LAIFIN ƁOYE Chapter 2
*LAIFIN ƁOYE* Arewabook@ayshadansabo
©️Aysha Ɗansabo Lemu✍🏻
Free page's
Chapter 2
"Aysha kiyi hanzari ki fito mana,nikam bani son yanayin sanyin jikinki ace mutum tun ɗazu bai gama shiri ba har yanzu."
Wata kyakykyawar mace ce ke wannan maganar tana zaune cikin ƙayataccen falonta,yayin da Aysha ke cikin room ɗinta tana shiryawa.Maganar da Umman tayi ne ya sanya tayi saurin rataya jakarta ta fito cikin takunta a nutse kuma cike da birgewa.
Aysha kyakykyawar mace ce matuƙa wankan,tana da matsakaicin tsayi ba kuma za a kirata gajera ba.Allah ya bata baiwar structure ɗin jiki wanda ake kira da kirar kalangu,ko'ina a jikinta a cike yake tap akwaita da baiwar kugu da dukiyar fulani tubarkalla.Hakan ne kuma ke janyo hankalin da yawan maza zuwa gareta,chocolate colour ne fatarta wanda ya haɗu da hutu yasa fatar tayi wani irin fresh. Aysha nutsatstsiyar mace ce tana da kamun kai matuƙa,sai dai a wasu lokutan miskilace ta gaske.
Fitowarta kai tsaye kusa da Ummanta ta nufa tana faɗin,
"Umma to ba gashi yanzu na fito ba,kuma ma banda abinki Umma zuwa gurin saloon har wani sauri ake masa?"
Umman ta dubi Aysha tana cewa,"To ai sai kije bedroom ɗina ki ɗauki 5k,sannan ina so idan kin dawo kice da Bala ku tsaya gidan Hajiya Kubrah munyi waya akwai saƙo da za ki karɓo mini." Aysha cewa tayi kawai,
"To Umma."Daga haka ta nufi bedroom ɗin Umman ta ɗauki kuɗin ta fito tana ma Umma saita dawo ta fice.
Bala na ganin fitowarta yayi saurin gyara parking,back seat ta shige suka bar gidan kuma kai tsaye a haɗaɗɗen gurin saloon ɗin yayi parking Aysha ta fito ta shige ciki.
Kamar yadda tayi tunani hakan ne ya kasance ta tadda mutane ba laifi,hakan yasa saida ta ɓata lokaci kafin ai mata straching da wankin ƙafa ta baro gurin. Kamar yadda Umma tace hakan aka yi daga saloon ɗin kai tsaye gidan Hajiya Kubrah dake Maitama suka nufa.
*******
Farkawa Shureim yayi ya gansa kwance anan cikin falon dake upstairs ɗin,Daddynsa da Alhaji Adam ne tsaye a kansa hankulansu a matuƙar tashe.Kallo ɗaya zakai musu kasan cewa dukkaninsu suna cikin gagarumin tashin hankali,musamman Alhaji Shu'aib da fuskarsa tayi tamkar zai fashe da kuka.
A hankali Shushu yake ƙara buɗe idanunsa akan fuskar Daddynsa abubuwan da suka faru na dawo masa fresh,sai yayi saurin sake rufe idanunsa kafin ya sake buɗesu a saman fuskokinsu yana fata ya kasance cewa mafarki yake.Sai dai kuma ganinsu tsaye a kansa ya sake tabbatar masa da cewa ba daga mafarki ya tashi ba,wasu hawaye masu zafi suka shiga sintiri a saman fuskarsa hakan yasa zuciyar Alhaji Shu'aib sake tsinkewa.Cikin ƙarfin hali da dakiya ya tsugunna yana ƙoƙarin kama hannun Shureim ɗin,shi kuma Shushu sai yayi saurin janye hannuwansa yana watsawa Daddyn wani kallo mai cike da nuna tsana da ƙyamata.Hakan ba ƙaramin sake tsinkar da zuciyar Dad ɗin yayi ba,tashi zaune yayi yana duban Alhaji Adam wanda yayi ƙarfin halin faɗin,
"Shureim kada ka zargi mahaifinka akan abinda idanuwanka suka gani,wallahi sharrin shaiɗan ne da kuma son zuciya,haƙiƙa yau ni da shi munyi matuƙar nadamar wannan mummunar harkar da muka jefa kanmu ciki."Alhaji Adam ya ƙare maganar cikin zallar nadama da shiga ruɗu.
A hankali Shureim ya samu ya mike tsaye duk da irin jirin dake ɗibarsa haka ya daure yana takawa a hankali ya nufi hanyar stairs ba tare da ya tsaya jin abinda Alhaji Adamu ke ƙoƙarin sanar dashi ba,sabida a ganinsa basu da wani hujjar dazai gamsar dashi akan abinda idanunsa suka gane masa.
Allah ne kaɗai yakai Shureim zuwa gida,tun daga irin mahaukacin horn ɗin da yake saki Mai gadin yasan cewa babu lafiya.A guje ya shige da motar bayan an ɗage masa gate ya nufi parking lot yayi parking motar,kai tsaye part ɗinsa ya nufa ko takalmin kafarsa bai cire ba ya kwanta a saman 3 seater.Idanunsa ya lumshe yana juya dukkanin abinda ya faru a yinin yau ɗin,haƙiƙa tunda yake bai taɓa yin mugun ganin daya firgitashi irin na yau ɗin ba.
Bai taɓa tunanin cewa Mahaifinsa daya bashi ingantacciyar tarbiya zai kasance cikin masu aikata saɓo irin wannan ba,bai taɓa tunanin cewa Mahaifinsa yana aikata wani ɓoyayyen LAIFI irin wannan ba.A hankali wani irin haushi da jin tsanar Mahaifinsa ke ƙoƙarin mamaye zuciyarsa farat ɗaya,abinda bai taɓa tunani ko a mafarki zai ji hakan game da Daddynsa ba.A nutse ya kai hannu ya dafe kansa yana mai fashewa da kuka tamkar ƙaramin yaro,a fili yake furta,"Why Dady? Meyasa ka sauya halayenka daga kyawawa zuwa aikata ƙazamin LAIFIN ƁOYE irin wannan?"
Wayarsa ne ya ɗauki ruri hakan ya sanya shi ɗauka domin ganin mai kiran nasa,'Sweet Mum' Sunan dake yawo akan screen ɗin wayar kenan. A hankali ya ɗaga kansa ya kalli agogon dake daure a tsintsiyar hannunsa,ƙarfe 5pm har ta gota ya gani,sai kuma lokacin ya tuna da zance ɗakko Yusra daga airport da zaiyi.Time ɗin daya ɗaga call ɗin,jin muryarsa kawai da Mum ɗin tayi tasan cewa akwai matsala.Cike da tashin hankali ta furta,"Shushu lafiyarka kuwa?" Muryarsa can ƙasa ya furta,"Mummy bana jin daɗi ne zazzaɓi da ciwan kai ke damuna."
Salati ta dauka tana faɗin,"To kana ina ne yanzu?" Shureim jin hankalinta ya tashi ya sanya shi saurin faɗin,"Mum ina gurin Dr Sudais ya bani magani zan ɗan huta zuwa anjima sai in dawo gidan,lokacin na ɗan ji ƙarfin jikina sosai, maganar ɗakko Yussy a tura driver ya ɗakkota please Mum."Hajiya Kubrah tayi saurin amsashi da faɗin,"Hakan ya zama dole Shushun Mummy,da kaina ni da driver za mu ɗakkota nidai fatana Allah yasa jikin naka da sauki?"
Da kyar ya amsata da cewa,"Mummy karki damu da sauƙi sosai, yanzu haka kaina ne kaɗai ke sarawa magani nasha ina so da nayi bacci na tashi watakila inji daɗi sosai.Cikin sauri Mummy ta furta,"Maza kwanta my son ka huta." Momy ta faɗi hakan tana katse wayar,hakan ya yiwa Shureim daɗi yayi saurin miƙewa ya nufi bedroom ɗinsa kai tsaye kuma tiolet ya wuce.
Ya jima sosai kafin ya fito ya gabatar da sallolin da suka wucesa,ya daɗe sosai yana addu'a akan Allah kada yasa abinda yake ji game da mahaifinshi ya ɗaure,domin wata iriyar zazzafar tsana yake ji nasa a cikin zuciyarsa.
**********
Aysha ce take takawa cikin takunta mai cike da natsuwa zuwa cikin gidan Hajiya Kubrah bayan driver ya gama parking motar,sallama tayi cikin muryarta mai matuƙar sanyi da daɗin amo.Jin shiru babu motsin kowa a cikin ƙaton falon daya gaji da haɗuwa ya sanya ta samarwa kanta da mazauni,mintuna kusan 10 ta share a zaune kafin ta fara jiyo ƙaran takun takalmi ana sakkowa daga stairs ɗin benan.Ta ɗaga kanta ta dubi hanyar stairs ɗin sukai ido 4 da Hajiya Kubrah dake sakkowa zuwa ƙasa,cikin fara'a da sakin fuska take faɗin,"Lale da Ayshatu,ai tun ɗazu Hajiya
Safiyah tace gaki nan bisa hanya sai naji shuru."
Takai ƙarshen kalamanta tana ƙarisowa zuwa cikin falon ta zauna,hakan yaba Aisha damar zamowa kaɗan ta fara gaida Hajiya Kubrah.
Cikin matuƙar sakin fuska Hajiya Kubrah take amsa gaisuwar tata,kafin ta ɗaura da faɗin,"Kinga yanzu haka ma aminiyarki Auta zan je ɗakkowa yau za ta sauka."Farin cikin Aysha ya kasa ɓoyuwa hakan yasa ta saki murmush tana faɗin,"Wow! Mummy kice gobe anan zan yini dani za a kwance tsarabar CAIRO."Hajiya Kubrah ta amsata da fara'a tana juyawa zuwa upstairs ɗin domin ɗakko saƙon da za ta ba Ayshan.Koda ta sakko saƙon ta miƙawa Aysha tare da turaruka data haɗo mata dasu,tare suka fito daga cikin gidan Aysha suka ɗauki hanyar gida,yayinda motar Hajiya Kubrah suka nufi airport domin ɗakko autarta wacce za ta duro daga ƙasar Cairo.Ta kammala karatunta gaba ɗaya ta zama cikakkiyar ƴar jarida ,kamar yadda ta rayu da burin son zama ƴar jarida sai gashi cikin sauƙi Allah ya cika mata burinta.......✍🏻