ZINARE 2

28

by @nafisatusasaal01

SULAIM
Tun lokacin da Malik ya ce ya ɗaure Naila zuciyarsa ta canza bugu rauni ya shigesa, ɗorawa da bayanin mutuwar Kaka da sam bai san da shi ba yasa ƙwalla  tararwa idanunsa har suka ɗan gargaro su ka taɓa gashin ƙasar idonsa..

Bai daina kallon Malik ba, har sai da Malik ya tsargu ya ɗan ɗago kansa suka kalli cikin idon juna.

Ƙwallar da Malik ya gani a ƙasan idonsa ne yasa shi rintse nasa idon yana jin zuciyarsa a ƙuntace. 

Sun ɗan ɗauki mintina a haka sannan Sulaim ya fara magana da muryarsa da ke fita a hankali;

"Dukiyar Dhahab da ƙarfin ikon ka a cikinta ba zai tabbata gareka kai kaɗai ba har sai shaiɗan ya yi kutse a cikin al'umuranka Malik, shiyasa nasa Sadiq Ma'aikaci na musamman  kula da motsinka a matsayin mai bawa shuka ruwa.. laifinka gare ni mai girma ne, saboda  laifi ne da ya shafi lafiyata da Raina,  ko mutuwa na yi Naila  tafi ƙarfin ɗauri  a wajenka da duk wani jami'i ko Ma'aikacin cikin Dhahab, domin ita ba a madadin Budurwata ko Matar da zan Aura take ba, amadadin rayuwata take, ba bu wani tsanani da zai sauya soyayyata a  zuciyar Naila har ta yi yunƙurin kasheni da gan-gan.. kai ma kuma Matsayinka gareni ya fi  gaban na kasa yi maka afuwa akan duk girman laifin da za ka aikatamin, sai na taɓamin rayuwa da kayi... Amma duk da wannan matso na ji ɗuminka Ɗan Uwana"

Da wani irin takun da ya haɗe da zafin nama Malik ya isa ga Sulaim suka ƙanƙame juna, kafin kowannensu ya saki kuka...

Itama Farheen hawayenta ta share tana zaro wayarta, Ummi Aysha ta kira sai dai bata ɗaga ba, don haka tayi maza ta ɗaukesu hoto ta tura mata idan ta samu lokaci ta gani..

Tari ne ya sarke Sulaim, ya hau yinsa babu ƙaƙƙautawa, a hanzare Malik ya sakeshi yana ɗan shafa bayansa, Farheen kuma ta fita dasuri kiran Likita..

Har mataimakin Dr. Nabil da shine a Asibitin ya iso Sulaim bai daina tari ba..

Farheen da Malik reception suka dawo, domin bawa likita damar aikinsa.  
Kasa zama sukayi saboda fargaba.

Tarin Sulaim  bai tsagaita ba har sai da Dr.Nabil ya iso da kansa..

Ɗaki Dr. Nabil ya sa aka canzawa Sulaim zuwa wanda suke iya hangosa ta gilashi ba sai sun shiga ciki ba.

Bayan komai ya dai-daita Dr.Nabil bai yi musu wani dogon bayani ba, ya dai ce musu babu wanda zai ƙara shiga Inda Sulaim ya ke sai dai su zo su ganshi kawai, har ya sai ya ƙara samun sauƙi...

Jiki a sanyaye suka bar Asibitin zuwa Masauƙinta Farheen...

NAILA

Bata tsara dawowarta wajen ƴan uwan Mahaifinta ba nan kusa ba, har sai Sufyan ya gama aikin da ya kawosa ya koma Babban Birnin Abyad, saboda har cikin zuciyarta ba ta jin soyayyarsa ba kuma ta son ƙara ganinsa..

A ɗaki kullum take wuni, sai ta ga dama take fitowa tsakar gida su yi hira..

Ranar wata Asabar ta na maƙale a ɗaki, ta ji yaro ya ce ana Sallama da Kakanta, wai baƙine daga Yankin Tudu..

A kwance take tana jin ance Yankin Tudu ta zabura ta zauna tana zare ido sai dai ba ta fito ba, domin bata raba ɗayan biyu ko Sufyan ne ya zo nemanta ko kuma Kawunta ne ya biyota, tunda ta anshemai jari ba tare da ta cigaba da ƙera kayan sana'ar da ta ce zata yi ba..

A can waje, da farin cikin Kakan Naila ya amshi su Kawu, bayan sun gaisa ya ƙara dawowa cikin gidansa ya yiwa mai ɗakinsa magana tayi musu shimfiɗa a wadaccen tsakar gidansu. Duk Naila ta jinsu amma bata leƙo ba, sai ƙara ma kwanciya da tayi ta rintse idonta kamar mai barci.

Bayan su Kawun Naila sun shigo, anƙara gaisawa, sai Babban cikinsu wanda ya tattauna da Sufyan ya fara korowa Kakan Naila bayanin abinda Sufyan ya zo da shi, da kuma su a nasu  ɓangaren shawarar da suka yanke na gara Naila ta koma wajen tsohon mijinta duba da ƙaracin shekarunta, amma ba su san shi mai zai ce ba, ita kanta Nailan, shiyasa suka yi tattaki tun daga Yankin Tudu zuwa Yankinsu, domin a samu masalaha a junansu..

Ɗan jim Kakan Naila ya yi, shima a cikin zuciyarsa ya fi son ace Naila ta komawa aurensu da Sufyan akan ace ta sake yin wani, tunda Sufyan ba shi da munanan ɗabi'un Mahaifinsa..

Shirunsa ya ɗan ɗauki lokaci sannan ya ce;

"Ni ma zan fi son Naila ta koma Gidan Sufyan, tunda halayyarsa sun sha ban-ban da na Mahaifinsa, amma ba zan yi gaggawar yanke hukunci ba, zan zauna da ita mu tattauna na ji ita menene na ta ra'ayin, duk abinda muka yanke zaku ji a bakinta"

Kai Ƴan uwan Mahaifin Naila suka jinjina suna yi masa godiya. 

Ba su wani jima ba, bayan taɓa abin shan da aka gabatar mu su, su ka fara haramar tafiya, sai a lokacin Kakan Naila ya fara ƙwala mata kira, amma tayi biris kamar mai Barcin gaske, har sai da mai ɗakinsa ta fito daga ɗakinta ta leƙa wanda Naila take ciki..

Amsar Naila ta na barci ta bashi, sannan ta bar ɗakin.

Babu wanda ya gamsu Dagaske Naila barci takeyi amma sai duk sukayi shiru kowa ya barwa zuciyarsa.

Duk tattaunawarsu Naila ta na ji, kuma har cikin ranta bata jin zata ƙara karɓar Sufyan a karo na biyu a matsayin Miji, domin idan ta tuna azabar da ya gana mata a Birnin Abyad da zuri'arsa da sukayi sanadiyyar mutuwar Mahaifiyarta sai ta ji ta tsanesa ko ganinsa bata son yi.

Da dare ya yi, Kakanta har ɗaki ya tura Kakarta ta kirata..

Kamar yadda Kawunta ya zayyane masa bayanin abinda Sufyan ya zo da shi, haka shima ya zayyane mata sannan ya ɗora da;

"Kar ki waiwayi komai Naila, ki fuskanci gobenki, mu da dake bamu isa mu halatta abinda Allah Ya haramta ba, kuma ba mu isa mu haramta abinda Ya halatta ba. Shawarata gareki tunda bazan tursasaki ba, ki bawa Sufyan dama ya dinga ziyartarki kafin komen aurenku mu ga kamun ludayinsa, shin Dagaske ya canza ko kuma bai canza ba yananan a waccen Sufyan ɗin..
Ina so ki rabu da kowa lafiya Naila, duba da yadda ƴan uwan Mahaifinka da mu kanmu muke son ki a yanzu kuma muke son komen aurenki da Sufyan, bijiremana da ƙin karɓar shawararmu zai kawo nakasu a soyayyar da muke yi miki, amma idan kika karɓi shawarata ki ka ba shi dama kuma ki ka dage da addu'a, idan shi ɗin ba alkhairi ba ne cikin ruwan sanyi Ubangiji zai kawo miki mafita ta inda baki taɓa tsammani ko hasashe ba, ko ya ya kika gani?" ya ƙarasa faɗa yana Kallon mai ɗakinsa dake zaune a gefen Naila.

Na'am tayi da zancensa sannan itama ta ɗora da ta-ta nasihar.. 

A wannan dare suka lallaɓa Naila ta amince washe gari zata koma Yankin Tudu..

Da Naila ta koma ɗakinta Barcinta tasha, domin babu batun wani Sufyan da zai hanata runtsawa, ta haƙura ma da tunanin Sulaim tayi barci balle wani  Sufyan da bashi da wani matsayi a wajenta..

★washe gari ranta ba daɗi tayi wanka ta shirya. Har kuɗi Kakanta da Kakarta suka ƙara mata akan jarin da ta ce Kawunta ya bata, sunyi mata nasiha tare da ƙara jamata kunnen ta dage da addu'a babu sanya, In Sha Allahu zata ga komai ya zo mata cikin sauƙi..

Har tasha Kakanta ya yi mata rakiya ya sata a Mota..

Naila tana sauka a tashar motar Unguwarsu ko Gida bata  shiga ba aka kaiwa Sufyan labari, ga Nailarsa can ta dawo😄...✍🏻


Jiya Network ya yi tsiya page 27 ya yi published har sau biyu, kuma da yawa wasu sun buɗe dukka ba su sani ba, ku yimin afuwa sharri network ne, amma yau ga wannan paging a free madadin kuɗinku na jiya...