Kishi..... A tsakanin zubda jini!
1
by @maidambu41
🖤⚪KISHI..!!⚪🖤
~_A Tsakanin Zubda Jini🩸_~
Mai_Dambu
*Sadaukarwa ga Halimatu Kangiwa (halilsoss). Mrs J Moon. A'isha Fareedah Ya'u Nusaiba Sulaiman Ayuba jikalle na*
*01*
Huci yake kamar zuciyar shi tana ci da wuta, yana kallon fararrem takardan da aka ajiye Mishi. Idanun shi yana tara kwallar bakin ciki. Murmushi yayi tare da furza da iskar bakin shi.
Gyara zaman medical glass din shi yayi , dattijon siyasa ɗan kimanin shekaru saba'in da bakwai. Dr Abdul Hamid Jamil Bagauda. Farin bafulatani kyakkyawar dogo da shi.
"Dr Yanzun abinda Mai Girma Gwamna Rabi'u Ado yayi mana ya kyauta?" inji PA,
Murmushi Bagauda yayi tare da lumshe idanun shi yayi kafin ya bude akan P.A,
"Ka kira Qarib ku tattara min kayana baki daya, ku bar musu office din su." Yadda yayi maganar ba zaka tab'a hango sarewa ko faduwa ba, asalima kamar bai damu da abinda aka MISHI ba, wani irin juriya yake dashi da zai yi wahala ka fahimci b'acin ran shi. Ya san kan siyasa, kuma yayi gwagwarmaya masu yawa, ya zauna cikin yan adawa ya kuma san yadda ake nasara akan mutane, yana da karfin iya karya gwamnatin jahar cikin hikima da basira, kuma mutum ne mai farin jinin jama'a.
"Toh Yallabai. Amma yan jam'iyyar suna waje." Inji P.A,
Gyada kai yayi tare da mik'ewa ya kwashi wayar shi da sauran kayan shi ya fito.
"Ba zamu tab'a lamunta ba, Dr Bagauda kai ne jigon siyasan jahar nan, idan muka rasa ka iya zamu sami mai tsaya mana. Duk wani shugaban jam'iyyar sai yayi koyi da kai, don Allah kar ka manta akwai mutanen da suke buƙatar ka."
"Wali meye muke yi da ba zamu bayyana sabon kungiyar mu ba, ba sai mun nemi taimakon wasu ba! Daga yau Dr Bagauda shine Jigon Jam'iyyar Gaskiya Democracy Party."
"Eyeeeee!" Suka fada da karfi suka kuma cewa.
Hayaniyar da tayi yawa ce yasa P.A. Wali yace musu.
"Ku dakata! Dr Abdul Hamid Jamil Bagauda zai magana"
Fitowa yayi yana kallon su daya bayan daya, sanye suke da fararren kayan wacce take alamar kayan kungiyar ce suka ware ta na musamman. Jim yayi sannan ya kalle su bayan ya zare medical glass din shi.
"Ina jin tsoron tsayar da wanin ku! Ina jin tsoron sake baku damar tsayawa akan matsayin siyasa, Idan Jami'ya Dan Ladi Barau ya fita bayan samun damar zama Senata, Rabi'u Adamu Gwarzo ya dakatar dani a Jigon jam'iyyar PLP ban ga laifin su ba, Har yau Jahar mu tana niman hanyar magance wasu matsalolin da ya addabe su. Har yau mun kasa siyasa da akida kullum siyasa domin aljuhun mu muke.
Ni nan dan kishin kasa ne Ni nan ina son kawo cigaba da canji a cikin jahata me yasa duk wanda aka zab'a yake juya min baya? Ban san me yasa suke boye kudirin su ba amma daga yau na ajiye siyasa har Abada."
Yana fadan haka ya share kwallar idanun shi, bayan ya saka kai zai fita daga ofishin jami'ayyar.
"Wallahi bamu yarda ba, Bama yi Bama yi dole a dawo mana da Jigon mu."
Haka suka fita bakin hanya suna bin motar shi suna ihu. "Bama yi Bama yi."
Haka ya bar gurin tare da nufar hanyar gidan shi yana me jin b'acin rai a ranshi.
----
"Sallau yau naga Bankad'a da tijara wata watsatsiyar ce ta watsa min ruwa a barandan gidana? Bana ciki da Iskanci da rashin mutunci har wani ya isa ya kawo min Iskanci da watsewa, wannan sai na sha damara na buga gwatso musha dambe kowacce watsatsiyar"
Duk babu wanda ya fito waje zunzurutun tsoron da Allah ya daura musu na Hajiya Turai, masifaffiyar mata ce gata ita daya ta mallaki katon gidan da ake haya dashi daga ita sai yaranta uku biyu Hassan da Hussaini, sai karamar su Karime.
Hassan bai da kwaranniya, amma kuma yana harkan kasuwancin shi da matar da ya auro a chadi dake yana bin babbar mota har can, me suna Zehra, fara kyakyawa shuwa Arab na Chad.
Yayinda Husaini ya kasance yana bibiyar al'amuran siyasa, babban mabiyan Dr Bagauda ne, kuma yana samun Alkhairi a tare dashi.
Sai Karime itace autarta, tana masifar kaunarta kamar tayi yayya, haka ma yan biyun ta, musamman Zehra da Allah ya daurata akan Hajiya Turai take masifar kaunar ta. Gata ba wata babba bace amma tasan yadda take tafiyar da uwar mijinta.
A kaf unguwar kuka babu wanda bai san gidan Hajiya Turai Yar Jidali ba, domin ita Allah yayi mata mugun masifa da fada, zata iya wuni guda tana Bala'i da masifa bata gaji ba, haka kuma sai Allah ya daurawa Hassan hakuri da kawaici, bai iya fada ba. Saba'in Husaini da Allah ya daura mishi fada da niman tadda zaune tsaye.
Amma kuma duk bala'in Hajiya Turai tana da mutunci da sanin ya kamata, kuma a fadin unguwar kaf bata ragawa kowa. Kuma masu haya a gidanta basu da ikon mata barna ba zaka biya ba amma kuma wallahi sai kayi dan sani, kuma tsafta wajibi ne, gyaran gida da shara wajibi ne, kuma ba a fada a gidanta, ba a gulma a gidan ta, ba a rigima.karewa dai Hajiya Turai Bala'i bata bawa Gwauro ko gwauruwa hayar daki sai masu aure dan tace gidanta ba loja bane da za ayi ta kwaso mata ana watsa mata zunubi akanta.
Kuma wani hikimar da tayi bata tashi hada yaranta da mutnen gidan hayar ba, bude musu kofar su tayi ta bayan gidan, babu abinda ya dame ta. Kullum tana da wata dabi'a asuba nayi zata fito waje ta shimfid'a taburma da butar ta, da abin sallah ta, har sai kowa ya fito ya same ta tana sallah. Wannan yawan Ibadar nata ya sake kara mata kwarjini a idanun jama'ar gidan, har suma sun fahimci fada a jininta yake.
"Hajiya don Allah kiyi hakuri, Nazirah ce ta watsa ruwa bata sani ba, kinsan halin dan yau ka haife shi baka haife halin shi ba"
Shiru yayi ya kuma kaskantar da kanshi domin Hajiya Turai akwai bala'in son girma.
"Ayya Hajiya kiyi hakuri mana" inji Zehra da ta fito da abin karyawa.
"Sannun Yar nan, kina fama da tsofa gashi kina hidima dani, don Allah ki hakura haka mana"
"Kai Hajiya babu wani hutu a tsakanin mu, dan haka gashi ki karya ayi hakuri ba zata kuma ba" inji Zehra,
Murmushi Hajiya Turai tayi sannan tace mata.
"Yar nan ai sunci albarkacin ki, maza tashi sallau ayi ta musu fada dan bana son rashin hankali. Allah ya bada sa'a."
Sallau dan hayan Hajiya Turai ne, tun yana matashin saurayi har zuwa yanzun da girma yazo mishi. A gidan yayi aure har ya tara yara, kuma yana da kirki domin yana cikin mutanen da suke tsayawa Hajiya take gyaran gidanta, sabida haka ta cire mishi biyan kudin hayan gidan sakamakon yadda Hassan ya gaya mata, shima kamar dan ta ne.
Shigowar Husain da buhun shinkafa, yasa Hajiya ta tsare shi da ido.
"Daga gidan Uban waye ka tawo da shinkafa? Hussain tun bayan mutuwar aurenka da Balaraba ka zama soko baki daya, yanzun baka jin kunyar Umar yasan abinda kake aikatawa meye a cikin bangar siyasa? Don Allah ka daina wannan abin wallahi ina tsoron kar wani abu ya same ku ba zan iya dauka ba na rantse da Allah."
"Toh Hajiyar mu, amma dai ai wannan lamari ba na kowa na dauko ba, shugaban Jam'iyyar Peace Land Party ya bani domin sun bukatar irin mu a tafiyar su" yana magana irinta yan daba, takaici yasa ta katse shi da cewa.
"Kai ungo naka? Sakarai daga alamun abu ne suke shi yasa suka maka wannan shirin kar na kuma ganinka a cikin al'amarin siyasa wallahi sai na sab'a maka"
"Toh Ni kome nayi sai nayi laifi wannan ma na kawowa matar Hassan ne tana mana girki tunda baku so shikenan ai zan je na sayar na samu na kaiwa wancan Yaron kudin da zasu saya mishi abinci."
Bakin ciki ya kama Hajiya Turai sosai dan haka cikin kallon takaici tace mishi.
"Allah ya wadaran naka ya lalace"
"Hajiya Addu'a zaki na musu Banda baki" gyada kai tayi tana kallon Zehra. Hassan da Hussaini Allah yayi musu mugun kama, kamar su tayi yawa, kuma abin ba a cika gane su ba. Sai dai ta hanyar Amfani da muryan su, idan Hassan yana magana a sanyayye ne, yayinda idan Hussain yana magana irinta yan iska ne.
***
Manyan yan jam'iyyar Gaskiya Democracy Party ne suka nufi gidan Bagauda kamar yadda suke tsammani haka ya amshe su hannu bibbiyu, yana me zama cikin mutumtaka.
Bayan an gaishe gaishe sai da suka kallo juna kafin suka ce.
"Mun sami hukumar zab'e munyi musu magana, tare da shigar da dan takarar da muke son ganin ya tsaya, Salahudeen Kabiru. Kayi wani abu saura kwanaki arba'in a tsayar da Campaign."
"A'a ba wannan bane masalaha, muna niman Dr Bagauda ya dawo,ba dan mun isa ba. Ya duba kafaffun mu a kasa yan jam'iyyar mu suna bukatar shi."
Sunkuyar da kai yayi tare da kasa cewa kome.
"Don Allah kayi hakuri kamar yadda muka sanka a me kishin kasa ka nuna mana haka."
"An makara na fito nayi wani abu a akan siyasa. Kuyi hakuri don Allah"
Haka yaki karban uzurin su, daga nan manyan malamai da mutanen masana ilimin siyasa suka fara fashin bakin akan rabuwa da Dr Bagauda, haka yayi matukar gigita hankalin Yan jam'iyyar Gaskiya Democracy Party.
Yayinda gefe guda Yan jam'iyyar Peace Land Party suke ta samun haɓakar kungiyar su.
Sai da ya rage saura kwanaki ƙalilan za a rufe campaign, sannan Dr Bagauda ya amshi damar nuna Salahudeen Kabiru, a matsayin dan takarar Senata a Jahar , dan dama basu kai da sun tsayar da maganar Gwamna ba, iya kacin su Senata ne.
Ana jibi zab'e hukumar zaben Najeriya ta saka doka tare da yarjejeniya a tsakanin Kungiyoyin yan takara. Dokar itace matukar aka kama dan kungiyar ku da sace a kwatin zab'e zaku shekara goma sha shida baku tsaya a kowacce matsayi ba, sannan kuma duk wanda aka kama da sace akwatin zabe a harbe shi. Kowaye ne,
Gyada kai suka yi bayan sun amince da sharuddan da aka kafa musu. Haka suka mike tare da kallon juna suka yi sallama.
.....
Ranar zab'e.
Kwance take tana kallon shi yana ta shiryawa, jikinta a mace.
"Ni kam ba zaka hakura da zuwa zab'en nan ba kuwa? Wallahi bana jin dadin baki ɗaya."
Zama yayi tare da riko hannun ta, yana murmushi.
"Insha Allah zan dawo lafiya lau gare ki, kadda kuri'a kawai zanyi na dawo ai kodan abin cikin ki zan dawo da wuri."
"Don Allah ka kula"
Haka ya mike har ya fita ya dawo yana niman wani abu sai da ya gama zaga dakin sannan ya dawo ya zauna a gaban ta, tare da sauke ajiyar zuciya.
"Ashe gaki nan. Ke nake ta nima ban ganki ba."
Gyada kai nayi tare da tashi zaune ina kallon shi.
"Gani nan"
Murmushi yayi sannan ya sumbaci goshinta, ya fita.
***
"Ka tabbatar abinda ka gaya min haka ne? Toh indai haka ne idan kome ya faru afka mishi, domin dama haka nake so baki daya na durkusar da Bagauda, na hana shi walwala kamar kowa. Ya shekara goma sha shida bai d'aga hannun dan takara ba. Idan aka yi haka an gama min kome"
"Haka ne yallabai ai ta karewa Dr Bagauda, yana ji yana gani shi da daura wani mai mulki sai a lahira"
Suka kwashe da dariya, sannan yace mishi.
"Ina son duk abinda za ayi Gaskiya Democracy Party su rasa damar su, ina son na ga gazawar su, yadda zasu dawo Jam'iyar Peace Land Party. Wanna shine kudirina."
Dan haka suna gama abinda zasu tattauna aka kira yan daba da yan barandan siyasa, aka basu kayan maye sai da suka sha tatil sannan aka mika musu makamai.
"Ka tabbatar sun saka kayan Jami'ayyar Gaskiya Democracy Party, sannan su sace akwatinan zab'en."
"Toh Yallabai amma kuma kashe su za ayi fa?" Kallon shi yayi sannan yace mishi.
"Idan suka mutu taimaka mana suka yi da nasara, idan suna raye basu da amfanin sadaukar da rayuwar su domin mu dan haka basu" gyada ko yayi sannan, ya basu kayan GDP suka saka sannan suka nufi cikin gari tare da tadda tarzoma, bayan an hargitsa sassan gurin zab'en. A take aka bada Oda duk inda aka kama wanda ya dace akwatin zabe a kashe shi."
Aikuwa kafin kace kwabo sojoji da yan sanda sun fara sakewa yan iskan nan wuta. Hussain da yake gudun ceton rayuwar shi, ya hadu da hassan daidai an sakewa Husain harbi a gadon bayan shi,, haka Hassan ya tsaya ya goye shi.
Suka kuma fantsamawa da gudu, yan sanda na binsu suke, harbin Hassan aka yi a kafa, garin gudu ceton dan uwanshi. Ya jifa Hussain a kwata me dauke da ruwan kwata. Shi kuma ya zube a gurin, suna zuwa suka bude mishi wuta, sai da suka ga baya numfashin. Sannan suka fantsama niman Hussain.
Wanda shima fadawar shi kwatar wani ƙarfe ya cake shi har sai da ya bula cikin shi zuwa bayan shi. Dakyar ya samu yafito, tare da ɗaukar gawan dan uwan shi yana tafiya yana hutawa.
Garin ya hargitse sosai babu masaka tsinke, ko ina aka ratsa gawarwakin yan daba ne da basu ji ba basu gani ba an kashe su..
_A gaskiya wannan labarin a hargitse yake kuma yana dauke da wasu part part na kowa Ni mutum so mutanen da suke ganin ina sauka akan Jigon labarin na please And Please babu ruwanku da labarina a bar min kayana mana! Dole ne? Kaje ka karanta masu kyakyawan jigo a bar min kayana don Allah ina son abuna haka_
_Ban san yawan free Pages ba amma Insha Allah zamu tafi yadda ya dace amma ba kullum zan na Posting ba idan nayi yau sai jibi Insha Allah🙄🤣💓😍💃💞_
#Mai_
Dambu
#freepage
#Paidbook300₦ katin mtn ko shaida ta wannan Numbers👇🏽
0472282105 Ramlat abdulrahman manga GT bank! *** or ***