RAMIN ƘARYA...

Chapter 29-30

by @amanarcool323

💫 *RAMIN ƘARYA....* 💫




              Story & writing 

                         By

    Mrs Muttala (Amanar cool)




*YOUNG TALENT WRITER'S ASSOCIATION (YOTA/021)* 




Sadaukarwa ne ga Aysharcool 




Free book ✍️



Page 29&30



__________Misalin ƙarfe goma na safe Alhaji Munir da iyalinsa suka zo duba jikin Ammi, a falo suka tarar da su, Abba na bata shayi a baki, zama suka yi, tare da gaisawa, sannu da jiki suka yi mata, Sharifa ma gaisheta tayi, ta na sunkuyar da kai ƙasa, ganin Abba kusa da ita kamar zai shige jikinta, basu daɗe da zama ba sai ga Mami ta shigo, zama tayi ta na yi wa Ammi sannu da jiki, ta gaida Alhaji Munir, sannan ta dubi Fatima ta ce "Hajiya Fati barka da safiya, ya ki ke ya gida?" 

"Lafiya ƙalau Alhamdulillah, fatan mun same ku lafiya?" "Alhamdulillah mun gode Allah, za a ce".


Sharifa a dole ba dan ranta ya so ba, ta ce "Barka da safiya Mami" sai a lokacin Mami ta lura da Sharifa dake zaune a ƙasa ta laɓe gefen kujera, "Ah Daughter ashe tare kuka zo? ai ban lura dake ba, lafiya ƙalau, ya ki ke ya karatu?" . Tayi maganar cikin iyayi wai ita mai sirika.


 Ta amsa mata da "Alhamdulillah"

 "To ma sha Allah, Allah ya taimaka, tashi a ƙasa mana ki hau kujera" ƙara sunkuyar da kai tayi, ta kasa tashi. Abba ya dubi Mami ya ce "Ina Mudan da Huda? suma yakamata su zo" "Huda na ɗakinta, shima haka, bari na kirasu".


Mudan na kwance abin duniya ya dame shi, tunda Huda tayi masa zancen ta na da ciki ya ke cikin fargaba, da tashin hankali, ya kasa sukuni, sannan ya na son sanin gaskiya ne ko dai ta faɗa ne, dan ta ɗaga mishi hankali, to amma ai ba abin mamaki bane dan ta ce ta na da juna biyu, lumshe idanuwansa ya yi, ya na jin zuciyarsa na ƙara buɗewa, baƙon al amarin da yake ji a tattare da shi na ƙara kutsa kanshi a cikin zuciyarsa, ƙara rufe idanuwansa ya yi, hoton fuskarta ne yake yi masa gizau. Ƙarar kiran da ya shigo wayarsa ne ya sa shi buɗe idon, Mamina ya gani a kan fuskar wayar, ɗauka ya yi, ya ji ta ce "Ka zo ɓangaren Zainab yanzun nan" daga haka ta kashe wayar, tashi ya yi, ya fita.


Huda ma Mami ta kirata, ba dan ranta na so ba, haka ta nufi sashen ita ma. Ita ta fara shiga da sallama, amsawa suka yi, ta gaishesu ta nemi guri akan kura tayi zamanta, idonta ne ya sauka akan Sharifa, nan take ta ji zuciyarta na mata zafi da raɗaɗi, wani irin azababben kishi ta ji ya na ta so mata. Muryar Mudan ta ji, yana gaisawa da su Abba, sannan ya gaida Ammi da Momyn Sharifa, shima zama ya yi, sarai ya ga Sharifa amma sai ya yi banza da ita kamar bai ganta ba, saboda a yanzu ko fuskarta baya son gani.


Abba ya ce "Mudan ba ka ga ƙanwarka Sharifa ba ne? na ga baku gaisaba". Dady ya ce "Ai ita yakamata ta fara gaisheshe, tunda ita ce ƙarama" dariya Abba ya yi, ya ce "Ina ga kunyarmu suke ji ne, bari muyi musaka ranar bikin nan da wuri". Mami ta ce "Lallai kam gara a yi a gama, ba sai an saka dogon lokaci ba" Daga Huda har Sharifa da kuma uban gayyar Mudan, kowa da abin da yake ji kuma yake saƙawa a ransa, cikin takaici da kishi Huda ta ce "Mami zan iya tafiya?" "Ki tafi ina? bayan duk ga ƴan mu a nan, wato kin fi so ki je ki ƙunshe kanki a ɗaki kamar wata amarya? to ba inda zaki" . Kamar ta zunduma ihu haka take ji. 

Sharifa kuwa ji tayi zaman falon ya isheta gaba ɗaya, miƙewa tayi ta nufi hanyar bedroom ɗin Ammi, Mami ta ce "A'a Sharifa me za ki yi a ɗaki? ki fa saki jikinki, ki daina jin kunyar mu, mu fa iyayenki ne ba surukai ba, dawo ki zauna ƴar albarka". Ba yanda ta iya haka ta dawo ta zauna, Huda sai binta take yi da wani mugun kallo, su Ammi na lura da hakan, sannan sun san cewar zancen auren yasa Sharifa za ta bar falon. 

"Ni dai Abba da za a bi shawarata a daina zancen auren nan gaba ɗaya, a haƙura da maganar" Mudan ne ya yi wannan maganar, ya na kawar da kai gefe kamar ba shi ya yi ba.


"Kai Mudan wace irin magana ce wannan? akan wane dalili zaka ce a fasa auren? bayan da bakinka ka ce mini ka na sonta?" Abba ya yi maganar fuskarsa a murɗe babu alamar wasa. Shiru ya yi bai yi magana ba, cikin takwaici da jin haushi Mami ta ce "Ba magana ake yi maka ba? wannan ai iskanci ne da rainin hankali, dan ubanka tun farko da a ka zo ma da zance mai yasa baka ce a'a ba sai yanzu?".  

Dady ne ya yi gyara murya ya ce "Ku bi shi a hankali, a ji ta bakin sa, kai Mudan me yasa ka ce a fasa auren" .

"Dady ba komai, kawai ni dai ba na son auren ne, a yi haƙuri, a bar wannan maganar, dan Allah".


"Wallahi Mudan baka isa ba, ka yi kaɗan, ni za ka kunyata, auren ne ba ka so? saboda shashanci, to muddin kaga ba a yi auren nan ba sai dai in ita Sharifar ce ta ce ba ta sonka" Mami ta ƙare maganar cikin masifa da ɗaga muraya. Sharifa da Momy wani irin farin ciki ne ya mamaye su, sai hamdala suke yi a zuciyarsu, Huda ko da ta na da halin tashi ta taka rawa da tayi, rabon da ta ji farin ciki a zuciyarta tun kafin ƙulluwar wannan maganar. Ammi kuwa sam ba ta ji daɗin abin da Mudan ya ce ba, duk da ta san Sharifa da Mamanta ba son auren suke yi ba, amma ta so a yi auren ko Allah zai sa Mudan ɗin ya yi hankali ya rage wannan yawon da yake yi. 


"Mudassir"

"Na'am Abba"

"Me yasa tun farko da na yi maka maganar baka nuna rashin amincewarka ba sai yanzu?"

"Abba a lokacin ina jin sonta ne a raina"

"To yanzu fa? ba ka sonta ka ke nufi ko me?"

"Abba dan Allah ka yi haƙuri, ba wai rashin kunya ce zan yi maka ba, ba kuma nuna maka cewar baka isa ka bani umarni ba ne, Abba a yanzu ina da wadda nake jin sonta a raina..." bai ƙarasa ba ya ji saukan mari a fuskar shi, Mami ce cike da baƙin ciki ta ce "Rufe mini baki, sakarai mara hankali, ana ƙoƙarin yi maka gata ka na yi wa mutane iskanci da shirme, to matuƙar ni ce uwarka Sharifa za ka aura". Dady ya ce "Saratu koma ki zauna abin duk bai kai haka ba. Zama tayi ta na ciga ba da masifa shikuma uban gayyar ko a jikinsa.

Dady ya dubi Sharifa ya ce "Ke ki faɗa mini idan ke ce ki ka masa wani abin? ko ki ka nuna masa ba kya sonsa" 

"Wallahi Dady ba abin da na yi masa, kuma ni ban ce masa ba na sonsa ba, ai gashi nan da bakinsa sai ya faɗa" Abba ya ce "Kama bakin ki Sharifa, ai dama na san ba za ki ce haka ba, kuma shima ya bani mamaki, amma ba komai, tunda har ya iya dubin idonmu ya ce baya so, to tabbas ba za a yi auran ba, gara da ka faɗi tun kafin a yi auran a zo ana samun saɓani, dan haka na janye wannan maganar, auran dole baya cikin tsarina, Allah ya fito mata da wani mijin, kai kuma ya haɗaka da wadda ka ke so ɗin".

"Haba Alhaji ya za ka ce haka, dan me za ka biye masa, shi ɗin banza, ai bai isa ba" Mami tayi maganar kamar za ta yi kuka. 

"Haba Zainab ya isa mana, shi fa zai zauna da ita, sannan ya ce ya na da wadda yake so, to gara abar shi ya aure wadda yake so ɗin, daga yanzu ina son abar wannan maganar kar a ƙara ta da ita". Duban Mudan tayi da yake ta murmushi ta ce "Ka kyauta Mudan, kuma da ni ka ke zancen, sai na ga wadda zai aura maka wadda ka ke so ɗin" ta na kai wa nan ta miƙe fuuu ta bar falon, Huda ma bin bayanta tayi, ta na jin kamar an yi mata albishir da aljanna, shima tashi ya yi kamar wani munafuki sum-sum ya fita.

*********


Afnan da wani matsanancin ciwon kai ta tashi, da ƙyar ta iya fitowa waje, ga wata kasala da ta take ji, gaba ɗaya ba ta jin daɗin jikinta, Mama na zaune, ita ma zaman tayi, Mama ta dube ta ta ce "Lafiya dai? na ganki haka kamar wadda aka zarewa jijiyoyin jiki" "Mama kaina ne ki mini ciwo, sannan ba na jin daɗin jikina" "To Allah ya sauwwaƙe, tashi ki je ɗakina ki duba akwai maganin ciwon kai na nan, ki sha" amsawa tayi da "To" sannan ta miƙe ta ɗakko maganin ta sha. Bayan ta sha ne ta ce "Mama ina Maryam?" 

"Ta na Makaranta, ba ta dawo ba, ina ga matsalar abin hawa ne, tunda yau juma'a ce ba daɗewa suke yi ba". "Eh haka ne kuma"


Inna Hajara ta zo har ɗakin Gwaggo, bayan ta zauna ta ce "Gwaggo wai ni ko mai Sanusi ya je yi a ƙauye? na tambaye shi ya yi mini shiru, da ga baya ya ce idan ya dawo koma minene zan ji" "Eh ni ce na umarce da hakan, saboda ba na son kowa ya sani sai komai ya kammala" Hajara ta ƙara lanƙwashe kafa ta karye muraya ta ce "Gwaggo faɗa mini mana ba wanda zai ji, ai kin san ni ba irin sauran ba ne". "Hajara ki yi Haƙuri zuwa anjima zaki ji koma minene, akwai abin da nake shiryawa ne akan waƴancan yaranne" Hajara ta ji haushin rashin faɗa matan da ba ta yi ba, amma da ji ance akan su Afnan sai ta ji sanyi a ranta, nan ta fara aikin na ta na ƙara ruru wutar ƙiyayyar su a zuciyar Gwaggo. 


Sai wuraren ƙarfe ɗaya kawu Sanya isa ƙauyen, an yi masa tarba mai kyau, Mai gari ya ce "A'a ya muka ganka kai ɗaya ina shi Abbakar ɗin?" 

"Ai ba zai samu damar zuwa ba ne, ya na da wani babban uzuri ne, shiyasa ya ce ni na zo, ai na wadatar tunda dama ni ne ma ɗaurin aurenta" 

"To ya yi ba damuwa, Allah ya tabbatar mana da alkhairi, yanzu sai ka shirya saboda lokacin zuwa sallan juma'a ya yi, kowa da shirinsa zai je, ana idarwa sai a ɗaura auren"

Shiryawa kawu ya yi gaba ɗaya mutanen gidan kowa ya shirya, suka nufi masallaci, dama ansanar da jama'a tun jiya cewar akwai ɗauren auren da za a yi bayan an idar da sallan. Sarkin fada ma ya zo da ƴan uwan shi.

Bayan sallan juma'a ne, jama'ar suka shaida ɗauren auren Afnan wanda kawu Sanusi ne ya bada aurenta akan sadaki dubu hamsin.

A dai-dai lokacin gaban Afnan ya buga da ƙarfi, haka kawai sai ta saki kukan da ba ta san dalilin yinsa ba, daga Mama har Maryam da kallo suka bita, suna mamakin me ya sakata kuka kuma. 


 Ina Hajara na zaune ta ji ana kiran wayarta kawu Sanusi ne, ta na ɗauka ya ce "Hajara kawai Gwaggo wayar" ba ɓata lokaci ta kai mata, Gwaggo na amsa ya ce "Anɗaura yanzun nan" guɗa Gwaggo ta rafka sannan ta nufi sashensu Afnan ɗin 

Ganin kukan na Afnan yaƙi ƙarewa yasa Mama ta ce "Ke wai wane irin abu ne haka za ki saka mutane a gaba ki na kuka babu laifin zaune ba na tsaye" 

"To Amina ai dama duk wanda ya tsinci kansa a irin wannan ranar dole ne ya shiga wannan yanayin, kuma ya yi kukan rabuwa da gida". Juyawa suka yi suna kallon Gwaggo dake maganar ta na yi musu murmushi.



_Gaskiya zan daina yin posting ɗin nan, saboda rashin comment, comment ɗinku shi ke ƙara mana ƙarfin gwiwar yin typing. To ba kwa yi, dan haka zan daina yi._


Amanar cool ce ✍️ 
***