FreeThe story
Synopsis
No synopsis yet.
About the author
Am so proud to be a hausa writer.
Sample · LAIFIN ƁOYE Chapter 1
*LAIFIN ƁOYE* Arewabook@ayshadansabo ©️Ayshat Ɗansabo Lemu✍🏻 Free pages Chapter 1 Alhaji Shu'aib Abbah Aji ne zaune a cikin katafaren falon gidansa hannunsa riƙe da waya samfurin iPhone,waya yake kuma bisa ga dukkanin alamu yana cikin matukar farin ciki. Hajiya Kubra ce ke sakkowa daga stairs ɗin benen cikin takunta irin na ƙasaitattun mata,kallo ɗaya zakai mata kasan cewa hutu da jin daɗi sunyi zaman dirshan a jikinta.Shigarta kaɗai ya isa ya tabbatar maka da cewa ita ɗin hamshaƙiyace kuma gogaggiyar mace,wacce ilimi da wayewa na zamani yayi matuƙar taka rawa wajen goggewarta da sanin rayuwa.A hankali take takowa zuwa cikin falon fuskarta ɗauke da murmushin da tasan yana matuƙar tasiri a cikin zuciyar gogan nata,bayan ta zauna kusa dashi har jikinsu na gugar juna ne wani ƙamshi mai matukar sanyin daɗi ya doki hancin Alhaji Shu'aib ɗin,hakan ya sanya shi...
Contents
Table of contents
Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.