CHAPTER 3
Game bukatar document din sa ko kuma PDF sai ya siya 500 ne ga lambar account dina sai ya turamin da receipt din ta Whatsapp ***
Number account dina
9115902627
Abubakar Ishaku
Opay Bank
Thanks ๐ ๐
Chapter 3
Lokacin da Alhaji Kabir ya ji hakan daga bakin Mallam Bukar sai ya dube shi a fusace sannan ya daka masa tsawa yace masa. "Ka fice min daga cikin gida na yanzun nan tun kafin ranka ya yi mummunan baci yanzun nan." Koda jin hakan sai Mallam Bukar yayi murmushi a karo na biyu sannan ya ce masa. "Ko baka fada ba zan fice maka daga cikin gidan ka, amma kuma ka sani cewar alkawarin da na daukar maka na tafiya da 'yar ka tabbas sai na cika shi, da wannan kalamin nake yi maka bankwana." Lokacin da Mallam Bukar ya zo dai-dai nan a zancen sa, bai jira Alhaji Kabir ya sake ce masa komai ba sai ya fice daga cikin falon gidan yayi tafiyar sa.
Ashe dukkanin abun da ya faru tsakanin Alhaji Kabir da Mallam Bukar duk Maryam ta saurari komai ta ji yadda suka yi, fitar Mallam Bukar din ke da wuya kuwa sai Maryam ta fito daga cikin dakin ta tazo ta tsaya kikam agaban baban nata sannan ta dube shi a fusace tace masa. "Dadi yanzu abunda kayi wa Bukar yayi dai-dai kenan? Wadannan kalaman basu dace ba ace sun fito daga cikin bakin ka ba, domin wannan cin zarafi ne da cin mutunci ka sani cewar Allah shi yake azurta wanda ya so sannan kuma shi yake talauta wanda ya so.
To kaga kenan kai ma baka fi karfin Allah ya jarabci rayuwar ka ba..." Ai bata gama rufe bakin ta ba sai taji saukar mari akan kuncin ta ji kake tas!! Maryam ta dafe kuncin nata ba wani bane ya zabga mata mari ba face mahaifiyar ta Hajiya Salma, nan take kuwa Hajiya Salma ta daka mata tsawa tace mata. "Ke dan ubanki yanzu mahaifin naki kike fadawa wadannan kalaman masu daci haka akan wani matsiyacin yaro wanda shi kansa ma bashi da hanyar da zai iya ciyar da kansa?"
Lokacin da Hajiya Salma ta zo dai-dai nan a zancen ta, sai Maryam ta dube ta tace mata. "Umma yanzu ni kika mara don ina fada muku gaskiya?" Koda jin hakan sai Alhaji Kabir ya dube ta a fusace sannan yace mata. "Ke dan uwar ki yaushe aka haife ki da zaki fada mana gaskiya? To ki sani cewar baza ki taba auren sa ba muddin ina raye a doron kasa sai wanda na baki shi zaki aura, kuma daga yau ki fara irga kwanakin auren ki nan da sati biyu rak zan aurar da ke ga dan yaya na."
Lokacin da Maryam ta ji wannan batun daga bakin mahaifinta, sai ta dube shi a fusace tace masa. "Wallahi banga wanda ya isa yayi min auren dole ba, domin ku ma na tabbatar da cewar ba auren dole aka yi muku ba lokacin da kuke kanana, ni bana son yaya Sadiq din ni Bukar nake so." Hajiya Salma ta dube ta cikin mamaki tace mata. " Eyeh.. ke yanzu har wuyan ki ya isa yanka haka, da zaki ce zaki bujirewa umarnin mu?" Alhaji Kabir ya ce. "Hajiya kyale ta, tabbas hausawa sun yi gaskiya da sukace.
"So yana iya makantar da mutum har ya manta asalin ko waye shi." In ba haka ba ta yaya za'a ce yau 'yata ta ciki na ce take furta mana wadannan bakaken maganganun, to shikenan daga yau na cire ki daga cikin ahalina maza ki je ki nemi wani uban, tunda kinfi karfin mu ki fice daga cikin gidan nan tun kafin in rufe ido na in bude." Koda jin hakan sai Hajiya Salma ta dubi Alhaji Kabir cikin kaduwa tace masa. "Alhaji kada ka.." Alhaji Kabir ya dakatadda ita ta hanyar daga mata hannu sannan yace.
"Bana bukatar wani magana daga bakin ki na riga da na yanke hukunci, saboda haka dole ne ta bi umarnin abunda na fada mata ko kuma ranta ya yi mummunan baci yanzun nan, ina fatan dai kun ji ni." Lokacin da Maryam ta ji hakan daga bakin mahaifinta sai ta dube shi shi da mahaifiyar ta ta, kwalla ta cika mata idanuwan ta, sannan tace musu. "Shikenan Dadi naji zanbar muku gidan ku kamar yadda kuka bukata kuma na daukar muku alkawarin cewar bazan sake taka cikin gidan ku ba har abada daga wannan ranar."
Lokacin da Maryam ta zo dai-dai nan a zancen ta, sai ta wuce dakinta kai tsaye da nufin ta kwaso kayan ta, koda ganin hakan sai Alhaji Kabir ya daka mata tsawa a karo na biyu sannan ya ce mata. "Ai babu wani abu da zaki dauka acikin gidan nan tunda ba ke kika siya ba kayan dake jikin ki ma ahalin yanzu ba naki bane, bazan so in bari ki fita tsirara ba daga cikin gidan nan, badon komai ba sai don kada duniya ta zage ni, amma kuma ki sani da zarar kin samu wasu kayan, ki maido min da nawa kayan saboda haka yanzu ki fice min daga cikin gida na."
Lokacin da Maryam ta ji hakan daga bakin mahaifinta, sai ta dube shi a karo na biyu cikin mamaki sannan ta girgiza kai ta fice daga cikin falon gidan, daga ita sai takalmin dake kafarta da kuma wani dan mayafi da ta yafa akan ta, ta fice daga cikin gidan baki daya, ita kuwa Hajiya Salma ta na son ta baiwa Alhaji Kabir hakuri amma kuma tana jin tsoron yin hakan, domin ta riga da tasan halin sa tun a baya indai ya fadi magana tofa baya canjawa har sai anyi amfani da maganar tasa.
Nan take kuwa hankalin Hajiya Salma ya dugunzuma ta rasa me yake yi mata dadi, shi kuwa Alhaji Kabir ko a jikin sa sai ma ya dakko jarida ya ci gaba da karatun jaridar sa, kamar babu wani abu da ya faru a cikin gidan, Hajiya Salma kuwa kasa zama da tsayuwa tayi sai safa da marwa take tayi kamar wacce ta hadiyi tabarya, koda ganin hakan sai Alhaji Kabir ya ce mata. "Ki nemi waje ki zauna ko kuma ki bace min da gani tun kafin in huce haushi na akanki yanzun nan."
Lokacin da Hajiya Salma ta ji hakan daga bakin Alhaji Kabir, sai ta wuce dakinta idanuwan ta suna zubar da kwallar takaici, shi kuwa Alhaji Kabir sai ya ci gaba da karatun jaridar sa kawai, babu wani alamun da ya sauya a tattare da shi a zahiri, amma kuma a badini wani irin yanayi yake ji a cikin zuciyar sa, tamkar zata kone haka zuciyar ta sa take ta tafarfasa, badon komai ba sai don ya yi nadamar korar 'yar tasa guda daya domin ita kadai Allah ya basu a duniya, amma kuma babu yadda ya iya dole ne ya jurewa yanayin rashi da ya ke ji a cikin zuciyar sa, domin kuwa bakin alkalami ya riga da ya bushe, tunda ya yanke danyen hukunci ba tare da yayi tunani ba.
WANNAN KENAN
*************************************************
Al'amarin Maryam kuwa lokacin da ta fito daga cikin gidan su sai ta tsaya a kofar gidan cikin tashin hankali tana tunanin wanne hanya ya kamata ace ta bi domin ta riski masoyin nata, amma kuma sai ta tuna cewa ita fa a halin yanzu bata da ko kwandala a tattare da ita ballantana kuma ace ta samu kudin da zata shiga adaidaita sahu domin ta isa gidan su Mallam Bukar din, sai da ta dauki tsawon lokaci a kofar gidan nasu tana nazarin hanyar da ya kamata ace ta bi domin ta riski masoyin nata, bayan kamar mintuna talatin da ta yi a tsaye sai wata zuciyar ta ce mata. "Gara fa ki kama hanyar tafiya tun kafin mahaifin ki ya fito daga cikin gida ya ganki anan."
Aikuwa da wannan shawarar tayi amfani ta kama hanyar tafiya har ta iso babban titin da ke anguwar, titin da ya raba anguwan da take da kuma anguwan da Mallam Bukar din yake, koda zuwanta bakin titin, har ta yunkura zata tsallake titin sai ta ga motar mahaifinta ya zo ya gifta a guje ta gabanta, nan take kuwa ta bi motar da kallo idanuwan ta suna zubar da kwallar nadama, nan dai ta tsallake titin sannan ta shiga anguwan da Mallam Bukar ya ke, sai da ta shafe tsawon mintuna goma sha biyar tana tafiya sannan ta shigo layin gidan su Mallam Bukar din.
Ai kuwa tana shawo kwanar gidan sai tayi arba da Mallam Bukar a zaune a kofar gidan su yayi tagumi ya fada cikin kogin tunani, koda ganin sa a cikin wannan halin sai ta yi sauri ta karaso inda yake a zaune da zuwan ta wajen sai ta kura masa ido tana kallon sa kawai, domin kuwa har a sannan baisan ta karaso wajen ba sakamakon fadawa kogin tunani da yayi, har sai da ta yi gyaran murya sannan ya yi firgigit tamkar wanda aka tsikara da allura sannan ya dube ta a razane suka hada ido, har sai da suka dauki tsawon mintuna biyar suna kallon junan su ba tare da dayan su yace uffan ba.
Mallam Bukar shi ya katse musu shirun ta hanyar yi mata magana yace mata. "Ya ke farin ciki na shin lafiya kuwa na ganki a wannan lokacin kin zo gare ni kuma gashi ga dukkanin alamu da kafa kika zo nan din shin lafiya kuwa?" Yayin da Maryam ta ji wannan tambayar daga bakin Mallam Bukar sai wani zazzafan hawaye ya subuto daga cikin idanuwan ta ya sauko izuwa kan kyawawan kumatun ta sannan ta dube shi a karo na biyu tace masa.
"Ya kai abin kaunata na zo ne domin na baka hakuri akan cin zarafin da mahaifina yayi maka sannan ina mai farin cikin sanar da kai cewa daga yau na yanke duk wata alaka dake tsakanina da mahaifi na da kuma mahaifiya ta domin kuwa sunyi min korar kare daga cikin gidan su." Nan take Maryam ta kwashe dukkanin abunda ya faru tsakanin ta da iyayen ta ta zaiyanewa Mallam Bukar. Koda ya gama jin abubuwan da suka faru sai nan take yaji tausayin ta ya turnike shi matuka.
Sannan ya dube ta cikin tausayi yace mata. "Ya ke a bar kaunata kiyi sani cewar a halin yanzu a duk fadin wannan duniyar baki da wani masoyi da ya wuce ni saboda haka zan kare lafiyar ki iyakar iyawa ta, kuma bazan taba barin ki ki wulakanta ba saboda ke kadai nake so a duk fadin duniya babu wata 'ya mace da zan taba jin sonta acikin zuciya ta bayan soyayyar ki, kece rayuwa ta ke kadai ce wacce ta bar iyayen ta saboda ni tabbas kin nuna min halacci saboda haka inason ki sani cewar daga yau zaki tabbatar da cewar bazan taba barin ki ki wulakanta ba a wannan duniyar saboda haka ki biyo baya na."
Game bukatar document din sa ko kuma PDF sai ya siya 500 ne ga lambar account dina sai ya turamin da receipt din ta Whatsapp ***
Number account dina
9115902627
Abubakar Ishaku
Opay Bank
Thanks ๐ ๐