Page 49
*KARAGAR MULKI*
BY
*CWT-SUMIEY*
*YOTA*
~Page 49
"Wallahi a cikin ku ba wanda zai sa ke ko da motsawa har sai kun biya ni hak'k'ina,wannan ai cutarwa ce ,ace mutum har Goma sha d'aya mu kwashe tafiya da ku ta tsawon makwanni sai yau Allah ya kawo mu kuma ku ce ba abinda za ku ba ni a matsayin lada,to wallahi ba ku isaba daganan ko gaban waye mu je ,amma ba zan kyale ku ba".
" Ayub ne yai k'arfin hali ya ce da shi ka yi hak'uri ba wai mun ce ba za mu biya ka hak'k'in ka ba ne,a'a amma anan inda mu ke ba mu da abinda za mu ba ka,ko ba ka kula da halin da mu ke a ciki ba babu wani mai isashiyar lafiya a cikinmu kai ko takalmin arzik'i ba wanda ya ke da shi,don haka ka amince mu shiga cikin Garinnan sai mu biya ka ladanka".
"Nanfa Allah ke na shi ikon,na yi maku iyakar iyawata idan kun ga kun motsa daganan to an biya ni hak'k'i na,ban tsaro tafiya ta da niyar zan shiga cikin Gari ba".
A fusace Jamal ya ce da shi,"Kar Allah ya sa ka amince idon dan abinda za a ba ka ne ka je an cinye ba a biya,kasan mu d'in ko su waye kuwa?, Haba taya sai faman lallashin ka ake kai kuma kana ta botsarewa sai ka ce mun ce ba za mu biya ka ba".
Dasauri Salim ya ja hannun Jamal ba ya ya ce da shi ,"Me ye zai sa ka yi mishi tsawa taimakon mu fa yai ba dan shi ba da tuni ba mu san a ina mu ke ba yanzu don haka ya kamata ka rik'a tausasa harshe a gabansa".
"Don ya taimake mu sai akace yai mana duk abinda ya gadama kalli k'afar Ayub yanda ta ke zubar da ruwan ciwo ta zama tamkar gyambo,ga Habbinan gefan cikinsa ya kunbura ,hakama Shahul a tsakanin mutuwa da rayuwa ya ke a haka za ku cigaba da lalla'ba shi,nan fa garinmu ne k'asar BIHINAR ce fa,Mu d'in ba gama garin mutane ne ne ba mu d'in Dakarun k'asar BIHINAR ne, muna buk'atar taimako muna son a kawo mana d'auki cikin gaggawa".
Nan fa hayani ta 'barke a tsakaninsu wasu na goyan bayan Jamal wasu kuma na bin bayan wannan matuk'in Jirgin,wannan hayaniyar ce ta jawo hankalin wasu daga cikin Dakarun da su ke tsaron ga'bar kogin,ba k'aramin fushi ne ya bayyana a fuskar Dakarun da su ka zo domin su ga hayaniyar me ake.
"Kai me yake faruwa anan da za ku cika ma na kunnuwa da hatsaniya? ",cewar d'aya daga cikin Dakarun.
Mai Jirgin ne yai tsalle ya dire yana kwashe duk abinda ya faru ya sanar da shi batare da yayi ragi ko k'ari ba.
Juyawa yai 'bangaren da su Salim su ke tsaitsaye sun zuba ma sarautar Allah Ido ya ce da su cikin kakkausar murya," Kai abinda ya fad'a gaskiya ko da akwai abinda ya k'ara ko ya rage?","A'a ba abinda ya rage ko ya k'ara iya gaskiyar sa ya fad'a ",Ayub ya ba shi amsa.
A razane wannan Dakare ya sa ke bud'e idanunsa dalilin jin muryar da bai zato ko tunani ba k'ara firgita yai sakamakon cin karo da fuskar wa'inda bai yi zato da tsammani ba,da gudu d'ayan ya koma dan ya sanar da shugaban su abinda ya faru, shi kuma d'ayan ya zube gwuiyawunsa a k'asa ya na mai cewa," Ku gafarce ni wallahi ban gane ku d'in ko su waye ba gabad'aya kun canja kun fita a cikin suffa da kuma haiyacin ku hakan ya sa ko kusa ko da wasa ban gane ku ba".
"Ta shi ka yi tafiyarka domin mu ma mun san ba ka gane mu ba tun da farko",Hamid ya ce da shi ya na mai mik'ar da shi tsaye .
Ba tare da ya ja wani lokaci ba sai ga Shugaban Dakarun na bakin kogin sun taho tare da wannan Dakaren da ya je ya sanar da shi abinda ke faruw har k'asa Dakare Isa ya zube ya na mai cewa,"Ka gafarce ni ya Shugabana ban son kuna cikin wannan Tasha ta mu ba yanzu labarin haka ya riske ni a gafarce ni domin ban yi zato dà tsanmanin ku anan ba,ba ni da labarin kun tsira da da kaina zan zo nan in rik'a tsumayin ku daga safe har Rana"
"Tashi tsaye Dakare Isa kar ka wani damu muma yanzu jirginmu ya tsaya ".
" Tooo Godiya na ke,yanzu ko akwai abinda ku ke buk'ata yanzu in sa a kawo mu ku kafin mu wuce da ku can Fada?".
Jamal ne ya bashi amsa da cewa,"Ba abinda mu ke buk'ata mun fi so mu ga mun isa can Fada domin muna tare da marasa lafiya da ma su dama da jinya,sai dai ko wannan mutumin da ya kawo mu ba mu biyashi hak'in sa ba ya d'auko mu a kwalekwalensa na tsawon mako uku,in ka tashi samo abun hawa ka taho da na shi dan da buk'atar ace Masarauta ce za ta biya shi ba mu ba domin ya taka muhimmiyar rawa a zuwanmu nan don ba dan shi ba da bamu san a ina mu ke ko a wanne hali mu ke a ciki ba zuwa yanzu".
Da to Dakaren ya amsa ma sa ya na mai nufar hanyar da zai samo mu su abinda za su hau,ba k'aramin kad'awa cikin wannan me Jirgin yai ba zuciyarsa ta kad'u ji ya ke kamar shigo-shigo ba zurfi za su yi masa ya sani ya taimaka ma su amma kuma daga k'arshe ya 'bata rawarsa da tsalle,ba tare da 'bata lokaci sai ga Dakare Isa ya dawo da Dawakan da su ka zo a kansu wasu su ka hau mutum biyu wasu uku su ka rankaya su ka tafi Gabad'aya.
Tunda su ka shiga k'ofar farko ta cikin Garin mutane su ka sowa,ihu da murnar ganin su,kafin ka ce me labari ya gama karad'e kowanne lungu da sak'o na cikin Garin BIHINAR cewar ga Dakarun da K'ASAR BAIBAH ta tsarenan sun dawo,Mata daga gidajen su su ka fara fitowa su na gud'a,sanda su ka k'arasa Fada tuni ta kacame da bushe-bushen sarewa da kad'e-kad'e,kowa ka kalla fuskarsa wasai d'auke da farinciki da murna,Kai tsaye Fadar da Me Martaba Sarki Abdullah a ka kai su inda ya ke ganawa da manyan baki ko tattaunawa tsakaninsa da wakilansa nan a ka kai su ba k'aramin tashin hankalin Me Martaba yai ba alokacin da ya gansu ya kuma ga irin munmunan yanayin da su ke a ciki da sauri ya sa a kira masa likitan Masarauta don ya ba su agajin gaggawa .
'Bangare guda a ka ware wanda ake duba marasa lafiya 'yan cikin masarautar can ya ba da umarnin a kai su har sun mik'e za su tafi Madaki ya dakatar da su da cewa,"Na ga kun tashi za ku tafi amma har yanzu banga d'ana Yarima Sadauki ba kuma ko wani a cikin ku ba wanda ya ambaci ko da sunannsa ince dai ba wani abu ne ya sane shi ba,don ba zan ta'ba iya ko lamuntar jin wannan furucin a bakin d'aya daga cikin ku ba ?".
Ko kyakyawan motsi ba wanda ya yi a cikin su balle Madaki ya sa ran wani a cikin su zai ce dashi wani abu,wanda hakan da su kai kad'ai ya nuna masa cewa da akwai wata matsalar.
Kabir da ke kusa da shi ya kai ma Shak'a har ya na girgiza shi tare da cewa,"Yana ina,me ya same shi,garin ya akai kuka taho ku ka barshi,yana ina zuciyata a cunkushe ta ke ba zan iya d'aukar wata kalma me nauyi a yanzu ba,duk wanda ya kuskura ya ce da ni ya mutu na rantse da wanda raina ya ke a hannunsa sai na sa takobi ta na sauke ma sa kai sai dai uwarsa ta haifi wani amma ba dai shi ba ,ku fad'i min ya na Ina?,",Ya kai zance da sigar tambaya cikin tsawa da hargagi.
Dukkanin su sai da su ka tsorata,Salim ne yai ta maza ya ce cikin in'ina, ya ce da shi,"Yyyy......Yyyy....yana can sun tsare sa ba tare da mun san dalilin da ya sa suka aikata hakan ba".
Da wani irin yunk'uri Madaki Idris yai kan Salim da sauri Me Martaba ya umarci d'aid'aikun Dakarun da ke tare da su nan da su dakatar da shi,aiko su ka rik'e shi gam su kuma su Jamal su ka wuce Sashen da za a duba su,sai nan da kwana biyu ko uku za su gana da Me Martaba,nan fa kowa ya watse bakin sa d'auke da magana,kafin ka ce me labari ya sake karad'e ilahirin kowanne lungu da sak'o cewa Dakarun da aka tsare sun dawo amma ba tare da Yarima Sadauki ba.
Tuni gulmace-gulmace gami da rad'e-rad'e sun fara fita,ma su k'arama miya gishiri na yi masu canja ma labarin suna na canjawa, wasu ma gabad'aya ma'anar labarin su ke sakewa,ko ina ka zagaya za ka ga mutane kufi-kufi kowa na tofa albarcin abinkinsa.
" Kinga Zarah ki natsu ki kwantar da hankali ki,wannan abun duk bai kai ki tada hankalin ki har haka ba, duk abinda ki ka ji duk jita-jita ce da kuma k'anzon kurege".
Cikin rawar murya Zara tace ,"Eh dama dama nima ban yarda da duk abinda na ji ba shiyasa na garzayo wajen ki dan in samu sahihancin abinda ya wakana".
Sai da Sarauniya Mubina ta numfasa kana ta d'ora da cewa,"Har yanzu ban samu damar ganawa da Me Martaba ba,tunda su ka dawo ya kulle kan shi ya k'i ya saurari kowa don haka ba ni da wani abu da zan iya ce mi ki game da wannan lamarin illa dai in baki hak'uri tare da ba ki shawarar ki kwantar da hankalin ki Komi zai dai-dai ta da izinin Ubangiji".
"Innalillahi wa'inna ilaihirraju'una lalle ina cikin musiba da tashin hankali hankalina ba zai ta'ba kwantawa ba haka kuma Zuciyata ba za ta ta'ba samun salama ba matuk'ar ban san halin da Yarima Haisam ya ke a ciki ba,don haka yanzu zan nufi masaukin da aka aje Dakarun ko ta halin k'ak'a be sai na samu damar ganawa da wani a cikin su".....
Sarauniya Mubina ta dakatar da ita,"A'a kar ki kuskura ki yi yunk'urin aikata hakan domin wannan babban laifine da zai iya jawo miki fushin Me Martaba don haka karma ki soma ki jira zuwa Dare duk yanda zan yi zan san yanda nai na shawo kan Me Martaba har mu zauna mu tattauna akan wannan lamarin amma kar ki azar'ba'bi ki aikata aikin danasani ".
Sai da Zarah ta duk'ar da kanta k'asa kana ta ce," Ki gafarce ni ya ke wannan Sarauniya Amma ba zan iya jurewa har zuwa wannan lokacin da ki ka d'iba ba mai yiwuwa kafin lokacin Zuciyata ta fashe ta tarwatse,don haka ina rok'on ki kiyi min addu'ah gami da fatan alkairi in Allah ya yarda ba abinda zai faru da ni".
Duk yanda Sarauniya Mubina ta so ta shawo kan Zarah ta hak'ura kar ta je amma ina ta k'i daga k'arshe ta ce da ita,"To shikenan ki je ba damuwa Allah ya sa ki samu damar ganawa da wani a cikin na su d'in".
Ta ji dad'in wannan furici na Sarauniya Mubina duk da itama ta fad'a ma ta ne kawai amma ta san ko shakka ba ta yi ba za ta samu cikar wannan burin na taba.
Ilai kuwa sanda ta Isa wurin zaratan Dakaru ta iske Me Martaba ya baza su na gadin k'ofar shigar bawan da ya Isa ya shiga sai da umarninsa gefe guda kuma ga Zulfa sai faman kokowar son a barta ta shiga ta ke amma k'ememe Dakarun sun k'i barinta,Ganin da Zarah tai ma ta ne ya sa ta juya da nufin ta je ta sake wani sabon shirin amma tabbas yau tai alwashin sai ta san a wanne hali Yarimanta ya ke a ciki.
Gefe guda kuma ga Madaki can a cikin wani mawuyacin hali na rashin ganin dawowar sanyin idaniyarsa ko ya abun zai kasance oho...
*Masoyana, littafin KARAGAR MULKI zai kammala kyauta a shafi na 50. Idan kuna son ci gaba da bibiyar wannan labari mai cike da tarihi, sihiri da kuma ƙauna*
*For more Imformation Contact me via ****