Page 48
*KARAGAR MULKI*
BY
*CWT-SUMIEY*
*YOTA*
~Page 48
"Ki rik'a sassautawa zuciyar ki Zarah domin naga kamar kin d'auki wannan lamarin da zafi".
" Ki dai yi shiru Zainaba domin ba ki ga irin wulak'anci da cin kashin da su kai min ba,k'ilama inda ke ce sai kin aikata fiye da haka daga Innaro d'in har ita Zubaidar ba su cika kirki ba wani lokacin".
"Ni kam ba kamar ke na ke ba don kinsan na fi ki sauk'in kai,kawai dai abinda na sa ni ban san raini,ba ni da saurin fushi kamar ki, duk da kema na ga kin fi d'aukaka abin in aka zo kan lamarin Yarima Sadauki ".
" Ke dai bari Zainaba ina tsananin son Yarima har inajin tamkar son shi zai illata ni,tamkar zai tsaga k'irjina ya fito sarari kowama ya gani,Ina jin kamar in kai kaina gabansa a matsayin Mata,ke ni ko Sad'aka ne zan so Yarima yai da ni ba wai sai ya Aure ni don dole ba".
"Da alama dai Son da ki ke ikirarin ki na yi masa ya zautar da ke, domin in ba haka ba ina ki ka ta'ba ji ko ganin inda akai sadak'a da 'ya ba baiwaba,ko dai kin koma Baiwa ne ba mu sa ni ba?".
"Ke ki ke iya banbance matsayin 'ya da Baiwa amma ni a gare ni duk d'aya ne in har zan iya kasancewar da Yarimana a tawannan sigar to ba abinda zai same ni da duk abinda zai biyo baya".
Dakatawa Zainaba tai da tafiyar da su ke tana mai tsurawa Zarah idanu tare da cewa,"Anya kuwa kina Lafiya Zarah,wannan wanne irin kurma kuma makahon So ne ki ke ma Yarima alhalin shi bai ma san ki na yi ba ?".
Yanayin fuskarta ne ya canza alamun abinda za ta fad'a ba k'aramin 'bata ma ta rai gami da ci ma ta tuwo a kwarya ya ke ba ta ce,"A kaf rayuwata wannan shine abu mafi tsananin girma da kuma nauyi da ya zo ya kanannad'e gami da jefa rayuwata cikin garari da kuma halin ha'ula'i, ina cikin sark'ak'iyar rayuwa inajin kamar ba wata Mace da aka ta'ba jarabta da Son wani d'an Namiji kamar ni,gasaki ko a baya ina zuwa Gidan ku ne don in samu damar da zan ganshi ko sau d'aya ne, domin nasan duk inda aka ga Yayan ki Nurain za a ga Yarima Haisam, dagaske ina wahala akan son shi,ina dakon kayansa ban san rana ko watan da zan sauke su ba".
Kamo hannayenta Zainaba tai tare da cewa cikin muryar tausayi da kuma lallashi,"Na tausaya na ki k'awata,na ji bad'i game da yanayin yanda ki dakon So ba tare da wanda ki ke dan shi ya sa ni ba,ina ma da Ina da hanyar da zan taimaka mi ki da na yi sai dai kash ba ni da ita,sai dai zan bi ki da addu'ah iyakar iyawata,in alkairi ne Allah ya tabbatar da shi kuma ya sauk'ak'a mi ki in ba alkairi ba ne ya maida ma ki da wanda ya fishi".......
Da sauri ta dakatar da ita da cewa,"Dakata Zainaba,dakata indai wannan itace addu'ahar da za ki ta ya ni da ita ki bar shi ba na so ban buk'ata".
Da d'anjimami Zainaba ta ce da ita,"Kamar ya ba ki so sai ka ce wacce tai naki fatan mugun abu".
"Eh mana mugun abu ne wannan taya za ai ki ce rabuwa da Yarima Haisam abu ne a gare ni da za a kira shi da abun alkairi, ai sai dai a kira shi da sharri,bala'i ko kuma masifa".
Da sauri Zainaba ta kai hannunta saitin bakinta ta na rufewa gami da cewa,"Kai A'a lalle abun na ki ya girmama har ya kai matsayin da za a fara ba ki rubutu ki na sha,irin wannan zaburewa gami da afkawa cikin ramin Soyayya haka,don haka ni yanzu ba abinda zan ce don gudun kar ta sa ke kwa'bewa sai dai inyi maki fatan alkairi".
Da murmushi ta ida sa matsawa wajen ta tare da cewa,"Yauwa ko ke fa,shiyasa ai a koda yaushe na ke k'ara son k'awance na da ke akwai ki akwai saurin fahimta,yanzu mu yi sauri mu isa wurin taron kar a fara hawan dawakin ba mu gani ba".
Da haka su ka rufe wancan zance su ka tsunduba kan labarin kan yanda ake zaton shagulgulan bikin zai kasance,tunin sun had'e da sauran k'awayensu sai shan cafka ake
Kamar walk'iya haka Zarah ta hango gilmawar Zulfa itama da tata tawagar, da sauri ta ja hannun Zainaba ta rufa ma ta baya,ganin kamar ba za ta iske ta da wuri ba ya sa ta sha gabanta domin dama can jiranta ta ke neman ta ta ke ruwa a jallo Ido rufe,tamkar wacce ba ta gani haka ta je ta bangajeta alamun bata gani d'innan,"Yi hak'uri dan Allah ban gani ba ne ba shiyasa "........ta d'an dakata kafin ta d'ora da cewa," Au su O'o ne masu cusa kai inda ba su da farin jini balle a kai kan maganar kwarjin".
Ya mutsa fuska Zulfa tai irin ba ta fahimci abinda ta ke son ta isar mata da shi ba,wata irin dariyar rainin wayo Zarah da k'awar Zainaba su ka kwashe da ita wanda hakan ba k'aramin k'ular da Zulfa da ta ta tawagar yai ba.
A d'an zafafe ta ce da ita,"Kinga ba na son kwano-kwano,ko wani salon yada magana ki fito fili ki fad'i abinda ke cikin ki ko kin manta an ce habaici da gugar zana d'abi'a ce ko halayyar matsoraci,ki fito kan ki tsaye ki fad'i sak'on ki in ba ga tsoro ba".
"Tsoro kuma ai ke karan kan ki kin san ko Giwa ta fad'i k'ashin gwuiwarta ya fi k'arfin wawaso a wurin kare ko mage, sannan da ki ke maganar habaici da gugar zana da ki gani duk sun wuce ki kira su da d'abiar matsoraci sai dai ki kira shi da "......d'aya daga cikin k'awayensu Zulfa ce ta katseta da cewa," Idan har ke ba matsoraciyar ba ce ki fad'i abinda ke tafe da ke kai tsaye mana za ki zo ki tasa mutane a gaba sai faman raragefe ki ke".
"Kinga A'i kar wanda ya k'ara sa bakin shi a cikin wannan lamarin da'alama kamar da ni kad'ai ta ke son mu goge raini,".
"Ba najin tsoran kowa hakan ne ma ya sa na tunkare ku,na zo ne in samu sahihancin maganar da ke yawo gami da yamad'id'i a cikin wannan Masarautar, shin da gaske ne wai kun je ku gana da Me Martaba Sarki Abdullah tare da Mai d'akinsa Sarauniya Mubina akan Maganar ki da Yarima Haisam, in hakan da gaske ne,to tun wuri ki hak'ura domin akwai maza a gaban ki in har dai a wannan k'adamin ne".
"Ashe ke sha-sha ce kuma lusara,akan Soyayyar d'a Namiji za ki zo ki tsaida mu a saman hanya,ashe ba ki cika Mace ba da ba za ki iya kwatar abinda ki ke so a hannun ko ma wace ce ba,ko kin manta da sannu akuya ke shiga cikin ramin Kura kuma ta ci ta da yak'i, har ta Kai ga mallake KARAGAR ikon mulkin ta".
"Kar ki cika baki domin na san kin san kwace goriba a hannun kuturu abu ne mai sauk'i,don haka ina mai shawartar ki tun wuri ki fita a harkar shi,domin kin san ance dole ne gyad'a tai mai in ta k'iyayya ta sha matsa,".Cewar Zarah
"Hhhhhhh yaro dai yaro ne",cewar Zulfa " Wai ko kun ga ne wannan yarinyar wacce tun shekarun baya ake cewa,wai ta na son Yarima Haisam amma ta ka sa fad'a masa saboda tsabagen tsoro da sakarci".
Nan fa kowa bakin sa ya bud'e sai faman tofa albakacin bakin su ke, a fusace Zarah ta ce da ita,"Tabbas duk abinda ya samu Shamuwa watan bakwai ne ya jawo ma ta dan haka ki kuka da kan ki zunan da wani d'an lokaci zan shayar da ke ruwan mamaki, sannan ina mai yi ma ki alk'awari ni d'in da ki ka raina ki ka kira da matsoraciyar ni ce zan mallaki Yarima Haisam a matsayin Mata,sannan Soyayyata ita ce za ta zama abu mafi soyuwa gami da tsayawa a cikin ransa,ban damu ki cigaba da son shi ko ki daina ba ,ki je ke ta fama, ki ta dakon shi bai dame ni ba,wata k'ila ma ya zama sanadin cuta ma fi muni da tsanani a gare ki domin ina mai tabbatar mi ki da ba ki da wurin da za ki rayu a cikin zuciyarsa"
"Ni kuma na yi ma ki alk'awari ni ce Macen da zai fara amincewa da ita,gami da bata amanna da kuma mik'a mata ragamar rayuwar sa,dan haka kinga ta fiyata",Zulfa ta kad'a da niyar barin gurin,
"A gayas a sauka lafiya Uwar kishiya ta hau kura, kuma ki sani da sauran kuka an raba gumba an hana maye".
Kasa tafiya Zulfa tai har sai da ta jiyo ta ce da ita,"Ina so ki sa a ranki kuma ki rink'a yawan tuna a a cikin ranki sai na zame mi ki dutsen d'anawa wajen ruguza duk wani shirin ki,kin riga da kin makaro tunda har ki ka bari na fara son shi a cikin raina ko kin manta cewa mai neman Mulkar wata KARAGAR MULKI ba ruwansa da duba waye Sarkin da ke MULKIN ta a wannan lokacin,damuwarsa kacokan takan ta'allak'a a kan yarda zai samu wannan cikar burin nasa dan haka ni da ke mu zuba mu gani,ga filinan ga doki inda ba wuri nan ake gaddamar kokowa,Idan har Kura tai kuka masu akuya ke d'aurewa don haka ni nafi k'arfin in yi gogayya ko tarayya da ke a fagen Soyayya ko kin manta cewa Ubana shine Wazirin k'asarnan yana da kusanci da Mahaifinsa ?,magana d'aya in ya yi ta wadatar".
"Da kusancin ki da Me Martaba da rashinsa duk d'aya ne mamaci ya karye a wuya,domin ba ta da wani amfani,banga amfanin sanya kusanci ko alak'a a irin wannan lamarin ba,idan da zan aikata hakan da tuni na dad'e da zama Mata a wurin Yarima Sadauki domin mahaifinsa da Mahaifina Mahaifin su d'aya don haka tun wuri ki janye wannan furucin in kuma so ki ke ki nuna min gazawar ki tun kafin tafiyar tai nisa to Bissimillah".
Wannan lafazin ba k'aramin bugun zuciyar Zulfa yai ba har bata San me za ta ce da Zarah ba.
"Duk kunfar sabulu ta banza ce in har Babu ruwa,dan haka ne ke ba ki shawara da ki tsaya saman k'afafun ki dai-dai ya fi ye mi ki ki dogara da wani",tana kaiwa anan a zancenta ta ja hannun Zainaba da tai mutuwar tsaye tun fara wannan zancen na su,su ka bar wurin.
Ko motsin kirki Zulfa ta kasa yi sai faman bin Zarah da kallo ta ke,daga k'arshe ta maida kallonta kan abokan tafiyarta da sai faman sadda kai k'asa suke daga bisani duk su ka fara zanzare jikinsu su kai tafiyarsu,su ka barta da k'awarta Zahiyya.
"Ki kwantar da hankalin ki k'awata kar ki bar maganganun wannan yarinyar su yi tasiri a cikin ranki,".
"Zahiyya dole in damu,k'aramar yarinya kamar wannan tai min irin wannan dizgin ai dole ya tsaya min a rai".
"Ba fushi ko damuwa za ki nuna anan ba,domin ba su da wani muhimanci kawai ki k'ara k'aimi gami da dagewa wajen nuna ma ta kin fi k'arfinta kin wuce da da sa'arta,ki bi duk hanyar da za ki bi wajen ganin kin rigata mallakar Zuciyar Yarima Haisam shine mafita kuma abinda ya kamata".
"Tabbas maganar ki dutse dan haka zan ta na ji makaman yak'i da kuma tarin dabaru irin namu na Mata har sai naga na rabata da shi wanda ko sunansa ta ji an ambata sai ta rud'e gami da rikicewa tare da neman mafaka"
"Yanzu na ji Batu domin nasan za ki iya aikata fiye da hakan ma saboda ke d'in 'yar na gada ce ba wai na koya ba sai kace ba 'yar A wurin Wazirin k'asarnan ba".
Zahiyya ta ce da ita,Ba k'aramin samun k'warin gwuiwa Zulfa tai da maganganun Zahiyya ba,daganan su ka nufi inda za su Zahiyya na k'ara kwantar mata da hankali da ba ta shawarwari da kuma k'arin dabarun Mata da za tai amfani da su.
*Masoyana, littafin KARAGAR MULKI zai kammala kyauta a shafi na 50. Idan kuna son ci gaba da bibiyar wannan labari mai cike da tarihi, sihiri da kuma ƙauna*
*For more Imformation Contact me via ****