KARAGAR MULKI

Page 47

by @cwtsumiey19988

*KARAGAR MULKI*

    BY

  *CWT-SUMIEY*

*YOTA*

*~Page 47*. 

Ko ina  ka wurga idanunka a cikin Masarautar ta k'asar BIHINAR mutane ne sai kai kawo su ke,Bayi masu dafa abinci na ta faman saukewa da d'ora abinci cika kala da kala su ke girkawa,hakama masu su kwalliya da k'yalek'yalen masarauta,da masuyima Dawakai kwalliya, 
     Ba iya 'ya'yan Sarakuna ba,ba ma su kud'i ko ma su fad'a aji na cikin Garin ba,hatta da 'ya'yan talakawan Garin su na cikin farinciki gami da cin ado iya dai-dai k'arfin kowa,
Ranace a gare su ta musanman Rana ce da kowa na k'asar BIHINAR kan ci ya k'oshi  kuma ya baje kolin shi a ita,wasu su kan d'auki buri su d'ora a wannan ranar,ranar Takutuha ranar murnar sabuwar shekarar musuluncin,akwai hawan dawaki na musanman da  ake a wannan ranar wanda har mutanen k'auyika kan zo domin su ba ma idanunsu abinci.

Cikin sand'a gami da taka tsan-tsan Zubaida ke bin bango dan ta samu ta fita daga cikin Gidan zuwa inda ta ke so ba tare da Mahaifiyarta Bahijja ta gani ba amma ina cikin rashin sa'a ta na gab da za ta fita su ka had'a idanu biyu da ita,madadin Zubaida ta hak'ura ta fasa fitar tunda har an riga da an kamata ,amma ina sai aron na kare tai ta zura da gudu ta yi waje Mahaifiyar ta kam sai faman ki ranta ta ke amma ko juyowa ba tai ba balle ta sa ran za ta dawo.
   Ko da Zubaida ta tabbatar da ruwa ta sha sai ta dakata da gudun da take a sanda ta ke da tabbacin ba wanda ya biyo bayanta,kayan jikin ta ta fara gyarawa gami da sa ke rik'on kwanan hannunta da kyau ta ce," 'Dan rainin hankali wallahi ba ka cin wannan abinci ya fi k'arfin ka, Masoyina Hisham zan kaiwa nasan yana can ya na jirana duk da bai san zan zo inda ya ke ba a wannan lokacin",duk ta na wannan maganar ne ta na mai cigaba da tafiyar ta.
Ko a jikinta ba ta jin komi kai tsaye ta nufi Sashen da samarin Masarautar su ke kan ta tsaye ta nufi d'akin Hisham,kasancewar yau kowa hidima ta sha kansa ya sa ba wanda ya kulata har ta kai d'akin Hisham ta tura ta shiga kanta tsaye ba tare da ta jira an ma ta iso ba.
Taurus ta ja ta tsaya sakamakon ganin d'akin wayam ba kowa ,jiki ba kwari ta juya za ta fita ,har ta sa k'afarta d'aya za ta fita ta fasa ta koma ta na mai samun wuri ta zauna a cikin d'akin, da 'yan wak'e-wak'en a saman bakin sa ya shiga cikin d'akin da sauri ya dakata ya na mai cewa da ita,cikin yanayin sa irin na Mata,wadda hata yanayin karin ko fitar sautin muryarsa irin na mata ne ya ce da ita,"Kan Uba waye ya ba ki izini ko damar da za ki shigo min d'aki har da samun wuri ki zauna ke ga isashiya ?".
"Haba Hisham me yai za fi haka da zaka taso min da masifa irin haka,ni ce fa Zubaida ko ba ka gane ni ba ne".
"Allah ya sa ke ce Bahijja ba Zubaida ba, ba abinda ya shafe ni"ya k'are zancen yana mai karyar da wuya gefe guda irin na Mata,....
"Kai Hisham wannan fa sunan uwata ne,","Eh na sani ai ba gayyatar ki nai ba,ban aika sak'on wasik'a ko da baka ba akan ki zo inda ni ke,don haka ba wata darajawa ko girmamawa a tsakanin mu".
"Ba ka da adalci ,son kan ka ya yi yawa,bai kamata dan ina nuna ma ka tsantsar so, ka nemi ka wulak'anta ni har haka ba,duk da na ce zan iya jure komi a kan ka hakan ba ya nufin ka samu lasisin da za ka tozarta ni ko ka ci mutuncin iyayena ba",....
"To ki daina bibiyata mana ko ana so dole ne,na ce ba na yi,na ce ba na yi ko dolene haba dan Allah ayi Mace ba aji,sai nacin masifa don Allah ki barni ko na samu salamar rayuwa, ki samu wani ki aura ke ma ki huta".
"Ba zan iya barinka ba Hisham domin ina tsananin son ka zuciyata a koda yaushe tana bugawa ne da saran wata rana za ka so ni kamar yarda na ke son ka koma fiye da haka ".
" Ai ko ta na yaudarar ki domin ba ki a gabana ke ba ma ke ba ko da d'arinki za a aje min ba su ishe ni ko kallo ba ina jin wani abu ya na sukar min zuciya gami da tokare min mak'oshi a duk sanda na gan ki ko na ji an anbata irin son da ki ke min,ina da k'awaye Mata da Maza da yawa ishe ni dan Allah ki rabu da ni ".
Sai da Zubaida ta matso ku sa da shi sosai ta na mai sanyaya muryata gami da langwabar da kan ta gefe tai kalar ban tausai ka na ta ce da shi," Na rok'e ka dan Allah ka daina furta wannan kalmar ta in barka ko in rabu da kai domin ta na sa zuciyata yin wani tsalle tare da jin numfashina tamakar zai dakata,da gaske na ke Son ka ba zan iya rayuwa da wani ba in ba kai ba ,Kai kad'ai kawai zuciyata ke ma So,So irin na yankar shakku ka daure ka  amince da ni,kallanni fa ka gani har wanka nai na rangwad'a kwalliya gami da yin girki duk dan kai,ko kamanta yau ranar murna da farinciki ce,kar ka yi mana buk'ulun wannan ranar kar ka maida ta ta zama rana mafi muni da bak'in ciki a gare ni".
"Shirmen banza wai ko ba ki san ni ba ne ba,ba ki san sunan da ake kirana da shi ba?,Hisham Hisham d'an daudu ni d'in d'an daudu ne,duk wani kayan ado da ki ke da su nima ina da su,haka ma  duk wata lank'wasa da za ki min nima na iyata don haka ki bar ni ko na huta,ina da tarin abun wuya, awarwaro harma da zanin d'aurawa,zai fi mi ki kyau ki samu wani ki aura ko dan inganta rayuwar ki da ta 'ya'yan ki masu zuwa nan gaba".
"Bai dame ni ba koma me mutane za su suce ko su kiraka da shi a haka na ji kuma na gani na ke son ka,a koda yaushe ina ji a jikina gami da saran kai ma wata Rana za ka So ni ,don ko kafin in zo nan sai da zuciyata ta raya min zan zo in gan ka kana jirana domin mu yi firar Soyayya, ban ta'ba cire rai akan kan ka ba, ko da gegeto,kullum ka na cikin raina ".
Hisham rasa me zai ce da ita yai sai nuna mata hanya da yai alamun ta zo ta fita,sosai ya ke jin wani irin zafi na taso ma sa gami da mamaye ma sa dukkanin ilahirin jikinsa ji ya ke kamar a cikin wuta ko ruwan zafi ya ke.
Ba inda za ni ,har sai ka sassauta tsanar da kyamar da ka ke ma Soyayyata"....
"Ki fita na ce ",Ya katseta a d'an hassale.
" Ba fa inda za ni har"....ta kasa k'arasowa sakamakon nufo ta da ta ga yayi,gadan-gadan idanuwan shi a rufe ya kaima saitin inda ta ke ham'bari,cikin sa'a ya samu kwanon abincin da ta kawo masa tai saurin barin wurin ta na mai cewa da shi,"Wallahi sai na dawo ko anjima ne ko gobe don na gaji da irin rayuwar da mu ke gudanarwa a tsakanin mu,ya kamata ya zuwa yanzu mu samu matsaya mu kai k'arshen wannan lamarin".
Dafe Kai Hisham yai ya na cewa,"Wannan wacce irin fitinanniyar yarinya ce mai nacin tsiya da taurin kai me zan yi ma ta da zata gane har ta fita a cikin rayuwata ban da buk'atar ta kwata-kwata a cikin rayuwata ".
Zubaida da kukanta wiwi ta nufi Gidan su,tana shiga Mahaifiyarta ta re ta da cewa,"Kin ga dakata ko dai ki yi min shiru ko kuma ki koma inda ki ka fito domin ban aiki fara shan miya ba balle ta zo min da yauk'in baki".
" Cikin kukan na ta tace,"Haba Innaro ta ya za a dake ni in zo wurinki da niyar ki share min hawaye na sai ki k'ara watsa min k'asar da tafi wacce a ka watsamin".
"Zan iya cewa gwanda da akai indai a kan wannan lamarin ne,domin ke kan ki kin san garin banza a farau-farau d'in wofi ya ke k'arewa,waye bai san Yarima Hisham ba me ki ke tunanin za ki tsinta ko ki amfana a alak'ar da ki ke yunk'urin had'awa da shi?".
Yawaitar hayaniyar da Galadima ya ji ce ta sa ya fito daga cikin turakarsa,Zubaida da kukanta ta k'arasa gunshi,"Lafiya 'yarleleta me ya same ki,wa ya saka min ke kuka ?".
"Ba Hisham ba ne ba na je wurin sa yai min d'ibar albarka kuma ya koro ni ba".
"A'aha dama wai har yanzu wannan matsalar ba ta kau ba?"
"Yo ina za ta k'are tunda dama can ba ta had'a shirginta da kwarya mai kyau da kwari ba,waye Hisham me akai da shi da har za ta biye mi shi ya dunga wahalar da ita,bayan ga d'an Gidan Turaki can ya na ta faman dakon Soyayyar ta gami da bibiyarta amma a kullum sai watsa ma sa k'asa a Ido ta ke,Ni fa ban ga"......
Galadima ya dakatar da ita da cewa,"Kinga ba ruwan ki a cikin wannan lamarin in har ba za ki sa albarka ko ki ta ya ta yak'in cin nasara ba to ki ja bakin ki kiyi shiru ya fi ma ki a'ala ".
Ya mai da akalar maganar shi akan Zubaida," Ina ce dai ki na Son shi dai har yanzu ko ?",da zumud'i gami da tsalle ta ba shi amsa da cewa,"Sosaima Irin da yawa d'innan na ke son shi".
"To ki sha kurumin ki,indai zancen Auren ku ne kamar anyi an gama,da kaina zan shige mi ki gaba sai inda k'arfina ya k'are ko kuma ince sai na ga ranar Auren ku sannan zan huta".
Da wane irin murna ta fara gode ma sa gami da fatan Allah ya sa hakan ya kasance kuma ya tabbata.
Baki sake Innaro ta bi ta da kallo har ta na cewa,"Oh ni 'yasu na ga ta kaina wannan wacce irin jarabbata ce ta ke tunkaro ni 'ya'yana biyu Mata amma dukkanin su ba wacce tai za'ben Miji Nagari kowacce da irin sha-shan da ta kawo a matsayin wanda ta ke so kuma za'bin zuciyarta".
"A'a Innaro ni saurayi na ba sha-sha bane ba,tunda na san ai yafi Yarima Hsisam da kullum ya ke a cikin bak'in ciki da damuwa".
Da wani sauri Zarah ta yaye labulen d'akin da ta ke ta fito ta na mai nuna Zubaida da d'anyatsa," Kin ga ki fita idona in rufe don bakin rijiya ba wurin wasan makaho ba ne ba,in za yi shirgin ki ki yi duk abinda ki ka gadama amma kar ki kuskura ko da wasa ki sani a ciki ko ki sa Yarima Sadauki domin nasan kin san ruwa ba tsarar kwando ba neba, kuma ko da girgiza kanya tafi magarya 'ya'ya".
"Ina abun ya ke wai maye ya cinye kurwar jariri,ai ni ban ga fankamar da jaki  zai nuna ma alade ba,duk wani jin kai da ki ke nu nawa na banza da hofi ne,domin ko makaho aka jerama Yarima Haisam da Yarima Hisham ya san wanda zai za'ba,gara fa ni halayya ce ko ince d'abi'a ce wata rana zai iya dainawa amma mutum ace tamkar bishiyar kuka ko ta tsamiya haka ya ke kullum cikin fad'uwa ya ke ko k'ok'arin kashe rai,ai banga amfanin tarayya da shi ba,domin wata rana rayuwar ki zai fara barazanar raba ki da ita"......
Ta katseta da cewa,"Na rantse zan fasa ma ki baki in har ki ka cigaba da fad'in wad'annan munanan kalaman a gare ni".
"A kull d'in ki,banga dalilin da za ki hukunta ta ba,tunda ai  gaskiyar ta fad'a ma ki ba, ai har gara ita da ke duk da garar da ba tuwo ba miya ce,ba na ra'ayin za'bin ku ku duka,don haka duk ku shiga taita yin ku da ni,kafin in kai ga fusata da lamarin ku".
"To ki sanar da ita ta fita a harkata tun wuri"......."To in na k'i fa",ta katseta cikin tsiwa da neman rigima, nan fa su ka cigaba da musayar yawu wanda kafin ka ce me tuni sun kacame da danbe, ganin abun na su ba mai k'arewa ba ne ba ya sa Innaro ta rarake su da muciyar tuwanta su kai waje da gudu su duka biyun.
Sai sallallami da tafa hannaye ta ke gami da cewa,"Oh ni Innaro yau na ga abinda ya girmi hankali da tunanina,wa'innan wa'inne irin yara ne,da ba su ji ba su ganin komi sai kawunan su da abinda su ka sa gaba ?".
Kamar wacce a ka kwa'ba ta d'ora da cewa,"Ko da ya ke ai ance ba yanda za ai ka daka ta wani kuma kai ka samu turmin daka ta ka,bayanda za ai ka hana d'an wani zama lafiya kai kuma Allah ya bar ma ka na ka yanda ka ke So,dole ne kaima a jarabce ka ta inda ba kai zato da tsammani ba,gashinan kai ma garin lalata ko tarwatsa rayuwar 'ya'yan wasu kaima an had'a har da naka,ga yara har yara amma ba wanda ya ke da tunani mai kyau ko hangen nesa,ba su jin magana kuma ba su da tarbiya komi nasu a warwatse a tambad'e tamkar 'ya'yan fata,ba zai yiwu ba na gaji bazan cigaba da ganin wannan kayan takaicin ba dole ka dawo asan yarda za ai"......

*Masoyana, littafin KARAGAR MULKI zai kammala kyauta a shafi na 50. Idan kuna son ci gaba da bibiyar wannan labari mai cike da tarihi, sihiri da kuma ƙauna*
*For more Imformation Contact me via ****