KARAGAR MULKI

Page 50

by @cwtsumiey19988


KARAGAR MULKI*

    BY

  *CWT-SUMIEY*

*YOTA*

~Page 50

Kacokan Gimbiya Junainah ta maida hankalin ta akan duba ciwon da ya ke  a saman fuskar Yarima Haisam da Harzan ya  jima sa shi,wanda duk a zatonta barci Yariman ya ke.
   "Gimbiya Junainah zan d'an je can baya in dawo na ga wani d'an icce ina son in tsinko ?"
  "Kar ki je ko ina kinga yamma ta fara yi kar wani abun ya same ki a can".
   " Ba abinda zai same ni Uwargijiyata, na dad'e ban ganshi ba, sai yanzu muna kan hanya na ganshi   yanzu zan dawo ba zan jima ba".
   Kuyanga Jazila ta ce tana mai nuna tafi buk'atar ta barta ta je ,"Shikenan ki je amma kar ki dad'e kuma kar ki yi nisa,domin nasan Nurain ya na gab da dawowa zai tambaya ina ki ka tafi kuma kin san ba zai mi shi dad'i ba tunda yana iyakar bakin k'ok'arinsa akanmu".
   "Ba zan jima ba yanzu zan dawo kuma ba abinda zai same ni nayi maki alk'awari",da haka Kuyanga Jazila ta samu ta tafi.
     Ita kuma Gimbiya Junainah ta maida hankalinta akan Yarima Haisam, hannunta ta sake sawa a saman kan shi karo na biyu tana ganin ciwon ,cikin sa'a ya kusa warkewa ba ya Da k'an jiki.
      Da wani irin k'arfi ta ji an rik'i hannunta wanda ba tai zato da tsammani ba har k'aramar k'ara sai da ta saki tana waiyo hannunta,ji ta ke kamar za a tsaga ma ta k'ashin hannun na ta,"Ke wace ce me ki ke yi a nan wurin,wanne tsautsayi ne ya kawo ki har ki ka zauna kusa da shi?".
Itace tambayar da Yarima Haisam ya fara yi mata bayan ya farka daga barci,cikin in'ina ta ce da shi ,"Bbbbbb....Bbbb..ban gane ba ka na nufin ba ka gane ni ba nice fa Gimbiya Junainah kuma ai"......ta Kasa k'arasawa sakamakon shak'ar da ta kaimata,nan da nan ta fara kakari idanuwanta su ka fito waje tamkar za su fad'o k'asa jikin ta sai 'bari ya ke ta na cewa,"Ba ki da hankali ne,kin San kuwa ko shi waye ?".
     Ba tare da ta tsaya ba ta cigaba da cewa,"Har yau har gobe ba ayi wata Mace da ke da zarrar ra'bar ko da inuwarsa ce ba in kyale ta,shi d'in Mijina ne,ba wata mace da zata kusance shi in barta da rai da lafiyarta,domin da ni kad'ai ya dace don ni a ka halicce shi,ba don wata sakaryar mace irin ki ba".
       Duk tana wannan zancen ne shak'e da wuyan Gimbiya Junainah wacce ba abinda ta ke hangowa face lahira tuni ta sadak'ar da yau ne ranar da za ta riski Mahaifinta da ya ke can.
   K'arar saukar icce a gadon bayan Yarima Haisam shine yai sanadiyar jefar da Gimbiya Junainah can gefe ta juyo ta na fuskantar Nurain wanda k'arasowarsa kenan ya riski wannan al'amarin, bai bar Yarima Sadauki ya ja numfashi ko guda d'aya ne  ba ya danne shi ya kai shi k'asa ya had'a hannayensa biyu wuri guda ya d'aure.
"Mene ne haka Nurain ka sa ke ni,kar ka d'aure ni,wacce irin rayuwar ce wannan ,me ya sa ka ke haka ne ?".
" Ban zan kwance ki ba Azela domin tunda na tunkaro wurin na ji kakarinta na san ke ce,ko so ki ke ki kasheta ne ?".
   "Eh kasheta na ke son yi mene ne ya sa ta ke zaune a kusa da shi,waye ya kirata ko ya sa ta da har za ta je kusa da shi k'azama da ita,Ina son in nuna ma ta shi d'in ba irin gama gari ko sauran mutanen da ta saba cin karo da su ba ne ba,don haka ka kwance ni ina son in raunata ta ko in  illata ta wata k'ila zai zame mata darasi ta daina kusantar duk Namijin da ta gani a ko'ina ".
Rasa  mai zai ce da ita Nurain yai sa dai bin Yarima Haisam da kallo  ya ke ,da ya ke a matsayin Azela,gefe guda kuma ga Gimbiya Junainah sai faman  mai da numfashi sama-sams ta ke . 
Tausasa harshe yai ya ce da ita," Haba Azela me ya ke damun ki,kin ko san me ki ke yunk'urin aikatawa kisan kai fa ki ke shirinyi da ban zo ba".....
Cikin zafin rai Azela ta katse shi da cewa, "To sai me idan na kasheta tare da Mijina fa na ganta har ta kai hannu a jikinsa ta na ta'ba shi, ni na rasa wanne irin hukunci ne ya dace da ita hankalina ba zai ta'ba iya kwantawa ba har sai na kai ga ko da zubar ma ta da jini ne",
Ta k'are zancen ta na mai k'ok'arin kwance kanta da ta ga ba za ta iya ba sai ta fara jan jikinta domin ta Isa gare ta.ganin da gaske ta ke so take ta cimma Gimbiya Junainah Nurain ya ce da ita
  " Wanne irin hauka ne haka Azela,wanne irin bak'in kishi ne ki ke nunawa haka,Wai in banda abun ki ina ki ka ta'ba ji ko ganin alak'ar auratayya ta shiga tsakanin Mutum da Aljan,Mutumi da a kullum cikin cutar da shi ki ke ,ta ya hakan za ta kasance in ban da ?".....
     Da kakkausar murya ta dakatar da shi da cewa,"Idan ba ka ta'ba ji ko gani ba akan mu za ka fara,idan kuma ban Aure shi ba to ba wata  'ya mace da za ta mallake shi a doran duniya domin na sha alwashin illata ko ma wace ce,Yarima nawa ne kuma ni ni kad'ai na".
"Ai ko kin sha alwashin banza da wofi,domin ina me tabbatar ma ki da ba abinda za ki iya muna da Maganin ki Allah ya fi k'arfin ki Aljanar banza da wofi kawai".
Nan fa Rikici ko musayar miyau ta 'barke a tsakanin su Nurain na yi itama Azela na yi had'i da k'ok'arin son ganin ta kwance ta riski Gimbiya Junainah wace a tsorace ta ke sai faman 'boyewa a bayan Nurain ta ke.
     Gudu ta ke iya gudu tana waigen bayanta,Iya kacin k'arfinta ta ke gudun amma duk da hakan gani ta ke kamar ba gudu ta ke ba tamkar iska na k'ok'arin maida ta baya haka ta ke gani,firgici,tsoro,d'imuwa tare da kid'ima duk sun bayyana a jiki da fuskarta.
Ganin alamun kamar ta kusa isa zuwa inda su ka yada zango tafara sa ran ta tsira daga mugun abinda ya biyota,ta so ta bud'e murya tai ihu ko ta kira wani daga cikin su amma ina ta kasa,hankali da tunaninta ya rabu gida biyu d'aya na kan su Nurain da ta fara ganinsu d'ayan kuma na ga abinda ya biyo bayanta,daga k'arshema zamewa tai ta fad'i ta fara mirginawa har ta idasa wurin da su ke.
A rud'e Nurain ya idasa indata ke ya na mai tambayar ta lafiya me ya biyota?,Kasa cewa Komi tai sai nuna ma sa hanya da ta ke, jikinta sai faman rawa ya ke ,numfashinta sai kai kawo ya ke,k'irjina sai hawa da sauka ya ke.
  'Daga kan da Nurain zai yi ya hango Damusa tsaye a gabansa sai faman bud'e baki ta ke,da sauri Nurain ya mai da Kuyanga Jazila bayan shi gami da maida dubansa kan Yarima Sadauki da ke kulle ya na ta faman son kwance kansa tare da son isa inda Gimbiya Junainah ta ke ko ta halin k'ak'a ne.
Cikin d'aga murya Nurain ya ce da Gimbiya Junainah, "Ki kula da shi,Kar ki bari ya kwance zan san yanda zan yi da wannan Damusar, da ka ta iya ba shi amma amma a matuk'ar tsorace ta ke dama ga shi ba ta dad'e da dawo daga sabuwar duniyar da Azela ta kai ta ba.
A  matuk'ar haukace wannan Damusar ta yo kansu bakinta har dalalar miyau ya ke,Nurain da iya kacin k'arfin sa ya tare ta suka fara mirgina mirgina-mirgina in ta dannesa shima in tasamu sa'a ya danneta,ko ina ta samu a jikinsa yunk'urin kaimasa cizo ta ke shikuma ya na k'ok'arin karewa ta hanyar rik'e bakinta.
Ta kowacce hanya neman inda zata illata ko raunata shi take,sun kwashi lokaci mai tsawo a haka suna ta fad'uwa da tashi amma bawanda ya sami nasara akan d'an'uwansa cikin sa'a ya samu wani icce ya kaimata duka kwarara guda biyu saitin kanta ba shiri ta fad'i k'asa wanwar,numfashi Nurain ya fara saki gami da juyowa ya ga halin da Gimbiya Junainah su ke a ciki ya nufo inda su ke.
Gaba ki d'ayansu sun duk'ufa akan Yarima Haisam don son gano waye a tare da shi domin sai faman wasa da hankalinsu Azela ta ke sai tayi kamar ta tafi sai ta dowa,hucin numfashin Damusar kawai su ka ji a kusa da su inda kai tsaye ta nufi inda Nurain yake,da wani irin zafin nama Kuyanga Jazila ta shiga tsakanin su da nufin koma me zai faru ya faru da ita,duk yanda Nurain ya so wajen ganin ya ceci Kuyanga Jazila hakan ta gagara domin sai da Damusar nan ta samu nasar sa farantanta ta yagi naman k'afarta ta hagu,a fusace Nurain ya zari 'yar k'aramar wuk'a a k'ugun Yarima Haisam ya nufeta yanda ya taho a fusace haka itama ta taho a matuk'ar fusace, naman cinyar shi ta cafka ta cizgi rabonta ta wurgar da shi can gefe,shi kuma ya samu nasarar kartar fatar jikinta,tana gama had'iye abinda ta samu a jikin Nurain ta nufi inda Gimbiya Junainah ta ke ita da Yarima Sadauki duk da shi yana k'asa a d'aure.
   Ja baya Gimbiya Junainah ta fara a hankali ba tare da tasan me ya kamata ta yi ba,duk wani tunani da basira na kanta sun dakata ba tasan kuma me za ta aikata ba,sannu-sannu ta ke ja da baya haka ita ma Damusar ta ke binta har ta kai ga ta cimma wata bishiya a bayanta,gabad'aya mafarki da kuma burin rayuwarta ne su ka fara zuwan mata a rai ashe dai ba ta da rabon cika su,Ashe dama gajeriyar rayuwa ce da ita,Ashe dama ajalinta ne yai kiranta cikin wannan Dajin, akan idonta ta ga sanda Damusar ta bud'e bakinta ta nuso saitinta,gami da fara gurnani.
Tamkar saukar tsawa ko ta walk'iya haka ya gifta a tsakanin su,Babu wani a cikin su da yansan sanda ya kwance ko ya akai ya kwance kawai dai sunga giftawar shi tamkar Aljani.
Yanda ta bud'e bakinta haka Allah ya ba shi sa'a ya ya kama bakin ya raba shi gida biyu da iyakacin k'arfin sa ,da iyakacin k'ara ko amon muryar wannan Damusar haka take kuwwa da naiman taimako ko agaji,amma hakan bai sa Yarima Haisam ya dakata ba har sai da ya raba kanta gida biyu yana reto a jikin gangar jikinta ,bai sa ke bi ta kanta ba ya nufi inda Gimbiya Junainah ta ke yana kai hannunsa saman kanshi ya tara gashin kansa a tsakiya,da gudunta ta nufi inda ya ke ta na mai fad'awa jikinsa tare da fashewa da kuka.
"Ya Isa haka ki bar kuka ba abinda ya same ki,ki kwantar da hankalin ki kin ji Matana",k'arasowar Nurain da Kuyanga Jazila da su ke  ke jan k'afarsu d'aya ya sa ta d'ago gami da nufar inda su ke.
Sosai ta k'ara k'arfin kukanta sakamakon ganin irin rauni kan da su ke a jikin su,ba k'aramin cizo tai ma Nurain ba don ta kwashe naman wurin sosai,sai faman zubar da jini ya ke har da wani yanka babba a gefan fuskarsa da alama dai da farcenta ta ji masa shi.
Kuyanga Jazila kuwa da sawun farantanta ne kwance a k'afarta sunyi zurfi sosai  ,duk wannan abun da ke faruwa gabad'aya hankalin Yarima Haisam ba ya kan su yana ga wuyan Gimbiya Junainah da ya ganin kamar an shak'e ta,sakamakon duk'awar da tai tana kallon k'afar Kuyanga Jazila  ga sawun hannun ya fita sosai kuma wuyan ya yi jajajur alamun dai ta sha shak'a ne.
Ture Kuyanga Jazila yai da hannu,har tana faɗuwa ƙasa ya na mai cewa,"Matsanan Bera",gami da mik'ar da Gimbiya Junainah  tsaye yasa hannunsa ya na mai ta'ba wurin,"Matana me ya same ki haka na ga kamar an shak'e ki,ko dai wani ne ya ke wa rayuwar ki barazana ban sa ni ba ?".
"Au dama kai ne ?",Nurain ya ce da shi yana daga can zaune ya na k'ok'arin tsaida jinin da ya ke zuba a jikinsa.
"Hmmmm to da wa kai zato  lusarin Namiji,a tunaninka zan bar ma ka Matana a hannunka ne,ka kashe min ita,ka ga  ba don kai na zo ba na so ma ace madadin Naman cinyarka da kan ka d'ungurungum ta cire da na ji dad'i kuma na huta".
Mai da kallonsa yai saitin inda Gimbiya Junainah ta ke ya na cewa da ita," Waye a cikin su yai mi ki haka,a cikinsu ne ko ko wani ne can daban ya aikata ma ki haka ?".
"Azela ce,shed'aniyar banza d'aya daga cikin ku,ita ta aikata hakan a gareta so tai ma ta kasheta gabad'aya".
Nurain ya bashi amsa,kasa cewa komi Harzan yai sai dai ganin Yarima Haisam na shirin fad'uwa k'asa su kai da sauri Gimbiya Junainah ta tare sa su kai k'asa a tare.

*Masoyanaj, littafin KARAGAR MULKI zai kammala kyauta a shafi na 50. Idan kuna son ci gaba da bibiyar wanjnan labari mai cike da tarihi, sihiri da kuma ƙauna*
*For more Imformation Contact me via ****