MASOYIN ALJANA! complete

CHAPTER 8

by @abubakarmarubuci

Game bukatar document din sa ko kuma PDF sai ya siya 500 ne ga lambar account dina sai ya turamin da receipt din ta Whatsapp ***

Number account dina

9115902627

Abubakar Ishaku

Opay Bank

Thanks ๐Ÿ‘ ๐Ÿ˜Š

CHAPTER 8

Nan take Maryam ta soma kokarin shawo kansa akan ya hakura da abunda yake kokarin aikatawa, amma ina yace shifa tunda akace su suka yi ajalin mahaifin sa, to babu gudu babu ja da baya sai ya dauki fansar ran mahaifin sa akan su, nan take kuwa Maryam ta fashe da kuka, ganin cewar yaron ta ya ki ya saurari abunda take kokarin fahimtar da shi, shi kuwa Hafeez sai ya mike ya fice daga cikin dakin ya barta ya koma cikin dakin sa ya kwanta, domin ya jira dare, don ya sake haduwa da 'yan matan biyu domin ya san irin dabarar da zai yi musu don ganin ya samu nasara akan su.

Lokacin da dare ya fara yi majalisar su Hafeez ya cika makil da abokanan sa, ana ta hira amma kuma ga mamakin su sai suka ga babu Hafeez babu alamar sa, har suka soma tunanin cewar yaji tsoro ne hakan yasa ya kasa zuwa majalisa, basu san cewar yana gida yana kokarin tunanin yaudarar da zai yi wa 'yan matan domin ya samu nasara akan su ba, wannan shine dalilin rashin fitowar sa daga cikin gida zuwa majalisar ta su.

Har sai da karfe sha dayan dare ya buga ba tare da sunga baiyanar Hafeez ba, nan take wasu suka soma dariya suna cewar yaji tsoro yaki zuwa, a lokacin ne kuma majalisar take watsewa har sun gama yin sallama da junan su kwatsam!! Sai suka ga Hafeez ya baiyana a wajen, cikin mamaki suka dube shi suka watso masa tambayoyi kamar haka: "A ina ka tsaya kaki fitowa majalisa sai yanzu da ake kokarin tashi? Ai munyi zaton cewar ka ji tsoro ne yasa kaki zuwa." Hafeez yayi murmushi sannan yace musu. "Ai ni ba jinin tsoro bane domin kuwa da ace naji tsoro gara ace na mutu, saboda haka babu gudu babu ja da baya sai buri na ya cika koda kuwa ajali na ne zai riske ni a kokarin yin hakan."

Lokacin da Hafeez ya zo dai-dai nan a zancen sa, sai nan take kuwa majalisar ta rude da shewa aka soma zuga shi shi kuwa sai ya ji wani kwarin gwiwa ya shige shi, nan take kuwa suka yi masa sallama suka watse daga majalisar suka bar Hafeez shi kadai a wajen, nan take shima ya wuce kai tsaye inda 'yan matan suke baiyana, da zuwan sa wajen sai tsaya sannan ya nemi guri ya zauna, yana jira domin ganin baiyanar su.

Sai da Hafeez yayi mintuna talatin yana zaune ba tare da yaga giftawar su ba, a minti na talatin din ne kwatsam!! Sai yayi arba da su sun baiyana dan nesa kadan da inda yake, a karon farko kenan a rayuwar sa da yaji zuciyar sa tana dakan uku-uku, tunda yake a rayuwar sa bai taba jin zuciyar sa ta buga ba sai a wannan karon. Nan take kuwa sai ya kura musu ido ko kiftawa ba yayi yana kallon irin tsananin kyawun da Allah yayi musu, bai gushe ba yana kallon su har suka iso inda yake a zaune, koda isowar su wajen da yake, sai ya mike tsaye cikin hanzari yasha gaban su, har suka iso inda yake ba tare da ya basu hanya ba, sai murmushi kawai yake yi yana kallon su.

Ga mamakin sa sai yaga sun ratsa ta cikin jikin sa tamkar yadda damshi ke ratsa jikin bango suka yi tafiyar su, koda ganin hakan sai Hafeez ya bi bayansu cikin hanzari yana cewa. "Baku ji ba 'yan mata minti biyu Dan Allah." Ko uffan babu wacce tace masa daga cikin su, kawai sai suka ci gaba da tafiyar su tamkar ba dasu yake ba. Sai da suka yi nisa cikin tafiyar da suke yi, ganin cewar ya takura musu sai suka tsaya cak, tsayuwar tasu ke da wuya kuwa sai daya daga cikin su ta dube shi tace masa.

"Bawan Allah kai baka san tsoro bane?" Budar bakin sa sai yace mata. "Shin meye hakan tsoron wai?" Budurwar tayi murmushi sannan tace masa. "Babu shakka barewa bata yi gudu danta yayi rarrafe ba, jarumtar da mahaifin ka ya nuna a baya shi kake nunawa kai ma a halin yanzu, tabbas kayi matukar burgeni domin kai ne mutum na biyu da ya taba burgeni a wannan duniyar, kuma mahaifin ka shine mutum na farko kai ne na biyu saboda haka kai ne Hafeez ko?" Yayin da Hafeez ya ji wannan tambayar daga bakin budurwar sai ya kamu da matukar mamaki sannan ya dube ta yace mata.

"Ta yaya akayi kika san suna na? Sannan kuma tayaya akayi kikasa mahaifi na?" Yayin da budurwar taji wadannan tambayoyin daga bakin Hafeez sai ta dube shi cikin murmushi tace masa. "Haba Hafeez ina mahaifiyar ka ta riga da ta sanar da kai dangantakar dake tsakanin mu da mhaifinka? To ai ni a tunanina gaskiya ta fada maka, to wanne karin bayani kuma kake so daga gare ni? Inason ka sani cewar tun ranar da aka haife ka muke tare da kai ni da 'yar uwata muke ganin duk wani motsinka, badon komai ba sai don jarumtar da mahaifin ka ya nuna yayin da ya sadaukar da rayuwar sa don ganin ya farantawa mahaifiyarka rai.

Sannan duk wani abu da mahaifiyar ka ta fada maka a gaban mu ta fada maka shi muna wajen amma kuma babu wanda zai iya ganin mu acikin ku wannan ne dalilin da yasa baka ganmu ba, hatta alwashin da ka dauka na cewar sai ka dauki fansar ran mahaifinka munji da kunnuwan mu, tabbas kayi matukar burge mu domin haka muke son mu ga Da namiji marar tsoro mai jajurcewa akan abunda yake son aikatawa, kamar dai kai dinnan saboda haka zamu baka dama guda daya inkuwa har ka kuskura wannan damar ta wuce ka, to fa ka rasata kenan har abada damar bata komai bace illa jarrabawa zamu yi maka guda uku kacal in kuwa har ka fadi a jarrabawar koda daya ne daga cikin ukun tofa zaka rasa rayuwar ka ko kuma ka rasa mahaifiyar ka saboda haka ka amince da wannan jarrabawar?"

Yayin da Hafeez ya ji wannan tambayar daga bakin budurwar sai yayi murmushi sannan yace mata. "Na amince da dukkanin jarrabawar da zaku yimin amma kuma inna yi nasara akan jarrabawar fa menene sakamako na? Tunda dai kunce faduwar jarrabawar dai-dai take da rasa rayuwata ko kuma rayuwar mahaifiya ta shin ku kuma wanne abu mai muhimmanci zaku sadaukar domin jarrabawar?" Lokacin da budurwar taji wannan tambayar daga bakin Hafeez sai tayi murmushi sannan tace masa. "Kai kafi mahaifin ka ma kaifin basira tunda har kake da hangen nesa.

Saboda haka a halin yanzu babu wanda yake gabanka akan kaifin basirar ka a wannan duniyar kuma nayi imanin cewar zaka cinye wannan jarrabawar ko tantama babu." Hafeez yace mata. "To zan iya yi miki wadansu tambayoyi guda biyu?" Budurwar tace. "Fadi tambayoyinka koda kuwa sunkai goma ne zan baka amsar su." Koda jin hakan sai Hafeez yayi murmushi a karo na biyu sannan yace mata. "Tambaya ta ta farko ita ce menene sunan ku ke da 'yar uwar ki? Tambaya ta ta biyu kuwa me yasa ita 'yar uwar taki bata yin magana? Kodai kurmace ita? Wannan shine kadai tambayoyin da nake son in san amsar su daga gare ki." Lokacin da Hafeez ya zo dai-dai nan a zancen sa sai budurwar tayi murmushi sanan tace masa.

"Tabbas kai ba karamin mutum bane domin na sha haduwa da mutane da dama amma kuma ban taba haduwa da mutumin da ya taba yimin irin wannan tambayar ba sai kai, don haka inason ka sani cewar tambayar da kayi min yana daya daga cikin jarrabawar da za mu yi maka, saboda haka a halin yanzu ka cinye daya daga cikin jarrabawa ukun da zamu yi maka, saboda haka yanzu saura jarrabawa biyu kacal. Amsar ka ta farko ita ce sunana Malisat ita kuwa 'yar uwata sunan ta Halisat, mun kasance 'yan tagwaye ne ga wani babban sarkin aljanu mai suna Isnadil Imran wanda ke mulkin wata babbar kasa ta aljanu.

Kuma Halisat ta kasance tana da matsala ce guda daya tak, matsalar kuwa bata komai bace illa ta kasance tana soyayya da wani saurayin aljani ne mai suna Larhat, wandake karkashin mulkin mahaifin mu, amma kuma shi ya kasance azzalumi ne na gaske domin shi yayiwa Halisat asiri sakamakon sabanin da aka samu a tsakanin su, asirin kuwa shine idan tayi magana to zata kamu da wani mummunan rashin lafiya wanda zai fitar da ita haiyacin ta, wannan nan ne dalilin da yasa bata yin magana, izuwa yau shekaru Dari biyar da Hamsin kenan da yi mata asirin, amma kuma bamu samu makarin asirin ba sai a wannan karon ne muka yi bincike muka gano makarin asirin yana tattare da bil'adama ne, wannan shine dalilin da yasa muke baiyana duk bayan shekaru ashirin da biyar domin mu samu bil'adaman da zai karya mana asirin da aka yi mata.

Amma kuma har izuwa yanzu ba mu samu ba duk wani bil'adama da muka samu sai muga bashi da karfi da juriyar da zai iya karya asirin, don hakane muke saka jarrabawa a tsakanin mutane, duk wanda ya cinye jarrabawar to shine mutumin da zai iya karya asirin da aka yi mata, izuwa yanzu mutane dubu biyu ne suka salwanta wajen cinye jarrabawar, amma kuma babu wanda yayi nasara daga cikin su, domin a cikin jarrabawar ma babu wanda yake tsallake matakin farko sai kai kadai dinnan, yanzu muna da yakinin cewa kai ne kadai wanda zai iya karya asirin da aka yi mata.

Game bukatar document din sa ko kuma PDF sai ya siya 500 ne ga lambar account dina sai ya turamin da receipt din ta Whatsapp ***

Number account dina

9115902627

Abubakar Ishaku

Opay Bank

Thanks ๐Ÿ‘ ๐Ÿ˜Š