FreeThe story
Synopsis
No synopsis yet.
About the author
Novelist
Sample · 28
SULAIMTun lokacin da Malik ya ce ya ɗaure Naila zuciyarsa ta canza bugu rauni ya shigesa, ɗorawa da bayanin mutuwar Kaka da sam bai san da shi ba yasa ƙwalla tararwa idanunsa har suka ɗan gargaro su ka taɓa gashin ƙasar idonsa..Bai daina kallon Malik ba, har sai da Malik ya tsargu ya ɗan ɗago kansa suka kalli cikin idon juna.Ƙwallar da Malik ya gani a ƙasan idonsa ne yasa shi rintse nasa idon yana jin zuciyarsa a ƙuntace. Sun ɗan ɗauki mintina a haka sannan Sulaim ya fara magana da muryarsa da ke fita a hankali;"Dukiyar Dhahab da ƙarfin ikon ka a cikinta ba zai tabbata gareka kai kaɗai ba har sai shaiɗan ya yi kutse a cikin al'umuranka Malik, shiyasa nasa Sadiq Ma'aikaci na musamman kula da motsinka a matsayin mai bawa shuka ruwa.. laifinka gare ni mai girma ne, saboda laifi ne da ya shafi lafiyata da Raina, ko mutuwa na yi Naila tafi ƙarfin ɗauri ...
Contents
Table of contents
Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.