LAIFIN ƁOYE

LAIFIN ƁOYE Chapter 5

by @ayshadansabo

*LAIFIN ƁOYE* Arewabook@ayshadansabo

©️ Ayshat Ɗansabo Lemu ✍🏻

Free page's

Chapter 5

Cikin mutuwar jiki Daddy ya fito daga part ɗin Shureim ya nufi nasa,a hankali ya saɗaɗa zuwa bedroom ɗinsa ya samu har zuwa lokacin Hajiya Kubrah bacci take da alamu ko juyi bata yi daga yadda ya barta ba.

Kwanciya yayi tare da raɓa jikinsa da nata yana mai rufe idanunsa ruf,zuciyarsa cike take da tunani da tarin damuwa.

Ba yaji a daren yau zai iya rintsawa sam hakan ya sanya shi tunanin miƙewa ya ɗauro alwala,sallah yayi yana addu'ar Allah ya yafe masa ya kuma bashi ikon nesanta kanshi daga cigaba da aikata munanan laifukan da suke aikatawa na ƁOYE

**********

Washegari misalin 9am na safe suka hallara a saman dining domin yin kalaci,Yusrah na sanye cikin shigar riga da wando na bacci da yayi mata matuƙar kyau domin ita ɗin kyakykyawace sahun farko.Kowa yayi nisa cikin cin abincinsa Shushu ne kaɗai har zuwa lokacin bai shigo ba,Hajiya Kubrah na ƙoƙarin ɗaga waya ta kirashi suka jiyo ƙaran buɗe kofa tare da sararowan haɗaɗɗen ƙamshinsa daya fara cika kafofin hancinansu.Sanye yake cikin shirin zuwa office yaci suite ɗinsa da yayi matuƙar yi masa kyau tare da fito da ƙuruciyarsa zallah,a hankali ya ƙariso cikin falon har ya iso ɓangaren dining area ɗin.Yusrah da murnarta take faɗin,"Yaya Shureim good morning."Shureim yaja kujerar dake kusa da ita ya zauna yana ƙoƙarin wadata fuskarsa da murmushi kafin yakai hannu ya dafa kanta yana faɗin,"Morning baby Yussy ya gajiyar tafiya,ko ince ya gajiyar zaman flight?"Cike da murmushi da shagwaɓa take fadin "Babu gajiya my big Bros."Daddy ya fara gaisarwa amma sam bai yarda sun haɗa idanunsu ba,saiya juya gurin Mummy wacce zuciyarsa ke cike da fal da tausayinta domin yafi kowa sanin idan har taji abinda Daddy suke aikatawa a ɓoye za ta ji baƙin ciki tare da ƙaurace masa domin kullin nasiharta a kansu baya wuce cewa su tsaya ma halas su guji aikata duk wata saɓo.Tana yawan kwaɗaitar dashi game da aje iyali,domin gujewa faɗawa halaka ko aikata zina."Ya za ta ji idan taji cewa wai Daddy ne yake kawalcin mata har da matasa? Bai kuma tsaya anan ba shima yana aikata zina dasu?"Shushu ya tambayi kansa wani takaicin Mahaifin nasa na sake kamashi.Kaɗan ya iya shan ruwan shayi ya wuce office,yana aiki da National Health Insurance ne dake nan Abuja.

**********

Jakar hannunta ta ajiye tare da zubewa bisa seater tana faɗin,"Wash! Umma na gaji wallahi yadda kika san a motar kasuwa nayi fitarnan."Ayshace take wannan maganar bayan ta dawo tana miƙawa Ummanta saƙon data amso daga gurin Hajiya Kubrah ta ɗaura da faɗin,"Wallahi Umma kinsan muna gaisawa bamu jima ba itama tace za ta ɗakko Yusrah yau za ta dawo har ta kammala karatunta,gaskiya karatun Yussy yayi sauri sosai." Hajiya Safiyyah ta dubi tilon ƴar tata tana faɗin,"Ai haka karatun yake idan bakai kake ba mussamman idan ka tafi waje nan da nan saiki ga ka dawo ka kammala."Aysha ta miƙe tana faɗin,"Wallahi kuwa Umma muma dai Alhamdulillh tunda mun kammala a sa a har mun ƙare service lafiya." Tana ƙarisa kalamanta ta ɗauki hand bag ɗinta ta nufi room ɗinta yayin da tabar Umma na buɗe saƙonta data amso mata daga gidan Hajiya Kubrah.

***********

KADUNA

Matashiyar budurwa ce da ba za ta wuce shekaru 19 a duniya ba,duk da cewa hijab ne sanye a jikinta hakan bai ɓoye kyawunta ba.Fara ce tas da ita da alamu kuma Allah yayi mata baiwar zubin halitta mai matuƙar ɗaukar hankali,tafiya take a nutse ta yadda duk namijin daya ɗaura idanunsa a kanta zaiyi zaton cewa wata nutsatstsiyar mace ce mai matukar kamun kai.Koda ta iso wani ƙaton gida wanda kai tsaye ba za ka kirashi da gidan talakawa ba,sai dai ka lissafashi a jerin gidaje na masu rufin asiri.Tura ƙofar gate ɗin shiga tayi ta sanya kanta ciki,kamar jira ake yi ta shigo gidan wayarta ta fara ruri.Zaro wayar tayi daga cikin jakarta bayan taja ta tsaya,cikin rawar jiki ta amsa wayar tana faɗin,"Hello bakin rai bakin fama." Banji abinda me kiran take faɗi ba,na daiji wannan budurwar na faɗin,"Karki damu dole gobe mu kasance tare nima ɗin nayi kewarki matuƙa aminiya,daurewa kawai nake yi kinsan halin Abbah bayi ƙaunar yawan fitata,dama skull ke sawa kaji koda yaushe kana free to yanzu bani da wani sakewa amma karki damu nasan yadda zanyi."Suna gama wayar tayi shigewarta cikin gidan tana riƙe da wayarta samfurin iphone,kai tsaye falon gidan ta shiga tana kwaɗa sallama.Mahaifiyarta ce a kwance da alamu kamar bata da lafiya ne,domin kuwa tana kwance ne bisa 3 seater ta rufa da bargo.Jin sallama ya sanya ta buɗe fuskarta tana duban bakin ƙofar take faɗin,"Aneesah sai yanzu kika dawo?Yi maza ki aje jaka ki shiga kitchen."Aneesah tana ƙoƙarin shiga ɗakinta take faɗin, "To Umma,ya jikin naki to?"Umman ta amsa da da cewa,"Da sauƙi sosai Aneesah kawai dai har yanzu jikina ne babu ƙarfi sosai shiyasa,kiyi maza ki ɗaura girki kinga har yanzu Lantana bata dawo ba idan ta dawo ɗin saiku ƙarisa tare."Aneesa ta amsa da,"Toh Umma karki damu bari in sauya kaya."Tana shiga room ɗinta ta cire pitted gown ɗin dake jikinta bayan ta cire hijab ɗin.Aneesah tana da matuƙar diri mai ɗaukar hankali,kyakykyawace matuƙa wacce ta mallaki duk wani abu da mace zatai ɗagawa dashi.Wata riga mara nauyi ta saka tare da ɗaura zani akai,ta fito ta nufi kitchen domin ɗaura girkin rana kamar yadda Umma ta bata umurni.

Washegari tun wuri ta fara shiri domin tana so yau duk yadda za ai su kasance tare da Rufaidah,wasu riga da wando ta saka waɗanda basu da maraba da tsirara sai ta ɗakko wani haɗaɗɗen after dress ta ɗaura akai.Light make-up tayi ma face ɗinta tayi kyau tamkar ka saceta ka gudu,safar ƙafa ta saka bayan ta ɗakko hijab cream colour ta saka wanda tsayinsa ya sauka mata har guiwarta.Ta fito fes cikin shiga ta kamala,ga duk wanda ya kalleta zaiyi mata kallo ne na mace kamila ta gaske.Around 11am ta fito daga room ɗinta,Ummanta wacce tayi garas tana faman kai kawo tsakanin kitchen da kuma falon Abban na Aneesan da yake weekend ne yana gida ba kasafai ya faye fita ba ta kalli Aneesa tana faɗin,"Har kin fito?Saiki je ki sake sanarda Abban naki cewa za ki fita,duk da dai na sanar dashi cewa za ki dubiya Rufaidah ce babu lafiya."Aneesa ta saki murmushi tana faɗin,"To Umma." Daga haka ta shige ɓangaren Abban nata.A zaune yake yana kallon tashar CNN,ya amsa sallamar Aneesah yana aje ganinsa a saman kyakykyawar fuskarta.Sake gaidashi tayi tare da shaida masa cewa za ta gidansu Rufaidah ne domin duba jikinta,Abban nata ya dubeta tare da kallon shigarta dake jikinta wanda sam bai ga makusa a shigar ba illa sake yaba natsuwar Yarinyar tasa da yake gani.1k ya zaro ya bata yana faɗin,"Aneesah karɓi ki hau abin hawa da wannan,ki tabbatar zuwa ƙarfe 5pm na yamma yayi miki a cikin gidannan,kin sani sarai bana son yawon banza."Ƙasa da kanta Aneesah ta sake yi tana faɗin,"To Abba In Sha Allah zan dawo kafin lokacin." Daga haka ta ɗauki kuɗin tayi gaba.

Ba wani tafiya mai tsawo suka yi ba ita da mai adaidaitan suka isa gidansu Rufaida wanda yake unguwar Rimi Kaduna,ƙaton gida ne sosai wanda kana kallo kasan cewa mai kuɗin gaske ne mamallakinsa.

Koda mai gadi ya buɗe yaga cewa Aneesah ce gaisuwa ya shiga miƙa mata,domin duk wanda ya kwana ya tashi a cikin gidansu Rufaidah yasan matsayin da take dashi a gurin shalelen gidan wato Rufy.Gaidashi tayi cikin girmamawa kamar yadda ta saba kasancewarsa dattijo da take ganin mutuncin sa,jaka ta ɓalle ta bashi 2k sabbi gal cikin irin kuɗaɗen da take samu daga abokanan harkarta da kuma Rufy wacce bata ƙyashin kashe mata kuɗi ko mallaka mata duk abinda take so.

Koda ta shige cikin ƙaton main parlour na gidan babu motsin kowa,hakan ya sanya kai tsaye ta nufi bedroom ɗin Hajiya Khairiyyah.Sallama take dokawa cikin sanyin muryarta Hajiya Khairiyyah da suke kira da Momy ta amsa tana faɗin,"Barka dai Aneesah ai tun jiya Rufaidah ke shelar zuwanki gidannan."Cikin girmamawa Aneesah ta gaida Momyn kafin ta fito ta nufi wani corridor wanda zai kaita ɗakin Rufaidah.

Tun kafin ta ƙarisa ƙofar room ɗin ta fara ƙwalla mata kira tana faɗin,My bakin rai,bakin fama ki fito mana." A guje wata budurwa da ta gaji da haɗuwa tayo waje suka rungume juna,sosai Rufaidah ta sake ƙwaƙume Aneesah tana shaƙar haɗaɗɗen ƙamshinta dake fita a jikin Aneesan,yayin da hannuwanta ke ƙoƙarin kama wadataccen ƙugun Aneesah.Aneesah ne ta janye jikinta tana faɗin,"Shegiya tawan ai kya bari dai mu shiga daga ciki ko?"Dukkaninsu dariya suka saki kafin su shige ɗakin Rufaidah,wanda bashi da maraba da ɗakin mace mai aure domin babu abinda ba a zuba na jin daɗin rayuwa a cikinsa ba.

Basu tsaya a ƙaramin falonta ba kai tsaye bedroom ɗinta suka yada zango,suna shiga Ruffy takai hannu ta cire hijab ɗin dake jikin Aneesa tare da after dress ɗin daya ɓoye asalin shigar dake jikin Aneey ɗin tana binta da wani mayen kallo tamkar za ta cinyeta ɗanya.....

**********

ABUJA

Alhaji Adam ne zaune ababban falon gidansa,gefensa matarsa ce Hajiya Safeeyah.Wayarsa ce ta ɗauki ruri Umman Aysha takai hannu ta ɗauki wayar tare da miƙa masa,amsa yayi ya kara a kunni bayan ya latsa ok.Alhaji Shu'aib ne mai kiran hakan ya sanya shi ƙoƙarin miƙewa ya nufi hanyar bedroom ɗinsa domin keɓewa,daga ɓangaren Alhaji Shu'aib kuwa sanar da Alhaji Adam ɗin yayi cewa gashinan bisa hanya yana so su tattauna magana akan abinda ya faru hakan yasa Alhaji Adam ɗin sanar dashi cewa su haɗu a farm house ne na shi Alhaji Adam ɗin domin ko kaɗan baya son su tattauna matsalar a cikin gidansa.

Cikin sauri ya ɗauki hula da car key ɗinsa bayan ya sake feshe jikinsa da turare,ya fito yana duban Hajiya Safeeya yana faɗin,"Umman Aysha zan je farm house muna da meeting ne da za mu gabatar yanzu."Adawo lafiya tayi masa suka jero tare har zuwa babban main parlor na gidan,Ayshat dake kwance a saman doguwar seater tana sanye cikin shigar wata haɗaɗɗiyar gown na voile tayi kyau har ta gaji.Ganin Abbanta ya fito cikin shirin fita ya sanya ta miƙe ta iso garesa kai tsaye,kanta ta kwantar a saman kafaɗunsa tana faɗin,"Abba fita zakai? Da yanzu nake shirin zuwa maka hira."Shafa kanta yayi yana faɗin,"Aysha meeting garemu yanzu haka su Daddynki Alhaji Shu'aib suna can suna jirana."Shagwaɓe face tayi tana faɗin,"Shikenan Abba a dawo lafiya nima zuwa anjima nake so inje gurin Yusrah kasan jiya ta dawo,gara inje a kwance tsaraba dani."

Murmushi yayi yana faɗin,"Good gal,to a dawo lafiya."Daga haka ya fice abinsa ita kuma Ayshat ta nufi room ɗinta domin gyara face ɗinta kafin ta fito cikin shirin zuwa gurin Yusrah.

**********

A can Farm house ɗin Alhaji Shu'aib kuwa,shi da Alhaji Adam ne zaune suna hira akan abinda ya shafi harkokin business ɗinsu na shigo da kayan gini zuwa motocin hawa da sauran kayayyaki da suke daga ƙasashen ƙetare.

Alhaji Shu'aib ya dubi Alhaji Adam yana faɗin,

"Wato Adamu duk yadda nake tunanin Shushu zai fahimceni abin yaci tura,hasalima tsanata nake hangowa a cikin idanunsa ƙarara,haƙiƙa nayi nadamar aikata LAIFIN ƁOYE."Alhaji Adam ya nisa kafin ya furta,"Ka kwantar da hankalinka Shu'aib,Shureim bazai taɓa iya juyama baya ba,kasancewarsa ɗa na ƙwarai dole yaji zafin abinda muke aikatawa,amma ina tabbatar maka zai sakko ne."Alhaji Shu'aib ya karɓi maganar da faɗin,"To Allah yasa hakan,ni yanzu abinda nakeso kasani shine,bani ba cigaba da yin duk wata harka da muke gudanarwa abaya,bazan cigaba da amsar duk wata ƙazamar kwangila ba,hasalima duk wata dukiyata da nasan cewa ta hanyar ƙazaman kwangilar da muke na sameta na yanke shawarar sadaukar da ita ga marayu,zan gina musu gidaje in kuma basu tallafi,zan cigaba da juya dukiyata ta hanyar kasuwancinmu ta halas kaɗai ta wadatar dani,domin banga amfanin inci gaba da wannan mummunar sana'ar alhali jinina tilo Namiji dana mallaka na neman juya mini baya ba,Adamu na kunyata jiya a gaban Shushu,na kuma haƙiƙance cewa ban masa adalci ba idan har zan cigaba da aikata LAIFIN ƁOYE domin tara ƙazaman dukiya,su kuma in cigaba da jefasu cikin baƙin ciki,Shureim ya sanar dani cewa baya son duk wani abu dana mallaka masa matuƙar da dukiyar wannan harka na sameshi,kai takai har yana faɗin cewa yana ƙyamar duk wani abu dana ciyar dashi da wannan dukiya ta kawalci da ɓarnar da muke aikatawa a ban ƙasa,to miye ribar wannan harka tamu Adamu?Ai gara mu tuba mubi tafarkin tsira ko Yaranmu za su yafe mana mummunar tabon da mukai musu,domin wannan kaɗai ya isa abin gori a garesu,tun daga ranar da Shushu ya ganmu cikin mummunar yanayinnan naji na tsani wannan fasadi da muke aikatawa,naji na tsani su minister da duk wasu manyan ƙasarnan masu aikata laifuka irin namu,zanbar wannan harkar koda hakan zai zama sanadiyar karayar arziƙina ne."Alhaji Shu'aib yakai ƙarshen kalamansa yana jin tsananin nadama na sake ratsa zuciyarsa.Jikin Alhaji Adam gaba ɗaya ya gama yin sanyi,tabbas ya sani maganganun aminin nashi sune zallar gaskiya.Tabbas ya zama dole su tuba domin Allah da kuma kare mutuncin Iyalansu duk da cewa sun riga sun musu tabon da bazai gogu ba,domin komin daren daɗewa sai an kira Yaransu da cewa Iyayensu kawalai ne kuma mazinata,tir da biyewa son zuciyarsu da suka yi a baya.Sun daɗe sosai suna tattauna yadda za su ɓullowa su minister,domin su rabu lafiya dasu da kuma yadda za su gina gidajen marayu da dukiyar da suka tara da wannan harka tasu.Daga ƙarshe suka watse ko wannensu driver ɗinsa ya jashi zuwa gida domin hutawa a cikin iyalansa,tunda sun saba duk ƙarshen mako suna zama ne tare da Iyalansu a gida suyi nishaɗi da sauraren matsalolin juna.

***********

KADUNA

Aneesh basu yi masauki a ko'ina ba sai a saman makeken gadon Rufaidah samfurin Turkish bed wanda ya gaji da haɗuwa,babu abinda ba a zuba na more jin daɗin rayuwa a cikin bedroom ɗin ba kai kace ɗakin wata babbar mace ce mai miji.

Irin kallon da take bin jikin Aneesan dashi yasa Aneesan ƙoƙarin saka hijab domin tsokanar Ruffyn,cikin azama takai hannu ta fisge hijab ɗin tana faɗin,"Please karki rufemin kayan daɗina mana,wai shin ma wani tsari kikai wa su Umma da suka barki fitowa da wuri haka?" Dariya Aneesah ta sanya tana faɗin,"Cewa nayi baki da lafiya sosai kina kwance,nadai tsatstsara Umma ta tambayar mini Abba,shine fa yau na sake sanar dashi shi kuma har da bani kuɗin mota."Ta ƙarishe kalamanta tana dariya sosai kafin daga bisani ta tsuke fuska,damuwace ƙarara ta bayyana a saman fuskarta kafin ta sake ɗaura idanunta akan Rufaidah wacce ta shagala a kallon dukiyar fulanin Aneesa waɗanda suka cika ƙirjinta taf.Cikin wani irin yanayi Aneesah ke faɗin,"Zumata wallahi na tsani Abba,na tsani halayyarsa nason kai da kuma son zuciya,a kullum na tuna shine silar jefani a halin da nake ciki a yanzu sai naji na sake tsanarsa." Ta ƙare maganar idanunta nayin ja alamun ɓacin rai.Rufaidah ce ta miƙe ta fice daga ɗakin ba tare da tace komi ba,bata jima ba ta sake shigowa cikin bedroom ɗin Rebecca mai aiki tana biye da ita hannunta ɗauke da ƙaton tray wanda aka shaƙoshi dasu juice da kayan lashe-lashe ta dire a saman table tare da juyawa ta fita bayan ta miƙa gaisuwa ga Aneey babe.

Tana fita Rufaida ta ƙulle bedroom ɗin kafin ta dawo ta ɗauki cup ta zuba juice mai sanyin gaske ta matsa dab da Aneesa ta kai cup ɗin bakinta,babu musu Aneey ta shiga shan ruwan juice ɗin sanyinsa na ratsa maƙoshinta.Saida ta shanyeshi tas sannan Rufaidah ta sauke cup ɗin ƙasa,wani kallo take bin Aneesan dashi tana sake noticing yadda ta sake fresh da kyau.A hankali takai hannu ta zare ƙaramar rigar da bata da maraba da babu dake jikin Aneesan,na shanunta suka fito muraran hakan yasa Rufaida kai hannunta kansu ta fara murzasu a hankali.Jikin Aneey sosai ta shiga,kafin takai bakinta kunnin Aneesan tana faɗin,"Kiyi haƙuri zumata nasan zafin da kike ji a cikin zuciyarki,but ina so ki sama ranki cewa za ki sami abinda kike so,kinsan ina kishin wannan jikin please kada ki yarda kice zaki mallakawa wani shi,wallahi ni da ke mun riga da mun zama bakin rai bakin fama,aure ma zan barki kiyi ne sabida cikar burinki nason ki ɗanɗani daɗin namiji,da kuma son ki haihu amma ki sani bazan iya rabuwa dake ba zumata."Duk waɗannan maganganun da Rufaidah keyi hannunta nakan ƙirjin Aneesah ne tana murzasu son ranta kafin Aneesan ta fara maida mata martani cikin ƙwarewa da sanin kan harkar,kafin kace me sun tube junansu tare da faɗawa wata duniya na aikata LAIFIN ƁOYE wanda dukkaninsu babu wacce iyayenta sukai nasarar gano halin da take ciki,sudai kawai sunsan irin zazzafar soyayyar da Yaran nasu kewa juna ne. Sun ɗauki tsawon lokaci suna gamsar da junansu kafin su sami natsuwa,Aneesah bayan gama samin nutsuwarsu ne ta ɓalle da hawaye sosai wanda na rasa dalilin zubarsu.Shin na tsananin daɗi ne da gamsuwa,ko kuwa akwai wani dalili na zubarsu?

To amsar dai na gareni sai ku cigaba da biyayata domin jin ya za ta kaya? Tabbas akwai cakwakiya gamida zazzafar soyayya da kuma ban tausayi a cikin wannan labarin.Labari ne daya taɓa zahirin abinda ke faruwa a cikin duniyarmu ta yau,irin yadda mutane da yawa suka faɗa ma aikata laifukan Ɓoye ba tare da cewa a zahiri ansan me suke aikatawa ba.Don haka kada ku bari a baku labari,Aysha Dansabo ke cewa ku bibiyi labarin LAIFIN ƁOYE domin jin cikakken da wani irin salo labarin ke tafe?