09
SAIFUDDEEN
(Ba mutum ba ne)
Wattpad:JamilaUmar315
Mallakar:Janafty♥️
Amnaf_sudanese _collection
Tana saida original laffaya kala daban daban daga Sudan kama daga na Amare da Kuma casual muna da available a Nigeria kuma Muna aikawa daga Sudan Zuwa Nigeria ko'ina a fadin Jahohi talatin da shida har ila yau dai akwai humra da turarrukka sadidan na matan aure daga Sudan,ba fa anan kada'i muka tsaya ba Muna saida kayan lalle akan sari da Rahusa da kuma siyan Daya,akwai mayuka da dilka da kayan gyaran jiki na ainahin ba Mix ba, wadan'da zasu fitar Miki da fatar ki tas ba bleaching fuskarki tayi haske tayi walwal kina kyalkyali and duk abunda kikeso a Sudan Muna kawo Miki shi har gda Nigeria Amnaf Sudanese collaction ba abunda bama saidawa kama daga kayan kamshin jiki na kaya da na fata +249923097401
🅿️9
Bama da Tim Amintattun Excort d'insa ne da gwamnati ta bashi domin kula da lafiyansa a matsayinsa na kwamishinar ilimi mai ci alokacin,abaya yana da Direba mai suna Nura,sai dai Allah yayi mai rasuwa yaso ya kara daukan wani sai kuma ya sha"afa ganin su Bama na tukasa duk inda zai je shiyasa bai damu da Daukan Direban ba.
Saifudeeen ba miskili bane yana mgana inda ya saba mganarsa inda bai saba bane ake mai kallon miskili Sai dai mutum ne mai zurfin Ciki wani Lokacin sai ya aiwatar da abu ma Ummi take sani ko Mujaheed sai yayi abu yake Fadamai har gwara Ummi yakan yi shawara da ita wani Lokacin Ammh Saifudeen yafi son aikata abu gaban kansa fiye da neman shawara wajen wani duk da Hausawa sunce Mai shawara bai da Sirri sai dai aikinsa mai kyau ne sai dai Zurfin Cikin Hallitarsa ne ba kasafai ake jin Cikinsa ba,Ko auran da aka aura mai na Amira ga na Majeeda banda chan gidan nasu na Lere,sai su Ummi dasu kawu babu wanda ya taba sani daman bai Fada ma kowa ba a wajen aikinsa da inda yake mu"amala a matsayin bai taba aure bane,yana Kafa kafa da kansa da kuma rayuwarsa,shi abunda ya sani kawai aikinsa duk da yana da Kasuwancin da yake samun kudi sosai anmh bai yarda ya zauna ba in da wani ne da ya samu Kwamishina sai ya watsar da aikin lacaring dinsa,ammh bai yi haka ba Saboda wannan din ma Ra"ayinsa ne Kaf Department din B.A English ba kamar Saifuddeen a gogewar Ilimi ta bangaran abunda ya karanta Kaf manyan littafan nan na Turanci Saifudden ya Dade da karancensu yayi karatu kamar bazai bari kwakwalwarsa ta Huta ba,in ko yana Turanci kamar wani Baturen kasar Burtaniya ya iya Turanci kala kala in ya juya turancinsa Ba kasafai wasu ke ganewa ba kamar bai taba sanin zo in kashe ka da hausa ba.
Sannan abangaran aikinsa a matsayin kwamishinar ilimi,bai zauna ba sosai yake gudanar dashi Cikin Aminci da Amana balle kuma suna Dasawa da gwamna alokacin saboda daman jajircewansa da Iliminsa yasa ya jawosa har ya bashi wannan matsayin sannan anci sa"a gwamnan mai adalci ne da Kaunar talakawansa,Sannan ya samu kwamishinoni da yan majulusu Adalai masu sanin ya kamata duk wani abunda suka ga ya kamata kama Daga gyaran makarantu Kawo kujeru da,gina tiolet na makaranta Zagaye makaranta gyaran Hanya,Tituna da albashin ma'aikata Da yan Fansho da Sauransu su kuma a bangaran mikamin shi duka da parmanent Secatary suke zama su Rubutu duk abunda ya kamata in sunje zama sai Saifudden ya shigar da korafinsu Cikin shekaru biyun da sukayi a kan mulki an yaba da aikinsu matuka an gyara makarantu sannan an samu kwararrun malamai abun sai son barka.
Sannan bangaran Rayuwarsa ta gida sosai yake da mu"amala mai kyau da kanwarsa Sadiya ba domin suna uwa daya uba daya ba sai domin akwai shakuwa a tsakaninasu kafin ya koma Lere da zama har bayan ma yana chan Sadiya na zuwa Hutu shima yana zuwa gaya Hutu su zauna tare sunan Addata kuma shi ya saka mata Tun tana karama in tana kuka sai ya kamata ya Rumgume yana yi shuru Addata da haka sunan ya bita kowa Adda Sadiya Laala da Zeeha kuwa sanda aka Haifesu ma baya kasar ya Dawo har sun fara girma kuma alokacin bai zauna ba basu da shakuwa a tsakaninsu,Suna jin tsoron shi duk da bamai Tsanani bane sai dai a wajensu yana da Tsanani yara ne marasa ji musamman ma Laala tafi kowa Zakewa ga Gulma Zeehaa kuma daman ta Dade batayi tafiya ba Sanda aka Haifeta kusan Haihuwan Laala ce ta fara takawa shiyasa suka taso kai Daya,Yana kaunarsu domin Daya suke da Sadiya a wajensa ko don yadda Mahaifinsu ya rikeshi da Amana.
Suna zuwa Suleja wajen Dangin Babansu in sun samu Hutu kowani sha"ani ya tashi Tunda Kakarsu Wacce ta Haifi mahaifinsu Hajiya Kafayat da kannensa suna da ransu sannan suma suna zuwa Dubasu sosai suke da kyakyawan alaqa da Ummi Fiye da Dangin su Saifudden sannan duk wata suna Turo musu da kudi kudin makarantarsu kuma sai da Saifudden yace ya Dauke suka Daina biya ammh kaya duk sallah ko wani sha"ani suna musu basu da matsalan komai na Rayuwa..
Dr.Saifudeen Conel.Salahudeen Lere ya mallaki gidajen har guda uku gidajensa biyu ne agarin kaduna sannan yana da wani a zaria sannan ga gidansu na lere fegin da Mahaifinsa ya gada ya bige yayi ginin zamani da komai na morewa rayuwa nan suke sauka ma in wani sha"ani ya kaisu na kwana shi da su Ummi,Sannan yana da taimako da kyauta yakan kai ziyara gidajen marayu da nakasasu domin bada Tallaffi ba amatsayin kwamishina ba a matsayin Saifudden d'an mutanen Lere.
A fuska ba wanda yasan shi ne Kwamishina sai a bangaran da aikin nasa yake,mutanen gari da Saifudden dinsa suka sanshi ana jin muryansa agidan Radion in bukarar hakan tataso ko sun je wani taro ko kuma Jawabi kan abunda ya shafi harkan ilimi,sannan in ka shiga goggle ka Rattaba matsayinsa zaka samu Jadawalin Bayanansa tunda Daga matakin Inda yayi karatu da mahaifarsa ammh ba Hotonsa shiyasa in ba wanda ya sani ba sai ya shiga ya Fita dai a matsayinsa na Dr.a bangaran kwalayen iliminsa.
Saifudeen ya hallaci Seminars kan bangaran abunda ya karanta bai san iyaka ba shi baya wasa da dama duk inda Dama ta amshe shi yana amsarta ne sau tari yafi bama harkan karatunsa Muhimmanci fiye da wannan mikamin dake hannunsa Sai dai mutum ne dake yaba alheri yasan Gwamnatin kaduna itace ta Jagoranci Iliminsa to bazai watsa mata kasa a ido ba zai Hidima mata iya karfinsa da iyawarsa.
*********
Washegari Tun Safe Saifudden ya koma kaduna Saboda zai shiga Office,Ammh kafin tafiyarsa sai da ya kai Ummi asibiti ya Daukan mata Jaka har cikin Office din su,Ana ta musu Dariya domin an saba ganin haka,indai akan Ummi ne da yaronta in yana Tare da Ummi jinsa yake kamar dan yaro karami in ya ganta ganinta yake yi kamar Conel,ta cike mai wannan gibin,Motarta bata da Lafiya tana gareji shiyasa Daga asibitin Hanyar kaduna suka Dauka Dayake sun yi gudu karfe goma yana cikin Office dinsa yana Duba Jadawalin fayel fayel din dake gabansa da suka fi Sati bai waiwayesu ba.Ranar dai sai yammah ya tashi Daga aiki ya wuce gidansa yayi wanka ya Huta ya hada Tea ya sha ya zauna ya kunna Tab dinsa ya samu karatu na rabin awa sannan ya Duba Jadawalin Director Musa,da kuma Rokonsa na ya samu zuwa a matsayinsa na babban bako bai ce mai komai ba saboda bai sani ba ko zai iya zuwa har yanzu bayan Yan"uwansa,ba wanda yasan shi ke da wannan wajen kuma Hallatarsa kamar Fallasa hakan din ne,shi kuma abunda bayaso ne shiyasa sai bai bama Musan amsa ba ya sauka bayan ya kashe Tab din.
Kwata kwata satin bai samu zama ba,Yana ta shiga Office sannan sun yi Taron su na kwamishinoni sannan ya shiga Ministry,sannan sun zauna sun gana da parmanet Secetary akan gyaran makarantu 100 da gwamna ya bada kwangila anan kuduncin kaduna shiyasa bai samu kansa ba sai Ranar Friday da Daddare yaje gidan Sadiya,Mujaheed kin kulasa yayi shima yayi kamar bai gansa ba ya Dauki Nihad yana mata wasa Ita kuma Adda ta kasa zama sai rawan jikin jeramai abinci take saman Dinning.
Abu kadan tace Hamma kaza Hamma kaza Shi kuma Saifudden saboda ya kule Mujaheed ya saki jiki suna ta Hira da kanwarsa tasa ya bata labarin zuwansa Lere da yadda sukayi da su Iya Sadiya Dariya har da rike Ciki Tana faman jera Filets saman Dining Tace"Ammh Hamma ka iya tsiya..Don ka kara batar dasu har da basu kudin zuwa wajen mai mgani..!
Yana wasa da Nihad yace"Addata kinsan ba Halina bane gaddama..shiyasa nayi musu shuru suka gama kidansu sukayi rawansu.
Sadiya ta kariso Cikin Falon Tana Fadi "Ai ka bani yanzu Iya kusfa kusfa wajen masu mganganu tana fadin ku Taimakeni jikana ne aljana ta aura..!
Ta karishe Fada tana Kwaikwayon mganar Iya Saifuddeen yayi Dariya har Hakoransa Farare suka bayyana.
Sadiya ta juya tana kallon Mijin nata Mujaheed dake gefe ya Hade rai yana Danna wayarsa tace"Sweety kayi shuru..?
Kansa na kasa yace"Uhmm!
Daga haka bai kara mgana ba tasan abunda ya faru yasa tayi mirmishi kafin ta zauna tsakiyarsu ta sakalo Hannunta daya saman kafadan mijinta Dayan kuma saman kafadan dan"uwanta tana mirmishi dukkansu suka kalleta cikin mamakinta Ita kuma kai tsaye tace"Kusan dai Sharadin gaba a musulunce ko..?
Kwana uku ne in wani bai kula wani ba..Wani sai ya sauke girman kansa ya kula wani mana..!
Saifudden da Mujaheed suka kalli juna kafin kowa ya Dauke kansa Dariya tayi saboda tasan halinsu haduwa goma sai an rabu ba"a mgana Hamma Taurin kai mujaheed kafiya..
Mujaheed ta kallah kafin tace"Haba mana Sweety..!"
Kallonta yayi a fusace kafin yace"Ni kike ganin Laifina..?baza ki yi ma wannan yayanki naki mgana mai shegen girman kai ba sai ni..?
Sadiya ta lamgwabe kai tana fadin"Sweety yaci albarkacin shi Yayane..Kaga kuwa in da kara Hamma Surukin ka ne.."
Saifuddeen na Saba Nihad saman Kafadansa yace"Kara tunasa masa domin inaga ya manta da wannan.."
Mujaheed ya balla mai Harara yana Fadin"Allah ya kyauta ka zama surukina..Ai da duniya kuma ta lalace.
Saifudden na Dariya Tusa Haushi yace"Dole dai ace da mijin iya baba Mujaheed..!"
Mujaheed yace"Eh in mijin Iya Ba auri Saki bane kamar ka ba."
Saifudden yaji haushi ya zabura Sadiya ta Danne Hannunsa tana Fadin"Hamma..!
Cikin Fusata yace"Kina jinsa ko..?
Wlh ya fita idona kafin na rufe.
Mujaheed yace"Anki a fita din sai kayi abunda zakayi kuma da kake wani Hura Hanci kan Sadiya ai kada ka manta nima kanwatace kuma nafika iko da ita Tunda matsayin matata take..Wlh Saif Darajan Sadiya kaji har kaga ma na barka ka shigo Gidana na kuma barka ka zaunamin a kujera tunda na Fahimci kai girman ne kawai ba wayau..!"
Saifudden ya saki baki yana kallon Mujaheed kamar kiftawan ido ya Saukema Sadiya Diyarta kan Cinya ya mike ya chakumo Mujaheed shima ya Mike ya chakumesa suna kallon juna suna Sakin Huci Sadiya ta saki baki tana kallonsu.
Saifuddeen ya matse wuyan rigar Mujaheed yana fadin"Maimaita abunda ka fada kagani in ban yi kasa kasa dakai ba "
Mujaheed ma ya matse wuyan farar T.Shirt din dake jikin Saifudden yana Fadin"Ance girma ba waya..!"
Bai gama mgana ba Saif ya Dungule Hannu ya tausheshi a gefen fuska shima ko ya Dage ya Dungule hannu ya Nausa mai a kirji Sai Saif ya Duke yana Nishi fadi yake"Kai kai hannunka ya kara zafi Mujaheed..!"
Mujaheed ya kyalkyalce da Dariya yana Fadin"Ka Dauka ada ne da muna BUK.! Ai yanzu hannuna yafi naka Tauri na samu Tranining din da baka samu ba."
Saifudden ya Dago yana Daga Hannayensa sama alamun Sarranda yana Fadin"Na Tuna nabi Allah na bika Ya mujaheed..
Mujaheed yayi dariya yana Fadin"Dole ka Tuba..!
Tare sukayi Dariya kafin su Rumgume juna Sadiya tace"Ni fa kun ban tsoro na zata Dambe zaku yi.
Suka saki juna Mujaheed ke fadin"Ai baki ga komai ba Lokacin muna Jami"a Tare muke gwada gwanjinmu alokacin Hamman ki ke zane ni ammh banda yanzu.."
Sadiya ta ware ido kafin tace"Wai Fadan gaske..?
Saifuddeen yace"To fa..Kinsan sa bai da kunya ni kuma bana shiri da mara kunya sai muci Dambenmu muyi gaba na kwana hudu mu dawo mu shirya."
Mujaheed ya basa hannu suka tafa yana Fadin"Bari kawai Man har ka Tunamin da Rayuwar Campus..!
Ita Sadiya na zaune ne har suka wuceta suka Zauna Saman Dining da kansu sukayi Sarving din juna suna ci suna Hira jefi jefi ita sai da ta shimfidar da Nihad da tayi barci sannan tazo ta samesu hararan Mujaheed tayi kafin tace"Sweety haka zamu yi..?
Hannu ya Daga yana fadin"Ba ruwana..Taimakon wannan gauron yayan naki nayi da aljannah ta aura"
Me zasu yi in ba Dariya ba Har da Rike Ciki Saifudden har yana kwarewa Sadiya tayi Saurin Zubamai ruwa ta bashi ya sha sai da ya Dawo Daidai yace"Kufa ba azo gidan ku ba..Mugunta bazaku yi ma mutun rowan abinci ba ammh kuma in bai yi wasa ba sai ya dawo mai ta hanci."
Sadiya na Dariya tace"Hamma ban da Sharri..ni da na ke ta rokon ka ka rika zuwa nan kana Dinner in kana garin..!
Saifudden na goge Bakinsa da Tissue yace"Haka kurum Saboda abun kunya gotai gotai dani ina yawon zuwa gidan kanwata..Addata barni kawai na cigaba da lallaba rayuwata.."
Mujaheed na cin abincinsa yace"Zaka iya zuwa bakomai ai kai bakin Bature ne Abun kunya gaba ka basa ba baya ba..!"
Saifuddeen ya take ma Mujaheed kafa shi kuma ya kwace yana Dariya fadi yake"Nan Su Iya suka maka gata ka watsa musu kasa a ido..Allah Sarki Majeeda Ance haka take kuka tana Birgima tana Fadin na shiga uku ya sakeni..!
Yafada yana make Murya Saifudden yayi dariya kamar me Sadiya na Tayasa nan ya basu labarin lekosa da tayi da abunda mahaifiyarta tace Sadiya tace"Allah sarki ai majeeda tayi kuka kamar ranta zai fita..Daman sai iyayi take ta fi sauran dacen miji.
Mujaheed yace"Ke kuwa kaf Lere ai ba kamarsa ga gayu ga ilimi ga Turanci ga kyau ga kudi ga gwamnati..ai Sune gwamnati..!"
Saifuddeen ya mike yana Fadin"Na yafe maka abunda kamin ba laifinka bane ni na kawo kaina."
Walet dinsa ya ciro a aljihun bakin wandon dake jikinsa ya zaro yan Dari Biyar Sabbi bai san ko nawa bane ya Ijiye musu nan saman dining din ya Juya yana Fadin"Addata sai mun yi waya..
Ta mike tana fadin"Hamma da wuri haka..?
Bai juyo ba yace"Nagaji ne ina so naje na kwanta ne.
Sadiya tace"To basai ka kwana anan ba.."
Da Sauri mujahaeed yace"Ai bamu da wajensa anan gidan salon matarsa Aljana tazo masa cikin Dare mu shiga uku kinsan ance basu san mutane.."
Sadiya Hararansa tayi shi kuma yana Dariya Saifuddeen Tsaki yaja ya zura Takalminsa ya fice wayoyinsa duk agida ya barsu Mujaheed ne ya mike yana goge bakinsa ya bi bayansa yana Kwala masa kira da mijin Aljana.
A haraba ya gansa jikin motarsa Tim na wajen ya kame bai ko motsi bama kuma na cikin mota.
Hannu ya basa sukayi musabaha lokaci daya yana Fadin"Zan shigo Office dinka ina so muyi mgana...
Saifuddeen yace"Satin nan ba zan zauna a office ba ina da Sheldule sai dai in na samu Lokaci zan kiraka kazo gidana..!"
Mujaheed ya gyada kai nan sukayi sallama Tim ya budemai bayan mota ya shiga shima ya zagaya ya shiga gidan gaba mujaheed na Tsaye suka Fice Daga gidan har ya koma cikin gida yana kara nazarin wani abu shi fa ya fara wani Tunani ba rami me zai kawo mganar rami..?
Sai Washegari ya samu kiran Kawu suka gaisa yana sunne kai kawu daman ba bakon zafi bane fada kawai yayi mai da Nasiha kafin suyi sallama Mama zuwaira ya kira ita kam Masifa tayi mai kan yadda ya aikata laifi ya bar Ummi aciki shi dai nasa ayi hakuri kafin su rabu sai da tace yazo Gaya tana nemansa aransa ai yasan kwanan zencen abunda su Iya suka Ummi ne zata sauke akansa Mama Zuwaira aikowa ya santa tana da Zafi gata bata Daukan raini.
*******
Zaria..
Muhibba bata yarda ta koma gida ba sai da Sani ya koma makaranta Inna tayi Bikon Tayi bikon Ammh Muhibba tace bazata dawo ba sai Sani ya tafi kuma hakan din ne ta faru sai ranar asabar ta koma Dogarawa shima sai da Ya Habibu ya kira ya lallasheta tana hawaye ta Fadamai cin mutumcin da Sani yayi mata shi kuma yace zai kirasa ya saba mata sannan ta amince ta Dawo su Siyama nata kewa Har ita kanta Ya Habiban da ta rakota suka dawo tare.
Inna na Tsakar gida ita da Anty Zeenatu suna Hira,Anty zeenatu na surfan wake a turmi Inna kuma na gefe tana tsince mata wadanda suka zube kasa wajen surfen sukaji Sallamar Anty Habiba da Muhibba sun shigo Inna ta Saki Mirmishin jin Dadi Tana Fadin"Maraba da Auta..Auta yan Hijara. !
Anty Zeenatu na Dariya tace"Inna sai dai Auta yar daka barkonu..!"
Tafada Tana Dariya Anty Habiba ta kariso Tana fadin"Zeenatu har da ke ko..? Ba ruwana ke da Auta..Inna ni ba amin maraba rako Autarki fa nayi."
Inna ta mike tana Dariya tace"To Habiba ga Auta ina zan lura Dake.
Muhibba kuma rai ta bata zata shige Dakinta Inna tace"Auta ba mgana..?
Muhibba tace"Inna ba wata Auta..Nan kika samu Sani kika manta dani
Inna ta karisa ta riko Muhibba tana Fadin"Waye kuma wani sani..!ai sai in baki wani zai iya karban wannan kambu..Kece Autata kuma sani bai isa ya sauya miki matsayi ba. !"
Muhibba tace"Inna ammh baki mai Fada in yana min rashin mutumci"
Ta karishe fada cikin shagwaba Inna tace"Barni dashi in ya dawo sai ya raina kansa.
Anty Habiba da Anty Zeenatu na musu Dariya Muhibba ta rumgume Inna tana fadin"Yauwa Innata..Tafi ta kowa sona..!
Inna kice mai ya rabani da abokinsa bana son sa ba"a dole."
Inna tace"Shikenan kuwa tunda ba"a so Dole..
Anty zeenatu tace"Auta ba gaisuwa .?
Muhibba tace"Kema ai kin yimin laifi..? Ko biko na baki yi ba..?
Anty Zeenatu tace"Ayi hakuri Auta mun Tuba.!
Dariya tayi kafin ta gaisheta ta amsa Cikin Sakewa Inna ta daukan ma Muhibba jaka har Dakin ta fadi take"Kinga yadda na gyara miki Daki ko..?
Muhibba tace"Nagode Inna Allah ya baki Aljannah..
Inna tace"Ameen ya Allah Auta kema Allah ya baki miji nagari..
Ta amsa kasa kasa nan Inna ta Zauna suna ta Hira da Muhibba,Sai da Anty Habiba ta gaji ta shigo Dakin tana Fadin"Inna kina samun Autarki sai ni kuma kika wareni.."
Inna ta yafitota tana Fadin"Zo ayi dake Habiba kici albarkacin auta..!
Ta zauna tana Dariya Inna ta kara Fadin"Badai zeenatu kadai kika bari a waje ba..?
Anty Habiba tace"A"a tare muka wanke waken har ta bama yaron nan mai mata aike aike yakai mata nika ta shiga shashenta ne nima na shigo nan.."
Inna tace"ai kin kyauta..Zeenatu ai yarinyar kirkice Habibu ya gama yin dace.
Habiba tace"Kema Inna kin yi dacen samun Suruka.
Inna tace"kuma hakane to Allah ya Datar damu.
Daganan suka cigaba da hirarsu bayan an dawo da nikan Suka fita Taya Zeenatu Kulli har da Inna yau a shashen Inna zatayi girkin a icce ta Dora babban Tukunya saboda Baki sannan Anty Habiba tace su siyama ma Daga Hadda nan tace su huto.
Suna yi suna Hira gwanin sha"awa,suna gama wa sukayi alwalan sallar azahar domin an fara Hira Muhibba dai daganan ta kwanta barci Anty Habiba kuma na Dakin Inna suna Hira.
Ranar gidan ta Wuni har Dare ga su Siyama sun zo sun hade dasu Bello suna ta wasa Khalipa dai su yan makaranta ne yana zaune gefe yana Duba Littafinsa Waleed kam sai yamma ya dawo an shiga gari kwallo..
Har Ya habibu ya dawo daga kasuwa basu tafi ba nan aka hade dakin Inna ana ta Hira,acikin Hiran ne Inna ta kallesu shi da Habiba tana Fadin"Habibu kuna waya da Babanku Sunusi na gaya kuwa.?
Ya Habibu yace"Wlh inna mun kwana biyu bamu gaisa ba.
Habiba kuma tace"Inna ni kinsan Tunda aka sacemin waya na rasa lambarsa.."
Inna tace"Baku da zumunci kada ku manta abokin mahaifinku ne sannan mai kima awajensa mutum mai zumunci shi da iyalansa Wlh har kuka kawo girma hatsin Sunusi na isomana Dazu ya kirani muka gaisa yana Tambayana lafiyan ku.
Ya Habibu yace"ZAMU gyara Insha Allahu Inna."
Inna ta kada kai kafin tace"ALLAH yasa ku dai samu Lokaci kuje ku gaishesa ko wanchan zuwan namu ai bamu samu zuwa gidansa ba kuma nasan sai yaji mun zo garin."
Ya Habibu yace"Gaskiya ne Inna zamu gyara..Sani sun kusa fara Exam in suka gama yazo gida sai mu hadu mu tafi Dukkammu har da Muhibba da Zeenatu da yara insha Allahu.
Inna ta washe baki Tana Fadin"Yauwa hakan ya kamata Allah yayi muku albarka."
Suka amsa da Ameen ita Muhibba bata Dakin suna shashen Ya Habibu suna kallo ita da yaran sai da ya bar Dakin Inna ya shiga shashen nasu suka gaisa yana ta tsokanar da ta yi yaji tana Dariya,dawowarsa ne yasa ta tarkatasu siyama suka koma Dakin Inna Abban Walid sai goma yazo Daukansu yana chan babban gidan su sunyi Taro Inna Sai Fada take sun yi Dare Muhibba ta kalleta tana Fadin"Inna bafa motar haya bace ta gida ce .ai ba"a dare a gida.
Inna ta harareta tana fadin"To Sarkin Tsari gayamin yana da mota tunda bansani ba."
Yana Tsungunne yana Dariya shi da Anty Habiba sukayi musu sallama suka fita har waje Muhibba ta rakasu sai da taga tashin motarsu sannan ta koma gida,Dakin Inna suka kwana Daman haka suke watarana su kwana Dakinta watarana Dakin Inna,Muhibba ke hayewa gado Inna ita bata Damu da gado ba tana kan Darduma ma sai barci ya kwasheta Muhibba tayi tayi ta hau gado taki shiyasa take kyaleta inna itama akwai kafiyar tsiya.
Washegari Muhibba bata je ko"ina ba, kayanta ta wanke ta hada dana Inna suna kawo wuta ta hau guga bata gama ba, aka yi sallar la'asar tayi wanka tayi sallah ta shirya tatafi islamiya ta Dade bata Leka ba Dagachan ta wuce gidan mallam Haruna baya nan ma agidan tayi sallar mangariba sai da ta jira ya Dawo tasan in ta koma bata gansa ba Inna sai ta kusa sakata kuka da Mita.
Bayan ya dawo Matarsa ta fadamai zuwan Muhibba yace ta turota bayan tazo suka gaisa yamata tambayoyi tana mafarkin Saifudden..?
Tace A"a yace ta karajin kamshin Turaransa..?
Tace A"a tana jin wani alamu duk ta amsa mai da a"a yace tataba mafarkin ana Saduwa da ita..?
Tace bata tabayi ba,Mallam Haruna ya jinjina kai kafin yace taje gida zai zo gobe da yammah yama Inna bayani haka ta koma ta Fadama Inna Duk ta Damu tana Tunanin wata matsalan ne sai da ya zo washegarin Hankalin Inna ya kwanta daya Jaddamata Saifudden ya Rabu da Muhibba sannan shi bamai cutarwa bane gareta da taimakon Addu"a da Qur"ani ya bar Bibiyatan Ranar Inna Har Sadaka tayi saboda Murna Muhibba ta kalleta kawai batace komai ba sai chan tace"Inna wannan murnan kamar an biya miki makka..?
Inna tace"Ai yafi ma kujeran makka Auta..Allah ya taimakemu Wannan Aljanin ya daina Binki..ai dole nayi murna banda mugunta ina mutum ina Aljani abu ba jinsi ba hallita daya ba..Ai sadaka Dole ne Allah ya raba nagari da mugu..!
Shi kuma yaje shi da Allah."
Muhibba tayi dariya har da rike ciki Inna ta kalleta tana kyafci kafin tace"yarinyar nan baki da hankali.
Littafin Saifuddeen na kudi ne pay N500 via 0552179550 Jamila umar Gt bank,sai a turo evidence of payment ta wannan Lambar *** ko kuma katin waya na Mtn sai adauki Hoton katin a tura ta wannan Layin kai Tsaye *** mutanen mu na Niger kuma zasu tuntubi Kausar aglan Nissa ta wannan lambar domin karin bayani +22796562223 Ina maraba da masoya na a duk inda suke
NIMA MATARSA CE
NIMA MATARSA CE
NIMA MATARSA CE
NA
*HABIBA IMAN IKRA shahararriyar marubuciyar nan ne da kuka sani YAR GIDAN IMAN wacce ta dad'e tana Nishadantar da ku cikin Labaran ta masu Dadi da Ma"ana a lokacin Publishing sosai ta taka rawar gani Wajen baje muku kolin basirarta da Dad'ada'n Labaran ta masu* Fadakarwa da Nishad,antarwa game da Wa"azantarwa nasan bazaku manta da GARIN KALLO RUWA BA,Ko kun manta da Labarin Khaleesat da Faruk..?
Nasan ko kun manta dashi bazaku manta da MUSABABBI ba, Nasan ma bazaku taba mantawa da Labarin MUGUN BUTULCI ba labarin Samiha da Nasir ga BAKIN DUHU,Irin su BABBAR ILLAH labaran ta suna da yawa na sani kun sani alkalaminta bai zo da wasa ba,Saboda yadda komai na zamani ya koma ta Harkan wayoyin zamani sai itama Saboda masoyanta a wannan karon ta fara Rubutu muku SOFTCOPY na Sabon Labarinta mai Taken NIMA MATARSA CE..labarin da zai tabo bangaran zamantakewa har da ma soyayya da Fadarkarwar duka akan Farashi mai sauki N300 Acct: 0673978719
*Acct name:* Abubakar Habiba Imam
*Bank name:GT bank ko kuma a Tuntubi wada'anan Lambobin domin karin bayani *** ko kuma* ***
Janafty