sanyin jiki sannan ta dube shi a karo na biyu tace masa.
."Ya kai dana tabbas nima na sha yin mafarkin wadannan 'yan matan a baya, akan cewar kayi taraiya da daya daga cikin su, amma kuma daga karshe kasha bakar wahala wacce ta kusa yin sanadiyar ajalin ka, wannan shine kadai abunda ya ke matukar tayar min da hankali in na tuna, ka janye wannan batun naka sannan ka manta da batun sake haduwa da wadannan 'yan matan muddin kana bukatar ganin frinciki na." Yayin da Hafeez ya ji hakan daga bakin Maryam, sai ya yi ajiyar zuciya sannan ya dube ta cikin damuwa yace mata.
"Umma ki yi hakuri ki barni na gana da wadannan kyawawan 'yan matan, domin kamar yadda kika kasance kina mafarki a kansu, nima haka na kasance ina yi, banbancin nawa mafarkin da naki anan kawai shine, ke kina yin mafarki ne akan cewar zasu cutar da ni, amma ni kuma ina yin mafarki ne akan cewar za su taimake nine a rayuwata ta duniya, kuma ni ma zan taimake su ne, a cikin tasu rayuwar domin da akwai wani babban kudiri nasu da suke son cikawa suka kasa, dole ne sai da taimako na burin na su zai cika, ina fatan dai bazaki ki goyan baya na ba." Yayin da Maryam ta ji hakan daga bakin Hafeez sai nan take ta ji kirjin ta ya buga da karfin gaske tamkar wanda aka dokawa guduma, sannan ta dubi Hafeez a razane tace masa.
"Hafeez kada ka tunkari wadannan 'yan matan domin kuwa sune suka yi sanadiyar mutuwar mahaifink...." Sai ta yi shiru ta kasa karasa maganar ta ta, sakamakon kuka da ya kwace mata, Hafeez ya dube ta cikin mamaki yace mata. "Umma kina nufin cewar mahaifina ba mutuwar Allah da annabi yayi ba, wani ne ya kashe shi?" Yayin da Maryam ta ji wannan tambayar daga bakin Hafeez sai ta ji kukan ya sake kwace mata, nan take kuwa ta juya da gudu ta shige cikin dakin ta, shi kuwa Hafeez binta yayi da kallo kawai yana mamaki, domin kuwa abunda bai taba zato ba daga gare ta, sai kuma gashi ya ji daga bakin ta. Nan take sai ya nufi dakin mahaifiyar tasa domin ya tambaye ta me ye take boye masa, domin ya ji gaskiyar Al'amarin daga bakin ta. Da shigowar sa cikin dakin sai yayi arba da ita a kwance akan gadon ta, sai faman rusa uban kuka take ta yi, koda ganin ta a haka sai Hafeez din ya karaso wajen gadon da take kwance akai, sannan ya zauna a gefen gadon ya dube ta cikin sanyin jiki, sannan ya ce mata.
"Umma ki gafarce ni in ni na bata miki rai, na dauki tsawon lokaci ba tare da na ga hawayen ki ba, amma kuma sai gashi yau a sanadiya ta har kukan ki sai da na gani, nayi nadamar jayayyar da na yi dake ki yi hakuri bazan sake ba." Yayin da Maryam ta ji hakan daga bakin Hafeez sai ta dai na yin kukan sannan ta share hawayen dake fita daga cikin idanuwan ta sannan ta yi ajiyar zuciya cikin sanyin jiki, ta dube shi cikin damuwa tace masa. "Ba haka bane yasa ni kuka ba dana, face tunawa da nayi da mahaifinka da kuma abunda ya yi sanadiyar mutuwar sa." Koda jin hakan sai Hafeez ya dubi mahaifiyar tasa cikin mamaki sannan ya ce mata. "Umma shin mene ne yayi sanadiyar mutuwar mahaifin nawa?"
Koda jin wannan tambayar, sai Maryam ta dube shi cikin damuwa tace masa. "Banso ace ka ji wannan sirrin yanzu ba, amma kuma bani da wani zabi illa kawai in sanar da kai abunda ya faru ga mahaifin ka, yanzu ka nutsu ka saurare ni, ina ganin wannan labarin da zan baka na mahaifin ka, zai kara maka wani haske akan wadannan 'yan matan biyu, domin na tabbata za ka koyi darasi sosai acikin sa, inason ka sani cewar mahaifin ka wato Mallam Bukar shine wanda ya soma yin arba da wadannan kyawawan 'yan matan da kuke ikirarin cewar kun gansu, ina fatan dai zaka iya jurewa sauraren labarin da zan baka na mahaifinka, da kuma nawa labarin domin ka ji yadda akayi mahaifin ka ya soma yin arba da 'yan matan biyu?" Hafeez ya gyada kai alamar cewa Eh! Yana sauraron ta, Maryam ta ja dogon ajiyar zuciya sannan ta yi gyaran murya ta soma bashi labari kamar haka : *************************************************
"Asalina na kasance 'yar garin Kano ce ina anguwar Fagge tare da mahaifana shi kuwa mahaifin ka wato Mallam Bukar ya kasance dan Gwammaja ne dake garin Kano, a wajen aikin sa na wankin mota muka hadu lokacin da muka yi arba da juna ni da mahaifin ka, nan take kuwa kibiyar so ta ratsa zukatan mu, ni mahaifi na ya kasance dan boko ne ya na aikin gwamnati amma kuma mahaifin Mallam Bukar ya kasance baduku ne. Lokacin da mahaifi na da kuma mahaifiya ta suka ji labarin cewa ina soyayya da wani, sai suka bukaci ganin mahaifin ka, nan take kuwa ya amsa gaiyatar su cikin farinciki baisan me zai faru da shi ba, da zuwan sa gidan mu sai mahaifi na ya tarbeshi cikin farin ciki marar misaltuwa, kasancewar ya ganshi a cikin shiga ta kamala ba tare da sanin ko shi waye bane, lokacin da mahaifi na ya kadai ta da Mallam Bukar sai ya dube shi cikin murmushi sannan yace masa. "Yaro shin ko zaka iya fada min wanene mahaifin ka?" Koda jin wannan tambayar sai Mallam Bukar ya maida masa da martanin murmushin, sannan ya ce masa.
"Mallam Adam baduku shine mahaifina kuma ya kasance yana Anguw...." Mallam Bukar ya dakatad da shi da maganar tasa, sakamakon daga masa hannu da mahaifi na yayi, sannan mahaifin nawa ya dube shi a fusace ya ce masa. "Ai na jima da sanin Mallam Adam baduku, yanzu banda tsabagen rashin mutunci irin naka, ka rasa wacce zaka ce kana so sai 'yata alhalin mahaifin ka ya kasance baduku ne, ni kuma na kasance ma'aikacin gwamnati, lallai ku talakawan nan rashin kunyar ku ta wuce kima matuka. Ta yaya kake zaton cewar zan siyar da akuya ta sannan ta dawo ta na cimin danga, kai ma kasan abune mawuyaci hakan ta faru me baduku yaci da har zai iya ciyar da wani daban?
gaskiya ka fita hanyar 'yata tun kafin in tafka maka rashin mutunci, kada na sake jin cewar angan ka tare da 'yata, ina fatan dai ka ji abunda na fada maka don haka ka kama hanya ka fice min daga cikin gida na, tun kafin in hada ka da mai gadin gidan ya fitar min da kai waje." Lokacin da Mallam Bukar yaji abunda Alhaji Kabir wato mahaifin Maryam yace masa, sai nan take yaji zuciyar sa ta yi baki kirin ransa yayi matukar baci da ya ji irin munanan kalaman da suka fito daga bakin Alhaji Kabir din, nan take sai ya mike tsaye cikin sanyin jiki yace masa. "To na gode Alhaji da irin wannan tarbar da ka yimin, ina son ka sani daga yau baza ka sake gani na acikin wannan gidan naka ba,
kuma ka sani cewar daga kai na ka dai na wulakanta duk wani talaka, ai kudi Allah ne ke bada shi ba mutum ba. Kuma ka sani lokacin rabuwar ka da 'yar taka yazo, domin kuwa tana yimin son da zata iya bi na muje ko ma inane a cikin wannan duniyar, saboda haka nan da kwanaki biyu zuwa uku zamu gudu ni da ita muje mu yi auren mu, in har kana ganin cewa zaka iya dakatadda mu ga aikata hakan, to ka yi mu gani ni dai na baka kwanaki biyu rak in ka kasa hana mu tafiya to shikenan munyi nasara akan ka."
Game bukatar document din sa ko kuma PDF sai ya siya 500 ne ga lambar account dina sai ya turamin da receipt din ta Whatsapp ***
Number account dina
9115902627
Abubakar Ishaku
Opay Bank
Thanks ๐ ๐