RAMIN ƘARYA...

9-10

by @amanarcool323

💫 *RAMIN ƘARYA....* 💫 
             




            Story & writing 
       
                      By

  Mrs Muttala (Amanar cool)




        *YOUNG TALENT*
*WRITER'S ASSOCIATION*



Sadaukarwa ne ga Aysharcool 



Free book ✍️



Page 9&10


______Jikinta ne ya ɗauki rawa, ta ji jiri na ɗibarta, da sauri ta dafa ɗaya daga cikin kujeran falon.

Cikin sauri Abba ya isa inda ta ke, ya ce "Subhanallah Daughter me yake damunki? baki da lafiya ne?".

Girgiza kai ta yi, ta ce "Abba jiri ne nake ji" sannu ya yi mata, sannan ya ɗakko mata wayarta, ko da ya duba wayar fuskar wayar, ta farfashe, abu ne mawuyaci idan ba ta ci screen ba.

"Ya salam kin ga screen ɗin wayar ya samu matsala". 

Karɓar wayar ta yi tana kallo, idanunta ya ciko da ƙwalla, Abba ya ce "Sorry my Daughter, zan sa Yayanki ya kai ki ki za ɓi kalar wayar da ki ke so" murmushin ƙarfin hali ta yi, ta ce "To Abba na gode".

Hajiya Zainab tsaye ta yi tana ƙare mata kallo, mamaki take me zai sa Hudah ta shiga wannan tashin hankalin, lokacin ɗaya saboda kawai ta ji maganar za'a haɗa yayanta aure da wata, abin da ta gani kwanaki ne ya faɗo mata a rai, kawar da wannan tunani tayi , ta ce "Sannu Hudah jirin ya sauka ne?" ɗaga mata kai ta yi, tana ƙoƙarin miƙewa ta bar wajan, Abba ya ce "Zaki iya tafiyar ne?"

"Eh Abba zan iya na daina jin jirin"

Ammi ta ce "Hudah ina fatan ba wata damuwa?" tayi maganar ganin Hudah zata fita ba tare da sannin me ya kawo ta ba, "A'a Ammi ba damuwa, dama na zo na gaisheki ne." Ammi ta ce "To ina godiya sosai ki gaishe mini da ummanku". 


*****

WASHE GARI

Da safe, Baba ya ƙara shaidawa Afnan cewar ta fito da mijin aure, idan ba haka ba zai aurar da ita ga duk wanda ya ga dama.

Mama ta ce "Haba Baban Afnan, ka san yarinyar nan ba saurayi ne da ita ba yanzu, masu nemanta ɗin duk sun dai na zuwa, addu'a yakamata mu yi Allah ya fito mata da miji na gari, komai na da lokaci, idan lokacin auen ya yi babu zato, ba tsammani sai ka ga an yi." Bai kamata ka din ga yadda da ziga, da maganar abin da ba ka gani, ka tabattar ba.
 
A fusace ya ce "Rufe mini baki, mahaifiyata za ta yi ƙarya ne? dama na daɗe da sanin cewa ke ce ki ke goya mata baya, samari nawa ne ke bibiyar ta amma ta ƙi kulasu, to na ga ji a wannan karon ko ta fito da miji ko na ba da sadakarta ga duk wanda na samu".

Yana gama faɗar haka ya yi wucewarsa, ya na fita ya ci karo da Gwaggo a tsaye, ta na jin duk abin da suke faɗa.

Bayan sa Mama ta bi da kallo, tana mamakin sauyin da ya yi lokaci ɗaya.

Afnan kuwa kuka take sosai, dan ba ƙaramin tashin hankali take shiga ba a duk lokacin da ta ji Baba na yi mata faɗa akan aure, musamman daga jiya zuwa yau ta ji abin yafi damunta, mazan sun ƙara fita a zuciyarta gaba ɗaya.

Mama ta ce "Wannan kukan ba shine mafita a gareki ba, addu'a zaki yi har Allah ya fito miki da miji, tun farko ke ki ka yi wasa da damarki Afnan, abin da nake yi miki gudu kenan dama, gashi kuma ya zo". 

Gwaggo suka gani ta shigo musu ko sallama babu, ta ce "Au saboda an yi miki zance aure shine ki ke wa mutane kuka, saboda jin daɗin uwarki ta goya miki baya, to wallahi ko kukan jini zaki yi aure ba fashi, sakarar yarinya kawai, wato kin fi son ki zauna ki na gwada girma ke da uwarki da ta ke ɗaure miki gindi, to baku isa ba, dole ne ki fitar da miji, in ba haka ba wallahi ƙauye zan sa a bada sadakar ki".

Har Gwaggo ta ƙare faɗanta, ba wanda ya tanka mata.

  
*****

Haidar tun jiya daya shiga ɗakinsa, bai sake fitowa ba, ganin haka yasa Ummansa shiga ɗakin ta duba lafiya yake, a kwance ta tarar da shi, yayi zurfi a cikin tunani, ya kasa samun Maryam a waya, balle ya ji ya jikin Afnan. Kuma zuciyarsa na ci gaba da wassafo masa kamaninta a cikin idanunsa. Yana matuƙar son ya sake jarraba komawa, ko Allah zai sanya ya dace ya kuma ganinta.

Umma ta ce "Haidar ba ka da lafiya ne? me ya ke damunka?". 

Mirginawa ya yi ya tashi zaune,
ya ce "Ba wani damuwa Umma kawai jikina ne ba daɗi"

Umma ta ce "Haidar yaushe ka fara ɓoye mini damuwarka, rashin jin daɗin jikin ne zai saka, ka din ga zaman ɗaki, ko zuwa in da nake baka yi".

Zama Umma tayi a bakin katifar, ta ce "Haidar ni fa mahaifiyar ka ce, duk duniya baka da kamata, baka saba da ɓoye mini damuwarka ba, kar ka fara a wannan karon, ka gaya mini me yake damunka, ka ji shalelen Umman shi".

Haidar tsintar kansa ya yi da jin kunyar faɗawa Umma cewar ya kamu da son wata ne, sunkuyar da kansa ya yi, ya kasa magana, ganin hakan yasa "Umma ta ce Haidar ka yi magana mana ina sauraron ka".


Umma ta ƙare masa kallo, jin yaƙi cewa komai, sai sunkuyar da kansa yake yi kamar sabuwar amarya. Ta numfasa ta ce "Haidar ko sirika zaka kwaso mini ne? Wannan sunkuyar da kan, da magana.
Da sauri ya ɗago ya kalleta, jin yadda ta ramfo shi, lokaci guda haka.
Murmushi ta yi cikin dattaku ta ce "Labarin zuciya, ai a tambayi fuska. Ban tari numfashinka ba amma ina ga ka a jiye maganar auren nan a yanzu, duba da halin da muke ciki, ba mu da ƙarfin tunkarar aure a yanzu, wata rana abincin da zamuci ma wuya yake mana, in ba kwanakin nan da Allah ya haɗa ka da bawan Allah nan da ya baka babur ɗin nan muka samu sauƙin wasu abubuwan ba, to ka ga bai kamata ka jajiɓo maganar aure a yanzu ba, ka yi haƙuri da zancen aure yanzu, ka ƙara tsayawa da ƙafarka tukuna, ka fitar da ita a ran ka, mu ci gaba da addu'a, tun da ka kammala karatunka a ko wane lokaci Allah zai iya sa wa ka samu aiki".

Haidar Ya ce "To Umma na haƙura Allah yasa hakan shi ya fi alkhairi, ki taya ni da addu'a Allah ya ci re mini abin a rai na".

Umma ta ce "In sha Allah zan ta yaka da addu'a, Allah ya yi maka albarka" 


*******

Gaba ɗaya Hudah ta rasa nutsuwarta, kwana tayi kuka tana tunanin me ye makomarta, shekenan ita ta tashi a tutar babu, ji tayi ba zata iya haƙura wata macen ta aure ya Mudan ba, idan ba ƙarya kunnenta ya yi mata ba, kamar ɗiyar Alhaji Munir ta ji Abba ya ambata, ke nan hakan yana nufin Sharifa za a aurawa Ya Mudan. Da ƙarfi ta ce "Impossible ni a rasa da wa za a haɗa shi sai wannan yarinyar da ta raina wa mutane wayo, kowa kallon ɗan iska take masa, dole na nemawa kaina mafita, ko da Hakan yana nufin tonuwar asirin sune.

Abba na ɗakinsa Mami ta shiga da sallama zama tayi a bakin gado ta ce "Ashe ka shigo ban sani ba" Abba ya ce "Eh lokacin dana shigo ki na toilet ne" "Ok" ta ce.

Duban ta Abba ya yi ya ce "Dama ina son magana dake, Alhaji Munir ne ya zo mini da zancen a haɗa Mudan da ƴarsa Sharifa aure, shine na ce ya bari na shawarce ki na ji me ye ra'a yin ki, ko Mudan ɗin ban yi maganar da shi ba, bari na yi na fara jin ra'ayinki".


Washe baki Mami tayi ta ce "Alhamdulillah ai dama wannan ranar nake jira, ranar da zan ga Mudan ya fitar da matar aure, kai ma sha Allah wannan haɗin ya yi mini daɗi sosai, Allah ya sanya alkhairi, ya kai mu lokacin aure zamu musha biki na ke ce rai ni". Tayi maganar ta na ƙoƙarin miƙewa tsaye.

Abba ya ce "Ina za ki kuma?" . "Alhaji zan turo maka Mudan ɗin ne ka yi masa maganar".

"Dawo ki zauna zanne me shi da kaina"

Zama tayi tana wani shu'umin murmushi, wanda ita kaɗai ta san ma'anarsa.

Abba ya ce "Hajjaju wannan murmushin duk na jin daɗin auren ne?"

"Eh ba dole na ji daɗi ba, Mudan zai zama babban mutum". 

Murmushi ya yi ya ce "To ga wani abin farin cikin daya kuma samuwar mu, ƴar uwarki Zainab ta koma samun juna biyu, sai a taya mu da addu'a".

"Gabanta ne ya yi mummunar faɗuwa, amma ta daure, cikin kissa, da kisisina, ta ƙaƙalo wani munafukin murmushi, ta ce "Ma sha Allah, Allah abin godiya Allah ya inganta, ya raba lafiya" Abba ya amsa "Ameen".

Mami ji ta yi duk ɗakin ya yi mata duhu, wani irin tuƙuƙin baƙin ciki take ji a cikin zuciyarta, lokaci ɗaya farin cikin da take ciki ya juye ya koma baƙin ciki, zagi ta din ga ɗirkawa Ammi a zuciyarta.

Zumbur ta miƙe kamar wadda aka tsikara, ta ce "Alhaji zan je in dan kwanta, ina jin kaina na yi mini ciwo" ."To Allah ya ƙara afuwa, ki sha magani kafin ki kwanta" ficewa tayi har tana haɗa hanya ta bar ɗakin.


*****

Yau ma Maryam ta yi halin na ta, na guduwa daga makaranta, ita da sabuwar ƙawar da tayi Safena, wata yar unguwarsu ce da halinsu ya zo ɗaya, Safena na son Maryam sai dai Maryam ɗin bata sakar mata fuska ba, sai ƴan kwanakin nan, dalilin wani faɗa da Safinar ta shigar mata ne har ta fara kula ta.

Suna tafe a hanya sun yi wujiga-wujiga ga zafin rana Maryam ta dubi Safina ta ce "Feena wai babu sauran canji ne a hannun ki? wallahi duk na gaji da tafiyar nan" feena ta ce "Ko ficika bana magani" murmushi Maryam tayi ta ce "Yau za'a yi taɓara kenan, zo muje.

 Feena ta ce "Wace irin taɓara kuma?" 

"Ke dai zuba ido ki sha kallo"

Bakin titi suka ƙarasa suna tarar abin hawa, wani ɗan adaidaita sahu suka tsayar, har ya wuce su kaɗan ya dawo, ɗauke yake da wata matashiyar budurwa a ciki, tambayarsu in da za su ya yi, bayan sun faɗa masa, ya ce "Su shiga" shiga suka yi ba tare da sun kula budurwar dake ciki ba.

"Sannu" ku budurwar ta faɗa Feena ta ce "Yawwa sannu" Maryam ba ta ko kalleta ba, balle har ta amsa mata, kallon Maryam budurwar take yi, Maryam na lura da irin kallon data ke yi mata,
ƙwafa tayi ta ce "Malama lafiya, ni fa bana son kallo, kin wani tsare ni da ido sai kace ki na bi na bashi" murmushi budurwar tayi "Ta ce sunana Sharifa ba Malama ba, Allah ya baki haƙuri". 

Taɓe baki Maryam tayi bata kuma magana ba.

Ko da suka ƙaraso unguwarsu Feena aka fara saukewa, da yake gidansu ne a farkon layin, feena sai raba ido take yi, saboda ta san basu da gaskiyay, Maryam ta ce "Su tafi ita za ta biya shi kuɗin" tun Kafin napep ɗin ta tsaya, Maryam ta dira da mugun gudu ta afka cikin gida, cikin rashin sani, tayi wa Gwaggo dake tsaye bakin hanya, wani wawan bangaza ba tare data kula da tana tsaye a gurin ba.

Ihu Gwaggo ta saki tana zubewa a gurin, Maryam ko ta kan Gwaggo bata tsaya bi ba tayi shigewarta sashensu.

Bala'i mai napep ɗin ya fara yi, yana zage-zage tare da faɗin "Wallahi zai iya shiga har cikin gidan nan, shi za'a gwadawa iskanci, da rashin kunya".

Gwaggo dake kwance baje-baje a ƙasa, jin ana zage-zage a ƙofar gida ta yun ƙura da ƙyar ta tashi, fita ta yi ƙofar gidan. 

Yana ganin Gwaggo ya ƙara masifa yana faɗin "Sai an biya shi kuɗinsa, ko ya shiga har cikin gidan nan ya yi wa yarinyar nan shegen duka".

Tambayar shi Gwaggo tayi "Me yake faruwa?" ya kwashe komai ya gaya mata.

"Ka ga zo mu je na kai ka har gurin Uwarta a biya ka kuɗin ka, ko ka yi mata tsinanne duka, wannan fitinaniyar yarinya Allah ya a gajemu da ita".

Da sauri sharifa ta fito daga cikin napep ɗin ta ce "A'a Inna baza a yi haka ba, kaga Malam zo muje, ni zan biya kuɗin".

Ya ce "Ta kuru wallahi da yau taga yanda ake rashin kunya" Gwaggo ta ce "Nima ban so ta ce za ta biya ba, na so muje har gaban uwarta, ta ji ɗibar albarkar da ƴarta tayi".

Tada napep ɗin sa ya yi suka bar wajan Sharifa mamakin Maryam ya cika zuciyarta, gashi yarinyar ta burgeta, har so ta yi ta ƙullah ƙawance da ita, sai taga yarinyar na shan ƙamshi, murmushi tayi a fili ta ce "zan sake dawowa" dan har cikin ranta ta ji tana son Maryam ɗin.

Cikin gidan Gwaggo ta koma da masifa ta shiga ƙofar su Maryam, tana faɗin "Ina take shegeyar yarinya mara kunya, ni zaki hankaɗe kasa ki gudu saboda baki da hankali".

Mama na banɗaki ta ji Gwaggo na masifa, ƙin fitowa tayi ta nemi kujerar dake ciki tayi zamanta.

Afnan na ɗaki kwance ta ci kuka har ta gode Allah ta ji masifar Gwaggo ,fitowa ta yi a ɗakin ta ce "Haba Gwaggo wai meyasa ki ke son aibata mu ne, sai ka ce ba jininjiki muke ba, ke kullum cikin yi miki ba dai-dai muke ba". Afnan tayi maganar cike da jin haushin Gwaggo, saboda ta san duk ita ce ke ziga Baba a kan zancen ta fito da miji.

Baki bude Gwaggo ke kallon Afnan da idanuwata ya yi ja, ya kumbura saboda kuka.


Amanar cool ce✍️
***