MASOYIN ALJANA! complete

CHAPTER 4

by @abubakarmarubuci

Game bukatar document din sa ko kuma PDF sai ya siya 500 ne ga lambar account dina sai ya turamin da receipt din ta Whatsapp ***

Number account dina

9115902627

Abubakar Ishaku

Opay Bank

Thanks ๐Ÿ‘ ๐Ÿ˜Š

Chapter 4

Lokacin da Mallam Bukar ya zo dai-dai nan a zancen sa sai ya wuce ya soma tafiya nan take kuwa Maryam ta bi bayan sa ya tare musu adaidaita sahu sannan ya ce akai su zuwa Fagge, koda jin hakan har Maryam ta bude baki da nufin ta yi masa magana amma sai ta fasa sakamakon daga mata hannu da yayi sai ta yi shiru kawai, shi kuwa mai adaidaita sahu bai zame ako ina ba sai a kofar gidan su Maryam din, nan take Mallam Bukar ya sallami mai mashin din sannan ya shigo cikin gidan yayi sallama ya wuce kai tsaye izuwa cikin falon gidan,

Maryam ta na biye da shi cikin tsoro. Da shigowar su cikin falon gidan, sai suka iske Alhaji Kabir da Hajiya Salma suna zaune a falo, koda ganin su sai suka zuba musu ido kawai domin su ji dalilin da ya kawo su cikin gidan, Mallam Bukar ya dube su su biyun sannan ya ciro damin kudi daga cikin aljihun sa ya cilla musu kudin, sannan ya dube su a fusace ya ce musu. "Ga kudin kayan jikin ta daman kunce in ta samu wani kayan ta kawo muku na ku, saboda haka gashi nan mun biya ku daga yau babu ku kuma babu ita, tunda kun yafe ta daga cikin iyalan ku, daga yau ni zan kasance mahaifin ta kuma mahaifiyar ta."

Lokacin da Mallam Bukar ya zo dai-dai nan a zancen sa, sai ya wuce ya na mai kiran Maryam nan take kuwa itama ta rufa masa baya cikin sauri suka fice daga cikin falon gidan ba tare da sun tsaya sun saurari abun da Alhaji Kabir din zai ce musu ba, ita kuwa Hajiya Salma tsoron Alhaji Kabir din take ji shiyasa bata ce uffan ba ganin fitar Maryam da Mallam Bukar daga cikin gidan sai ta fashe da kuka, sannan ta mike tsaye ta shige cikin dakin ta a guje, shi kuwa Alhaji Kabir kasa magana yayi saboda mamakin da ya turnike shi matuka. Alhaji Kabir ya ce. "Tabbas wannan yaron ya kure ni sai na dauki mummunan mataki akan sa."

Su kuwa Mallam Bukar da Maryam lokacin da suka fito daga cikin gidan sai suka dada tarar mai adaidaita sahu suka nufi gidan su Mallam Bukar din, har suka iso kofar gidan babu wanda ya sake cewa uffan daga cikin su, nan take Mallam Bukar yayiwa Maryam jagora izuwa cikin gidan nasu tana biye da shi, ai kuwa suna shigowa cikin gidan sai sukayi arba da Mallam Adam da kuma Karima wato mahaifiyar Mallam Bukar din koda ganin shigowar su cikin gidan, sai suka zuba ido kawai suna kallon su cikin mamaki. Har Maryam ta gaishe da su suka amsa amma kuma basu gane ko wacece ita ba sai a sannan Mallam Adam ya dubi dan nasa sannan yace masa. "Ya kai dana shin wacece wannan din?" Koda jin wannan tambayar sai Bukar ya sunkuyar da kansa kasa ya rasa me zai fada musu, ko da ganin hakan sai Karima mahaifiyar sa itama ta kuma watso masa tambaya.

"Tambayar ka fa ake yi kayi shiru shin wacece wannan din da ka shigo da ita cikin gidan nan?" Koda jin wannan tambayar sai Bukar ya yi ajiyar zuciya cikin sanyin jiki sannan ya kwashe dukkanin abunda ya faru tsakanin su da mahaifan Maryam din ya zaiyane musu duka, koda gama sauraron hakan daga bakin Bukar din, sai Mallam Adam ya dube shi cikin tashin hankali sannan yace masa. "Kai daman baka da hankali ban sani ba? Shin don ta bijirewa iyayen ta shine kai kuma zaka bata mafaka shin tunanin ta da naka iri daya ne? Ai ban taba sanin cewar kai sakare bane sai yau tunda gashi ka aikata abun da ko karamin yaro bazai iya aikatawa ba.

To inason ka sani cewar acikin wannan gidan ma babu wata mafaka da zata samu maza ta koma gidan mahaifinta tun kafin lokaci ya kure mata ka fada mata wannan." Lokacin da Mallam Adam ya zo dai-dai nan a zancen sa sai Karima ta dubi Maryam sannan tace mata. "Ke yanzu Maryam saboda wani shashasha shine zaki bar gidan ku ki bar mahaifanki lallai kinyi katobara da kika gujewa mahaifan ki ina mai baki shawara da maza ki koma gida ki baiwa iyayen ki hakuri tun kafin lokaci ya kure miki, ki bi umarnin su sannan ki auri wanda suka baki in har kina son gamawa da duniya lafiya." Lokacin da Maryam ta ji hakan daga bakin Karima sai tayi ajiyar zuciya sannan ta ce mata.

"Umma ki sani cewar a halin yanzu bazan iya komawa gidan mu ba, domin na tabbata cewar mahaifina zai iya kashe ni saboda bijirewa umarnin sa da nayi saboda haka ahalin yanzu ni zan zauna a tare da ku acikin wannan gidan naku." Koda jin hakan sai Mallam Adam ya tari numfashin ta ta hanyar daka mata tsawa yace mata. "A'a ai awannan gidan baki da mafaka a cikin sa tunda har kika gujewa mahaifanki dole ne mu ma ki bar mana gidan mu yanzun nan." Koda jin wannan maganar sai Bukar ya dubi mahaifin sa yace masa. "Haba Abba idan ta tafi gidan waye zata je kenan? Bayan bata da kowa a halin yanzu a wannan duniyar?"

Lokacin da Karima ta ji wannan tambayar daga bakin Bukar sai tace masa. "Taje koma inane mana ai duniya fadi ne da ita amma a wannan gidan bata da makwanci." Bukar ya ce wa mahaifiyar sa. "Umma sai dai ni ma in zaku kore ni daga cikin wannan gidan, domin ni bazan iya barin ta tafi ba domin bata da inda zata je ahalin yanzu a duk fadin duniyar nan." Mallam Adam ya ce masa. "Mu dai baza mu kore ka ba domin kai dan mu ne amma kuma ita kam baza ta zauna acikin wannan gidan ba sai dai ta fita daga ciki." Bukar ya ce. "Tabbas wannan kora da hali ne ni kuma muddin zata bar gidan nan to nima zan bari domin bazan iya rayuwa ba tare da ita ba sai dai mu tafi tare koma inane a wannan duniyar."

Koda jin hakan sai Mallam Adam ya ce masa. "To ga hanya nan ya rage naka in kaga zaka iya binta to kabi ta ku tafi amma kuma ka sani in har ka fita daga cikin gidan nan dalilin binta to kada ka sake dawowa har abada." Bukar ya ce. "Na amince da wannan sharadin daka gindaya min." Nan take sai ya mike tsaye ya ce wa Maryam. "Ki tashi mu tafi." Nan take sai ta mike tsaye sannan suka kama hanyar fita daga cikin gidan, har Karima ta yunkura zata dakatadda su amma sai ta fasa sakamakon daga mata hannu da Mallam Adam din yayi, nan take sai ta fashe da kuka sannan ta shige cikin dakin ta a guje. Al'amarin Bukar da Maryam kuwa lokacin da suka fito daga cikin gidan, sai Bukar ya dube ta cikin murmushi sannan yace mata. "Ya ke abar kaunata shin kin shiryawa aure na a halin yanzu?"

Koda jin wannan tambayar sai Maryam ta maida masa da martanin murmushin sannan ta ce masa. "Kwarai kuwa a shirye nake kuma ashirye nake in bi ka koma inane a wannan duniyar, domin kuwa a halin yanzu kai kadai ne ka ragemin a wannan duniyar." Lokacin da Bukar ya ji hakan daga bakin Maryam sai ya kuma yi mata murmushi a karo na biyu, sannan ya ce to ki biyo ni mu bar garin nan baki daya sannan muje a daura mana auren mu, mu kafa sabuwar rayuwa." Maryam ta maida masa da martanin murmushin sannan ta ce masa.

"To muje koma inane ya kai masoyi na." Nan take kuwa suka wuce Tashar mariri dake birnin Kano kai tsaye, sannan suka shiga motar da zata kawo su izuwa yankin Borno State, a cikin local government din Borno mai suna Biu suka sauka, a wata anguwa da ake kira "Nayi nawa." To anguwan asalin sa jeji ne a wajen, ba'a jima da fara yin gone-gine ba a wajen, domin kuwa gidajen da ke wajen sunkai hamsin amma kuma ba'a tare aciki dukka ba, wadanda aka tare aciki baza su fi biyar ba. Wannan dalilin ne ya sa da zarar dare yayi a anguwan banda sautin karar macizai da kuma na aljanu babu abunda kunne yake ji,

hakan ne yasa da zarar an idar da sallah isha a anguwan to kowa zai watse ne akoma gida, saboda tsoron kada wani abu ya sami mutum, sai kaji anguwan yayi shiru tamkar makabarta ne ba anguwa ba, in banda sautin kukan kwadi babu abunda kunne ke ji. Lokacin da Bukar da Maryam suka sauka a tashar garin Biu, a wannan lokacin ranar juma'a ne da safe nan take kuwa sai Bukar ya samu limamin masallacin juma'ar tasha ya bashi labrin su sannan yace masa aure suke son a daura musu, koda gama sauraron labarin nasu sai limamin yace masa. "Tabbas na tausaya muku saboda haka zamu daura muku aure sannan kuma ina da gida da zan baku ku zauna har abada ba tare da kun biya kudin haya ba, amma kuma akwai hadari a anguwan da gidan yake."

Nan take sai limamin masallacin ya bayyana musu yadda anguwan, Nayi nawa yake da yadda mutane suke rayuwa a anguwan. Koda gama jin hakan sai Bukar ya ce. "Zamu iya zama a anguwan." Nan take kuwa aka samu shaidu sannan aka daura auren Mallam Bukar da kuma Maryam, sadakin ma limamin ne ya biya masa, bayan angama daurin auren ne, sai limamin ya hada su da wani mutum yayi musu jagora izuwa gidan da aka basu, nan take kuwa Bukar da matar sa Maryam suka soma cin amarcin su cikin farinciki da kuma annashuwa. Bukar ya samu aikin yi wanda suke rufawa kansu asiri duk wani kayan daki da kuma sutura ya siya mata su, nan take duniya ta sauya a gare su kamar ba su ba har suka soma mantawa da iyayen su baki daya. Allah sarki tamkar babu wani matsalar da zata iya kunno kai nan gaba.

Game bukatar document din sa ko kuma PDF sai ya siya 500 ne ga lambar account dina sai ya turamin da receipt din ta Whatsapp ***

Number account dina

9115902627

Abubakar Ishaku

Opay Bank

Thanks ๐Ÿ‘ ๐Ÿ˜Š