RAMIN ƘARYA...

Chapter 19-20

by @amanarcool323

💫 *RAMIN ƘARYA....*💫




               Story & writing

                        By

       Mrs Muttala (Amanar cool) 





*YOUNG TALENT WRITER'S ASSOCIATION*




Sadaukarwa ne ga Aysharcool 




Free book✍️




Page 19&20





_________Afnan wani irin yanayi ta tsinci kanta a ciki, ta ji duniya tana jujjuya mata, ga wani jiri da yake ɗibarta, yana kai ta can wata uwa duniyar da bata taɓa tunanin zuwa ba, tunda take ba ta taɓa tsayawa ta saurari saurayi ba, balle har ta tsaya jin irin wannan soki burutsun da wannan ɗin yake faɗa mata, riskar kanta tayi da jin wani baƙon al amari da ta kasa tantance me take ji a zuciyarta ta, a hankali ta ɗago da fuskarta ta dube shi, ido huɗu suka yi da juna, da sauri ta sunkuyar da kanta, cikin rawar murya ta ce "Na gaji da tsayuwa ina so zan shiga gida". 


Murmushi yayi, tare da shafa gemunsa, ganin yadda ta diririce baki ɗaya lokaci guda. Ya numfasa ya ce "Ina fatan ba maganganun nawa ne, suka sanya miki gajiyar ba?" Ta girgiza kai ba tare da ta ɗago ba.


Ya jinjina kai ya ce "To ya yi ba damuwa, ba zan takura miki ba, haka kuma ba zance dole sai kin ba ni amsa a yanzu ba, na baki dama ki je ki yi shawara, amma dan Allah ka da a yanke hukuncin da zuciyata ba zata iya ɗauka ba, a taimaki bawan Allah wanda zuciyarsa tayi rauni akan abin da yake so da muradin kasancewa tare da shi".

Ƙafafuwanta ne su ka hau rawa, hakan ya tilasta mata juyawa ba tare da ta ce masa ƙala ba, ta na ƙoƙarin shiga gidan domin kaucewa abin kunya ta faɗi a gabansa. Haidar ya kuma cewa "Afnan" cak ta tsaya sai dai ba ta juyo ba. Zuciyarta ta tsananta bugawa, wani irin gumi ya din ga keto mata, saboda yadda ƙwaƙwalwarta ta karɓi amon muryarsa da ya yi amfani da ita gurin kiran sunanta.

Ya ce "Babu mamaki yadda idanuwanki ke satar zuciya, haka murmushinki yake ƙara saurin buguwar zuciyata. Ki sani ke ce gaskiyar rayuwa, ke ce asalin burin da na ke fata, ke ce gaskiyar mafarkin da nake kowane dare, ke ce farko da ƙarshen kowane tunani da nake yi. Afnan wataƙila ba zan samu damar sanar dake a kullum ba, amma ki sani kalmomin da ke bakina ba za su iya gabatar da shauƙin da nake ji a kanki ba".

Da sauri ta ƙarasa shiga ciki, jin zuciyarta na bugu da ƙarfi! 

Murmushi Haidar ya yi, ya na girgiza kansa, wani irin sanyi ne ya ji yana ratsa zuciyarsa yana bin ko wane sassa na jikinsa, a hankali ya juya ya bar ƙofar gidan, yana jin sa cikin tsananin farin cikin yau ya samu damar ganin Afnan, kuma ya amaryar mata da abin da ke cikin zuciyarsa a game da ita, babur ɗinsa ya shiga ya na ƙoƙarin tadawa Ummansa ce ta faɗo masa a rai, maganganun da ta yi masa ne suke dawo masa ɗaya bayan ɗaya, dafe kansa ya yi "Oh may God Me yasa na kasa haƙura na bi umarnin Umma?. Ki yi haƙuri Ummana na kasa cika umarninki, zuciyata ta kasa haƙura". Kira ne ya shigo a wayarsa, da ƙyar ya iya cirota a aljihunsa, uban gidansa ne ke kira, ɗauka ya yi kafin ya yi magana ya ji ya ce "Haidar batun tafiyar da na ce ka rakani ka yi zamanka ba sai munje tare ba, yanzu haka ma na kama hanya, shi ne na ce bari na sanar da kai". 

Haidar ya ce "Mai gida Allah yasa ba wani laifin na yi ba?".

"A'a Haidar ko ɗaya dama wani dalili ne ne yasa na ce ka shirya mu yi tafiyar tare, to sai kuma dalilin ya janye, kar ka wani damu". "To ya yi mai gida Allah ya kai ka lafiya ya tsare hanya". "Ameen Ameen Haidar". Kashe wayar ya yi, ya tayar da babur ɗinsa ya bar gurin.

Afnan ɗaki ta shige tayi kwanciyarta, tana jin Maryam na yi mata magana amma ta shareta, maganganun Haidar ne ke ta amsa kuwwa a kunnenta, gefe ɗaya wani irin ciwo kanta yake mata kamar zai rabu gida biyu, Maryam ta ce "Aunty ya Haidar ɗin har ya tafi ne?". Ɗaga mata kai ta yi alamar eh Maryam za ta kuma yin magana Afnan ta ce "Please Maryam kar ki dame ni, ba na jin daɗi".


Gwaggo ta sa kawu ya kira mata Yaya Bala mai gari na can ƙauye, bayan sun gaisa ta ce "Yaya dama magana ce akan yarinyar wurin ɗan ladi A'isha" . Ya ce ya ce "Subhanallah! wani abune yasameta?" "A'a ko ɗaya ina so a cikin dangi a duba a samu wanda za'a haɗasu aure da shi, saboda nan garin taƙi ta fitar da miji, duk wanda ya zo nemanta sai ta ƙi, tun suna zuwa har sun daina zuwan, to shi ne na ce bari na yi maka magana, tun da ta ƙi ta fitar da miji a nan zansa a nema mata shi a nan gurinku, dan ni ba zan lamunci ganinta haka ba, yarinya ta na gwada ƙugu ita da uwarta, su kuma iyayen nata da yake basu da hankali, goya mata baya suke yi".

"Anya Halima ki na ganin wannan haɗin zai yi yu kuwa? bana tunanin yarinyar nan za ta iya zama nan garin, duba da yanayin na ku garin, kuna cikin birni, yarinyar da ta tashi a birni, kuma ta yi karatun boko, ta ina za ta iya zama a nan, sannan ki na ganin ita uwar yarinyar za ta yadda ne? Ai ƙwarya ta bi ƙwarya".

"Haba Yaya, ka daina zancen amincewar yarinya, da ta iyayenta, ai abin da na ce ayi dole shi za ayi, babu wanda ya isa ya saɓawa umarnina, a cikinsu, ni dai Yaya ina buƙatar ka yi mini wannan alfarmar, inda hali ma a ɗaura mata auren a can, in ya so sai a ɗauki amaryar a kai".

Shiru ya yi, yana nazarin maganarta, sannan ya ce "Shikenan ba damuwa, an jima zan zauna da ƴan uwa sai mu ji abin da yakamata ayi".

"To ya yi na gode sosai Allah ya ƙara girma, a gaishe mini da mutan gida, sai na ji ku". 



*******


Abba ya dubi Mudan ya ce "Mudassir shin ka samu zuwa gurin Sharifa?" "Eh Abba na je" "To ya kuka yi da ita? ina fatan kun dai-dai ta kanku?" "Eh Abba babu wata matsala, ita ma ta aminta da ni".

"To ma sha Allah, dama haka na ke son ji, tashi ka tafi, Allah ya yi muku albarka".

"Ameen Abba na gode sosai" bayan fitar Mudan Abba ya kira amininsa, bayan sun gaisa ne, "Ya ce maganar yaran nan ce, yanzu na tambaye Mudan ya je gurin Sharifa, ya ce ya je har sun dai-dai ta kansu".


Alhaji Munir ya ce "Ma sha Allah na ji daɗin wannan maganar, jiya nake tambayar Fatima Mudan ya zo, ta ce ya zo, sai dai ba ta san yanda suka yi da Sharifa ba, to ka ga ashema har sun dai-dai ta kansu, yanzu musa mu lokaci mu zauna, sai mu ga yanda za mu tsara lamarin". "To shikenan Allah ya tabbatar mana da alkhairi". Ya amsa da "Ameen " sannan suka yi sallama.


Haidar kai tsaye gida ya nufa, ko da ya isa Umma ta ce "Haidar ina ka je ne? Kai da ka ce mini zaku yi tafiya kai da mai gidanka, ko dai an fasa tafiyarki ne?" . "A'a Ummu ba fasawa aka yi ba, yanzu ma haka ya wuce" .

"To ka ce mini kuma tare zaku je, me yasa kuma baku tafi tare ba, ina fatan dai ba wani laifin ka yi masa ba?" "A'a Umma ba abin da na yi, dama akwai dalilin da yasa zamu yi tafiyar ne tare, to kuma yanzu dalilin ya janye shiyasa ya ce na yi zamana kurum".


Ta ce "To ya yi ba damuwa, Allah ya dawo da shi lafiya" . Da "Ameen" ya amsa ya na ƙoƙarin shigewa ɗakinsa sai ya ji ana sallama, a ƙofar gida dakatawa ya yi, ya na jin kamar muryar Faruk ce ke sallama, fita ya yi waje domin duba mai sallamar, aikuwa shi ɗin ne, cikin tsananin farin ciki suka rungume juna, Haidar ya ce "Yau kaine a gari babu sanarwa".

Faruk ya ce "Eh wallahi ni ne, dama cewa na yi ba zan faɗa maka ba, sai dai na yi maka zuwan bazata". Dariya Haidar ya yi ya ce "To zo mu shiga ciki ko". 

Cikin gidan suka shiga, Umma na ganin Faruk ta ce "Ma sha Allah Faruku yau kai ne a gidan na mu? saukar yaushe?" "Eh Umma ni ne, ɗazu nan na iso, mun same ku lafiya?". "Lafiya ƙalau Alhamdulillah, to ya hanya? ya karatun? ina fatan dai ka kammala karatun duka?" "Eh Umma na kammala gaba ɗaya" 

"Ma sha Allah to Allah ya yi albarka, yasa aci amfanisa kai da abokin naka" "Ameen ameen Umma mun gode sosai".

Ɗakin Haidar suka shiga, abinci Umma ta kai musu, bayan sun kammala cin abinci ne, Faruk ya lura da ya na yin Haidar kamar akwai abin da ke damunsa, duban sa ya yi sosai ya ce "Haidar kamar akwai abin da ke damunka. What is problem?". Haidar ya numfasa sannan ya ce "Abokina damuwa kam akwai ta, ka san ba abin da zan ɓoye ma" .


"Eh haka ne na sani, me yake damunka ne? "

"Soyayya" 

"Soyayya kamar ya? bangane ba?".

"Na kamu da soyayyar wata yarinya ne".

"To na ji ita yarinyar ba ta sonka ne? ko kuma akwai wata matsalar ne?".

"Abokina akwai matsala fa Umma ba ta bani goyon baya ba, sannan ita kanta yarinyar ban san matsayata a gurinta ba, kai in taƙaice maka yau ne na samu damar sanar da yarinyar cewar ina sonta" .

Faruk ya ce "Na ji, kenan Umma ka fara yiwa zancen yarinyar ko?" . "A'a ita ma ban fara faɗa mata ba, ka san iyayenmu da saurin fahimta" nan Haidar ya kwashe komai ya gayawa Faruk ya ce "Faruk na so na haƙura da zancen kamar yadda Umma ta buƙata, sai dai ina na kasa haƙura, ina son yarinyar nan sosai".

"To amma me yasa Umma za ta ce haka? duk da ta na da gaskiya, amma shi aure nufin Allah ne, kuma duk lokacin yinsa ya yi ko mutum bai da ko sisi Allah zai kawo masa buɗi da mafitar yanda zai yi lalurar auren ba tare da kowa ya sani".


"Haka ne abokina amma ka ji bayanin da Umma tayi" 

"To amma Haidar why can't you complain"?

"Faruk I can't complain because she is my Mom". Ya ce "To ka yi haƙuri ka bi umarninta mana, ka haƙura da zancen yarinyar tunda ma baka da tabbacin ta na sonka". Shiru Haidar ya yi bai kuma magana ba, ganin hakan yasa Faruk juya akalar firar su zuwa wata firar da ban.

Da yamma Feena ta zo gidan su Maryam ta duba lafiya Maryam ɗin take, saboda yau ba ta je makaranta ba, duk rashin kunyar Maryam ba ta fashin makaranta, sai dai idan ta je ta ga ji da zama za ta gudu, ko da ta isa Mama sai Afnan ta tarar, Maryam ba ta nan, ta na gurin Inna Bilki da ta dawo daga unguwa shine ta je gaisheta, Afnan ta ce "Safeena zo ki zauna yanzu za ta shigo".

Feena ta ce "A'a aunty bari na je can na same ta". Afnan ta ce "To shikenan".

Feena na fitowa tayi arba da Zaliha ɗiyar Inna Hajara wadda ita ma yau suka dawo, wani banzan kallo tayi wa Feena ganin ta fito daga ƙofar su Afnan, sannan ta ja tsaki tare da tofar da yawu, Feena ta ce "Ikon Allah ke kuma boyar Allah da wa ki ke?"

"Da ubanda da duk ya tambaya da shi nake" Feena ta ce " Me na yi miki da za ki zagar mini uba?"

"An zage shi ɗin, waye shi? da ba za'a zage shi ba". Ai ba ta gama rufe baki ba Fenaa ta kai mata wani bahagon mari, Maryam dake tsaye tunɗazu ta na kallon su ta ce "Kin yi mini dai-dai ƙarawa shegeya, ƴar iska, munafuka". Shaƙe Zaliha Feena tayi, ta na kai mata duka, Inna Hajara jin hayaniya yasa ta fitowa, ganin anshaƙe mata ɗiya yasa ta kurma ihu ta na faɗin "Gwaggo dan Allah ki zo zasu kashe mini yarinya yau yau da dawowarta". 

 

Amanar cool ce ✍️
***