LAIFIN ƁOYE

LAIFIN ƁOYE Chapter 1

by @ayshadansabo

*LAIFIN ƁOYE* Arewabook@ayshadansabo

©️Ayshat Ɗansabo Lemu✍🏻

Free pages

Chapter 1

Alhaji Shu'aib Abbah Aji ne zaune a cikin katafaren falon gidansa hannunsa riƙe da waya samfurin iPhone,waya yake kuma bisa ga dukkanin alamu yana cikin matukar farin ciki.

Hajiya Kubra ce ke sakkowa daga stairs ɗin benen cikin takunta irin na ƙasaitattun mata,kallo ɗaya zakai mata kasan cewa hutu da jin daɗi sunyi zaman dirshan a jikinta.

Shigarta kaɗai ya isa ya tabbatar maka da cewa ita ɗin hamshaƙiyace kuma gogaggiyar mace,wacce ilimi da wayewa na zamani yayi matuƙar taka rawa wajen goggewarta da sanin rayuwa.

A hankali take takowa zuwa cikin falon fuskarta ɗauke da murmushin da tasan yana matuƙar tasiri a cikin zuciyar gogan nata,bayan ta zauna kusa dashi har jikinsu na gugar juna ne wani ƙamshi mai matukar sanyin daɗi ya doki hancin Alhaji Shu'aib ɗin,hakan ya sanya shi gyara zama yana mai aje wayar hannunsa ya fuskanceta.Fuskarta yake kallo wanda yasha light makeup tamkar ba babbar mace ba kafin ya furta,"Madam kenan,sai yanzu kike sakkowa ina shirin fita?" Murmushinta mai tsada ta sake saki kafin ta furta, "To ai Daddyn su Yusrah gani yanxu na sakko ɗin ai,wai shin ya maganar zuwa ɗakko Yusrah ne?Kasan fa jirginsu zai sauka karfe 5pm ne ba kuma lallai ne Shushu ya ɗakkota ba,kasan kuma mutuniyar bata so driver shi kaɗai yaje daƙƙota."Ta ƙare maganar cikin tsaresa da idanunta.

Kallonta yayi kafin yayi magana wani haɗaɗɗen ƙamshi ya fara kai-kawo a cikin hancinansu,kafin suyi yunƙuri wata murya mai matukar daɗin amo ya doka sallama daga bakin ƙofar shigowa falon hakan yasa dukkaninsu suka mayar da dubansu ga ƙofar falon.

Wani haɗaɗɗen matashi ne ya doka sallama tare da sanyo kansa cikin falon,yaci ado cikin ƙananun kaya da sukai matukar fito da kyawunsa tare da tsantsar ƙuruciyarsa.A hankali yake takowa zuwa cikin falon fuskarsa ɗauke da murmushi,daga Hajiya Kubra har Alhaji Shu'aib suma murmushin ne a saman fuskokinsu su.

Kai tsaye kusa da ƙafafun Daddyn nasa ya tsuguna yana fadin,"Dady good morning." Shafa sumar kansa Daddyn yayi wanda yake kwance luff,kafin ya amsa da faɗin,"Morning my son,ya gajiyar tafiya?"

Murmushi matashin saurayin yayi yana faɗin

"Gajiya tabi lafiya Daddy."Matashin ya ƙare maganar yana ƙarisawa kusa da Hajiya Kubra ya kwantar da kansa a saman cinyoyinta yana faɗin,"Momy an tashi lafiya?"Hajiya Kubra ta

shafa kansa tana sakin murmushi tace"My son an fito lafiya,ya gajiya?"

A hankali ya furta,"Momy gajiya tabi lafiya ai."Ya ƙare maganar yana miƙewa tare da shafa cikinsa da yake a lafe yana kai dubansa ga dining area yake faɗin,

"Am very hungry Mom bari inyi kalaci inzo musha hira."

Miƙewa Alhaji Shu'aib yayi yana faɗin,

"Kazo dai kai shagwaɓar taka ta fama tunda jinka kake tamkar ɗan yaye idan ka raɓi jikin Mummyn taka."

Hajiya Kubrah ta saki murmushi tana saurin faɗin,"Bakomi dai Daddyn Yusrah,kai dai jeka sai ka dawo,ƙarfe 5pm Shureim sai ya ɗakko Yusrah idan ta sauka koni da kaina driver ya kaini in tarbo abata." Alhaji Shu'aib ya saki murmushi yana jinjina mata kansa,shi kuwa Shureim direct ɓangaren dining ya wuce domin yin kalacinsa.Zama yayi domin serving kansa abinda yake da buƙatar ciki,a nutse ya fara yin kalacin yanayin taunarsa da komi nasa da a nutse yake yinsa abin birgewa.

Kusan a ƙalla 30minutes ya shafe kafin ya miƙe yana aje cup ɗin daya shanye ruwan tea ɗin ya nufi cikin falon inda Momyn sa ke hakimce hannunta riƙe da jaridar daily trust tana dubawa,isowar Shureim cikin falon ya sanya ta aje jaridar tana dubansa kafin ta furta,

"My Shushu harka kammala?" Ya amsa da, "Eh Momy na kammala."Ya ƙare maganar yana kaiwa zaune kusa da ita.

Hira suke yi tamkar wasu sa'anin juna da Momyn,rabin hirar kuma suna yinsa akan tafiyar daya dawo daga kasar London inda ya shafe kusan watanni 2 a can sakamakon seminar da aka turashi ya kammala ya dawo gida.

Cikin hirar ne ya dubi Hajiya Kubra yana faɗin,

"Momy naji kina faɗin yau baby Yussy za ta dawo,kice yau kunnuwana sai sunyi ciwo sabida surutunta da za ta ishe mutane dashi."

Murmushi sosai Mummyn tayi kafin tace, "Kai Shushu 'yar autan nawa ake wa sharri?"

Miƙewa yayi yana faɗin,"Momy bari in tafi gurin Sudais ina son ganinsa kafin ya wuce hospital."

Adawo lafiya tace dashi kafin ta ɗauki jaridarta tayi sama,shi kuma ya fice kai tsaye zuwa ƙaton parking lot ɗin gidan inda motoci ne na alfarma girke a cikin wajen.

Wata haɗaɗɗiyar mota baƙa wuluk ya buɗe ya shiga,sabuwace kar ga dukkanin alamu ba a jima da kawota ba.

Dukkanin ma'aikatan dake kai-kawo a harabar gidan ne ke miƙa gaisuwa gurin shalelan gidan,kuma Ubangidansu Shureim Aji.

Suna matuƙar girmamashi da ganin mutuncinsa kasancewarsa mai sauƙin kai matuƙa,sannan yana musu alkhairy akai-akai matuƙar yana garin.

Tuƙi yake cikin natsuwa da gwanancewa,kai tsaye Garki ya nufa bayan ya kira Dr. Sudais ya shaida masa cewa yana bisa hanya.

Bayan ya baro gurin Dr. Sudais ɗin ne yaji kawai guest house ɗin Daddy yake son zuwa,sabida lokuta da dama yakan so keɓewa a guri guda ya huta.Sosai yake jin daɗin kasancewa a cikin ƙaton gurin hutawar dake guest house ɗin.

Koda ya isa Mai gadi ya buɗe masa gate ya kwashi gaisuwa sai ya wuce direct zuwa parking space,ganin motocin Daddy dana Alhaji Adam yaba Shureim mamaki sabida baiyi tunanin ganin Daddy a irin lokacin yazo hutawa a gidan ba.

Amma kuma ganin motar Alhaji Adam sai ya ɗan danne mamakin nasa,ya fara tunanin cewa wataƙil za su tattauna wasu harkokin kwangilolin nasu ne da sauran business ɗin da suke gudanarwa tare da juna.

Koda Shureim yayi parking kai tsaye ya nufi katafaren garden ɗin dake gidan,wanda duk wanda ya kasance a ciki dole ne ya sami natsuwa da nishaɗi.

Gurin yana da matuƙar ni'ima da shuke-shuke birjik ga resting chairs nan na hutawa,banda kukan tsintsaye dake kai kawo cikin kunnuwar mutum yana sanya mutum jin nishaɗi.

Teburin buga snooker dake cikin wajen ya nufa wanda shiyasa aka kafa shi,ya fara bugawa a hankali yana jin nishaɗi sosai a cikin zuciyarsa.Saida ya gaji ne ya sami guri ya kwanta ya fara danne-danne a wayarsa,shine shiga snap,shiga IG,shiga Facebook har lokaci yaja sosai.

A hankali ya miƙe ya nufi cikin gidan har kuma zuwa lokacin motacin su Daddy nanan alamun basu tafi ba,a cikin ƙaton falon ya zube bayan ya ɗauki ruwa a cikin fridge yana sha sanyin ruwan na ratsa maƙoshinsa.

Aje gorar ruwan yayi ya nufi upstairs,a tunaninsa zai sami su Daddy a cikin falon dake saman amma sai yaga wayam babu kowa a ciki.

Hakan ya sanya shi tunanin ko suna cikin bedroom ɗin Daddy ne inda yafi zama a ciki ya huta domin ba yau ne kaɗai Shushun ya saba zuwa hutawa a guest house ɗin ya tadda Daddyn yazo ba shima.

Sai dai kowa yana da bedroom ɗinsa,hakan yasa Shureim ya nufi ɗakin da yake mallakinsa ne,shi ya saba amfani dashi idan yazo domin hutawa a gidan.

Murɗa ƙofar yayi tare da sanya kansa ciki,lokaci guda numfashinsa ya fara barazanar dauƙewa sakamakon mummunar ganin da idanunsa sukai.

Janyo ƙofar yayi da saury hannuwansa duka biyun na rawa,kafin ya kaisu saman kansa ya dafe goshinsa.

Tunda yake a duniya bai taɓa yin mummunar gani irin na yau ba,tuni ya fara jin zuciyarsa na barazanar faɗowa ƙasa baki ɗaya.

A hankali ya nufi bedroom ɗin Daddy da nufin shiga ya zauna ko zai ji ya farka daga mummunar mafarkin da yake ganin ya faɗa,sai dai kash...!!! Koda ya buɗe dakin wani irin ƙara ya saki tare da zubewa a gurin yana salati hawaye masu tsananin zafi suka fara fuskarsa kafin a hankali ya sulale ƙasa yana sakin salatin daya ankarar da Alhaji Shu'aib cewa wani ya shigo cikin bedroom ɗin.

Cikin sauri yake ƙoƙarin rufe tsiraicinsa ba tare da yasan cewa ya makaro ba,domin aikin gama ya riga ya gama tuni Shureim ya gama ganin komi.Turesu yayi daga kansa yana ƙoƙarin ganin ko waye mai wannan kasadar daya shigo masa room yana a cikin wannan yanayin,sai dai kuma suna yin ido hudu da Shureim ya saki wani gigitaccen ƙara dukkanin jikinsa na ɗaukar rawa.Murya a shaƙe yake faɗin,"Shu...Shurei..M." Da ƙyar ya haɗo sunan ya furta cikin tsananin firgici da tashin hankali.

Tuni ya gama sadaƙarwa cewa yau azal ya faɗa masa,asirinsa daya daɗe yana binnewa yau ɗansa mafi soyuwa a cikin ransa ya kamashi yana aikata mummunar ɓarna.Ɓarnar da kunya kadai ta isheshi da kuma yadda mutuncinsa zai zube a idanun tilon ɗan nasa,wasu zafafan hawaye ke biyo fuskarsa yayin da

Shureim shi tuni ya dade da sumewa baima san abinda ya cigaba da gudana ba....✍🏻