11
SAIFUDDEEN
(Ba mutum ba ne)
Wattpad:JamilaUmar351
Mallakar:Janafty♥️
Amnaf_sudanese _collection
Tana saida original laffaya kala daban daban daga Sudan kama daga na Amare da Kuma casual muna da available a Nigeria kuma Muna aikawa daga Sudan Zuwa Nigeria ko'ina a fadin Jahohi talatin da shida har ila yau dai akwai humra da turarrukka sadidan na matan aure daga Sudan,ba fa anan kada'i muka tsaya ba Muna saida kayan lalle akan sari da Rahusa da kuma siyan Daya,akwai mayuka da dilka da kayan gyaran jiki na ainahin ba Mix ba, wadan'da zasu fitar Miki da fatar ki tas ba bleaching fuskarki tayi haske tayi walwal kina kyalkyali and duk abunda kikeso a Sudan Muna kawo Miki shi har gda Nigeria Amnaf Sudanese collaction ba abunda bama saidawa kama daga kayan kamshin jiki na kaya da na fata +249923097401
🅿️11
Ya dad'e kafin ya iya cire mganar Mujaheed acikin ransa,saboda yana ganin kamar in ya auna mganarsa da kamshin gaskiya in ya tuna abunda ya faru tsakaninsa da Janet shekarun da suka gabata sai dai kuma shi ba ma'abocin yadda da canfi ne ba ne ko Aminta da irin wad'anan abubuwan na Aljanu ba shiyasa sai ya watsar da mganar yasa a ranshi Bai samu Macen dayake so bane ya tabbata Ranar daya hadu da wacce yake so komai zai zama tarihi.
Dalilin haka ya watsar da mganar Mujaheed da kuma Iya dake chan lere ta Damu kanta ko da yaushe cikin saka Baffa Hashimu take yana kiransa tana jadaddamai ya rika shan mgangunar da ta aikomai dashi ana so in ya shanye yazo su koma wajen malamin Tare yayimai bayanin yanayin dayake ji lokaci daya fara shan mganin jinta kawai yake yi baya gaddama amsar sa daya ce to da shikenan shi ko kalan mganin bai taba gani ba suna cikin Booth din Motarsa Tunda Bama ya karbosu bai bada Umarnin afito dasu ba ballatana yaga kalansu abu daya ya sani bayan Farin ruwa da Tea bazai iya shan kowani Ruwa ba mgani kuma indai ba na asibiti bane bai da alaqa dashi.
Achan bangaran Mujaheed shima bai kara mai mganar ba sai ya kyalesa ganin ya nuna bakomai kuma ya nuna mai a fuska bayason mganar ammh kuma agefe daya mujaheed yasan da wani abu jikinsa bai basa Lafiya Saifuddeen yake ba sai dai da bai sa ikon sanin komai ba sai ya kyalesa ammh aransa ya kuduri tayasa da addu"an koma menene Allah yaye mishi,Shiyasa ko da suka sake Haduwa bai kara tadamai mganar ba sai hankalin Saifudeen ya kwanta har saki jiki suka sha Hiransu,Sannan Ko Ummi in ya kirata korafinta yake yazo yayi aure in kuma ta fara fada sai tace kila ma gaskiyan su Iyan ne Aljannar ce ta auresa shi fa in aka fadi haka Dariya abun ke basa kawai sai Aljannah ta auresa Saboda mene..?Shi kadai ne mutum a wannan Duniya da sai shi..?wannan wani abu ne Feeling kuma shi har yanzu bai ji sa kan wata mace ba shi dai abu daya yake fadama Ummi bai samu wacce yake so bane in ya samu zai yi auran in ta sako mganar su Majeeda sai yace baya son su ne shiyasa ya rabu dasu kada ya zauna dasu domin ya farantamusu gefe daya kuma ya kasa Sauke Nauyin dake kansa,Allah ya kamasa,Ummi in yace haka bata iya mgana sai dai tayi shuru..
********
Bayan Sati Uku.
Jiya da daddare aka wayi gari da rasuwar Diyar Yaya sunusi Rahina,yar kimanin shekara goma sha Daya daga ciwon ciki dare zuwa Safe Saifudeen yana office Ummi ta kirasa ta fadamai za"ayi Jana'iza karfe sha daya na Safe yayi mata gaisuwa yace yana da Taro a lokacin ammh in sun fito da wuri zai kamo Hanya in kuma yammah tayi sai gobe kenan da haka suka Rabu,ya kira kawu a waya yayi mai gaisuwa ya fadamai yadda ya fadama Ummi kawu yace in wani aikin ya rikesa ya bari sai gobe za"a wakilcesa da ga suka ijiye kan waya.
Zuwa chan Mujaheed ya kirasa yana Fadamai zai tafi gaya shi da Sadiya Saifudeen yace sai gobe zai tafi Shi yana da meeting Mujaheed yace shi yau in an kaita gidanta na gaskiya zai Dawo kaduna gobe in yana da Lokaci sai su koma tare.
Kamar ya sani bai samu kansa ba,sai Dare yadai kara kiran Ummi ta bama Umma ya mata gaisuwa tunda Ummi ajiyan ita dasu Laala suka je chan Gaya din Sadiya ma Mujaheed yace chan ya barta zata kwana shi dazu da yammah ya dawo kaduna,Suka shirya tafiyan gobe da wuri shi da Mujaheed saboda ba kwana zasu yi ba aranar zasu dawo kaduna.
Washegari tun takwas da wani abu suka fita a motar Saifudeen suka tafi wannan karon Tim ke Driving din Bama ya kame agidan gaba da wani bakin glass Saifudeen na gidan baya shi da Mujaheed da dukkansu ke sanye da manyan kaya Mujaheed shadda ce mai ruwan toka ajikinsa Har da Hula yayinda Saifuddeen ke sanye da wani sauka'ken yadi mai ruwan madara yana da cake cake ajikinsa sannan bai da wani Karfi Dinkin zamani yayi half Jamper sai dai kansa ba Hula gashinsa ya kwanta Daya sha gyara sau tari Saifudeen zai saka manya kaya ammh hula bata cika Damunsa ba,ba domin yana Tara suma ba, sai hulan ne bata dameahi sosai ba,kuma yana dasu kala kala kafarsa Takakmi ne sawu cikin kalan brown Na Fata mai kyau yana kyalli.
Hira suke yi Jefi jefi yayinda Saifudeen ke rike da Tab dinsa yana Duba karatun da sukayi na wannan Satin da bai samu duba ko Daya ba shima Mujaheed din waya ce a Hannunsa yana dannawa sanin Halin Saifudeen kayi ta mgana yayi kamar bai jika ba...
Sun bar kaduna sun Dumfari Hanyar Gaya Mujaheed kamar wanda ya Tuna wani abu ya dago da Sauri yana kallon Saifuddeen da hankalinsa ya tafi kan abunda yake karantawa Cikin Tab din tasa cikin Tambaya Mujaheed yace"Saifudeen kasan kuwa Director musa ya Kirani shekaran jiya...?
Saifudeen yadda ko motsi bai yi ba sai Mujaheed ya zata bai jisa bane har zai kara maimaita mganarsa sai yaji yace"Ta ina zan san ya Kira ka Tunda ni bai kirani ba."
Yafada hankalinsa na kan abunda yake yi Mujaheed yace"Ko bai kiraka ba nasan ya aiko maka da sakon da nima ya aikomin dashi.
Saifudeen ya tabe baki kafin yace"Wani Sako..?
Mujaheed yace"Kana wani abu kamar baka san komai ba..Invitation card na Speach din da yara zasu yi wacce makaranta ta shirya tare da Bikin Murnan makarantar ta cika shekaru shidda kafuwarta..!"
Saifudeen na jinsa bai ce komai ba kuma hankalinsa na kan Tab dinsa bai ko juyo ya kalli Mujaheed ba shi kuma ya cigaba da Fadin"Ya fadamin ya Tura maka komai tundaga farko Tsarin sannan yayi maka mganar Zuwanka nada muhimmanci a matsayin Bako na musamman,ammh kuma ya nuna min bakace komai har yanzu."
Saifudeen kamar bazai yi mgana ba sai daya nishadu sannan yace"Bazan samu zuwa bane shiyasa ban ce komai ba."
Muhajeed yace"To saboda wani Dalili..?
Saifudeen yace"Ina da Dalilina..Sai dai bai zama dole sai kaji ba."
Mujaheed yayi karamin Tsaki kafin yace"Kada Allah yasa kaje din kai ka sani ina ruwan wani..?.
Ya bashi amsa da Babu shima kai Tsaye Daganan kowa ya Dauke kansa har suka shiga garin Gaya ba wanda ya kara tanka wani..
Sun iske su kawu a waje suna karban gaisuwa Har da su Datti da Mudanasir sun zo garin suma ajiyan,nan suka fara zama aka gaggaisa,Kawu ya kalli Saifudeen da kansa ke duke yace"Saifudeen mutanen Lere kenan..Kai dai baka son saka Hula ko..?Baka san Cikon Shigar Hausawa da kamala itace Hula ba..?ko baka ga dan"uwanka bane..?
Saifudeen mirmishi kawai yayi kansa na kasa bai ce komai ba Isma"il na gefe yace"Baba gayu ne fa..ya tara gashi sai ya rufe shi da hula..?Hamma Saif wlh i like ur Staryle..!"
Kawu ya hararesa yana Fadin"Rufemin baki mashiririnci banza kawai."
Akayi dan yi dariya su Baba Surajo na wajen yazo gaisuwa ya kalli Saifudeeen kafin ya kalli kawu yana Fadin"Alhaji Sunusi Kar dai kace min wannan yaron d'an wajen Kanwar ka Zaliha ne da Marigayi Sojan nan mutumin Lere..?
Kawu yayi dariya kafin yace"kwarai shine..Ka tuna sanda muka Daura auran su a masallacin mai gari ko..?
Baba Surajo na kallon Saifudeen da kansa ke kasa yace"Allahu akbar..Rayuwa ba wahala..Allah ya rayasu shi kadai ne ko..?
Kawu yace"A"a akwai kanwarsa Sadiya..tana cikin gida Itama ita ke auran Mujaheed gashi nan yaron dan wajen dayar kanwar tawa Zuwaira ba."
Baba surajo yace"Ikon Allah anyi haka kuwa..Tabbas Allah yasa albarka Dayake yanzu zumunci yayi Rauni shiyasa duk ba"a san juna ba.
Kawu yace"Wlh kuwa ko Ita Innar Habiba rabonta dashi tun yana yaro bana jin ko Zalihar ma zata gane yanzu in ta ganta kila har gwara zuwaira ma...Zumunci ne sai a hankali kuma kaga anyi nisa suna Zaria haduwa tayi wahala.
Baba Surajo yace"Hakane kam ai munyi mgana da Habiba yace Zasu zo shi da Innar tasu yau ko gobe.
Kawu yace"Nima ya kirani..Nace wlh suyi zamansu ma don su matsa ne."
Saifudeen ya kallah dayake chan suna gaisawa da su Datti ya saka baki ya kirasa sai gashi ya Dawo gabansa ya Zube kansa ya Dafa yana Fadin"Dago ka kalleni Saifudeen..
Ba musu ya Dago Baba Surajo ya nuna mai yana fadin,'Kaga wannan..?
Saifudeen ya daga kai Kawu ya cigaba da Fadin"Shima baban ka ne..Yaya yake wajen wani Tsohon Aminina wanda shine silar arzikina..Allah yajikan bello da gafara.
Saifudden da Baba Surajo suka amsa da Ameen kawu ya cigaba da Fadin"Su suna nan Gaya da zama babban gidan su bai da nisa da nan..Sai dai iyalan marigayi bello sun koma Zaria tun kafin rasuwarsa..Watarana duk zakusan juna shima yana da iyalai."
Saifudeen kansa na kasa yace"Insha Allahu..,daganan ya juya yana kara gaida Baba Surajo ya amsa yana ta saka albarka Daganan cikin gida suka shiga su hudu da Muhajeed da Datti da Mudansir sai Saifudeen din..
Falon yana cike da baki yan gaisuwa da Dangin Umma karama tunda Diyartace kanwar Suwaiba nan suka yi musu gaisuwa daganan suka shiga Dakin Umma babba sukayi gaisuwa inda suke iske su Ummi adakin,Saifudeen ya gaisheta ta amsa tana tambayansa ayyuka yace Alhamdulillah,Dayake da Mutane bata tsaya bi ta kansa ba daganan suka fice zuwa Dakin Mama Zuwaira suka iske yara yaran duk suna ciki har da Sadiya Mama Zuwaira kuma ta shiga Tiolet din dake Dakin da farko Dakin ya kaure da hayaniya ammh suna jin Sallamarsu kowacce ta natsu sai Laala na ganin har Hamma suka shiga Taitayinsu shi daga baya ma ya Tsaya yana jin Datti na musu Fadan gidan mutuwa gidan Hayaniya ce..?
Sadiya ce ma tasa suka shigo Dakin suna gaisawa Hannu ta bama Hamman nata suka gaisa tana Fadin"Hamma na idon ka kenan..?
Mirmishi yayi mata kafin ya Dafa kafadarta yace"Addata ta.!
Lokaci daya yana Jan dogon Hancinta Mirmishi tayi kafin taje wajen mijinta su gaisa,Saifudeen fita yaso yi sai ga Mama zuwaira ta fito daga Tiolet Nihad dauke a Hannunta ita tayi ma wanka Tana fitowa ta gansu Tsaye tace"Lafiya ku kuma kuke tsaye kamar wasu zakaru..?
Sai kuma ta juya tana mikama Sadiya Nihad fadi take"Karbi yarki bata da aiki sai kuka.."
Mujaheed ne ya karbeta Tana cikin Zani An nadeta,yana fadin"Kai Mama da har naso mu baki ita har sai kin aurar da ita.."
Hararansa tayi kafin tace"Ba wanda zan yi ma wahalan ya"ya nima da nayi wahala da nawa ya"yan ba wanda ya taimakeni.
Su Laala ta kalla tana fadin"Baku da kunya ko..?kuna ganin yayinku a tsaye bazaku fita ku basu waje ba..Suna Tsaye ku kuma kuna zaune."
Sum sum suka fara fita Daya bayan Daya Mama zuwaira ta rakasu da Harara Lokaci daya tana Fadin"Marasa kunya yara kawai."
Gefen gado ta zauna kafin tace"Ga Cafet ne basai ku zauna ba kun wani Coge min a tsaye..!"
Dole suka nemi cafet suka zauna agabanta Mujaheed ya fara gaisheta ta amsa bayan yayi mata gaisuwa sai Saifuddeen sai da ya gaisheta sannan ta Rike baki tana fadin"Saifudeen manyan gari i donka kenan..?
Ni da kaina daka kirani nace kazo ina nemanka shuru..Mujaheed yazo na ce ya fadama ka,kai ko baka Fada masa ne..?
Da Sauri mujaheed yace"Wlh Mama na Fadamai Allah ne shaida na.
Sadiya na gefe nata Dariya Datti yace"Mama ai fa sai kin hadama Saifudeen da duka domin naga bayajin mgana."
Yafada yana kallonsa Hararansa yayi bai yi mgana ba kansa na kasa,Mama zuwaira tace"Rabu dashi ya raina mu ne shiyasa.."
Saifudeen yace"Kiyi hakuri Mama....
"Kiyi hakuri mama aiki ne ya rikeni shiyasa baki ganni ba ko..?
Mama Zuwaira ta katseshi Da fadin Haka Lokaci daya da kwaikwayan muryan Saifudeen din gabadayansu suka Fashe mata da dariya Saifudeen ma sai da ya murmusa,bai dai ce komai ba Murya ta kara dagawa tana Fadin"Ko ba Haka zakace ba..?
Saifudeen na sosan kansa yace"Eh Mama ina ta son nazo sai dai ban samu Dama ba.!"
Mama zuwaira tace"Karyan banza ammh ai kaje lere ko..?
Dangin Uban naka da suka gama Zagin Ya zaliha dukanta ne kadai basu yi akanka ba Kuma duk uban wa ya ja in ba kai ba..!Sai gashi ka wanke kafa kaje ka lallashesu da wannan Dadin Bakin naka da ka saba siyan mutane dashi to ahir dinka ni Taushin Bakinka baya sani naji Tsoronka daman nace sai nayi maka Fata fata in dai bazaka rika gudun bacin ran yar'uwata ba..Kana ja mata tozarcin Dangin Ubanka marasa mutumci to akan ka zan dinga saukewa whl..Ina Dalili Tsohuwa kin tsufa baki Daina Bala"i ba Ita da wannan goggon taku mai kama da kadar yan ruwa.."
Ta karishe Fada tana kufan baki Dariya ta kusa subucema Su Datti sukayi saurin Dannewa shi kuma Saifuddeen kansa na kasa bai kara wani motsi ba har Mama zuwaira ta gama Fadanta sai kuma ta koma tana Fadin"Ai naji dadi da ka saki yarinyar nan Allah ya kara..In ba kwadayi ba Ina Yaro ina wannan bakauyiyar yarinyar..?kun hada na Farko ya nuna bai so ya saketa to basai ku hakura ba..ai gwara da kayi mganinsu Naga kuma yanzun in zasu kara wannan karambanin auran wannan zamanin ma miji ya ganka yace yana so ya aureka ya ka kare..?Ballatana an cusamai ai sai abunda Allah yayi.
Datti yace"Hakane Mama Allah yasa mu dace.
Hararansa tayi kafin tace"To ai baka da maraba dashi..Kaima ai ina jiranka..Kaje chan garin Arna kayi zamanka ba mata sai wad'anda iyayensu sukacee suje sa gani ko..?
Da Sauri Datti yace"Wlh ba ruwana Mama."
Tana yar dariya tace"Kudai kuka sani..Dukkanku Allah yayi muku albarka kun sani in nayi fada sai nazo kuma na sakama ya"yana albarka.
Suna Mirmishi suka amsa mata,Sadiya tama mgana tace ta kawo musu abinci sannan tatashi ta fita Tana fita Mujaheed ya kwashe da Dariya Saifudeen ya daga mai hannu yana Fadin"Mallam ka kyaleni naji da Daya mana..wannan fadan na Mama ai 10×10 ne..!
Gabadayansu suka kwashe mai da Dariya Datti yace"Ai da naji ka saki wannan Sweet bby din nan sai da naji Haushinka."
Saifudden yace"baka makara ba ko yau kaje za"a daura muku aure Daman ai ban bata idda ba.
Mudansir yace"Shikenan kuwa.
Datti yace"Ai ni ban ce ina sonta ba..Kuma ai sun san dani din suka Zabe ka suka baka sun ga kana ta zama gauro ba mata..
Saifudeen yace"Ok kai Tuzuru ne kenan..?
Nan ma Dariyan suka saka Datti sai Caccakansa yake shima yana ramawa Har Sadiya ta kawo musu kayan Tea da Kofuna sai Doya da kwai Sai soyayya kwai da buredi data soyama Hammanta taTusamai filet din gabansa Tana fadin"Hamma nasan baka cika son kwai da Doya ba"
Ya kalleta yana Fadin"Allah yayi miki albarka Addata.
Ta amsa da Ameen tana Dariya ganin yadda Mujaheed ke hararanta Datti yayi kasake kafin yace"Sadiya kina son samun Aljana kuwa..?kin Tsallake mijin ki kin je kina kokaron ji da wani katon daya Dace yana da matar da zata ji dashi..Kin kuma Tsallakemu mu yayyinki ko..?
Sadiya na dariya tace"Hammana bai da kowa sai ni fa kadai...Marayan Allah.
Mujaheed yace"mu kuma muna marayu ne..?
Ya karishe Fada yana kara hararanta kunnenta ta kama tana Fadin"Haba mana Sweety..!
Saifudeen dai ko tankasu bai yi ba yahada tea dinsa ya fara sha domin bai ci komai ba ya fito daga gida,yana shan Tea,yana hadawa da soyayyan Buredinsa Datti ya lekasa har yana kai hannu ya dauke ya juya musu baya Mudassir yace"Tsakani ga Allah an nuna son kai anan wajen.
Mujaheed yace"indai kan wannan katon banza ne kadan kagani indai Sadiya ce!
Ita dai ficewa tayi ta barsu suna ta caccakan Hammanta bai san ma sunayi ba ya juya musu baya,sai da suka gama koshi sannan suka fice kofar gida wajensu kawu,har La"asar suna garin Gaya sai da sukayi sallar La"asar ne sukayi shirin Tafiya,Sadiya sai gobe zata biyo su Ummi su sauketa Kaduna su wuce Abuja,Cikin gida suka shiga sukayi musu sallama sannan suka fito kofar gida su Datti sun rakosu bakim mota su Tim daman Tun zuwansu suna bakin mota kamar ita suke tsaro.
Da zasu yi sallama da Kawu sai yayi ma Saifudeen Nasiha fadi yake"Baka sha"awar Dan"uwanka Saifudeen..?ka isa aure kana da abun yin auran nan me zai hana kayi ko domin ka saka zuciyar Mahaifiyarka tayi sanyi..In wadanchan baka son su ai sai ka zaba ga mata nan birjit daidai da Zabinka duk yarinyar da kace kana so ko yar gwamnace wlh bamai cewa bazai baka ba Don Allah kayi Tunani kaji ko zama haka din ba amfani.
Sun kama Hanyar barin Kano Saifudeen yace"Zuwana Gaya yau ban je a sa"a ba..Fada ne nasha shi Step by Step.."
Mujaheed sai kwasan Dariya yake yi Saifudeeen yace"Wlh kamin shuru kafin na Sauke ka a dajin nan..
Mujaheed yace"Ai ba wulakantattace bane ni..Balle in ka Saukeni na wulakanta.
Daga haka suka bar mgana Daganan ma kowa sai ya koma Danna wayarsa,Sun shiga kaduna bayan mangariba har gida suka kai mujaheed sannan ya wuce gidansa Ranar bayan ya gama abunda zai yi ya kwamta mganar kawu sai ta Dawo mai to shi a ina zai samu wacce ta Dace dashi?
Ina take..?
Wacece ita..?
Kuma zai ji ya fara sonta.?.
Shima yana so yayi auran zabin sa ko domin Farimcikin Ummi ammh wacce zau auran ne wacce zata Dace dashin bai gani ba har yau duk da ga tarin mata nan kala kala masu kyau da Nasaba da ilimi har yau bai ji in ya kallesu yaji wani abu so in ya auresu zasu iya taka matsayin da su Majeeda suka taka suma shima bai taba kwantatawa ba Har barci ya kwashe shi bai samu mafita ba.
Washegari Zaria ya shigo Yana da lecture karfe10 na safe bayan ya gama Dasu Kaura ya wuce daganan Saboda Duba aikin kwangilan makarantar da gwamna ya bada har an fara dagachan yayi zagaye sosai sai yammah ya Dawo gida duk ya gaji aikin al"umma daman sai an Daure.
Suma su Inna da Yaya Habibu aranar sukaje gaya din ta hadu da Ummi da Mama zuwaira sun dade basu ga juna aka zauna aka gaisa da tambayan bayan Rabuwa sun yi gaisuwa sannan sun karisa gidansu Inna ta gaida Hajiya,da su goggo Naja sannan tayi musu Allah sanya alheri da Ranar da aka sanya ma Autar Inna Firdausi Basu kwana ba aranar suka juyo zuwa zaria.
********
*Zaria.
Muhibba ta Zage Damtse batayi wasa da aikin da D.Musa ya bata ba,wani karin jin Dadinta Taimakon Hafiz gareta sai abun yazo mata da Sauki Cikin ikon Allah yaran sun yi Rizahal kuma komai ya tafi daidai bangaran Drama ma haka ranar kawai ake jira sannan an tsara za"a raba kyattuka ga Prefect da Dalibai masu hazaka da wadanda suka ci duka Quiz da Debete din da za"a gudanar.
Komai sun shirya kawai suna jiran Ramar ne tunda Har Daliban SS3 din sunfara Neco,An buga Invitation card an saka acikin Farin Mblog an bama kowani Dalibi ya kai ma iyayansa sannan an yi na waya an Turama wadanda katin bazai je hannunsu ba,Duk da dai mai makarantar yace Iyayen yara kadai ya amince a gayyata bayason yan Siyasa ko wasu masu Mulki makarantarsa bata yan siyasa bace bata masu mulki bace shiyasa ba wani sunan wani bako ajiki banda Babban bako Wato shugaban makarantar sai iyayan yara da yan"uwansu kawai.
Duk da basu da tabbacin zuwanshi ammh Dan"uwanshi ya Tabbatar ma da D.Musa zai hallata insha Allahu shiyasa sai ya samu yakini.
Bayan sun gama da wannan bangaran sai bangaran tsara Halla da Mc da zai gabatar da wajen Wannan Uncle James zaj ji da bangaran,Sai kuma barayin Snkas da za'a raba da lemuka Shi kuma Uncle Hafiz yace Muhibba ta iya irin wadanan abubuwan ita da yayarta,Sai D.Musa ya ce tayi lissafin abunda za"a kashe na Meatpie da Cake da Donut,Ruwa kuma da Lemu mota guda ce zata zo ta sauke shi basu da matsalan wannan bangran gift kuma Hafiz da sauran malaman sun Tsara shi Daki daki Daga matakin Farko har zuwa mataki na wanda yayi na uku.
Muhibba gidan Anty Habiba taje ta Fadamata abunda D.Musa yace,Duka kowanne yana son Spicess 400 ne aikin da yawa tare suka zauna suka Lissafa komai da komai,washegari da taje makaranta ta fadamai yace ta bashi acct Number dinta in lokacin ya kusa zai Tura mata kudin Komai da komai harda na Ladan aikin.
Su Khadija basu sani ba Dayake ba"a gaban Mutane akayi ba,Hafiz ne a wajen dasu Headteacher kuma ai ita bazataje ta fada ba ballatana Hafiz Dayake Namiji,Ba wanda ya sani sai Anty jidda ita kuma ba Shashensu daya da Su ba ballatana su dameta iyakarta dasu gaisuwa in sun hadu.
Kwanci tashi ba wuya a wajen Allah gashi har Taron ya matso ana Saura Sati Daya D.Musa ya turo ma Anty Habiba kudin abunda za"a kashe har da 20k kudin aikinta Daman Acct Nomber dinta Muhibba ta basa,ta Kirata tana fadamata tace ta kirasa ta mai godiya bata da lambarsa sai ta shiga group dinsu na Managent na makaranta dake manhajar WhatApps,ta Dauka ta kirasa tamai godiya yace kada ta damu she Deserve it,Suna tsakar gida Ranar Asabar din ita da Inna tana tayata bare waken Yaya Habiba na gona da aka ciro,Inna ta shanya sai da ya Bushe suka zauna suna barewa Dayake ma bai da wani yawa irin karshen gona ne.
Suna barewan suna hira Tana Fadama Inma yadda sukayi da Yaya Habiba Inna tace"To yaushe ne Taron..?
Muhibba tace"Inna Saura kwana bakwai fa Rana ita yau ne.
Inna tace"Allah ya kaimu..Sau kuyi musu da wuri saboda su ji dadin aikin naku kunga in sukaji dadi sai ima wata makaranta zata yi sai kuji an yaba da aikin ku har kun ci gaba."
Muhibba tace"Hakane Inna..Anty Habiba tace nazo Tun ranar Laraba ne mu fara aikin tunda yana da yawa kilama sai ta kira kanwar Baban Waled Asma"u ta tayamu.
Inna tace"Eh to sai ta kira ta din Allah ya taimaka.
Kafin Muhibba ta amsa da Ameen Sani yayi sallama ya shigo gidan,Sanye da riga da wando,sai Katuwar bakar jaka goye a bayansa sai Akwatinsa trolley yana ja Muhibba ta waiga ta gansa ai sai ta saki aikin Inna ta Nufesa tamai oyoyo ta Daka Tsalle ta Rumgumesa tana Fadin"Oyoyo..oyoyo..!
Riketa yayi tana neman kada su Cikin Dariya yace"Inna me kika bama Autar naki ne ta kara girma haka.
Yafada yana dariya Dayake sun shirya Tuni sun daina gaba.
Inna da bakinta yaki rufuwa tace"Maraba da sani.maraba da kanawa..!
Muhibba ta sakeshi Lokaci Daya tana karban Akwatinsa ta sa hannu taja jakar bayansa yace"Ke ban da wannan..yara basa tabawa.
Baki ta tabe kafin tace"Ai nasan Shopping din yan matanka ne cike a cikin Jakar..!"
Yana karisawa gaban Inna yace"Eh sune acikin ina ruwanki..?
Muhibba ta ja akwatinsa zuwa Dakin Inna Tana fadin"Babu fa.
Gaban Inna ya durkusa yana gaisheta ta amsa cikin Fara"a tana fadin"Dawowa ba sanarwa Sani haka ake yi..?
Yana dariya yace"Inna suprise nake son baku..mun gama jarabawa tun wanchan satin na tsaya wani abu ne yasa ma kuka ganni sai yau.
Inna tace"Masha Allah haka jiya yayanku sai cewa yake yana Tunanin kun gama jarabawa baya samun wayarka yace Auta tace kasheta kayi saboda jarabawa.
Sani yace"Eh Inna saboda mutun ya natsu waje daya..
Inna tace"Hakane kuma Allah ya bada sa"a gashi Tuwo Muhibba tayi mana da Rana Zeenatu na kaduna kanwarta ta haihu yau suna.
Sani ya bata rai kafin yace"Tuwo kuma Inna..?
Muhibba ta fito tana Dariya tace"Miyar kuka ce ammh kada ka damu taji kifi.
Hararanta yayi kafin yace"Muguwa ai nasan ke zaki tursasa ma inna ayi tuwon nan..Kije don kanki muhibba.
Dariya ta sakamai har da gwallo ya nuna kansa alamun ni ta daga kai ya kallli Inna yana Fadin"Inna ki na ganin Abunda Autarki kemin ko..?
Salon na maketa Ya habibu ya dawo ta Fadamai yace nayi zalunci.
Inna tace"Rabu da ita yau kaine Autana me zakaci na tashi na Dafa maka.?
Yana kallon muhibba yace"Inna Shinkafa da wake..ammh ki bar muhibba ta dafa min.
Muhibba na tsaye tace"Tab ai ni tuwona har dare nayi ni da shiga kitchen sai kuma gobe.
Sani ya mike yana fadin"Yarinya nazo miki da gurasa fa..!"
Muhibba ta washe baki tace"Da gaske..?
Sani yace"Ki dafamin abinci na baki..In kuma kikayi mungunta to kanki zata kare."
Muhibba tace"Inna kina ji ko..?
Inna na Dariya tace"Naji kina gamawa zai miko miki gurasarki"
Yana dariyan keta yace ya yarda jikin Muhibba na rawa ta fada kitchen din Inna tana Fadin"Yanzu za"a gama.
Sani sai dariya yake mata Inna ta dauko mai key din Dakinsa ya Bude duk yayi kura afili ya furta"Muhibba bata da mutumci irin kanne masu kirki kiga suna gyara dakin yayansu banda yarinyar chan."
Karsheta dai shi ya zage ya gyara yana gamawa ana kiran sallar La"asar ya fita yaje masallaci bai dawo ba sai wajen Biyar koda ya dawo Muhibba ta gama mai shinkafa da wakensa datace ya fito da gurasa yace ta bari yaci ya koshi yana gamawa suka mike zuwa Dakinsu inda zai Dauko mata suna zuwa Zaure ya arce a guje yana Fadin"Kin yi aikin Allah Autar Inna.
Muhibba ta cije yatsa kamar tayi kuka ta koma ta na Fadama Inna,hakuri kawai ta bata itama Auta ta manta Sani ne ita daman ta sani ya mata wayau ne kawai.
Littafin Saifuddeen na kudi ne pay N500 via 0552179550 Jamila umar Gt bank,sai a turo evidence of payment ta wannan Lambar *** ko kuma katin waya na Mtn sai adauki Hoton katin a tura ta wannan Layin kai Tsaye *** mutanen mu na Niger kuma zasu tuntubi Kausar aglan Nissa ta wannan lambar domin karin bayani +22796562223 Ina maraba da masoya na a duk inda suke
Janafty