RAMIN ƘARYA...

Chapter 33-34

by @amanarcool323

💫 *RAMIN ƘARYA....* 💫



_WRITING BY AMANAR COOL_✍️



*YOUNG TALENTED WRITER'S ASSOCIATION (YOTA/021)*



_A yi haƙuri ji na shiru da aka yi na kwana biyu, bani da lafiya ne. Sannan ina baran addu'arku Allah ya yi wa sirikina rasuwa😭 Allah ya jiƙansa da rahama, yasa aljannace makoma a gareshi, da jama'ar musulmi baki daya🙏_


Free book 📚 


Page 33&34


___________Cak ya tsaya ba tare da ya juyo ba, "Ba magana nake yi maka ba?" Mami tayi maganar cikin jin haushin sa, juyowa ya yi ya dawo ya zauna, kafin Mami tayi magana Huda ta ce "Ya Mudan. Why are you not picking my calls?". 

"I have been busy" ya bata amsa ba tare da ya kalli inda take ba. Shiru tayi ba ta kuma kula shi ba, amma ƙasan zuciyarta ta ji haushin yanda ya ba ta amsa ɗin.

Ta dube shi Mami tayi da kyau sannan ta ce "Mudan wato saboda kai shashasha ne, baka da hankali, Shi ne za ka yanke wannan ɗanyen hukunci ba tare da sani na ba ko neman shawarata ba?  Mudan ni zaka kunyata? Ka tozarta ni a gaban kishiya? Ka barbaɗa mini ƙasa a ido, saboda baka da tunani ina kwaɓar bakinka amma sai da kayi abin da ranka yake so". 

"Mami ni fa..."   "Rufe mini baki ko yanzu nayi mugun saɓa maka, Mudan na raina wayon ka, tukuna ma ƴar gidan ubawa ye ka samu da har ka aikata mini wannan aiki?" .

Shiru ya yi mata, "Wai ba magana nake yi da kai ba? Ba na son wannan sabon iskanci da ka tsiro mini da shi, ke Huda ki na da masaniya akan wannan maganar? idan ya faɗa miki wani abin ki gaya mini".

"Wa ni rufamin asiri Mami yaushe rabon ki ga mun zauna da shi muna hira? I have no idea"

"Ko ma ƴar gidan uban waye, ai dole zan sani, tashi ka fita ka bani guri, sakarai kawai". Miƙewa ya yi ya fita daga cikin falon. Da sauri Huda ta bi bayansa, da ido Mami ta raka su tayi tsaki.

Ya na fita Huda ta sha gabansa ta ce, "Ni zaka cewa uzuri ka ke yi? Har akwai uzurin da zai hana ka ɗaukar kirana, wai me ka ke nufi ne? Kar ka manta ina ɗauke da cikinka a jikina. Dan haka stop mistreating me.

"Huda joking aside. Da gaske ki na da ciki?"

"Au ka ɗauka wasa nake yi ne? To idan ka na kokwanto sai muje asibiti mana"  

"Ai kuwa Huda in dai ciki ne dake sai dai a zubar da shi, taya ki ke son mu kalli. Mami da wannan abin kunyar?".

"What! Impossible na je garin zubar da cikin na mutu a banza. I am really into it wallahi".

"Ok haka ma zaki ce?" 

"Eh na faɗa ɗin, kuma wallahi ina dab da yi mana terere a bainar nasi"

Haushi ne ya sa Mudan barin wurin bai sake kula ta ba, ita ma ciki ta koma, Mami na zaune a falo taga Huda ta wuce fuuuu ranta a ɓace.

***********

Sai bayan magariba kawu Sanusi ya iso gida,  kai tsaye inda Gwaggo ya wuce, cikin murna take yi masa ya hanya, zama ya yi, tare da cewa "Gwaggo sannu da gida"  "Yawwa ɗan albarka, ya gajiyar tafiya?"

"Gajiya kam akwai ta, na sha hanya, kin san tafiyar ɗai rana a wannan ƙauyen a kwai wahala"  "Haka ne, amma ai mun gode Allah da yasa ka je lafiya ka dawo lafiya. To ya ka baro su Yaya ɗin?" 

"Duk suna lafiya, sun ce a gaishe ki"

"Ma sha Allah, abu yayi kyau sosai, yau ina cikin farin ciki, burina ya cika. Amina ba yanda za tayi da ni, to ya batun ɗaukar amaryar? Yaushe zasu zo?"

Kawu Sanusi ya ce "Gwaggo bari na je dai na watsa ruwa, na ci abinci sai na dawo muyi magana".  "To shikenan, Allah yayi maka albarka". Miƙewa yayi ya nufi sashensa.

Gaba ɗaya su Afnan a cikin damuwa suke hadda Baba. Duk da shi bai nuna musu irin ya damu ɗin nan ba, amma yanayinsa ya nuna hakan, Mama rasa abin yi tayi, tana son kiran ƴan uwanta ta shaida musu abin da ke faruwa amma ta kasa sanin me za ta ce musu, shiru tayi abin duniya duk ya isheta, wani irin tausayin ƴarta ne ya addabi zuciyarta, ta na tunanin taya Afnan zata iya rayuwar aure a wannan garin. Duk da shi aure nufin Allah ne, kuma babu inda baya kai mutum, amma ta na tausayin ƴarta da irin zaman da za tayi a can ɗin. 

Afnan kuwa tunda ta shiga ɗaki ta kwanta bata fito ba, ko kiran sallan magariba bai fito da ita ba, saboda ta na fashin sallan, da farko zuciyarta ƙeƙashewa tayi kukan ma ya ƙi zuwar mata, sai dai tana tuna Haidar da irin kalaman da yake yi mata, ba ta san lokacin da wani kuka ya suɓuce mata ba, kuka tayi kamar ranta zai fita. Duk wata tsanar Haidar da take ji ta nemeta ta rasa, wani irin tausayinsa take ji a zuciyarta, tana tuna irin magiyar da yake yi mata, da irin son da yake cewa ya na yi mata, yanzu ya zai ji idan ya samu labarin auren ta? Tayi wa kanta tambayar da ba ta da amsar ta. A hankali ta ce "Allah Sarki Ya Haidai, ka yi haƙuri, ka yi haƙuri, ni ma ban yi tunanin hakan zata faru ba, da na sani tun farkon zuwan ka na baka dama. Amma ina ban san abin da ya hau kaina ba, a lokacin, na kasa amsarka ba, sai ma haushinka da na ke ji. Ka yi haƙuri my Haidar, dama can ni ba matarka ba ce, i love you, I love you, i really love you my Haidar. Da sauri tayi istigfari data tuna da auren wani akanta take cewa tana son wani, duk da ba sanin mijin tayi ba, kuma ba son shi take ba, amma ko ba komai za ta ki yaye haƙƙin aure, gudun kar Allah ya yi fushi da ita.

"Aunty dama kina son Ya Haidar ki ka tsaya yi masa kwana kwana har ki ka yi wasa da damar ki? Yanzu me ye amfanin ɓoyon da ki ka yi? ribar me ki ka ci? Kin ja an aura miki wani can wanda baki sanshi ba, baki taɓa ganin shi ba, baki san halinshi ba, kuma wai tsabar mugunta a ƙauye".  Sai da Maryam tayi magana sannan Afnan ta san da ba ita kaɗai ce a ɗakin ba, dan bata san lokacin da Maryam ɗin ta shigo ɗakin ba.

A hankali ta tashi zaune, ta dubi Maryam sannan ta ce "Ni kaina ban san me yake damuna ba ba, Maryam a lokacin haushinsa nake ji, duk da ina jin daɗin kalaman sa, sai dai a ƙasan zuciyata sai na ji tsanarsa da haushinsa, Maryam ban san na damu dashi ba sai yanzu da aka yi mini wannan auren, na rasa ya zan yi, ina tausayinsa, ina tunanin halin da zai shiga. Idan ya samu labarin auren nan". Ta ƙarasa maganar tana sakin wani sabon kuka, zafi take ji sosai a cikin zuciyarta.

"Aunty Afnan ki yi haƙuri, dan Allah ki daina wannan kukan, in sha Allah wannan auren sai sun ga abin da basu yi zato ba akansa, ina ji a jikina wulaƙantar da ake son a ga ke yi, ba za su taɓa ganin hakan ba, mu ci gaba da addu'a Allah yana tare damu, kuma in sha sai sun ji kunya". Haka Maryam ta ce gaba da rarrashin Afnan cikin kalaman kwantar da hankali da sa nutsuwa, kamar ba ita ce mai wannan rashin kunyar ba.

Kawu Sanusi tunda ya dawo Hajara ke ɗauke masa kai, da hura hanci, ita a dole fushi take yi dashi, saboda an munafunceta da shi. 

"Hajara" kawu ya kira sunanta, sai dai tayi masa banza kamar bata ji ba. 

"Hajara" ya kuma kiran sunanta.

Kamar ta kuma share shi sai ta fasa cikin tsiwa da rashin sanin darajar miji ta ce "Lafiya wai da zaka zo ka dame ni da kira sai ka ce na ci ban biya ba?" 

Sakin baki yayi ya na kallonta, tare da tambayar kansa me aka yi mata? Take wannan abin kuma a gaban ƴarta.

"Hajara lafiya kuwa? Tunda na dawo naga kina fushi dani, magana ma da ƙyar ki ke yi mini"

"Ban sani ba, ka ga malam kar ka dame ni, ka je can ku ƙarata, wai har ni zaka ɓoyewa abin da zai kaika ƙauye, saboda an tsane mu ni da ƴata ba a sonmu, Sai ji na yi an ɗaurawa Afnan aure, su da yake ana son su ba a son ganinsu a gida, an fi son suna ɗakinsu hankali kwance, shiyasa aka nema mata mijin aure, har ake iƙirarin ko ƙanwarta, za a nemo mata nata. Ni kuma tawa ƴar ko oho".

Shiru yayi yana kallonta, ya kasa ƙwaƙwaran motsi, sai da tayi masa tijara son ranta. Duk wani haushin da Gwaggo ta bata a kansa ta huce. 

Sannan ya kalleta ya ce "Haba Hajara kema kin san wannan auren ba daɗi zai yi wa Amina da ƴa,ƴanta ba, sannan karki manta duk gidan nan ba wadda Gwaggo ke so kamar Zaliha, taya ki ke tunanin za ta yi mata irin wannan auren? Ke ma kin san hakan ba za ta faru ba. Sannan abin da yasa Gwaggo ta ce a ɓoye maganar ba ta son Amina ta sani ne, saboda kar tayi yunƙurin hana auren, na tabbata yanzu da zaki je inda suke ba za ki gansu cikin walwalaba. Dan Allah kiyi haƙuri rashin faɗa miki ɗin da ban yi ba, kin ji Hajarata, kin san bana son ɓacin ranki"

Tsaki tayi ta ce "Ai dai ko yane  kana faɗa mini, tunda dai ka san ba faɗi zan yi ba"

"To kiyi haƙuri nayi kuskure hakan ba zai sake faruwa ba" . Da ƙyar ya samu ya shawo kanta, ta haƙura, duk wannan cin mutuncin a gaban Zaliha tayi wa Sanusi shi. 

Afnan yanda taga rana haka taga dare, dan kwana ƙaura cewa idonta yayi, banda tunanin Haidar ba abin da take yi. Da ƙyar ta iya fitowa daga ɗaki idanuwanta sunyi ja sun kumbura saboda kuka, zama tayi a tsakar gidan, tana son shiga banɗaki amma ta kasa tashi, saboda jirin da take ji, ga ciwon kai da ya addabeta, Mama ta dube ta, cikin tausayawa ta ce "Baki da lafiya ne Afnan?"

A hankali ta ce "Mama kaina ke ciwo kamar zai rabe mini gida biyu"

"Subhanallah wannan ciwon kan ya uzzura miki kwanakin nan, ki daure ki tashi ki karya sai ki sha magani, sannan kiyi haƙuri, ki cire duk wata damuwa a ranki, in sha Allah zaki ci ribar haƙurinki". 

"To" ta ce sannan ta miƙe da ƙyar ta nufi banɗaki.

*******

Momy da Sharifa. Hamdala suka yi, suna ƙara godiya ga Allah da ya kawo musu mafita cikin sauƙi ba tare da an fahimci suma ba son auren suke ba, ko kuma sun yi abin da zai jawo musu matsala da Dady ba. Especially ma Sharifa da tafi kowa ƙin auren. Yanzu ma zaune take a falo, tana chat da ƙawayenta na makaranta sai dariya take, saboda ba ta da wata damuwa. Momy ta zo falon ta zauna, duban Sharifa tayi ta ce "Sharifa bani hankalinki a nan magana zamu yi"

A jiye wayar tayi ta na faɗin "To Momyna"

Momy ta ce "Sharifa  tunda mun samu Allah ya warware mana maganar auren nan naki cikin sauƙi, ya kamata ace ki fito da miji, kafin wata ɓarakar ta kuma tasowa, a yanayin da naga Saratu ta shiga lokacin janye maganar auren nan, na san ba zata haƙura ba. Duk hanyar da ta san zata bi domin ganin faruwar auren nan za ta bi".

"Momy ni fa bana kula samari, shi ya sa ko ki ka ga ba wanda yake zuwa gurina"

Momy ta ce "Ya zama dole ki fara saurararsu Sharifa, tunda ki ka ga an fara da zancen aurar dake, to ko ba Mudan ba, Dadynki zai iya haɗa ki da wani da ban, saboda haka in dai har ba kya son hakan ta faru, ki yi ƙoƙarin fito da miji".

"To Momy zan duba in sha Allah"

******

Bayan Afnan ta karya, ɗakin Mama ta je ta kwanta, kwanciyarta ke da wuya ta ji kira ya shigo wayar Mama, da ƙyar ta miƙe zaune ta ɗakko wayar, ta na ƙoƙarin kiran  Mama domin ta amsa kiran, sai dai ganin mai kiran yasa ta zaro ido, ta na bin wayar da kallo.


_Zanfa daina yin posting ɗin nan, in dai ba kwayin comment yanda yakamata_


Amanar cool ce ✍️ 
***