Chapter 13-14
💫 *RAMIN ƘARYA....* 💫
Story & writing
By
Mrs Muttala (Amanar cool)
*YOUNG TALENT*
*WRITER'S ASSOCIATION*
Sadaukarwa ne ga Aysharcool
Free book ✍️
Page 13&14
________Jiki a sanyaye Baba ya yi wa Gwaggo sallama, ya fita da isar sa sashensu, da Maryam ya fara cin karo, bata yi aune ba, ta ji saukar tagwayen maruka hagu da dama. A gigice ta dafe fuska, cikin tashin hankali da kaɗuwa.
Murya Baba ta ji, cikin tsananin fushi da fusata, ya ke magana
"Baki da hankali ne?. Ke mahaukaciyar ina ce? Mahaifiyar tawa za ki yi wa irin wannan rashin mutuncin, saboda ba ki da kunya? to na fara gajiya da wannan halin naku, ba zai yiwu ku rinƙa haɗa ni da mahaifiyata ba".
Maryam kuka take yi, sosai marukan sun ratsa ta, za ta iya cewa tunda ta girma, ta yi wayo, Baba bai taɓa saka hannu ya dake ta ba sai yau, sanadiyyar waccan tsohuwar, lallai Gwaggo za ta gane shayi ruwa ne.
Cikin rawar jiki da ruɗani, Afnan ta ce "Baba ɗan Allah ka yi haƙuri, in sha Allah ba za mu sake ba".
"Rufe min baki shashasha kafin na zo na make ki kema, ai ke da ita duk kanwar ja ce, da ne ki ke mai hankali, yanzu ke ma kin koyi halin da ba na ki ba. To bari ku ji daga yau duk wadda ta sake gaya wa Gwaggo ko da baƙar magana ce sai na yi mugun saɓa mata".
Shiru suka yi ba wanda ya kuma magana, sai da ya yi faɗa sosai har Mama bai raga wa ba, sannan ya bar gurin, ya yi shigewarsa ɗaki.
Bayan sa Mama ta bi ta na mamakin sauyin halinsa lokaci ɗaya, a zaune ta same shi ya tsurawa guri ɗaya ido ya na kallo, zama ta yi a bakin katifar ta ce "Baban Afnan" shiru ya yi bai kula ta ba, ta sake cewa "Baban Afnan dan Allah ka yi haƙuri, in sha Allah ba za su sake ba".
"Kar ma su daina, zan yi maganinsu ne, sannan ina son ki kasance a cikin shiri, saboda a kowane lokaci za ki iya jin na ba da auren Afnan".
"Aure kamar?" ta yi tambayar ta na ƙura masa ido.
"Kamar yanda ki ka ji na faɗa, aurar da ita zan yi ga duk wanda na samu, tunda ita ta gagara fitar da miji, Idan Allah ya kai muna rai gobe zan ba da sadakarta a masallaci ga mai so".
Cikin ƙunar rai, da jin zafin maganar, ta ce "Haba Baban Afnan wannan wa ce irin magana ce, Afnan ɗin ce za ka ba da sadakarta, sai ka ce ta rasa mashinshini, gaskiya ni ban yarda da wannan abin ba".
Duban ta ya yi ya ce "Ke ki ke aurena ko ni nake aurenki? sannan maganarki zan bi ko ta mahaifiyata? to bari ki ji in faɗa miki ke dai baki isa ki hana ni aikata abin da na yi niyyar yi ba, idan har ki na son zaman lafiya tsakanina da ke, dole ne ki yi biyayya wa umarnina".
"Ban taɓa tunanin akwai ranar da zaka yi wa ƴa,ƴanka irin wannan auren ba, sai dai a yanzu ba zan yi mamaki da hakan ban, duk abin da yafi zama alkhairi a cikin wannan lamarin, ina roƙon Allah ya tabbatar mana da shi" daga haka tayi shiru, bata kuma magana ba, saboda a yanda ta lura da mijin nata, komai zai iya faruwa idan ta ce zata yi wani yunƙuri, ta na lura da shi kwana biyun nan ƙiris yake jira sai ya hau faɗa da banbami ba gaira ba dalili, ta rasa dalilin faruwan hakan, amma ba komai za ta ci gaba da addu'a komai ya yi farko zai yi ƙarshe.
"Kin taimaki kan ki, kuma hakan shine zaman lafiya a gareki". Ya yi maganar tare da ƙara kawar da kansa gefe, shi kansa mamaki yake yi, me yasa yake yawan jin haushinsu har cikin ransa baya jin daɗin hakan.
Da kallo kawai Mama ke bin sa, sannan ta miƙe ta ɗauko masa abincinsa, ta ajiye.
******
Bayan fitar Mudan a gidansu Sharifa, kai tsaye gurin sharholiyarsa ya wuce, domin ya rage damuwar abin da Sharifa tayi masa, sai dai ya ƙudiri aniyar auren ta ko ta na so, ko ba ta so, sai ya cika muradinsa, kuma idan ta shigo hannunsa sai tayi da na sani da nadamar abin da tayi masa.
Mami na zaune kira ya shigo wayarta, ko da ta duba Turai ce, cikin zumuɗi ta ɗaga wayar, ta ce "Hello. Aminiya ta hannun dama, yanzu nake tunani kiran ki, sai gashi kin kira, ya ake ciki kin samo mana mafitar ne?"
Turai ta ce "Daɗina da ke gajen haƙuri, ai kya bari mu gaisa".
"Ba zaki gane bane, mu a je gaisuwar nan a gefe, yanzu me ye labari? dan wallahi a yanda nake ji ɗin nan komai zan iya aikatawa matar nan, ta tsaya mini a maƙogarona, ni fa har zarginta nake, anya ba asiri tayi mini ba, akan rashin samun cikin nan nawa, ki duba ki ga shekarata nawa a gidan nan ko ɓari ban taɓa yi ba, ni dai ba juya ba ce, balle a ce bana haihuwa, amma kullum ita ce ke ɗaukar ciki a gidan nan ban da ni".
Dariya Turai tayi, ta ce "Haba ƙawata, faɗi dai wani zancen ba wannan ba, ke ma kin san Zainab ba zata aikata hakan ba, wannan matar zuciyarta tsarkakakiyyace, kamar ta Aysharcool, shiyasa ki ka ga wani lokacin duk abin da muke yi mata baya tasiri, saboda ta dogara da Allah, sannan gata da son ibada".
Cikin fushi da ƙunar zuciya, Mami ta ce "Turai me ki ka nufi ne? ki na nufin ni bana tsoron Allah ne? ko kuma ni kin kafurta ni ne?".
"Ni fa ba haka nake nufi ba, kin san halina, duk da ina da mugun hali, amma hakan ba zai hana ni faɗar gaskiya ba, komai ɗacinta".
Mami ta ce"Ba na son irin wannan maganar, zamu iya samun saɓani dake, matuƙar ki na mini irin wannan zancen, ki riƙe gaskiyar in dai akan wannan matar ne".
"To na ji mu bar wannan maganar Allah ya baki haƙuri zan ki ya ye". "Da dai yafi, yanzu ya ake ciki?"
"Yawwa mun yi magana da wata ƙawata ne, ta ce mini zata haɗa ni da wani malaminta, aikinsa kamar yankan wuƙa, ba irin aikin da baya yi, kuma shi ko mutum bai je ba, zai iya yi masa aiki, kuma yasa a kawo masa har gida, sai dai aikin na sa akwai tsada sosai, sannan kuma aikinsa yafi tasiri ne akan masu saka ce da ibada, kin ga kenan ba lallai aikinsa ya yi tasiri akan kishiyarki ba, sai dai a yi wa shi mai gidan. Duk da ita ma ɗin zamu gwada yi mata mu gani ko za mu yi nasara".
Nisawa Mami tayi ta ce "Wannan matar an yi tsinanniyya, ba komai, kin san kuɗi ba matsalata bane, ni dai burina cikin ya fita, sannan a lalata mahaifar ta yanda ba zata sake ɗaukar ciki ba, amma kuma ki na ga idan asirin bai yi tasiri a kanta ba ta ya za a yi cikin ya bar jikinta? ko kuma ta ɓangaren Alhaji ma za a iya samun
nasara ya zubi".
"Eh to wannan dai ne ban sani ba, yanzu dai sai na yi magana da malamin, tukuna na ji me zai ce".
"Tom shikenan ba damuwa, ina jiranki duk yanda kuka yi ki taɓo ni, zan tura miki kuɗi, idan ma basu isa ba sai ki yi mini magana". "Ok sai kin ji ni" Turai tayi maganar tare da kashe wayar.
Sai bayan isha Mudan ya dawo gida, a gajiye, kai tsaye sashensa ya wuce, a falo ya zauna, ya na rage kayan jikinsa, tsabar gajiya ko ƙofar bai tsaya rufewa ba, ji ya yi an banko ƙofar da ƙarfi, da sauri ya ɗago da kansa, Hudah ya gani tsaye ta na bin sa da wani irin kallo, gabansa ne ya yi mummunar faɗuwa, ji ya yi shakku, da tsoro, haɗe da razani, sun yi masa dirar mikiya a zuciyarsa, ya ji Hudah tayi masa wani kwarjini, tunda yake bai taɓa ganin Hudah a irin wannan yanayi na ɓacin rai ba, kuma ya san hakan baya rasa nasaba da abin da ya faɗa ɗazu a gabanta. Tattaro jarumtarsa ya yi, ya ɓoye duk wata fargaba, ya ce "Suweety lafiya na ga kin shigo ba ko sallama? kuma na ganki cikin yanayi na damuwa?".
Lallai wato a duniyar ƴan iskan ma. Ya Mudan tantirin ƙwallon ɗan iskane, cewar Huda a zuciyarta, "Kar ka raina mini wayo me ka ɗauke ne? ko kuma ni ƙaramar yarinya ce da zaka yi wa pretending kamar baka san me nake nufi ba, to wallahi wallahi wallahi. Ya Mudan ka yi kaɗan baka isa ba. Kuma ka bani mamaki, ka yi mini abin da ban taɓa tunani ba, sannan kasa wa ranka cewar ba zaka taɓa auren Sharifa ba, wato ni ka rusa mini rayuwata, kai kuma ka na ƙoƙarin inganta taka ina matsayin ƴar uwarka ta jini, amma zaka iya yi mini wannan cutar, idan har kai zaka iya guduna, ba zaka rufa mini asiri ba, tom wa ka ke tunanin zai rufa mini?".
"Please Hudah ki fahimci ni, ni fa ban ce ba zan aureki ba, sannan ba fa ni na ce zan aure Sharifa ba, wannan haɗin na su Abba ne, kuma kin san ba zan iya ce masa a'a ba, dan haka ki kwantar da hankalinki, aure tsakanina dake ba fashi, but ina son ki ba ni dama na fara auren Sharifa, kafin" bai ƙarasa maganar ba, Hudah ta katse sa da faɗin "I don't like mistreatment Ya Mudan".
"Haba Hudah ba zancen wulaƙanci ba ne, kin san fa you are the one my heart chose so kar ki wani damu".
Kallonsa kawai tayi, ba tare da ta kuma magana ba, ta juya ta bar falon, don idan ta tsaya ba abin da zai hana ta ƙundumamasa uwar ashar.
Ajiyar zuciya ya sauke, ganin ta fita ya ce "Jarababiyya kawai, sai dai ki yi haƙuri, aure ne dai ba fashi, sai na aure Sharifa".
******
Mama fitowa tayi waje, bayan ta a je wa Baba abincisa, ta tarar su Afnan basa gurin sun shige ɗakinsu, ɗakin ta shiga ta same su, Maryam sai cika take, ta na batsewa, zama tayi ta dube su ta ce "Shiyasa a ko da yaushe nake cewa ku kasance masu haƙuri, da kawar da kai akan komai. Duk abin da za a yi muku a gidan nan, na ce ku yi haƙuri, ku yi kamar ba ku ji ba, ba ku gani ba, amma ina, kun kasa fahimta, musamman ma ke Maryam, na rasa in da ki ka ɗakko wannan rashin haƙurin, yanzu ki du bi abin da ki ka jawa kan ki, rabon da Babanku ya dake ki tun ku na yara".
"Wallahi ba wani rashin haƙuri, kawai dai an tsanemu ne, kuma duk abin da Baba zai yi mana ziga ce, irin ta Gwaggo da wancan baƙar muna fukar matar mai shegen kai kamar an yi dakon alewa, wallah Mama duk ranar da wannan figagiyyar ƴarta ta dawo, duk abin da tasa aka yi mini akan ta zan rama".
Dariya ce taso suɓucewa Mama, jin Maryam ta ce "kan Hajara kamar an yi dakon alewa" amma sai ta fuske ta ce "Ai kin ji matsalarki rashin haƙuri, tom ko kusa kar in ji kin taɓa yarinyar nan".
Sannan ta dubi Afnan ta ce "Afnan ina so zamu yi magana dake, kuma ina son duk abin da ya zo miki, mai kyau ne ko akasin haka, ki ɗauka tun ran gini tun ran zane Allah ya ƙaddara hakan a cikin kundin ƙaddarar rayuwarki, sannan komai ya faru da mutum da sanin Ubangiji".
Cikin yanayi na rauni, da buguwar zuciya, Afnan ta ce "Mama meyafaru? wani abin ne ya faru da ni ko kuma yake shirin faruwa da ni?".
"Afnan mahaifinki ya na son aurar dake ga duk wanda yasa mu" nan ta gaya musu duk yanda suka yi da Baba.
Wata irin zabura Afnan tayi, ta miƙe tsaye, jikinta ya ɗau rawa, da sauri Maryam ta miƙe tsaye ta riƙe Afnan dake ƙoƙarin faɗuwa, ta ce "Aunty Afnan ki kwantar da hankalinki, ki natsu, in sha Allah kin fi ƙarfin a yi miki irin wannan auren, sai dai mu ji ana yi a wani gurin, ba dai nan gidan ba".
"To ki bari idan aka tashi ɗaura mata auren ki hana, ko kuma ki bi dare ki kashe mijin". suka ji an yi maganar daga bakin ƙofar ɗakin.
Amanar cool ce ✍️
***