SAIFUDEEN

04

by @jamilaumarjanafty

SAIFUDDEEN

(Ba mutum ba ne)

Wattpad:JamilaUmar315

Mallakar:Janafty♥️

Amnaf_sudanese _collection

Tana saida original laffaya kala daban daban daga Sudan kama daga na Amare da Kuma casual muna da available a Nigeria kuma Muna aikawa daga Sudan Zuwa Nigeria ko'ina a fadin Jahohi talatin da shida har ila yau dai akwai humra da turarrukka sadidan na matan aure daga Sudan,ba fa anan kada'i muka tsaya ba Muna saida kayan lalle akan sari da Rahusa da kuma siyan Daya,akwai mayuka da dilka da kayan gyaran jiki na ainahin ba Mix ba, wadan'da zasu fitar Miki da fatar ki tas ba bleaching fuskarki tayi haske tayi walwal kina kyalkyali and duk abunda kikeso a Sudan Muna kawo Miki shi har gda Nigeria Amnaf Sudanese collaction ba abunda bama saidawa kama daga kayan kamshin jiki na kaya da na fata +249923097401

🅿️4

Har Anty Habiba ta fito daga Kitchen,Muhibba na zaune ta kasa ko kakkwaran motsi ga yanayin data shigo,Sannan ga karin mganar Anty Habiba yasa sai abubuwan suka taru suka mata yawa,batama san Anty Habiba ta kariso gefenta ba sai da taji Tana fadin"Zaki ci abinci yanzu ko sai kin yi sallah..?

Muhibba ta sauke Numfashi kafin tace"Ina hutu..ammh ba zan ci yanzu ba sai an juma."

Anty Habiba tace"Kwana zaki yi ammh ko..?

Muhibba ta muskuta kafin tace"In tayi min Dadi sai Lahadi zan koma in batamin ba na koma wajen uwata goben nan.".

Anty Habiba tayi Dariya kafin tayi mgana Sai ga Siyama ta fito Daga Dakinsu,Ta saka wani kaya riga da sikat na wani leshi mai kyau Anty Habiba ta saki baki tana kallonta ita kuma sai ta juya tana fadin"Mommy Anty nayi kyau?

Muhibba tace"Sosai kuwa My Bby u look so fine."

Siyama tace"thank u Anty.

Anty Habiba tace"Ke a ina kika ga kayan nan..?

Siyama yar shekara shidda tace"Mommy a wardrope din ki nagani."

Anty Habiba tace"To maza kije ki cire basu zaki saka ba..Ki je ki saka wannan Atamfar ta jiya da na goge miki wannan less din ki bari gobe in zamu je sunan Maman Arfat.

Siyama ta tura baki Tana fushi Anty Habiba tace"Wlh zan make ki fa."

Siyama sai ta fashe da kuka Anty Habiba ta gyada kai kafin tace"Kina son Duka kenan ko..?

Dameni da kukan banza siyama.

Ganin ta mike yasa Siyama ta nufi wajen Muhibba tana fadin"Anty Kada ki bari mommy ta Dakeni.

Muhibba ta riketa ajikinta tana Fadin"Mommy bazata tabamin Baby girl dina ba..Daina kuka kin ji.

Anty Habiba ta kama Hanyar Dakinta tana Fadin"Indai bata sauya kayan nan ba sai na Daketa..

Muhibba tace"Zata sauya yanzu.

Ta kalli Siyama data tsorata domin Tana da tsoron duka hawayenta ta share mata tana Fadin"Ki daina kuka kada Su walid su dawo suga kina kuka suyi miki Dariya ko..?

Ta Daga kai da Sauri Lokaci Daya tana Share hawayenta Muhibba ta mike lokaci Daya tana daukan jakarta da Littafanta tana Fadin"Muje ki sauya kayan gobe sai ki saka wannan mu fita anguwa ko.?

Siyama tace"Har dake zamu je Anty..?

Muhibba tace"Insha Allahu.

Hannunta suka kama Har Dakin da nan Siyama ke kwana wani Lokacin Sannan anan Muhibba ke sauka in tazo gidan katifa ne kadai a Dakin sai Tarkacen kayan yaran sai da ta zube kayan Hannunta Lokaci Daya ta kwabe hijabin jikinta Doguwar Atamfar mai kalan ja Dake jikinta ta bayyana.

Hannun siyama ta kara kamawa suka fito Daga Dakin suka shiga na Anty Habiba Dake Dauke da gado da katon Wardrope dinta na zamani bata adakin sai dai suna jin karan ruwa a bandakin Dake Dakin Muhibba ita ta Daukoma Siyama Atamfar da Anty Habiba tace ta saka ta Cire mata na jikinta tana Lallashinta har ta sauya mata da wanda mahaifiyarta ke son ta saka.

Sai ga Anty Habiba ta fito Fuskarta duk Ruwa alamun alwala tayi Muhibba ta kalleta tana Fadin"To mun sauya ba zencen duka yanzu.

Anty Habiba tace"Kun kuri kuwa da yau kun Daku."

Muhibba tayi dariya batayi mgana ba Anty Habiba ta isa saman gadonta inda Hijabinta take ta Dauka tana Fadin"Yauwa wlh naji dadin zuwanki..zaki tayani aikin Cake da Donot da Maman Arfat ta bani nayi mata na sunan gobe.

Muhibba tace"Ita ce ta Haihu..?

Anty Habiba tace"A"a kanwarta ce."

Muhibba tace"Allah ya raya..ta amsa mata da Ameen Lokaci daya tana Shimfida Darduma Muhibba taja Siyama suka fice Daga Dakin.

Dayake Anty Habiba tayi Catering School,Sannan kuma Home economis ta karanta a makaranta sosai ta iya girke girken zamani har da ma na gargajiya Dayake tasu ta zo Daya da Muhibba duk da suna Fada ba ammh ba sosai ba,tana yawan zama awajenta in bata da makaranta shiyasa ta koyi abubuwa dadama Daga bangaranta.

Sannan ko agida tana taya Anty Zeenatu matar Ya Habibu girki tunda ita ke ciyar dasu sai dai in tayi Tafiya Muhibba ke musu girki duk da itama Innar Habibu ba malalaciya bace.

Koda Anty Habiba ta idar da Sallah ta Fito Falo su Walid sun dawo masallaci suna Baje a tsakar falon Muhibba ta Zubo musu abinci a wani babban Faranti sun hadu suna ci gabadaya Daman haka suke yi sosai suke kaunar kanwar uwar tasu saboda tana son yara saboda aikinta yasa tasan yadda take iya bi da yara.

Itama cikin su Anty Habiban ta shige suna cin Farar shinkafa da miyar Jajjage data ji kifi suna ci suna Santi sannan Siyama da Walid suna Fadan su na Fama Siyama ke kuka saboda sai ta Debo abinci walid ya kabe Hannunta Muhibba data gaji ta rankwasheshi akai tana fadin zai tashi ya Debo nasa sannan ya daina Tsokanar siyama.

Suna gama cin abinci Khalipa ya kwashe komai yakai kitchen Walid kuma ya Dauko Tsintsiya ya tattara inda suka bata ita kuma Siyama ta kwashe kofunan da suka sha ruwa da Zobon da Anty Habiba bata rabo dashi.

Khalipa Littafan makarantarsa ya Dauko yana Dubawa Walid kuma ya Dauko kwallonsu ya fita compound din Gidan su da sauran abokansa na makotan Anty Habiba suna Bugawa Siyama kuma daman Raguwa ce kan Jikin Muhibba tayi barci Sai Anty Habiba da Muhibba aka bari suna Hirar abunda ya shafesu.

Cikin Hirar ne ma Anty Habiba ta kalli Muhibba tana fadin"Kun yi waya da Sanin Inna...?

Muhibba taa tabe baki kafin tace"Ni ai satin nan kaf bai kirani ba..Fada mukayi."

Anty Habiba tace"Me ya hadaku sababbu..?

Muhibba tace"Kirana yayi Ranar da Daddare kan mganar abokinsa Abbati..Har yana cemin wai abokinsa yafi ni kyau taimakamim zai yi ina wulakanci."

Anty Habiba ta kyalkyace da Dariya Muhibba ta bata fuska ta cigaba da Fadin"Wulakanci fa yayi min ni kuwa na mai Masifa nace kada ya kara kirana kan mganar shashashan abokinsa baya gabana..tun daga ranar bai kara kirana ba nima na watsasa a kwandon shara."

Anty Habiba ta Dakata da Dariyarta Tana Fadin"Daman kun saba Inna ce ko Ya Habibu ke iya shiga Fadan ku ke da sani Auta..ammh so yake yaga kin yi aure sannan yana ma abokinsa Compaing ne.."

Muhibba tace"Kada ya kiyaye ni da mganar abokinsa ya gani sai mun Daina mgana ta kan haka."

Anty Habiba na dariya take fadin"Baza ayi haka ba..Dazu da Safe ya Kirani wai ina da Sauran Snaks..? Domin sun samu break na Sati Daya yau yana Hanya yana so in yazo nayi mai in zai koma ya tafi dashi."

Muhibba tace"Ai Dayake na banza ne dole yace ko kina dashi..? Ai wlh kice baki da kudi in zai bada ayi mai ya bada in bazai bada ba ya barshi Matsolon banza kawai."

Anty Habiba tace"Ke Auta kiji Tsoron Allah Sani fa dan makaranta ne bai da komai sai abunda muka taimake sa dashi.

Muhibba tace"In jiwa..? Bai dashi yake kashema yanmata kudi."

Anty Habiba ta zaro ido cikin Dannen Dariyarta tana fadin"Budurwa..?

Ke Auta bansan sharri.

Muhibba tace"Bafa budurwa ba yan mata zaki ce domin yan matan ya sani bazasu kirgu ba a zaria..Kar ma muje ga na chan jami"arsu ko a islamiyan mu na san yanmatan sa fin biyar ciki har da Nusaiba gidan Alhaji Ashiru,Da Bakinta take fadamin irin kashe mata kudin da Ya sani yake yi kuma jamila ma Aminiyarta muna mutumci da ita ta sha Fadamin ina karya ta wa,sai da naga Zahiri,daman mun rabu da Jamila in yaje wajen Nusaiban zata kirani naje nagani aiko ina zuwa Daidai ya Sani na mika mata leda Cike da Shooping din kayan kwalliya ko kunya bai ji ba."

Ya Habiba na Danne cikinta tace"To ya yayi da kuka ga juna..?

Muhibba na Dariya tace"Ya kuwa..?kinsan san dan duniya ne ballatana karatun Lauya fa yake yi ai ya fara sanin kan lauyanci mazewa yayi ya hade rai..ni kuma na komawata gida na Fesa ma Inna nace kina nan komai kika samu kice na Sani ne maraya dan makaranta bai da kowa achan to gayichan ya zama bawan mata har kashe musu kudi yake yi..Inna kinsanta bata yarda ba ammh yana Dawowa ta mai mganar sai ya fara Fada har da cewa in ya kamani sai ya barni kwance ni munafuka ina Hadasa da Inna.aiko na hadasa da Ya Habibu shi yace in ya tabani sai ya sabamai Tunda ya iya yima Budurwa Shoopping to zai iya rike kansa a Jami"a."

Anty Habiba na kara dariya tace"Lalle Sani ya gamu da Autan Inna..

Muhibba tace"Wlh kuna ganinsa hakane mugun dan rainin hankali ne..Nifa ko aure nayi Ya sani yazo gida na sai ya raina kansa shima yace ko a yar aiki bazai Daukeni agidansa ba..."

Anty Habiba tace"Duka karyan tsiya kuke..Sanda zaku nemi juna Habiba bata sani ba..Yau dai Sani dan gatan Inna ce domin nasan ya Kirata ya Fadamata zai dawo,tana chan ta kasa zama saboda shi.

Muhibba tace"Wlh komai ta samu yau na Ya Sani ne ai shiyasa ma kina cewa zai dawo na bar mai Innar har sai ya koma saboda in yana nan yana Hadamu da Inna ne kinsan sa akwai munafunci."

Anty Habiba dai har sai da ta gaji da Dariya Saboda indai Sani da Muhibba ne sai cikin ka ya kule suna Mugun Sako a tsakaninsu,Saboda shekaru uku ne a tsakaninsu Inna ma tace bai gama kaiwa bama shiyasa suke Takun saka ko zaman minti goma ba ayin shi Tsakanin Sani da Muhibba sai an bare da Fada kamar wasu yara har yau bazasu girma ba.

Anty Habibar ce tace"Na manta ma ban tambayesa ko yana zuwa gidan Baba Sunusi na gaya In yaje gidan su Baban mu kuwa..?

Muhibba tace"Kamar yana zuwa ba sosai ba dai kamar naji Inna na Fadin suna karatu tare da yaron Baba Sunusin anan Kano din ya kan je ammh kinsan Halin ya Sani bai da Sakewa da Mutane bar rainin wayausa a inda ya raina..

Anty Habiba tace"Nasan ai zai zo Biko.

Muhibba tace"Yazo din ya gani.

Anty Habiba ta gyara zama tana Fadin"Tsakani ga Allah Auta abar mganar wasa meye laifin Abbati..? Yari mai kokarin neman na kansa sannan iyayensa mutanen kirki ne Auta ni wlh na yaba da yaron har nan Falo na sun sha zuwa da Sani.

Muhibba ta tabe baki wanda Daga gani ya zame mata Dabi"a kafin tace"Aini ban ce yana da wani aibu ba Anty..kawai dai bana son shi ne wlh.

Anty Habiba ta tsuramata ido tana kallonta kafin ta girgiza kai tana Fadin"Ko dai mganar Sanin da gaske ne..?

Muhibba tace"Me yace..?

Anty Habiba tace"To eh mana..Cewa yayi gaskiya Mallam haruna bai gani Daidai ba wannan aljani yana tare Dake kila ma auran ki yayi shiyasa baki san mganar aure ko na Saurayi.

Muhibba ta karkace kai tana fadin"Ai ya Dade yana fadin haka..Ni bani da lokacin sa ba aljani ba Allah yasa aljanun duniya ne suka aure ni ba zan Kula wannan kazamin abokim nasa ba.."

Anty Habiba tace"Ai shikenan Allah yayi mana zabin Alheri."

Muhibba ta amsa mata hira suka cigaba da yi sama sama kafin Muhibba ta fara Hamma Anty Habiba tace"ke ji ki kwanta nasan kin gaji gama Siyama ta kara miki gajiya..Bayan La"asar in kin huta sai mu yi aikin daman jiya na shiga kasuwa na siyo komai...

Da toh Muhibba ta amsa mata domin da gasken ta gaji. Kowa yasan yadda aikin koyarwa ke da sakar da gajiyan gobobi.

Ni da Siyama muka baje sai barci kamar nasha wani abu Daman bana samun barcin sai karshen sati sauran ranakun ban da da Lokaci saboda har alokacin ban Daina zuwa islamiyar yammah ba Sai dai muna ajin manya ne..

********

Saifuddeen tun safe ya shigo Zaria Saboda yana da class da yan Masters karfe goma na safiyar Ranar jumma"a to da wuri ya shigo zarian ya bata awa Uku cikin Abu zaria kafin ya baro Cikin makaranta shi da Exscort dinsa Tim da Bama zuwa Kebetattacen gidansa Dake Gra domin ya huta.

Barci ya kwanta yayi tayi sai bayan La"asar ya tashi yayi sallar la"asar sannan ya zauna yana Duba Tab dinsa Yana amsa sakonni masu muhimmanci Sakon Musa Diractor ya fara Dubawa sama sama ya bashi amsa da cewa ya gani in ya gama Duba Tsarin zasu yi mgana.

Daganan ya Duba jadawalin Aikinsa na satin zai shiga da Sakataransa Michel ya turo masa,sauran sakonnin bai Duba ba sai ya shiga email dinsa ya dan Duba Sakonni kafin ya fita nan ya Dade bai duba karatun da sukayi na wannan watan ba.Saifuddeen zai yi wasa da komai ammh banda abunda ya Shafi ilmi a wannan Lokacin ya zauna yana Duba duk karatun da akayi ya wucesa,Domin Unites State University(Usu) dake San_Diego california.karatunsu na Online ne ranar nan ya wuni ya Duba abunda ya wuce sa har sabon Darasin da sukayi yau sallah kadai ke tadasa,abinci kuma su Bama ya bama kudi suka je Restaurant suka siyomai,yaso ya Dauki kuku sai kuma ya fasa ganin zamansa a zaria na lokaci ne wani Lokacin ma in ya shigo baya kwana yafi zama a kaduna ko Abuja sai su Ummi suyi sati uku basu gansa ba..

Megadi ma Saboda Tsaro da kuma kada ya bar gidan a haka ammh Shekara daya da wani abu daya mallaki wannan gidan bai kwana aciki sau goma ba.

Anguwan ba wanda yasan sa shiyasa shima baisan kowa ba Dayake waje ne na masu kudi kazo nazo ba wanda ya Damu da wani ba kamar sauran anguwannin Takalawa marasa karfi ba..

Bai waye da wajen ba sosai shiyasa ko salla acikin gida yake yin kayansa,Abunda yasa ma zai kwana Gobe yake so yayi sammako ya tafi lere Saboda ya fara wanke kansa wajen su Baffa Hashimu,dagachan zai wuce Abuja wajen Ummi saboda yakasa kwanciyar Hankali yasan tana Fushi mai Tsanani dashi bata kirasa ko sau daya ba.

Sannan sai Addarsa Sadiya ko kowa zai yi fushi da shi ita tana yi mai Uzuri fin sau Saba"in ammh wannan karon sai yaga sabanin haka kenan itama tana Fushi dashi yasan Halin Mujaheed shi zai rika kashe mata gwiwan kiransa yasan Halinsa Sarai.

Sai after Isha"i sannan ya gama duba karatunsa ya kashe Laptop din Ruwan Zafi ya dafa saboda yana so ya sha Tea banda ruwan zafi bai taba Dafa komai agidan ba duk da akwai komai na amfani acikin kitchen din.

A Falo ya Hada Tea din yana da kayan Tea agidan saboda shi ma"abocin shan Tea ne sai ya sha ya wuni bai ci komai ba kuma bai Damu ba.

Yana rike da karamin mug fari yana shan Tea din wayarsa guda Daya da kowa yasan shi da ita tana kunne a gefensa,Tv yake kallo Cikin tashar Mbc2 sosai yake son tashar saboda yana son Finafinan da suke haskawa..

Dayake sai da yayi sallah sannan ya zauna yana shan Tea din Hankalinsa na wajen kallo sanda yaji wayarsa na tashin Sautin daya san yamata a kasalance ya jawota ya Duba sunan ADDATA ya gani yana yawo a saman Sreen din wayar tasa sai yaji wani sanyi acikin ransa da Hanzari ya ijiye Mug din hannusa,saman Center table din Dake falon Lokaci daya yana Daga Kiran.

Cikin yanayin Sanyin Muryansa yace"Addata..Sai yau..?

Sadiya Dake zaune gefen gadonta sanye da kayan barci tace"Hamma..Hamma meyasa kayi haka..?

Saifudden ya Lumshe ido Lokaci daya yana maida kansa bayan kujeran ya Jingina kafin yace"Addata abunda nayi shine mafita fa ba domin na batama kowa rai ba.

Sadiya tace"Haba Hamma kasan irin tashin hankalin da ka jefa mu..?.sanda zaka aikata wannan aikin baka Tuna da wani Hali Ummi zata shiga ba..?

Da Sauri yace"Me ya faru da Ummi Sadiya..?

Ya Kirata sunanta cikin kaushinsa da taso tace bata sani ba sai dai ko a waya yana da kwarjini Cikin Sanyi tace"kaima kasan abunda zai faru..Su Iya sun zo sun ta fadan cewa da saninta ka Saki Majeeda har sai da akayi sa"insa da Goggo Atika da Mama zuwaira fa."

Saifuddeen daman yasan za"ayi hakan yasa bai ji mamaki ba cikin Danne yanayinsa yace"Subhanallah abun har yakai haka..?

Sadiya tace"Sosai fa akayi ta Hayaniya Ummi nata kuka sai da kawu fa yazo Daga Gaya shi da Iyami sannan ya samu ya lallashi su Iya suka tashi akan sai kazo sannan zasu yi zaman sannan da alkawaarin auran ka da Majeeda ba Fashi.

Saifuddeen yace"Meyasa su Iya suke haka ne..? Da ma sun yi hakuri kamar yadda aurena da Amira ya kare haka itama Tsakanina da Majeeda ya kare har Abada.

Sadiya ta saki baki kafin tace"Ammh Hamma..!"

Ya katseta da Fadin"Kin ga Addata ki bar wannan mganar kawai..na riga na yanke aurena tsakanina da yarinyar nan bana ji kuma zan maidata..

Sadiya ta saki ajiyar rai kafin tace"To ya zakayi da Su iya..?

Saifuddeen yace"Da Sabama D'an adam da sabama Allah wanne ne abun gudu Addata...?

Sadiya tace"Sabama Ubangiji..

Dagachan bangaran Saifudden yace"Good..To ki bar mganar nan ahaka..Da in zauna da majeeda ban sauke Hakokinta na aure ba..Allah ya kamani da laifin haka gwara na Sauwake mata in yaso laifin ne sai na bada Hakuri daga baya ba shikenan ba"

Sadiya tace"Ammh Hamma meyasa kasan hakane ka amsa mganar auran..?

Saifuddeen yayi wani mirmishi kafin yace"Kin sani Sadiya gaddama ba Dabi"ata bace..biyayya tsakanina dasu Baffa ne kan gaba kafin komai shiyasa na amsa musu umarnin auran suka bani basu san zan saki ba,ai nayi abunda suke so nayi auran ba shikenan ba.

Sai Sadiya ta kasa mgana ita fa har mamakin Hamman nasu take yi Saboda indai mganace in ya fara ko waye kai sai kayi shuru da bakinka kaji ka kasa mgana Saboda kwarjini da baiwar iya Sarrafa harshe.

Sadiya taji ajiyar rai kafin tace"Majeedan tana ta kuka fa Hamma.

Mamaki yasa bai yi mgana yara kanana sun iya shegentaka yaushe ma ta san shi ballatana har don ya saketa ta rika kuka..?gwara ma Amira yafi saninta tunda tana wajen iya ne alokacin kuma yana ganinta in yaje garin Majeeda kuma yawanci suna makaranta sanda yake zuwa shi fa kamaninta ma ko Bindiga za"a samai bazai iya nunata ba.

Yana jin sanda Mujaheed ke tambayan Sadiya dawa take mgana..?

Yana Tunanin yanzu ya shigo Dakin.

Yana ji tace mai Hamma ne cikin mamaki ya maimaita"Hamma..?

Sadiya tace"Eh ina gwada layinsa yau sai gashi ya shiga..

Mujaheed daya fito daga wanka yana Daure da Towel ya tabe baki ya isa gaban madubi yana kokarin tsane kansa.

Tabe baki yayi bai yi mgana ba Sadiya tace"Hamma kana jina..?

Murya shake yace"Yes..!

Sai tace"Ga ya Mujaheed ku gaisa..!

Yace mata toh ta mike ta isa ga Mujaheed tana fadin"Sweety Hamma na mgana."

Ko kallonta Mujaheed bai yi ba sai ma ce mata da yayi"Hamman ki dai ko..?

Ni ai ba Hamma na bane ballatana kice min ga Hamma..!

Sadiya sai ta kasa mgana sai tayi sororo da waya ahannunta Mujaheed ya yar dariya kafin yace"Yana da lambata in ya matsu ya kirani.

Saifudden duk yana jinsu mirmishi kawai yayi yana jin Sadiya na mai magiyan ya karba yace bazai karba Saboda ba karamin batamai rai Saif din yayi ba dan wulakanci ai yasan Michel ya fadamai yaje Office dinsa ba adadi ammh bai nemesa ai ko zai Rufe kowa ya Dauka ban dashi a yadda dai suka taso tare tun suna yara.

Saifudden ya katse sadiya da Fadin"Kinga Adda kyalesa kada Allah yasa ya karba din..."

Sadiya ta shagwabe tana fadin"Hamma ka basa hakuru shima yayi Fushi dakai..!

Saif yace"Saboda Uba ne Salahudden da zan bashi Hakuri..?

Sadiya ta juya da sauri tana kallon Mujaheed yadda yayi ne yasa tashan yaji Abunda Hamman nata yace.

Da sauri ta matsa daga baya tana Fadin"Hamma...!

Katseta yayi da Fadin"Gobe zan je lere Daga lere zan wuce Abuja in Ummi ta min Gafara jibi zan dawo kaduna in batamin ba sai Monday.

Sadiya tace"Gasiiya gwara kaje Hamma..Nasan kana zuwa Su iya baki zai mutu.

Mirmishi yayi kafin yace"Ina nihad..?

Tayi barci ne..?

Sadiya tace"Eh tun barcin dazu ne bata tashi ba.

Saifudden yace"Ki shafamin kanta ok..

Sadiya tace"I will insha Allah sai da Safe."

Daganan sukayi sallama dashi Suna gama Wayar Sadiya ta kalli mujaheed dake saka kayan barci kafin tace"Sweety kaji abunda Hamma yace..?

Mujaheed yace"Naji dan iska ki bar ni dashi karya yake ni din ubansa ne muna nan dake zaki ga yazo ban Hakuri.

Sadiya tayi dariya tana fadin"Gobe yace min zai je lere dagachan zai wuce Abuja wajen Ummi.

Mujaheed yace"Saif..Shegen sama kenan kuma fa wlh mganar yarinyar ta mutu kenan har Abada."

Sadiya tace"Haka ma yace min..

Ta fada tana karisawa kusa dashi Hannunsa ta riko tana fadin"Sweety kasan wani abu..?.

Kai ya girgiza mata alamun a"a cikin wani yanayi tace"ina tsoron kada mganar su Laala ta tabbata..

Mujahed yace"Wata mgana ce..?

Sadiya tace"Na cewar da sukayi kila Aljanace ta auresa..Na fara yarda dasu ace Hamma na neman 36 ashekaru ammh bai jiye iyali ba sannan in an aura masa sai ya saki a washegarin bikin anya..?

Mujaheed yayi dariya kafin ya Sagalo Hannunsa saman kafadanta yana Fadin"Ni ai nafi ma Tunanin shine Aljanin..!

Sadiya ta zaro ido kafin tace"Shi wa..?

Mujaheed na Dariyan yanayin ta yace"Shi Hamma din naki..SAIFUDDEEN."

Sadiya ta saki baki tana kallon mijinta shi kuma yana ta mata Dariya Lokaci Daya ya lakace mata hanci yana Fadin"Kanwar Aljani."

Dukan kirjinsa ta farayi cikin Shagwaba tana fadin bataso shi kuma yana mata dariya kafin ya rumgumeta da karfi yana fadin"Sweety..!

Cikin wani yanayin da su kadai suka sani..

******

Washegari Asabar tun wajen Sha daya na Safe Muhibba da Anty Habiba suka gama shirinsu Siyama Saboda alkwarin da Anty Habiba tayi mata yasa bataje Hadda ba su walid kadai suka tafi itama din Muhibba ta kara rokan mata Abban su walid domin da Farko yace sai tatafi makaranta bai ga Dalilin da zai saka tayi fashi ba sai da Muhibba ta saka baki sannan ya barta aje da itan.

Sun gama shiryansu tsab,Dayake tun Safe Maman Arfat din ta aiko aka karban mata Snaks dinta jiya suka yi Dare suna aikinsa ita da Muhibba.

Maman Arfat din kawar Anty Habiba ce Tare sukayi karatunsu a nan Abu zaria,Ita maman Arfat din tana Banzazzau ne da aure kanwar nata kuma tana cikin kongo ne sun gama karatunsu tuni ita Anty Habiba ce bata aiki sai ta maida hankali wajen yin su Snaks din nan da girke girke kuma ba Laifi tana samu sosai dashi.

Abban walid yakai su cikin Kongo gidan sunan sun samu tarba Sosai Saboda Maman Arfat din da Anty Habiba sosai suke kawance.

Muhibba Less ta sanya irin na Siyama saboda kayan Anty Habiba ne daman sun mata kadan sai ta bama Muhibban ta saka sukayi anko da Siyama.

Suna chan har bayan La"asar Su Walid daman Tace in sun dawo akai su Gwarbai gidan su kakaninsu na Bangaran Uba tunda Abban walid din d'an chan kwarbai ne,Domin sai dare zasu dawo.,Anty Habiba kawayensu wadanda sukayo karatu tare duk sun zo sun hade suna ta Fira siyama kuma ta shige cikin yara sa"aninta suna wasa sai Muhibba ita kadai tana zaune tana Faman Danna waya sai Daga baya kanwar su Maman Arfat din Aisha tazo suna dan taba Hira Dayake itama B.Ed dinta take yi a Fce zaria.

Suna cikin Hirar ne taga Sani nata Kiranta tayi mirsisi taki Dauka har Kira Hudu har sai da Aisha tace mata"Muhibba ba kiran ki ake yi ba..

Ta tabe baki kafin tace"Bamai muhimmanci bane..

Dariya tayi ta zata ko Saurayinta ne take ja ma aji suna zaunen sai ga Ya Habiba ta fito daga Dakin maijego tana Fadin"Muhibba ina kika bar wayarki sani yace yana ta kira baki Daga ba.?

Tace "Gata a hannuna ban ga Dama bane..

Anty Habiba tace"Kun fi kusa..yace gashi fa agidana bama nan.

Muhibba batace komai ba Daidai Lokacin Wayar Anty Habiba ta Sake Daukan kara ta Daga tana fadin"Sani gamu nan zuwa.

Dagachan bangaran Sani yace"Yarinyar nan ni ke kiranta tana banza dani..Wlh ki gayamata haduwarmu bazai yi kyau ba sai na mata rashim mutumci.

Anty Habiba na Dariya tace"Kun fi kusa bazan shiga ba sai mun taho..ba nisa nan cikim kongo ne.

Daga haka ta katse wayar tana kallon Muhibba kafin tace"Yace wlh haduwarki baza tayi kyau ba.

Muhibba tace"Ni ai robar wando ce Daidai da kugun kowani mara mutumci."

Wannan karon har Aisha sai da ta Dara kafin tace"Hala yayanta ne..?

Anty Habiba tace"Daga ita sai shi..Fadan sako da sako ne.

Aisha na Dariya tace"Dama yazo nan naga ya wannan haduwar zata kare.

Hararanta Muhibba tayi batayi mgana ba saboda bata da Hayaniya sosai.

Anty Habiba ta shiga tayi ma mai jego sallama har da muhibba ta basu abun Rabo su Snaks din Anty Habiba tace bazata karba ba,Maman Arfat tace bata isa ba,karshe dai Siyama aka bama ledan har Bakin kongo Aisha ta raka su Muhibba bayan sun karbi lambar juna sannanta koma su kuma suka Hau adaidaita zuwa gida.

Suna zuwa kofar Apartment din Su Anty Habiba Muhibba taji ranta ya kara baci ganin Ya Sani da abokinsa Abbati suna jingine jikin mashin Roba roba ta Abbati din ce.

Itace karshen Fitowa Daga adaidaita Anty Habiba ta tsaya basa kudi ita kuma Muhibba ta hade girar sama da kasa bayan ta kara gyara mayafin jikinta.

Ina rike da Hannun Siyama muka zo muka wuce su Sani dake tsaye suna kallona Siyama ce ta fizge hannunta ta Nufi Sani da gudu Tana Fadin"Oyoyo Uncle.

Da Sauri ya Dagata sama ita da ledan Hannunta yana Fadin"Eye yar gidan Uncle me aka samu ne..?

Suna wannan Anty Habiba ta kariso ita kuwa Muhibba daman key na Hannunta har ta Bude gidan ta shige.

Anty Habiba da Fara"arta tace"Sannun ku da zuwa..Sani yan Kano..Abbati barka da zuwa.

Abbati Dogo ne baki,kansa na kasa yace"Yauwa Anty ina yini.

Ta amsa tana kallon Sani wanda yake Biyema siyama bayan ya bata Tsaraban Biskit din daya siyo musu ita dasu Walid.

Tace"Mu shiga ciki sani..Hala Auta ta shige ne..?

Sani yace"Ai yarinyar nan muguwar yar raini ce haka fa ta wuce ko kallo bamu samu ba kamar taga kashi.

Anty Habiba na dariya tace"kun yi Fada ne kila.

Sani na bin bayanta yana Fadin"Wlh ba kowa yajamin ba sai Abbati..Yarinya karama na raina ni.

Abbati yace"Sorry abokina.

Sanda suka shiga Falon gidan ne Sani ya Bude murya yana Fadin"Ka nace ma yarinya sai wulakantaka take yi..Ga manyan bbya chan yan jami"a wlh sai ma ana rubibinka ka tsaya wajen wannan Tsamiyar tana maka yarda ta ga dama..!

Anty Habiba dariya take yi tana Fadin"Sani ka bari Autan inna ce fa.

Sani yayi tsaki yana zama gefen Abbati Dauke da Siyama kafin yace"Ai shiyasa take iskanci Saboda taga kuna ce mata Auta..ni ba Auta ba ko bakwaini ce sai na yanka mata rashin mutumci wlh badai ni zata wulakanta ba.

Anty Habiba yar dariya tayi batace komai ba kitchen ta shiga ta Dauko musu ruwa da Snaks din da sukayi jiya ta kawo musu tana Fadin"Ku fara da wannan kafin mu dora wani abun sunan kanwar kawata mukaje nan kongo.

Sani yace"Ba Case Anty Habiba.

Abbati bismillah.

Abbati dai bai ce komai ba Muhibba yake son gani duk ya takura.

Ganin haka yasa Sani ya kalli Anty Habiba yana fadin"Kira ta saboda ita fa ya matsa sai munzo.

Anty Habiba ta kwalama min kira Murya shake nq amsa mata sai da ta na bata Lokaci sannan na leko daga kofar Dakin na tsaya Dogon Hijabin Anty Duk ya yamutse ajikina yayi Datti Saboda bana so ma ya ganni da kyau yasa na saka.

Dagachan na tsaya ina fadin"Gani Anty.

Anty Habiba tace"Daganan muhibba..?

Ko baki ga Abbaati bane..?

Muhibba ta tabe kafin tace"Waye Abbati kuma..?

Ba Abbati Kadai ba har Sani sai da ya bude baki ransa ya baci ai ba kyau cin ido,kallon Muhibba yayi yana Fadin"Ammh ke kam baki da mitumci..? In baki son shi ai bai kamata ki wulakantasa ba,Wlh in da Abbati na Daukan mganata da Tuni ya barki Haba..Ni narasa uban me ya gani a wajen ke yarinya ke ba kyau ba yar gidan masu kudi ba sai fadin Ran Tsiya Kada dai ki manta Bello mai Rago dan asalin gaya ne Ubanki Sannan kin ma samu zai taimaka miki ke fa Sauran Aljani ne waya sani ma ko auranki yayi har kun hayayyafa bamu sani ba..?ai shima Abbati wlh Jihadi zai yi in nine ko kafa aka Daura min ke sai na kwance ki na zura aguje."

Ya karishe fada yana hararansa Muhibba ranta ya baci wannan tozarci akan Abbati..?

Sai kawai ta Fashe da kuka ta juya Cikin Dakin Anty Habiba ta kalli Sani Tana fadin"Kaga ka saka Autan Inna kuka ko..?

Sani yace"Tayi na jini ma bazan fasa fada mata gaskiya ba.

Abbati cikin wani yanayi yace"Gaskiya ban ji dadi ba Sani..baka kyautamin ba in bazaka lallasamin ita bai kamata ka sakata kuka ba.

Sani yace"Ai shikenan na barka da ita.

Abbati yace"is better.

Anty Habiba dai Dakin da Muhibba ta ke ta leka Siyama na jikin Sani tana fadin"Uncle Anty kuka take yi..?

Kai Tsaye yace"Ohon mata.

Ita kuwa Anty Habiba daga kofar Dakin ta tsaya tana kallon Muhibba dake kwance kan gado tana kuka kai ta girgiza kafin tace"Auta baki son gaskiya ne..Sannan kinsan Halin Sani sai ya sakaki kuka sau goma arana bai Damu ba..Ni dai ba abunda zan ce sai kiyi hakuri.

Daga haka ta juya ta bar Dakin muhibba ta dago kanta idanuwanta sun yi jajir kamar gauta,Hawaye suka kara zubo mata shikenan sai arika Dangantata da Aljani ya aureta Saboda wata Kaddaranta..? Kuma ai basu Tabbatar da SAIFUDEEN Ba mutum bane hasashe suke yi bai kamata su rika jifanta da haka ba.

Ringigine tayi tana kallon P.OP Din Rufin D'akin Tunanin Asalin Labarinta da kuma Labarin Saifuddeen ya Fara Dawo mata Daki Daki.

Zaku rika ganin wani Lokacin Muhibba na karb'an Labarinta da kanta wani Lokacin kuma ni sai na karb'a,To haka salon yake tana karban Labarinta ne in Salon ciki ya fito in kuma Salon waje ne ni sai na karban mata,zamu je inda zata karbi Ragamar Labarin daga hannuna gabadaya

Littafin Saifuddeen na kudi ne pay N500 via 0552179550 Jamila umar Gt bank,sai a turo evidence of payment ta wannan Lambar *** ko kuma katin waya na Mtn sai adauki Hoton katin a tura ta wannan Layin kai Tsaye *** mutanen mu na Niger kuma zasu tuntubi Kausar aglan Nissa ta wannan lambar domin karin bayani +22796562223 Ina maraba da masoya na a duk inda suke

Janafty