SHIMFIƊA.
SAIFUDDEEN..!*
(Ba Mutum ba ne)
Wattpad:Jamilaumar315
Mallakar:Janafty❤️
A TRUE LIFE STORY- 50% Fiction
*Da sunan Allah mai Rahma mai jinkai Salati tare da Aminci su tabbata ga Annabin Rahma Annabi muhammad salallahu alaihi wassalam tare da iyalansa da Sahabbansa gabadaya*
SHIMFID'A...
Meyasa Inna da Ya Habibu suka ki yarda da ni ne..?Meyasa suke ikarari da cewa SAIFUDDEEN Ba mutum bane..?
Wata zuciya ta bani amsa da cewa"To in Mutum ne a ina yake MUHIBBA..?Rabon ki da ganin Saifuddeen shekaru wajen goma kenan ammh Tunaninsa bai fita daga ranki ba,in kuma mganar su Inna ba gaskiya ba ne meyasa baki kara ganinsa ba..?Baki san komai a kan sa ba..?baki san kowa na shi ba ballatana abunda ya Danganceshi..?Kai ina nima na fara jin tsoro ko dai ko dai..Saifuddeen da Gaske ba MUTUM BA NE"
***
Kamar wacce aka biyo haka ta fado cikin bedroom din da Mami take ciki ita da kanwarta Hajiya zuwaira cikin wata irin murya mai cike da kuka ta daga takardan hannunta tana fadin" YA SAKE NI..YA SAKE NI..Yaya Saifuddeen ya sakeni na shiga uku na.
Take fada kafin tayi zaman yan bori saman cafet din daya malale bedroom din, Mami dake saman Darduma tana lazimi ta mike a Firgice gabanta na faduwa Hajiya zuwaira data fara barci sama sama kan wani makeken Royal bed din Dake Dakin sai da ta tashi a Firgice gabadayansu suka yi kan Majeeda suna tambayanta me ya faru..?
Ta kara Daga farar takardan dake hannunta tana fadin"Ya sake ni..yace ya sake ni..!
Sai mami ta Dafe kanta tayi baya kamar zata fadi hannayen kanwarta Zuwaira ya tare ta tana fadin"Yaya zulai ki yi a hankali fa"
Mami ta kalleta kafin tace"Na shiga uku zuwaira YARO zai kasheni kwana na bai kare ba..?Jiya fa aka daura masa aure da Majeeda itama ya sake ta kamar yadda ya saki Amira..?
Anya yaro na da lafiya kuwa..?
***
Zaliha..!
Ina zalihar take."
Ummi ta Dago Jajayen Idanuwanta ta Sauke kan Adda Sadiya wacce itama ta Kalleta Cikin wani yanayi kafin ta samu Zarafin mgana Ummin ta mike tana Fadin"Ga su chan sun iso..Abunda nake jira ne bari naje na same su"
Mama zuwaira na sallah tana ta umh uhm da gyaran Murya Ummi bata Saurareta ba kafin Adda Sadiya tayi wani yunkuri Ummi ta Fice da Dogon Hijabinta Dauke da Carbi a Hannunta Fuskarta har ta kumbura Saboda kuka.
Sadiya ta Dafe kanta daya fara sara mata,Daman tasan ai hakan zai Faru,Iya bazata yi shuru ba koda kuwa wannan karon Baffa Hashimu bai yi mgana Majeeda wajenta ta girma duk cikin jikokinta tafi sonta kamar yadda Baffa Hashimun yake Dan lele awajenta.
Bata yi kasa a gwiwa ba ta bi bayan Ummi Mama zuwaira kuma sai Allah Allah take ta idar da Salla ta je Falo saboda tasan Yayar nata nachan duke Dangin Uban Saifuddeen suna kare mata Tanadin da suka saba.
Koda Adda Sadiya ta fito Falon karaf Daidai Lokacin da Inna Atika ke nuna Ummi Tana fadin"Karya take yi iya..Wlh ko Rantsuwa nayi bazan yi kaffara ba Tasan inda Dan iskan yaron nan yake..Tasani ai itace uwarsa sannan in akwai wacce ke zuga Saifuddeen wajen Bijiremana ai itace
Kada ku yarda da Magiyarta da wannan kukan munafuncin data saba Rudar ku dashi."
Ta fada tana jin kamar ta kai ma Ummi Duka wacce ke duke a kasan Saman Cafet din Dake falon inda Iya ke zaune ranta bace tana Faman jijjiga Jiki Baffa Hashimu na gefe ya kasa mgana Baffa Hayatu na zaune kan Hannun Kujeran da Iya ke Zaume Goggo Atika da Daman bata bar komai na Tijaran iya ba,Tana tsaye ta kasa zama tana Faman auna ma Ummi Dake duke tana sharan kwallah gaban Iya harara.
Kafin Sadiya tace wani abu Laala Dasuke leke a Dakin da suke tayi Zaraf ta fito Tana Fadin"Iya mganar gaskiya Ummi fa batasan ina Hamma yake ba..Muma nemansa muke yi."
Tafada idonta kar domin bata da Tsoro.
Ran Iya ya baci ta Dago tana kallonta kafin tayi kyaci Lokaci Daya tana Fadin"Su cin Danko har da su kaza..?
Ke kuma miye naki aciki..?
Da zaki sakomin baki ina mgana.
Kaji min ja"irar yarinya mara kunya.?
Tafada tana kumfar baki ko Tsufanta bata Duba ba,Domin ta tsufa kawai jin Dadi ne ya lullubeta Ammh zata bama Saba"in baya sai dai ganin yanayinta zakasan tun tana matashiyarta ta iya tijara da bala"i.
****
"Shikenan Sunusi naji batunka kuma na amince..Sai dai abu Daya nake so..Wannam auran Saifudden ko yak'i ko ya so bai isa ya tada shi ba..ko wa"adinsa ya wuce sai an kara maida shi..Ko shekara nawa zai yi bai Dawo ba watarana zai zo kuma duk inda yaje ya Dawo Dangin Uwa basu ishesa ba, Dolensa ne mu bashi da yarda zai yi..Hashimu ku tashi mu tafi.."
*****
Goggo Atika ta kurama Saifuddeen ido tana kallonsa kafin tace"Ko dai gaskiya ne kai ma Aljanar ta aureka kamar yadda ta auri musan gidan Alhaji isuhu shekararsa Sitti bai yi aure ba..
Sai iya ta Rude ta fara Salati Tana Fadin"Saifuddeen kardai mganar Atika gaskiya ne..?
Kana da lafiya kuwa..?
Kansa na kasa bai yi mgana ba kadan ya Rage bai yi dariya ba wai Aljanna ta auresa ba bazai manta ba har Ummi tasha tambayansa bai da wannan amsar,amsar kuma da zai gayamusu bai shirya fad'inta ba bazai iya sanar dasu acikin mafarki ne kadai zai iya Saduwa da mace ba, ammh ba"a Zahiri ba mace ko Tsirara zata yi agabansa bazai taba jin komai akanta ba.
Gajiya sukayi da Tambayansu yayi musu shuru yaki mgana Iya ta Fashe da kuka tana Fadin"Allah Sarki muna ta Zargin baiwar Allah Zaliha ashe shi lafiya ce bai da ita..Mun shige su.
Baffa Hashimu yace"Iya to menene mafita..?zamu maida masa da auran majeedan ne yanzu..?
Iya tace"Wani aure Hashimu..? Ana neman Lafiya ai in muka maida masa ita mun kwareta..Sannan yaron nan yafi mu hankali..Muna ta kokarin yi masa aure bamu taba tambayarsa yanayinsa ba, da sai aure yayi nisa ayi ta samun mtsala..Ai yanzu mganar maida aure ba ta Hashimu sai dai ayi mganar Lafiyarsa kawai.
Baffa Hashimu yayi shuru bai yi mgana ba goggo Atika tace"Tab Iya abun fa ba sauki Domin in suka aureka har Abada mutum bashi ba aure.
Iya ta zaro ido Kafin tace"Uban Aljana tayi kad'an ta auremin jika ta hanashi aure..Bata isa ba"
****
"SAI..FF...UUDEEEN....!
Ta fada kamar mai koyon mgana da Sauri ya Dago ya kalleta sai manyan idanuwansa suka shige cikin na Muhibba nan take gabansa ya yanke ya fadi Ras..Wani yar yabi jikinsa A karo na farko daya taba haduwa da macen da ya kalleta sau daya yaji yanayinsa ya sauya yaji bugawar zuciyarsa na kara gudu da Sauri da Sauri fat.Fat.Fat.
Meke shirin faruwa ne..?
Zanen kaddara ne..Haduwar Allah ne ya Tsarata daga wannan Rana Kaddaran Rayuwar Muhibba zata fara sannan Bayannar Boyayyen al"amarin dake tare da Saifuddeen zai bayyana
****
"Abu daya nake so ka tabbatar min kana sonta..Indai kana Sonta zan nema maka auranta"
Saifudeen yayi shuru ya kasa mgana a mganar kawu bai ji wani sauyi ba ko bakinciki ko Farinciki ba sai dai Tambayar ne tayi mai nauyi har sai da kawu ya kara maimaita mai sannan Cikin kasala yace"Eh zan iya zama da ita."
Kawu yace"Shiririta..Zaka iya zama da ita daman ai sai ana son mutum ake zama dashi..Kada ka damu gobe goben zam shiga zarian mu yi mgana da Innar Habibu in sun bamu Dama zan Kira Baffaninka mu taru mu nema maka auranta.
Saifudeen yaji kansa ya sara da karfi Cikin karfin Hali yace"Kawu Ummi tace na bar mganar fa"
Kawu yace"Rabu da ita sai komai ya Daidaita zan je na sameta naji Dalilinta.
Daga haka sukayi sallama Saifudeen ya Sauke waya wani abu na basa mamaki Karo na uku zai sake aure sai dai ya sha bambam da sauran Tunda har gashi ana mganar auransa dashi yanayinsa bai Sauya ba,shi dai bai ji K'i ba bai ji So ba acikin Ransa sai dai yana jin Zumudin zai iya zama da Muhibba ba..Zai iya tabbas zai iya Zama da ita.
****
iska ce mai bala"in karfi ta mamaye Dakin gabadaya Labulan window na kadawa tare da Bugawar glass din Windows din suna Gif Gif kamar zasu cire sannan kofar bedroom din yana Budewa yana Rufewa Bam!bam! Da kunnuwanta take jin komai ammh kuma Idanuwanta kamar an saka Super glue an danne su ta kasa Budewa,Ballatana jikinta da Hannayenta dataji kamar an saka Dutse mai nauyi an danneta bakinta kuma shima kamar an saka mai zare da Allura an dinke mata ta kasa Bude bakinta ballatana ta iya addu"a Sama sama take jin abun sai ya zama na kamar mafarki a mafarki komai ke Faruwa ba a zahiri ba.
Kamar wasa taji kamar wani abu ya fado saman kirjinta Ya daketa da Mugun karfi kafin kuma taji kamar kafafun mage ne a saman kanta tana Takata tun daga samanta har kasanta Lokaci daya kuma ta sake jin wannan gigitattaciyar Dariya acikin kunnuwanta lokaci daya ba"a daina Takata ba Akan kirjinta koma wani irin Hallita ne yake daka Tsalle yana Fado mata Lokaci daya ana Sakin wata Dariya mara Dadin ji da Saurare tana ji jikinta na Faman rawa Zufa na keto mata ammh kuma ko yatsanta ta kasa motsi dashi kamar almara taji an yi sama da gadon da take kai yana lilo a sama Lokaci daya iska taji tana kadawa da karfi har tana jin karan Gadon ta da kuma wardrope din Dake dakin Lokaci daya da madubin dake shake da kayan kwalliya Haka take jin karan Haduwar kwalabe suna bada Sauti Gif! gif! Karan ya Kaure Dakin Tare da Dariyar da bata san daga ina take Fitowa ba sai ya bada wani Sauti na Dabam mara Dadin ji da Saurare
Dum!dum!
Gif!Gif!
Gwaram!Gwaram!
Hif!Hif!
Huhuhu!Huhuhu!
****
DA asuba ma da ta tashi ita ta tashe shi,kin tashi yayi ya koma barci kasala bata sake sa ba,Ganin haka yasa ta janye bargon da ya shige aciki yana juyowa kafin yayi mgana ta rigasa da cewa" A cikin alamomin Munafuki akwai rashin Samun Sallar asuba da isha"i acikin jam"insu"
Tana gama Fadin haka ta sakar mai bargonsa ta juya ta tada sallar.
Ya dade yana kallonta yau ma kalamanta sun gama kashe mai jiki kenan shima Munafuki ne?tunda bazai iya Cewa yaushe da yaushe ne yake samun Sallar asuba acikin jam"i ba.
Tana sallar ya tashi ya shiga Tiolet ya Dauro alwala yazo ya sauya riga ya saka Farar jallabiya ya fice zuwa masallaci duk da lokacin ma an Tada sallah ita kuma tana Idarwa Sai tayi azkar sannan ta mike ta gyara gadon ta kwashe Filon da Blanket din nasa ta ninke ta aza mai bisa gado ta fice Kitchen ta iske Ummi da Zeeha suna aiki bayan sun gaisa taso ta karbi Firan Doyan hannun Ummi ta hanata Cikin Fara"arta take fadin"Kinga Muhibba bar shi maza kije ki shirya Yaro ya ce min da wuri zaku tafi yana da shiga Office da Safanan."
Muhibba bata yi mamaki ba sanin Daman ai ba komai yake fada mata ba Sai kawai ta juya ta koma Dakin Ta Fara Sauri Sauri ta shirya kafin ya Dawo kayan da zatayi amfani Dashi ta Dauko ta zube su kan gado ta Daura babban Towel din Da ta gani acikin Tiolet din ta shiga wanka har ga Allah bata san ya Dawo ba ta saki jiki Sanin sai wajen bakwai na Safe yake shigowa shiyasa ta fito kanta Tsaye har sai da ta kawo tsakiyar Falon Sannan ta gansa Tsaye ya juya baya yana mgana a waya da wani irin Uban Sauri ta juya zata koma Tiolet din kafarta sai ta Bige kujeran madubi sai ta Duke tana Fadin"Wash Innata..!
Sai alokacin yasan ta fito ya juyo a Hankali Lokaci daya yana Sauke wayar daga kunnensa karaf ta Dago kanta suka Hada ido hudu gabadaya Jikinta yana Bude ne Towel din iyakarsa Rabin Cinyarta gashi ta Duka hatta Shatin mamanta ana gani.
Jikinta sai yafara rawa Saboda kaifaffun idanuwansa da ya kasa Dauke su daga kanta kamar mayen karfe haka yaji yana jansa wajen kallonta Kirjinsa na bugawa wani Irin Feeling din da bai taba ji a kan mace a Farke acikin Hayyacinsa ba,yaji yana Tasomai Shiyasa ya kasa Daina kallon kowani kusurwa na jikinta Jikinsa na wani irin Yim..Yam..!
Kamar ana mai susa haka yake ji har Tafin Kafarsa na Motsi.
Ganin haka yasa ta dukar da kanta Jikinta na rawa ta mike duk da Kafanta na mata zafi haka ta juya tana Dingishi gudu gudu ta koma Cikin Tiolet din gabadaya albarkatun bayanta na Hadewa suna kuma Rabe kansu sai da ta shige karar Rufe Kofar Tiolet din yasa ya Sauke wani Gwaron Numfashi"Uhmmmm!"
Kamar irin wanda abu ya sarkeshi haka yaji iskar D'akin tamai kad'an Dakyar yake iya Shakan Numfashi Shiyasa shima ya Fice Daga Dakin da Sauri yana Dafe kansa dayaji ya Saramai
****
Fitowar su kenan Daga Meeting da His Excellency a office dinsa ya bar duka wayoyinsa yana komawa bai bi ta kan wayoyin ba sai ya fara duba Fayel din Daukan malaman da zasu sake yi a Jahar ta kaduna Sai yaga wayarsa na Haske a kasalace ya Dago wayar sunan Ummi daya gani Sai da gabansa ya Fadi Ras haka kurum yaji Tashin Hankalin da bai san Dalilinsa ba.,Da Hanzari ya Daga kiran Da Fadin"Ummi ina kwana."
Dagachan bangaran cikin wani yanayi Ummi tace"Kana Ina ne..?
Kai tsaye yace"Ina kaduna Ummi wani abu ne ya faru..?
Sai da ta sauke ajiyar rai sannan tace"Eh wani abu tabbas ya faru ammh ba"anan ba a chan zaria ne.
Da Hanzari ya mike da wani irin Firgici Sai da ya Ture Takardun Gabansa suka zube bai sani ba acikin ransa ya ambaci sunanta "Muhi"
A fili kuma cikin wani yanayi yace"Muhi Ummi me ya faru da ita..?
Ummi tace"Ka kwantar da Hankalinka nima yanzu Innar Habibu ta kirani take gayamin jiya basu runtsa Da Daddare Muhibba ta balle ta gudo gida,Sai kuka take da ihu tana Zabura tana Surutai da Sambatu."
Kai ya Dafe cikin mamaki kafin yace"Me kenan Ummi..?
Cikin Natsuwa tace"Abun kamar GAMO tayi yaro."
Gidan nan naku ina Tunanin akwai aljanu ni a Tunanina ita kuma Innar Habibu tace aljanin nan nata mai zuwa mata da Suffarka ne ya ke neman Razanata Saboda ya hanata zaman aure"
Ba wani jin Ummi yake sosai ba Shi ba ya,ce bai aminta da Aljanu bane har yanzu yasan akwai su ammh Siddabarun su ne bai sani ba Cikin Sautin muryansa yace"Yanzu ta na Ina..?
Ummi tace"Tana chan gidansu an kira malamin nan da yasan Laluran ita Muhibban suna kanta suna mata Rukiya nima gobe ina tafe naga Halin da ake ciki"
Bai gama jin bayani Ummi ba ya katse kiran saboda Tsabar Rudewa kadan ya Rage ya fadi wajen fita daga Office dinsa.
*****
Gani yake kamar Bama baya Sauri Kafin su iso zaria Bai san adadin Zagin daya riga kunduma su bama ba gani yake kamar basu taka motar dakyau ba Domin bai saba Tukin babban Hanya da sai ya sauke su ya Tuka kansa kila sai ya ma isa a kan Lokaci.
Motar bata gama Tsayawa a kofar gidan su Muhibba ba ya Balle murfin mota ya Daka Tsalle ya fice yau ko neman izini ko sallama haka ya Fado gidan da Bakaken Takalminsa Rufaffu bakake na Fata ya fada Dakin kawai sai dai ganinsa sukayi Tsaye a kansu Wurga ido ya dinga yi ya dai ga Inna da Ya Habibu sai Anty Habiba sai Wani malami da D'alibansa suna zaune wacce suka zagaye ya kai kallonsa sai da yaji kamar zai mutu Muhi dinsa ya gani Gardawan maza Uku su Dannenta wani na mata karatu a kunnenta wani na Uban Fesa mata ruwa kamar mahaukaciya.
Wani irin Sufa yayi sai gashi A gabansu Da mugun Hanzari ya saka Kafa ya shure dayan da ke rike da ita Sauran suna ganin haka suka Saketa Muhibba dake kuka ka shirban ta kyalla ido ta hangosa ai sai ta mike da wani irin gudu da kuka ta Nufesa ta Fada Jikinsa Cikin kyarma abun takaici kanta ba Dankwali ta kusa ma yaye Sikat din jikinta..
Karfaffan riko yayi mata kuka take kamar ranta zai fita cikin Fitan Hayyaci take fadin"Saif zata zata Kashe ni..Ka tafi dani ka boye ni"
Cikin tashin Hankali ya riketa fadi yake"Gani nan muhi..Ba abunda zai faru dake ni SAIFUDDEEN garkuwanki ne"
Mallam Haruna bai dakata ba ya cigaba da karatunsa cikin suratul Jinni Lokaci daya wani al"amajiransa ya watsa wani mgani acikin Rushin wuta dake cikin kasko a gabansu nan da nan Hayaki mara Dadi ya Turnike dakin dukkansu suka Fara Tari Saifudden yaji kansa na juyawa ganin yadda Muhi ke neman sikewa yasa yayi Fatali da Kaskon da takalminsa yaje ya Daki garun dakin ya tarwatse wuta yayi nasa gefen Mutane ma sukayi nasu barayin cikin tashin Hankali.
Inna Dake kuka ka shirban na ganin Halin da Muhibba ke ciki ta kasa mgana Ya Habibu ne ke fadin"Kayi a hankali fa"
Jajayen idanuwansa ya watsa ma mallam Haruna kafin yace"Mahaukaciya kuka mai da min mata..?wannan hayakin ai shi kan shi Cuta ne kada ku kara matsowa kusa da Matata ba in ba haka zan tarwataa komai yanzu nan"
Yadda yake mgana yasa ba wanda ya kulasa har ya Daga Muhibba cak suka fice Daga Dakin da ita Inna zatayi mgana Mallam Haruna ya Daga mata yana fadin"kyale shi..yanzu na Fahimci wani abu koma meke Faruwa yana da karfaffan alaqa da shi mijin nata"
****
Kallo Daya mallam Surajo yayi ma Muhibba bai kara ba sai dai ya D'aga ido ya kalli Saifudden kallo na sosai da sai da ya Tsargu cikin muryansa mai Taushi yace"Bawan Allah ya sunan ka?
Saifuddeen yace"Saifuddeen"
Gabansa na Faduwa Fat!Fat!Mallam Surajo ya murmusa kafin yace"Cikakken sunanka nake so naji"
Saifuddeen ya Runtse ido kafin yace"Dr.Saifuddeen Conel.Salahudden Lere"
Jinjina kai yayi bai kara mgana ba Inna da Ummi suka kalli juna Kawu ya kasa Hakuri ya gyara zama zai yi mgana kenan ya Daga mai Hannu Lokaci daya yana fadin"Ba sai kayi tambaya ba zan amsa muku tarin tambayoyin ku"
Sai da ya kara natsuwa sannan ya Dago kansa yana Fadin"Ba aljanu ajikin wannan yarinyar taku..Sai dai Naga wani al"amari ajikin wannan bawan Allah nan na kusa da ita"
Gabadaya sai kallo ya koma kan Saifuddeen cikin mamaki Ummi tace"Wani al"amari ne Mallam..?
Mirmishi yayi kafin yace"Zata bayyana kanta yanzu nan kun zo inda Aljani bai isa ya boye kansa ba komin karfinsa komin ikonsa..
Zata bayyana.
Zata fallasa komai...
Abubuwa zasu warware kansu.
Duk ita take aikata komai ba"a sani ba muguwa ce sannan bakar Kafura ce ita ta kusa haukata wannan yarinyar ba Domin ita din mai yawan Ibada bace da Tuni ta HAUKATA TA!
****
Waye kai..?
Wata kakkausar murya tayi mgana"Sunana SAIFUDDEEN Kuma ni ba Mutum ba ne ina Daga cikin jinsun Aljanu"
Miye hadin ka da wannan baiwar Allah..?me yasa kake Bibiyarta..?
Ko zaka cutar da ita ne..?
Shuru dakin ya Dauka na wani Lokaci kafin wata iska ta taso ta Tirnike Dakin kamar Hayaki Hatta da Tafin Hannunka baka iya gani Cikin abun da bai fi mintina goma ba sai Dakin ya washe gabadaya su Ummi sun Tsorata Adda Sadiya jikin Mijinta ta makale tana makyarkyata shi kan shi Mujaheed din jikinsa rawa yake yi sai dai ya Daure ne kada Adda Sadiya ta Fahimci ya Tsorata.
Abun da ya bama kowa mamaki Daya sa suka Zabura gabadayan su ban da Saifuddeen dake zaune gaban Mallam Surajo shi da Muhibba Yana kamkame da ita kamar wani zai kwace mishi ita.
Cikin wata irin murya wacce daga jinta sai jikinka ya yi sanyi in ma bai Fara rawa ba yace"Ni ba mai cutarwa bane..Amana ce Sannan Alaqa ce mai Girma Tsakanin Mahaifina Abu Gaddaz da mahaifin Muhibba tun Lokacin yana Raye..Aminci ne da Girman alkawari Tsakanina da wannan Ahalin"
Zabura Muhibba tayi Daga jikin Saifuddeen idanuwanta na kallon sa Ta nuna sa da Hannu cikin Rawar murya tace"SAI..F..DDEE...NN...!
Sai ta juya ta kalli na kusa da ita kawai sai tayi luu ta Fado jikinsa a Sume.
Madallah da mutanen kirki Madallah da mutanen da suka san karamci, madallah da mutane masu kima da Daraja ina mgana ne kan Al"ummar da alherin su ya Zagaye Rayuwata gabadaya,wato masoya na da sune Silar Mirmishi na da Nasara ta nagode kwarai bisa soyayyarku da kaunarku kan duka Littafaina Ina godiya bisa yadda kuke tare dani a koda yaushe Allah ya saka muku da alheri ya bar zumunci Allah ya Ribanya arzikin ku Allah ya kara Wadata da kwanciyar Hankali Janafty ta gode matuka kuma Godiyarta bazata taba karewa ba, Allah ya Hada Fuskokin mu a gidan aljannah gabadaya Nagode Nagode