SAIFUDEEN

03

by @jamilaumarjanafty

SAIFUDDEEN

(Ba mutum ba ne)

Wattpad:JamilaUmar315

Mallakar:Janafty♥️

Ga wadan'da ke amfani da Wattpad su yi following din Anty Habiba Iman ikra domin samun Labaranta masu Dadi da Ma'ana akan@habibaiman1986

Amnaf_sudanese _collection

Tana saida original laffaya kala daban daban daga Sudan kama daga na Amare da Kuma casual muna da available a Nigeria kuma Muna aikawa daga Sudan Zuwa Nigeria ko'ina a fadin Jahohi talatin da shida har ila yau dai akwai humra da turarrukka sadidan na matan aure daga Sudan,ba fa anan kada'i muka tsaya ba Muna saida kayan lalle akan sari da Rahusa da kuma siyan Daya,akwai mayuka da dilka da kayan gyaran jiki na ainahin ba Mix ba, wadan'da zasu fitar Miki da fatar ki tas ba bleaching fuskarki tayi haske tayi walwal kina kyalkyali and duk abunda kikeso a Sudan Muna kawo Miki shi har gda Nigeria Amnaf Sudanese collaction ba abunda bama saidawa kama daga kayan kamshin jiki na kaya da na fata +249923097401

🅿️3

misalin wajen biyu saura na Rana bayan Azahar sannan Ya sunusi ya iso Shi da D'ansa Isma"il da Inna iyami data kasance kamar uwa a wajensu saboda da Wanda ya Haifi mahaifinsu da ita ubansu Daya shiyasa bayan dawowarsu gaya da zama Kawu sunusi ya Daukota suna zaune tare tunda duk yan"uwan sunkare sai wadanda ba"a rasa ba.

Su iya suna nan basu jirka daga inda suke ba har gwara ma Baffa Hashimu sun je sun yi sallah sun dawo kafin isowar su Ya sunusin..

Koda suka iso Su Ummi suna cikin bedroom basu sake lekowa ba sai da sukaji Tashin muryan yayan nasu sannan suka Fito tunda ya iso.

Gaban iya suka sameshi ya baza Babban Rigansa kansa a kasa cikin Ladabi da Alhini Bayan sun gama hannu da su Baffa Hashimu ya kalli Iya Cikin Dattakonsa yace"Iya ashe abunda kuma ya faru kenan..?

Da Safan nan Zuwaira ta Kirani take Fadamin abunda kuka wayi gari dashi..Ban ji Dadi ba matuka Hankalina ya tashi,har nama fita na koma gida Isma"il makaranta yaso ya koma yau ni na Hanasa saboda ya Tukani zuwa Lere Inna iyami najin abunda ya Faru tace zata Biyo mu zo muji abunda ke Faruwa."

Yafada cikin bayyana jimaminsa Inna Iyami na zaune saman kujera tana gyara Lullubinta tace"Abu kam bai yi Dadi ba Sunusi..yaron nan bai kyauta ba ammh ni na fara Tunanin baza"a Tashi Tsaye ba kuwa..?

Irin wannan al"amarin sai kuga da Sa hannun Junnu aciki."

Iya data gama jinsu ta tabe baki kafin tace"Ba wani junnu Hajiya..Ba kowa ke sakashi yi mana rashin D'a ba sai Uwarsa Zaliha,Sunusi Ina ganin girmanka matuka domin tun shekarun baya saboda Ladabinka da Tausasawarka yasa da Salahudden ya kawomin Zaliha a matsayin matarsa nayi Hakuri na karbeta,To yanzu ma saboda kai ne nace zan jira na Saurare ka ammh Wlh da na Rantse ko ni ko Zaliha acikin gidan nan ita da kanwarta gatanan zuwaira sai abunda ta manta na ci mana Zarafi."

Iya ta karishe Fada tana Sharan hawaye da Haban zaninta Ya sunusi ya Rankwafa yana Fadin"Ashsh.Abu bai yi Dadi ba..Don Allah Iya kiyi Hakuri..Ina mai baki Hakuri akan wannan lamarin."

Iya batayi mgana ba Baffa Hashimu ne yace"Nifa duk bama wannan ba..?

Saifudden nake son gani yanzu agaba na kila sai na Huce Daga Takaicin Daya kunsamin."

Ya sunusi ya kallesa cikin wani yanayi lamarin bai mai Dadi ba ya juya yana kallon Ummi da Mama Zuwaira Dake gefen Inna iyami,su sadiya suna ciki basu fito ba, Isma"il ya shiga ya Dauke musu hankali da Hira Domin gaye ne sannan dan Fafa ne sannan dan Jami"a ne dake karatu a jami"ar Bayero kano.

Gaishesa suka farayi Ya amsa cikin wani yanayin bacin rai kafin yace"Zuwaira me nake jin kin aikata ne haka..?.

Ta Dago kanta da niyar mgana ya Dakatar da ita da Hannu Cikin bacin rai yace"Juya ki bata Hakuri ko bakomai ki Daraja girmanta..Sannan ki Mutumta zuru"ar Dake Tsskaninta da yar"uwanki nasha miki Fada bana son Haka Zuwaira.."

Ranta bai so ba ta juya kanta na kasa tace ma Iya"Kiyi Hakuri.."

Daganan ta juya kanta takaici na cinta ina Laifinta a wannan mganar..?

Ba domin Ya Sunusi kamar Uba suka Daukesa ba,Bata ga mai sata bama wannan Tsohuwar Hakuri ba.

Ummi kuma kanta na kasa tana sharan kwallah Inna iyami tace"Ai hakuri duka za"ayi..Abunda Hakurin nan bai bamu ba to rashinsa fa bazai bamu ba.

Iya ta jinjina kai tana Fadin"Hakane..Tunda kuka saka baki naji zuciyata tayi sanyi..yanzu sai muje ga mafitan domin bazan Dauki wannan iskancin Wajen Saifu ba..Wato yayi na Farko yaji Dadi shine yanzu ya kara jiya jiya Daga kai yarinya har ya sakota..?

Gata chan ita da uwarta da Danginta suna ta famam koke wazai ce su bari..?

Ai abun kuka ne ya same su dole su koka."

Ya Sunusi ya gyara zama yana Fadin"Sosai Iya gaskiya Saifudddeen bai kyauta ba..Ya kuma shammace mu domin jiyan nan muna tare dashi bai nuna komai ba Har nasiha nayi mai fa ya nuna ya Dauka ban taba Zaton zai aikata Hakan ba."

Mama zuwaira ta karkace kai tana Fadin"To ita kanta ya zalihan fa..?

Jiya kamar zata ari baki wajen yima Saifu Fada kuma ya nuna yaji,Sai dai kasan ita Uwa ko yaya D'anta yayi abun Tir sai ace laifinta ne..."

Kallon da Ya sunusi ya bita dashi ne yasa ta kasa karisa mganarta goggo Atika ta yi kyafci kafin tace"Indai zata shiga mganar da ba nata ba nima kuwa ashe zamln iya shiga.

Inna iyami ta kalli Mama zuwaira tana Fadin"Kul zuwaira kada na kara jin bakin ki anan wajen"

Dole ta koma tayi shuru tana maida ma Atika martanin Hararanta.

Ya sunusi ya kalli Baffa Hashimu yana Fadin"Kun samu wayar shi Saifudden din..?

Baffa Hashimu yace"Ina..Tun Safe muke kiransa a kashe wayarsa."

Ya sunusi yace"Nima na kirasa bayan mun yi mgana da zuwaira a kashe..Ke Zaliha jiya kafin ya bar wajen ki me ya Fada miki..?

Ummi kanta na kasa tana sharam kwallah tace"Wlh Allah d'aya Ya sunusi bai fadamin komai ba bai kuma nuna min wani abu ba.Mun rabu akan Sai da safe cike da Fatan alheri na uwa da abunda ta Haifa..Ammh wlh bansam komai ba."

Sai kuka wiwi Ya sunusi ya jinjina kai yana Fadin"Ya isa Zaliha..ya isa haka..!

Sai ta Saussauta kukanta Baffa Hashimu ya kallah kafin yace"Ya Rubuta takarda ne shi Saifun..?

Ba musu Baffa Hashimu ya Saka hannu a aljihu ya dauko wata Farar Takarda ya mikama Ya sunusi shi kuma ya karba ya bude ya karanta ai duk wanda yasan Saifuddeen da wannan Hand writting din ya san sa sannan Har da karin shedar saka Hannunsa.

Yana gama karanta Takardan yace"Bai kyauta ba sam..Sai dai naji Dadin da ba Saki uku bane saki Daya ne akwai yuyuwar zamu iya samun gyara."

Baffa Hashimu yace"Ta ina..?

Yaya Sunusi yace"Hakuri zamu taru muyi yanzu saboda bamu da tacewa Tunda Saifuddem bashi anan wajen..Ni kaina nayi ta nemansa ban Samesa ba,Kenan duk abunda zamu yanke ko mu Tattauna bai da amfani yanzu Dole sai in yana nan wajen.."

Baffa Hayatu ne yayi mgana yanzu yana Fadin"Ai naji ita Sadiya tana Fadin mijinta yaje chan gidan gwamnati ya samu suna taro da gwamna kuma yana da yakinin shi Saifuddeen zai je taron a kirasa aji indan sun hadu.

Ya Sunusi yace"To..To ai bansani bane..Ke Zuwaira haka akayi..?

Kai ta dagamai da Sauri yace"Kiramin Sadiyar..!

Ba musu ta mike ta shiga Cikin Mintina kadan sai gata ita da Sadiya ta Zube gaban Ya sunusi tana Fadin"Sannu da zuwa kawu..ya Hanya..?

Ya amsa mata cikin Sakewa ta juya tana gaida Inna Iyami itama ta amsa Kafin Ya Sunusi yace"Kin yi mgana da Megidan ki kan Saifudden ko..?

Ta daga kanta cikin,ladabi Ya sunusi yace"To kun sake mgana dashi ko sun hadu..?

Sadiya tace"Mun rabu zai kirani in ya samu ganinsa ammh har yanzu bai kira din ba."

Ya sunusi bai yi mgana ba ya karkace ya Fiddo wayarsa ya mikama Sadiya yana Fadin"Zaki ga Mujaheed kiramin shi.

Ba musu ta karba bata tsaya ma neman suna ba ta rattaba lambar Saboda ai yana kanta sai gata ta fito sai ta kira masa,Kiran har ya katse bai Dauka ba Sadiya ta kallesa tana Fadin"Kawu bai Dauki kiran ba.

Ya Sunusi yace"Baya Daukan kirana..Sai dai nasan zai kira Daga baya."

Ko gama rufe baki bai yi ba wayarsa ta fara kara Da Sauri Sadiya tace"Shi ne kawu..

Kai ya jinjina mata kafin yace"Daga kiran ki saka ta a amsa kuwwa."

Haka kuwa tayi ta Daga ta sanyata Cikin Speaker ta mika ma kawu ya amsa Lokaci Daya yana amsa sallamar Mujaheed bayan gaisuwa da Tambayan aiki kawu yace"Mujaheed gani na dawo lere saboda matsalan Dan"uwanka..Ko kun hadu dashi..?

Mujaheed Dagachan bangaran cikin Office dinsa yace"A"a bamu hadu ba kawu..koda na koma Gidan gwamnati Jami"an tsaro sun tabbatar min da an gama meeting din,sannan banda Tabbacin ko Saifudden yazo...Sannan naje har Office dinsa Sakaransa ya tabbatar min da yau bai shigo Office ba."

Ya Sunusi ya jinjina kai kafin yace"Shikenan mujaheed ku kyalesa duk inda yake yana lafiya..Sannan zai Dawo kamar yadda ya tafi da kafarsa."

Daga haka sukayi sallama ya sunusi ya kalli su Iya Cikin wani yanayi kafin yace"Ku na dai ji nayi waya da Dan"uwansa Mujaheed..mganar gaskiya Saifuddeen yasan yayi laifi nasan bazai yarda mu same sa ba..Sai dai ina kyautata zaton zai Tako nan da Kafarsa kamar yadda ya tafi..Don Allah Iya kuyi hakuri wlh duk ba Laifin mu bane hakan ta faru..Sai dai hali irin na yaran wannan zamanin da basa gudun mgana akan iyayansu ammh nasan Halin Zaliha sam bazata saka Saifudden ya aikata hakan ba,Ba kuma domin ina kareta ba."

Shuru Falon ya Dauka Domin Ya sunusi Allah ya basa baiwar iya Sarrafa kalamai ko agaban dubban jama"a duk yadda suka kai ga Taurin kai kalamsa na Sarrafasu Kuma ance shima gada yayi wajen mahaifinsu haka yake wajen iya Sarrafa Harshe uwa uba kuma Ummi ta Dade tana kallon Wannan halin wajen Saifudden ko yaya ya kai ga bata maka rai da kun Hadu ya fara maka ladabinsa da kalamansa sai kaji yayi maka kwarjini..to hakan ce ta faru da su Iya Tuni kalaman Ya sunusi ya sanyaya musu jiki matuka har Iya taji ta Sauka Daga Fushinta cikin Saukowa tace"Shikenan Sunusi naji batunka kuma na amince..Sai dai abu Daya nake so..Wannam auran Saifudden ko yaki ko ya so bai isa ya tada shi ba..ko wa"adinsa ya wuce sai an kara maidashi..Ko shekara nawa zai yi bai Dawo ba watarana zai zo kuma duk inda yaje ya Dawo Dangin Uwa basu ishesa ba Dolensa ne mu bashi da yarda zai yi..Hashimu ku tashi mu tafi.."

Daga haka ta mike Ya sunusi nata yi mata godiya Ummi ta Dago kanta da Idanuwanta da suka kumbura tace"Iya zamu bi Ya sunusi zuwa Gaya Dagachan zamu koma Abuja.

Ya sunusi yace"Ai zaku shiga kuyi sallama Zaliha kafin mu mika hanya..

Iya ta jinjina kai kafin tace"Allah ya Tsare.

Daga haka tayi gaba Atika tabi bayanta Su Baffa Hashimu kuma sai da suka tsaya sukayi musabaha da Ya Sunusi kafin su fice suna Fita Mama Zuwaira tayi Tsaki kafin tace"Aikin banza aini ban so su hakura ba sai naga yadda zasu yi.

Inna iyami ce tace"Ke zuwaira wai yaushe zaki girma ne..?

Ya sunusi yace"Ki kyaleta Inna sai na kara Daura mata aure tukunna zatayi Hankali"

Jin haka yasa Mama Zuwaira shiga Taitayinta domin tun bayan Rasuwar mahaifinsu Mujaheed taki aure,Duk da Ya sunusi yaso tayi auran,tunda har wani abokinsa anan Gaya yaso ta taki amincewa,Da farko a kano take zaune Gidan mijinta tunda dan kano ne,Daga baya ne Ya sunisu bai yarda ba Dole ta Dawo gabansa agidansa Dake gaya ta zauna,gidan su na kano kuma Daman gadon Mujaheed ne da Saudat.

Ya sunusi Ummi ya shiga yima Fada da Nasiha yana fadin"Ke komai na kuka ne Zaliha..?

Kina wannan kukan Dafi ne kan Saifuddeen an san da bacin rai ammh Sai ki Daure ma ranki kada ki kara yayyafama abun kuma Fetir..Ki yi hakuri komai zai wuce."

Kan Ummi na kasa tace"Yaya Tozarci ne bana so..Shi kuma Yaron nan ke kokaron jawomin koda yaushe.

Ya sunusi yace"Bai ma kamata ki Damu ba..Shi da Dangin Ubansa ne ina ruwanki aciki sanda akayi na yarinyar ta Farko da suka auramai Tunda yazo yayi mgana dasu kin kara jin tashin zencen..?

Kin so ma ki bata Hawayem ki ne in da Sabo yaci ki saba da irin wadanan Zaliha jiya ai ba yau ba."

Dole Ummi ta Hadiye Damuwarta Tun ma ba da Ya sunusi dayace In bakinta ya kama Saifudden ita ke da Asara ba Dangin su iya ba jin haka yasa ta Fara Istigifari aranta ta furta ta yafe ma yaro Duniya da Lahira.

Basu zauna ba,Dayake duk sun yi Sallar su su Laala suka fito Falo suka gaida kawu ya amsa yana tambayansu makaranta suka amsa da mai Lafiya lau,Isma"il Daya gani acikin su ne ya kalle sa kafin yace"Kai fa baka girma..

Su Saudat din ne kawayen naka yanzu.?

Isma"il yayi Dariya kafin yace"Abba haba ai ana Togeder..!

Gabadaya suka saka Dariya sanin Halinsa mai bakwarci sa"an Adda Sadiya ne shiyasa suke kwamawa.

Cikin Lokaci kadan suka gama Hada kayan su suka shirya Kayan abincin da suka zo dashi Ummu tace a mika Babban gidan su Saifudden Mama Zuwaira tace a saka amota su tafi dashi Gaya da dai amika ma su Iya Dole Ummi ta kyaleta suka Dora komai amota Daman Ummi tazo da Direbanta Daga Abuja ita dasu Laala Ita kuma Adda Sadiya tare da Mijinta suka zo da Saudat da taje yi musu hutu,shi ya bar su nan ya koma kaduna Saboda aikinsa sai ta yanke shawaran Bin motar kawu kawai tunda Mama zuwaira ta su Ummi zata shiga.

Sun shiga Ainihin Babban gidansu Saifudden,inda nan ne Iya ke zaune har da su Baffa Hashimu da basu fita agidan ba har Lokacin Dangin mahaifiyar Majeeda suna faman koke koke da su Ummi suka shiga suna ta sallama sukayi banza dasu Majeeda kuma sai da aka zo aka saka mata Drip aka mata allura haka take ta uban kuka kamar mahaukaciya,Daman Ummi ce dasu Sadiya suka shiga Mama zuwaira Mota ta shige taki fitowa domin batayi niyar shiga ba kada ma taje Ranta ya baci Wani abun ya faru..

Har Shashen Iya suka shiga suka mata Sallama ta amsa Kadahan Kadahan su goggo Atika kuma tana ta Habaici Ummi dai bata tanka su ba har suka fito nan suka hadu da Amira yarinyar diyar Kanin Iya ne da aka aiura ma Yaro da Farko ya saketa har ta sake wani auran ta Haihu da Fara"a suka gaisa da Ummi suna mgana Da Sadiya Dake kawarta ce,in tazo lere suna Haduwa Tunda itama Amiran kusan wajen Iyan tatashi anan lere.

Da kafa sukaje tunda ai gidan ba Nisa taku ne kadan,Suna fitowa suka shisshiga mota bayan sun kulle gidansu Dayake Mallakin su ita da ya"yanta yaro da Sadiya.

Karfe uku da wani abu suka Dauki Hanyar gaya amotocin nasu Biyu tasu Ummi ce agaba sai ta kawu abaya wanda Isma"il ke tukawa suna Tafe yana Faman Dannan waya sai da Kawu ya kwaceta aka samu Lafiya Sadiya nata mai Dariya ya shaka yayi Fam kamar zai fashe.

Saboda kawu ne yasa basu yi gudu sosai ba sai wajen Biyar suka shigo gaya,Motocin su suka yada Zango a Haraban gidan Ya sunusi ginin da ne ammh yaji kwaskwariman zamani.

Yaran suna jin Dirin mota suka fito suna Murnan ga Mama zuwaira ga Ummi ga su Laala Dayake yana da yara Kanana Umma karama Dake Amarya itace kusan haihuwan karshe karshe.

Kafin su isa cikin gidan kayan su sun isa suna shiga matan Ya sunusi guda Biyu Umma karama da Umma Babba suka Tarbesu Cikin Fara"a,Dayake ita Umma Babba jiyan da Ya sunusi zai je Daurin auranta tare sukaje suka Dawo Umma Karama ce bata samu zuwa ba saboda gida da kuma yara.

Su Laala kuma sun Hade da su Suwaiba ya'yan kawu har sun jasu Dakinsu su Ummi kuma suka Baje afalo ana gaisawa da yima juna jajen Abunda ya Faru kawu sunusi Shashensa ya wuce kai Tsaye yayi wanka ya Huta Isma"il kuwa sai Faman rokon Mama zuwaira da Inna iyami yake su saka baki Kawu ya bashi Wayarsa Ummi nayi musu Dariya.

Daganan Ummi Dakin Mama zuwaira ta sauka tayi wanka tayi sallah Sannan sukaci abinci Sadiya kuma Dakin Umma karama Daman take Sauka tana chan yaran kuma suna Tare da Suwaiba,har Dare gidan cike suna ta Farimciki kamar ba abunda ya Faru Dayake kawu ya"yansa sun fi yawa mata mazansa uku ne Datti ne babba sai Mudanssir shi yana cikin kano chan yake aiki da Hukumar Kidaya ta kasa reshen Jahar kano yana chan da matarsa Datti dai dake babba bai yi aure ba Har yanzu yana Azare yana aiki ta Bauchi Dan Sanda ne.

Dayake Yaya sunusi Sana"ar Fatauci Dabobbi yake yi Daga arewa zuwa gudu ko da ya"ya suka girma bai daina kasuwancin ba tun zuwansu gaya Allah ya Hadasa da marigayi Bello wanda shi lak'abinsa mai Rago ne shima Sana"ar gidansu ce Fataucin Dabbobin bazai taba mantawa dashi ba, Domin shine silar arzikinsa ya Rasu tun shekaru goma da suka gabata Sai dai iyalansa suna Zaria,Dayake kafin Rasuwarsa ya bar Gaya ya koma Zaria Saboda Fataucinsa yafi karfi achan sai dai suna zumunci da iyalan nasa yana aika musu da Alheri sannan in wani abu ya tashi yana zuwa shi da matansa suma in wani abu ya tashi na Murna ko Jaje Innar Habibu da shi kanshi Habibin suna zuwa.

*******

Saifudden da ya san Tabbas Mujaheed zai nemesa bai yarda yaje Office ko Gidansa ba Daga gidan gwamnati Restaurant yaje yaci abinci sannan yaje ya kama Daga cikin manyan Hotel din Dake kaduna ya kama Daki yayi kwanciyarsa Daman wayoyinsa suna kashe ne shiyasa hankalinsa kwance domin bai shirya amsa ma kowa Tambaya ba ayanzu.

Washegari ya kunna karamar wayarsa sun yi mgana da Sakataransa Michel ya tabbatamai da Mujaheed yazo nemamsa Har sau biyu bai shigo Office ba,Saifudden yasan haka zata faru shi baya ma kaunar su Fara Haduwa da Mujaheed bai je Lere da Abuja ya wanke kansa ba yasan Halin Mujaheed bazai taba mai uzuri ba.

Shi kuma bashi da Lokacin Rattamai bayanin da zai gane.

Tunda ya kama Daki a Hotel din sai da ya kwana uku bai fita ba komai yake Bukata nan ake kawomai,Waya kuma Tab dinsa kadai yake kunnawa yayi karatu yaga sakonni domin suna Online class yawancin karatunn nasu ma ta Online ne.

Sannan arana ta uku ne ya samu wayar parmanent Sacatary kan yana son ganinsa Dalilin Fitan ne kenan da yammah yaje chan Ministry suka Hadu suka Tattauna har yaja sa Gidansa sukayi Dinner awajen ma sai mai Tsiyan yaki aure yake yi shi dai baya mgana sai yake Allah fa na Rufamai asiri duka auransa da akayi mai ya saki bai taba gayyatan kowa ba Sannan har yanzu mganar bata Fasu ba.

Aranar Hotel din ya koma ya kwana Sai da Safe ne ya baro nan ya koma Gidansa Dake anguwan Sarki yasan Mujaheed ya kyalesa bazai kara Nemansa ba,Sannan yasa layin Ummi a Trak domin yaga ko ta na ina..?

Sai yaga ta koma Abuja tun jiya da Rana,Sai hankalinsa ya kwanta yasan yanzu matsalan kadan ne Lere zai Fara zuwa ya warware ta chan kafin Abuja Bangaram kawu mai Sauki ne bai da Zafafawa kan wasu al'muran Daga baya sai yaji da Muhajeed da Addarsa Domin yasa sun yi bala"in Daukan Zafi dashi

Kwana Hudu da Faruwar abun ya samu kiran Director Musa kan abunda ya shafi wata makaranta Dake Zaria sun Dade suna Tattauna kan dai abubuwan da makaranta ke bukata sannan da kuma Bikin Speech and Prize giving day din da za"a shiryama Dalibai a wannan Tearm din.

Duk da ba zuwa zai yi ba sai dai yana da Alhakin duba komai Kafin su Rabu da Director musa sai da yace ya Turamai jawalin duka Tsara tsaran ta Tab dinsa saboda ya Duba in ya samu Lokaci.

Shi kanshi bai da wani sukuni Saboda suna shiryen shiryen daukan Sabbin malaman sakandari,sannan akwai Jawalin Tsare tsaren gyaran makarantun gwamnati guda 100 ajahar kaduna kuma suna hannunsa shi zai gabatar ma gwamna duk da zaman da sukayi da shi ya dan shigar da mganar sannan sun Tattauna wasu da parmanent Sacatary da Diractor na Board Education ammh saboda yadda ya maida kansa Busy yasa abunda ya Faru a Lere ya bace gabadaya a Tunaninsa yana ganin abu ne mai sauki cikin lokaci daya zai Daidaita komai.

*******

Zaria.

Yau ta kama jumma'a ne gabadaya ake tashin makarantar ta SAIFUDDEEN ACADEMY 12:30pm ba kanar sauran ranakun ba da Shashen Nursing ke tashi 12:50pm Shashen Primary kuma su tashi 2:00pm Saboda basa lesson shashen Jss da SS kuwa sai 3:30pm suke tashi Gabadaya.

Gabadaya makaranta Ta Yamutse yara nata Haraman Tafiya Wadanda ake zuwa Daukansu a kan abun hawa suna Harama masu kekuna da mashina ma suna ta hawa abunsu malamai suna ta haraman tafiya ciki har da Muhibba Data Tattaro ya"yan yayar ta,Siyama dake primary 3,sai walid dake primary 5 sai babbansu Khalipa dake Jss2,Saboda ita yasa Babansu ya cire su a inda suke da farko nan Tudun wada ya kawo su inda muhibba ke koyarwa sannan makaranta ko wa ya santa akwai karatu saboda malamansu sun san abunda suke yi.

Akwai mai Adaidaitan dake kawo yaran yana kuma zuwa Daukansu to har yazo shi Muhibba zata bi domin yau tace ma Inna gidan Anty Habiban zata karishen yininta in ta sun tashi Daga makaranta.

Na gama saka yaran a daidaitan kenan zan shiga naji Muryan Uncle Hafiz na min mgana sai na Dataka na juyo ina kallonsu shi da Anty Khadija suna karisowa.

Sai da suka kariso sannan Uncle Hafiz yace"Anty Muhibba tafiya ba sallama.."

Cikin yanayin mirmishina na sakar mai kafin nace "Laa..Naje staffroom sanda zan kai ma Headtecher key din clasas ban gan ka ba Har Anty Debora sai da na Tambaya tace itama tun Safe rabonta Dakai.."

Kansa ya shafa kafin yace"Wlh ina wajen Director ya Kirani kan Tsare tsaren Speech din na yara da zamu yi shiyasa bani a Shashen namu yau.."

Muhibba "Ayya shi yasa.."

Khadija na kalla wacce ta Dauke kanta sama kamar bata a wajen muhibba zata mata mgana kenan Walid ya leko yana Fadin"Anty Auta yunwa plz ki zo mu tafi.."

Siyama ce tace"Lala..ba Mommy tace ba sunanta Auta ba..?

Sai na Fada mata in muka koma gida.

Muhibba tace"Barsa ai sai na Dirje bakin sa sannan zai daina ce min Anty Auta..!

Khalipa na jinsu yayi Dariya bai ce komai bayan ya leko ya gaida Uncle Hafiz Siyama kuma nokewa tayi tunda shine class room Teacher dinsu ada kafin ya koma aji shidda.

Uncle Hafiz yayi Dariya kafin ya leka adaidaitan yana Fadin"Siyama Gambo..!

Ta amsa da Sauri"Present sir.

Yana Dariya yace"Baki taba fadamin sunan Anty Muhibba Anty Auta ba..?

Sai Siyama ta rufe baki kafin tace"Kai kai Uncle bata so..ko mommy ma in tace mata Fada suke yi"

Harara Muhibba ta yankama Siyama bata yi mgana ba Uncle Hafiz ya Dago yana Fadin"Anty Auta sai monday kenan ko..?

Muhibba ta hararsa shi Shi kuma yana Dariya,Khadija Dake gefe ta tabe baki ta wuce Tana fadin"Hafiz na tafi bazan tsaya ina jiranka kana ta wani shiririta kamar mace ba..!

Tayi gaba abunta ganin haka yasa Muhibba tace"Uncle kuje kawai..Sai monday."

Ya amsa min da Allah ya kaimu Daganan mukayi sallama su siyama na Dagamai hannu tana fadin"Bye bye uncle.

Adaidaitan na shiga muka fara Tafiya acikin raina nayi shiru duk da ina jin yadda gaddama ta Sarke tsakanin Walid da Siyama ammh na kasa mgana Tunani tlnake yi me na tsare ma Anty Khadija a makarantar nan ne Datake Bakinciki da ni..?

Ita da Anty Usaina ne basa kaunata a makarantar nan tun sanda suka je Interviuw domin tare aka Dauke mu aiki ko basu so na samu bane ban sani ba ammh abun nasu yayi yawa ko ganina sukayi kamar sun ga kashi in nayi musu mgana sai sun ga Dama suke amsa min suna kuma jin haushin wani yayi min mgana ko Hafiz ba"a son ransu yake kulani ba,Shi anguwansu Daya da Khadija a Samaru suke da zama Anty Usaina kuma Matar aure ce Cikin muciya take aure.

Har mai adaidata ya kai Cikin FCE zaria Muhibba bata sani ba sai da taji Siyama na fadin Anty mun kawo sannan ta Dawo Hayyacinta ta Daga kallonta kan Jerin Quaters din ma"aikatan Fce zaria tunda mijin Anty Habibar babban ma"aikaci ne anan cikin makarantar.

Har yaran suka yi gaba tana ina baya jikinna a sanyaye ina rumgume da littafaina,na shigo Falon gidan da Sallama Anty Habibi dake kokarin Taimaka siyama ta cire Safarta ta Dago tana amsa sallamar kanwar tata.

Zubewa nayi kan kujera da ni da Littafan nawa,yasa Anty Habiban ta kara kallonta tana Nazarinta..

Walid ne ne ya kwanta a kasa yana Fadin"Mommy yunwa wlh..yau bamu je da basket ba..!

Anty Habiba ta kallesa kafin tace"To acici sarkin ci..ga kanwar ka nan siyama itama ai haka taje kuma bata Dawo tana wannan korafin ba.

Walid ya tura baki kafin yace"Ai bani kadai bane Anty Muhibba ma tana jin yunwa ko Anty..?

Hararansa nayi kafin nace"Tunda nice Sa"arka ba.."

Siyama tayi karaf tace"Mommy hauahi take ji ya walid fa agaban Uncle din mu yace mata Anty Auta..!

Tafada tana rufe baki Anty Habiba Tayi Dariya kafin tace"Lalle ko yau mun gan su arana..!

Tafada Lokaci Daya tana mikewa khalipa tuni ya wuce Dakinsu Walid ta kallah Tana fadin"Sai ka tashi kaje ka sauya kaya kabi khalipa ku tafi masallacin jumma"a..

Walid ya mike yana kunkunin yunwa Anty Habiba tace"aiko suma zakayi sai ka dawo masallaci zaka ci abinci acicin banza kawai..!

Haka ya wuce Siyama namai Dariya yana Fadin in ya kamata sai ta sani.

Anty Habiba Dakin da take tara Shirgi ta shiga Tunda wajen Bedroom Hudu gareta a flat din nata.

Har ta fito Muhibba na zaune tayi jugum da ita har zata shiga Kitchen sai ta fasa ta tsaya agaban muhibban tana kallonta itama kamar Muhibban haka take sai da ita tafi Muhibba jiki giant ga tsawo ga kiba sannan tafi muhibba hasken fata.

Ganin bata san ma tana Tsaye kanta bane yasa ta tabo kafarta tana Fadin"Ke Auta..?

Lafiyar ki kuwa..?

Sai sannan Muhibba ta Dawo Hayyacinta ajiyar rai na sauke ina kallon Anty Habiba kafin nace"Lafiya ne Gajiyar makaranta ce kawai..

Anty Habiba tace"Ko gaskiyan Walid ne da Yunwa kuma ko..?

Muhibba tace"A"a wlh ai kowa ba irin sa bane mai cin tsiya."

Anty Habiba tace"To kodai kin Hadu da Aljanin naki ne..?

Muhibba ta kalleta gabanta na Fadi kafin tace"Aljani na.?

Shi wa..?

Anty Habiba tace"Shi SAIFUDDEEN mana.."

Binta nayi da kallo sanda ta juya ta shige Kitchen din dake falon gabana na Fadi nima fa tunda su Inna suka ce Saifudden ba Mutim bane nake Fama da faduwar gaba duk sanda aka ambaci sunansa,Ni kaina dana zauna nayi nazari da kuma yadda Mallam Haruna yayi bayani ai naTabbatar ma da kaina Saifudden ba Mutum ba ne Aljanine..!

Littafin Saifuddeen na kudi ne pay N500 via 0552179550 Jamila umar Gt bank,sai a turo evidence of payment ta wannan Lambar *** ko kuma katin waya na Mtn sai adauki Hoton katin a tura ta wannan Layin kai Tsaye *** mutanen mu na Niger kuma zasu tuntubi Kausar aglan Nissa ta wannan lambar domin karin bayani +22796562223 Ina maraba da masoya na a duk inda suke

Janafty