RAMIN ƘARYA...

Chapter 39-40

by @amanarcool323

💫 *RAMIN ƘARYA....* 💫




*YOUNG TALENTED WRITER'S ASSOCIATION (YOTA/021)*



_WRITING BY AMANAR COOL_✍️




Free book 📚 



Page 39&40



____________"Why Afnan i m deeply in love with you. Ya ki ke so na yi da rayuwata? Afnan you are the one my heart chose. Ta ya za ki yi mini haka? Me yasa tun farko ba ki faɗa mini ki na da saurayi ba? Sai da ki ka bari na faɗa soyayyar ki, Afnan what do you mean da ɓoye minin da ki ka yi?".

"Dan Allah ka yi haƙuri, ni ma ba da sanina hakan ta faru ba, ka yi haƙuri, ka yi haƙuri my Haidar".


"Afnan Afnan"

Cikin razani ta farka da ga baccin daya ɗauke ta sakamakon kiran da Mama ke yi mata, cike da mamaki Mama ke bin Afnan da kallo, jin ta na ambatar sunan namiji a cikin baccin ta, abin da ko a fili ba ta taɓa yi ba.


Afnan kuwa sunkuyar da kai tayi ta na tuna mafarkin da tayi da Haidar. 


Mama ta ce "Afnan lafiya ki ke kuwa? Waye Haidar? Me ye alaƙarki da shi da har ki ke ambatar shi a cikin baccin ki? Ko a zahiri bantaɓa jin sunan sa a bakin ki ba, waye shi?"


Cikin kasala da sanyin jiki Afnan ta ce "Mama ni ma ban san shi ba, kawai sharrin mafarki ne"


Shiru Mama tayi ta na ƙare mata kallo sannan ta ce "Allah ya kyauta, zazzaɓin ya sauka ne?"


"Eh ya sauka da sauƙi"


"To Allah ya ƙara afuwa, ta so ga Bilki nan na jiran ki". 

Ta amsa da "To" Mama ta fita a ɗakin, ita ma a hankali ta miƙe ta fita daga ɗakin, a zaune ta tarar da Inna Bilki ta na riƙe da kofi a hannun ta, ta na juya wani abu da bata san ko meye ba, zama tayi ta gaishe ta. 


Cikin sakin fuska Inna Bilki ta amsa gaisuwar, tare da yi mata ya jikin.


"Da sauƙi" Afnan ta ba ta amsa, tare da tambayar Mama su Maryam basu dawo daga makaranta ba. Mama ta ce "Suna hanya ba su fara dawowa ba".


Inna Bilki ta dubi Afnan ta miƙa mata kofin hannun ta ta ce "Karɓi ki shanye wannan abin". Duban kofin tayi, ta kalli Inna Bilki sarai ta gane meye amma sai ta ce "Inna wannan fa?"

"Maganine" ta ba ta amsa.


"To ai na ji dama, zazzaɓin ma ya sauka"


Ɗaure fuska Bilki tayi ta ce "Karɓi kisha ba na son gardama" ganin babu alamar wasa a fuskar ta, ya sa ta karɓi kofin tsikar jikinta na tashi ta kafa kofin ta shaye.

Ta na gama sha ta ji zuciyar ta na tashi, ya mutsa fuska ta fara yi. Inna Bilki ta ce "Kar ki yarda ki amayar da maganin nan, ko anjima sai kin kuma sha, sauran kuma sai dai ki tafi da su can, ki ci gaba da amfani dasu". 


Kafin Afnan tayi magana Hajara ta shigo da sallama amsa mata suka yi, su na binta da kallo, Hajara ta ce "To gamu mun shigo ko ba a gayyace mu ba, mu ma a yi shirye shiryen tariyar da mu" ta maida duban ta ga Mama ta kuma cewa "Amina to barkanmu su Afnan dai an yi arzikin shiga daga ciki, duk da auren na haɗi ne, Allah ya nuna wa ƴan baya".

Bilki tayi caraf ta ce "Yawwa barka dai, ai ba ita za ki yi wa barka ba ni, domin ni ce uwar Afnan, yarinya kam tayi arziki babba, kin san ko a kai tallan ka kuma asamu wanda zai siya arziki ne, wasu ba na jin ko tallan su a ka kai za su samu masaya, dan abin rabo ne, kowa na son siyen abu mai inganci da kyaun kallo".


Hajara sakin baki tayi kamar garkar wawa, ta na bin Bilki da kallo. Da ga bisani ta ce "Bilki ina fatan dai ba magana ce ki ka faɗa mini ba?".


"Akan me zan faɗa miki magana Hahara? Amsa ce na baki dai-dai da maganar da ki ka yi".


Wani takaici ne ya ƙular da Hajara, domin sarai ta gane magana Bilki ta yaɓa mata, amma sai ta danne ta ce "Amina ba wani abin da za a yi ne? Kin san fa su mutanen ƙauye abin magana baya musu wuya. Duk da dai abin ya zo a bazata, gara a shirya ɗan wani abin da za a kai ta da shi, saboda gudun barwa yaro abin faɗa".



Mama ta ce "Hajara ba abin da zan yi, waƴanda suka haɗa auren su je suyi, idan kuma ba za suyi ba, sai a kai ta hakan, in ya so gidan mijin idan ba za su iya karɓarta a haka ba, sai a dawo mini da ita".


"Subhanallah Amina in jin dai ba baki ki ke yi wa auren ba? Ahh bai kamata ki na irin waɗannan maganganun ba gaskiya".


"Wai ke Hajara me ye naki a ciki ne, dama abin da ya kawo kenan? to ina ruwan ki, tayi wa auren baki sai ki je ki faɗa, dama aikin ki ne kin saba".

Ita ma Hajara cikin masifa ta hayayyaƙowa Bilki "Wai Bilki ina ruwan ki da ni ne? Na sakaki a magana ta ne?".


"Eh kin sakata, ai ita ba munafuka ba ce, sannan ba ta son ganin ɗan uwanta a damuwa, ita ɗin ta ɗauki damuwar ɗan uwanta ta ta ce". Gaba ɗaya suka juya duban su zuwa ga Maryam da shigowar ta kenan, ta ji Hajara na wannan maganar.


Hajara ta ce "Maryam ni ki ke gayawa magana haka? Saboda baki da kunya?"


"Eh na faɗa ɗin uwata ce ke, ko dan kunga kwana biyu na ɗaga muku ƙafa shi ne za a zo har inda muke a yi muna rashin kunya".

Mama ta ce "Ke Maryam ba na son na sake jin bakin ki a wurin nan". 

"To Mama sai ta zo har...." "Ba na ce ki rufe mini bakin ki ba, maza zo ki wuce daga wurin nan".


Hajara ta ce "Korar me za ki yi mata? Ai duk abin da tayi dai-dai ne, tun farko idan ba a basu damar yin hakan ba ai ba za suyi ba".

Mama ta ce "Hajara ba na son tashin hankali, dan Allah idan har fitina ce ta shigo da ke wurin nan ki yi tafiyar ki". " Ai ko baki kore ni ba tafiya zan yi, dan ba zama zan yi ba, wato tunda ita wadda ta haɗa auren tafi ƙarfin ku shi ne kuka juye haushin ku a guna? To aure dai ne sai dai ku mutu, kuma ƙauye ne zuwa babu fashi".


"Ai wasu suna biɗar ko na ƙauyen ya zo ya ce ya na son su basu samu ba, to Alhamdulillah ita ɗin da har ta samu na ƙauyen, idan fitsari banza ne kaza tayi mu gani" Bilki ta bata amsa.

Haka dai suka yi baran baran kafin Hajara ta bar wurin.


Maryam zama tayi ta na ƙunƙuni, don ta ji haushin hana ta maganar da Mama tayi.

Afnan da tunda aka fara magana ko tari ba ta yi ba, sai yanzu ta ce "Mama wai tariyar me na ji ana magana ne?". 


Mama ta ce "Hmmm Gwaggo ce ta ce lallai yau sai kin tare a ɗakin ki..." Kafin Mama ta ƙarasa magana Maryam ta yi wata zabura ta ce "Bala'i amma wannan tsohuwar ba Allah a ranta. Allah ya kasheta kowa ma ya huta".


Mama ta ce "Ke Maryam ki na da hankali? Gwaggon ki ke yi wa fatan mutuwa? Kar ki manta ita ta haifi mahaifin ku, kar na sake jin wannan maganar a bakin ki, idan ba haka zan yi mugun zaɓa miki".

Kuka Afnan ta fashe da shi ta ce "Mama wallahi ba inda za ni, ko lafiya ba ni da, abari sai na warke tukuna".


"Ai Afnan sai dai ki yi haƙuri, tunda har ta furta hakan, to wallahi babu wanda isa ya hanata". Cewar ina Bilki. Maryam kam ta cika tayi fam da ta na da iko, da ta laƙaɗawa Gwaggo shegen duka ko sanyi ta jiya. 

Rarrashin Afnan Bilki ta shiga yi, tare da bata haƙuri, ta ce "Ki yi haƙuri Afnan bawa baya wuce ƙaddarar sa, duk abin da ya same shi da sanin Ubangiji, kin ga su Bahijja sun dawo daga makaranta, yanzu sai ta zo tayi miki ƙunshi".


Cikin kuka ta ce "A'a Inna ba na so, ni a barni a haka".


Sallama Baba ya yi ya shigo, amsa masa suka yi, suna gaishe shi, bai ida shigowa ba sai ga Gwaggo ta shigo babu sallama, sakamakon zuwan da Hajara tayi, ta faɗa mata ƙarya da gaskiya.


"Eh lallai Amina kin gawurta, wuyan ki ya yi kauri ya isa yanka, saƙon ki ya same ni, to ina son ki sani, wallahi na rantse da girman Allah duk ki ka kashe auren nan, ke ma sai naki auren ya mutu, ke ma wannan A'isha ɗin duk ki ka ƙi zama a gidan auren ki, to sai dai ki zauna a gidan nan ba tare da uwarki ba. Ke kuma ɗayar marar kunya na san maganin ki, sai kin gane baki da wayo, ina ji dai Umar ɗana ne ko? To bari ya dawo ki ga mai zai faru". Tayi maganar ta na nuna Bilki.


Da sauri Baba ya dubi ta ya ce " Subhanallah Gwaggo lafiya? Mai ya yi zafi haka". 

"Tukuna saurara mini ban fara zuwa ta kan ka ba".


"Ke kuma jarababbiyar yarinya, da tayi gadon masifa can dangin uwarki, duk ki ka ƙara yi wa Hajara rashin kunya to ba ita ki ka yi wa ba, uwarki da ubanki gasu nan su ki ka yi wa".


"Kai kuma na dawo gareka, ina son maza maza ka je kasuwa ka siyo mata katifar kwanciya, da filo, da zanin gado, ka haɗo mata da labulayen ɗaki guda biyu, ni kuma nan ina da tukunya, da buta, da bokitin wanka. Hadda kwanukan cin abinci, Ina so yau ɗin nan a sada ta da gidan mijinta, kuma yanzu nan, nake buƙatar ka je kasuwa, ka kira ɗan uwanka a waya ku haɗu ku je tare a siyo komai da ya kamata, sai ku biɗo mota a can. Tunda na ga uwarta ba ta da niyyar yin wani abin arziki". 


Shiru Baba ya yi dan har cikin zuciyar shi ya ji babu daɗin wannan abin da Gwaggo tayi. 


"Ya na ji kayi shiru ne? Ko kaima gardamar za ka yi mini ne? To wallahi umarni ne na baka ba shawara ba, maza ka wuce yanzun nan, kar ku ɓata mini lokaci".


Jiki a sanyaye Baba ya amsa da "To Gwaggo"


Ta kuma duban su ta ce "Ke kuma sai ki tashi ki shirya, don ba na son a zo ana jira, kuma kin ji abin da na faɗa miki". Ta na gama faɗar haka ta bar wurin.

Baba ya miƙawa Mama maganin da ya zo wa Afnan da shi, sannan ya ce "Sai ta tashi ta shirya" da ga haka bai ko tsaya ba, ya juya ya fita.


Kuka Afnan take yi ba na wasa ba, Maryam ma kuka take, Mama kuwa ɗaki ta shiga ta kasa fitowa sai tausayin ƴarta take ji, banda sharar ƙwalla ba abin da take. Da ƙyar Bilki ta lallaɓa Afnan ta tashi ta shiga wanka sai kuka take yi.


Gaba ɗaya unguwa ta ɗauki anyi wa Afnan auen sadaka a ƙauye, sakamakon kawu Sanusi da yake ta yaɗa maganar a waje. 


Sai yau Feena take samun labari, babu shiri ta zo gidan su Maryam, sai dai jikin ta ya yi san yi ganin Maryam ɗin na kuka, ita ma kukan ta fara.

Gwaggo kuwa da kanta ta bi maƙota ta na sanar dasu batun auren Affan, sannan ta ce duk wanda ke samun zuwa ya shirya a je kai amarya da shi yanzu nan, sai dai a gidan Yayan ta ne za a kai ta, kafin mijinta ya ida gyara wurin da za a sakata. Mutane da son gulma nan fa suka ce za su je, sai dai wasu daga ciki mazan su ba su bar su ba, duba da tafiyar ta bazata ce.


Cikin abin da bai fi awa ɗaya ba, su Baba suka kammala duk wani abu da Gwaggo ta ce, sannan suka biɗo babbar motar nan mai ɗaukar mutum goma sha takwas.


A lokacin Afnan tayi wanka ta sanya doguwar rigar atamfa, da hijabinta, banda kuka ba abin da take, Mama ma kukan take yi, ta na mamakin wannan aure haka ace babu komai da ango kewa amarya, babu kayan lefe, sadaki gashi basu ganshi da idonsu ba.


A ƙofar gidan motar ta tsaya a nan ciki suka bar kayan, suka shiga ciki, kai tsaye inda Gwaggo suka nufa, cikin murna ta fito da sauran kayan, ta miƙawa Hajara, ta ce ta kai mota. Ita kuma ta nufi wurin su Mama. 

Ta na zuwa ta ce "A fito da ita ga motar nan ta iso". Babbar Yayar Mama ta ce "Haba ai kya bari ta gama ganawa da uwarta"

"Wace irin ganawa kuma, bayan duk tsawon lokacin da suka yi tare, dan Allah ban son ɓata lokaci, ku fito da ita".


Afnan jin hakan ta ƙara ririƙe Mama ta na kuka "Ta ce Mama dan Allah ka da ki bari a tafi da ni, Mamata ki yi mini addu'a".


Itama Mama cikin kuka ta ce "Afnan ki je Allah ya na tare dake, Allah ya baki haƙuri da juriya a gidan auren ki, Ubangiji ya wanzar da kwanciyar hankali a cikin rayuwar auren ki".

Gwaggo ganin Afnan ta ƙi fitowa ya sa ta shiga ɗakin da ƙarfi ta jawo Affan ta na kuka ta yi waje da ita, Inna Bilki da su Maryam da ƙawarta sai Bahijja da Aunty Murja yar Mama gaba ɗaya suka mara mata baya. Haidar na gefe cikin napep ɗin sa zuwansa kenan ya ga an fito da Afnan ta na gunjin kuka, an sakata a mota, su Maryam ma duk sun shiga motar da sauran mutanen da ke wurin. 

Kawu Sanusi ne a gaban motar, Baba na tsaye ya na musu fatan sauka lafiya. Duk da ƙasan zuciyarsa wani irin zafi yake ji, bayan mutane sun gama shiga motar ta tashi Gwaggo na ɗaga musu hannu har sai da mutar ta bacewa ganin ta, sannan ta kuma ciki.
 
A hankali Haidar ya sauke a jiyar zuciya ya ta da napep ɗin sa ya bar wajan.



Amanar cool ce ✍️ 
***