ƘITSO DA KWARKWATA

KITSO DA KWARKWATA 005

by @maimunabala209

   ðŸ©µ *ƘITSO DA KWARKWATA* 🩵005

 
Maimuna Bala -Shuukran


Young talented writers Association 



P5


Bayan wasu mintina Salam ta kai hannunta jikin kofar ta sake nucking nan take aka basu umurni shigowa daga ciki

Bayan shigarsu ciki wani babban mutum É—an kimanin shekaru sittin a duniya suka gani zaune kan wata kujerar alfarma, tarin takardu ne gabansa idanunsa sanye da fararen galashi,bai É—ago ya kallesu ya ce ''yes what is it?'' shi a tunaninsa ma'aikatan kamfanin ne 

Hafsah ce ta yi karfin hali ta ce 
''Good morning sir we are here for the interview'' sai a sannan ya É—ago ya kallesu cike da mamaki saboda sun makara tun É—azu aka gama interview amma sai yanzu suke zuwa so yake ya kore su ya ce masu an gama interview É—in,amma ya Æ™asa saboda yanayin da suke ciki kallo daya ya masu ya fahimci talauci ta gama rufesu nan take tausayinsu ta ziyarci zuciyarsa,kawai ya tsinci kansa da faÉ—in ''ok have a sit'' ya faÉ—i hakan tare da nuna masu wata kujera two sitter dake cikin babban Ofishin nasa bayan sun zauna ne ya rufe file dake gabansa ya kallesu ya ce 

''A gaskiya kun makara.. tun É—azu aka gama interview taimaka maku kawai na yi'' godiya suka yi masa ya ce babu komai kallon Hafsah ya yi ya ce ''dukkanku za'a yiwa interview É—in?" Hafsah ta ce ''eh''

''Ok a wani matakin karatu ku ka tsaya?" Duk suka haÉ—a baki suka ce ''N C E'' tausayi suka Æ™ara bashi amma bai nuna masu ba sai kawai ya ce ''masha Allah can l have your C V?" duk suka cire suka bashi ya shiga dubawa bayan ya gama dubawa ne ya ajiye C V É—in gefi ya kalle su ya ce 

''kamar yadda kuka sani aikin aikatau zaku yi a  gidajen mutane abinda ya haÉ—a wanke-wanke,shara,girki,zuwa kasuwa cefane har wankin kaya duk aikin da suka sako daga cikin wadannan dana lissafo maku dole ne koyi ba tare da musu ko jayayya ba,saÉ“anin haka kuwa Æ™arar ko za su kawo mana nan kamfani mu za mu yi maku hukunci basu da hurumin dukanku ko zaginku,da sunan mu ku ke aiki saboda haka duk wata hukunci mu za mu yi maku, sannan dole ne ku riÆ™a kwana a gidan da kuke aiki, ranaku biyu kadai kuke da damar zuwa ganin iyayen ku da Æ´an uwanku,amma in wa'inda kuke wa aiki sun baku damar zuwa gida kullum babu matsala,sa'an'nan  albashinku ta asusun kamfani za su tura naira dubu É—ari ce duk wata,amma kamfani zata cire naira dubu talatin cikin É—arin'' shiru ya yi yana kallonsu yana jiran amsar su jin sun yi shiru basu ce komai ba ya sa ya ce in har kun amince ga form ku cike ku rubuta mana cikakken sunan ku da kuma adrishin gidan iyayenku in kuma da mai aure a cikin ku sai ta rubuta adrishin gidan mijinta da kuma lambar waya akwai wajen sa hannu ku duba ku sa hannu'' lokaci guda suka tashi zuwa tebirin mutumin sun Æ™arÉ“i Form cikin nitsuwa suka cike Form É—in sun mayar masa da shi,bayan sun mayar masa da Form É—in ne sun koma inda suka tashi sun zauna,yayinda mutumin ya shiga duba Form É—in bayan ya gama duba Form É—in yaga basu yi kuskure ba sam wajen cike Form É—in,wani file ya buÉ—e inda ya zuba sauran Form É—in wa'inda  aka yiwa interview yau ya sa form É—in Hafsah da Salma ciki ya mayar da dubansa gare su ya ce ''shikenan za ku iya tafiya za mu kira ku da an samu client'' godiya suka yi masa kafin suka bar offishin nasa 









18 November 1980


Karfe 1:45am na dare babban jije ne mai tsananin duhu, manya-manyan dogayen bishiyoyi dake cikin jije ne suka Æ™arawa jijen duhu baka jin motsin komai sai kukan kwari tare da Æ™arar saukar ruwa dake fita daga wani babban dutse dake zuwa babban rafin dake É—an karamin Æ™auyen mai suna Lafia,wata doguwar mace ce tsaye can saman dutsen dake fitar da ruwa,sanye take cikin wata doguwar rigar saÆ™a,mayafen da ta rufe kanta ta yi amfani da shi wajen rufe fuskarta,wata babbar mayafe ta rufe jikinta gaba daya saboda yanayin sanyi da ake ciki,hakan yasa tun daga kanta har fuskarta a rufe yake baka iya ganin komai sai Æ™wayar idonta,hannunta riÆ™e da tocila irin ta waccan zamanin mai jikin karfe wadda ake sa wa manyan batir,ta kafe ruwan da ke gudu cikin kogi da ido tana mai haska ruwan da tocilar hannunta,ta dauki a Æ™alla mintina biyu a haka kafin daga bisani ta juyo a hankali cike da lura take daura kafafuwanta kan madaidaitan duwatsu dake wajen kafin daga bisani da sauko daga babban dutsen 





Zabga-zabga samari har biyar ne tsaye a wajen kowanensu ya rufe fuskarsa da jikinsa ta hanyar amfani da mayafin saƙa,inda suka kewaye wasu akwatunan karfe guda biyu irin ta masu wasa da macizai kowanen daga cikin su riƙe yake da tocilarsa bayan saukowar Neelam zama ta yi bisa daya daga cikin akwatunan yadda ta daura kafa daya kan daya kanta ta ɗaga sama tana kallon yadda taurari suka yiwa samaniya ado,lumshe idanuwanta ta yi tana me jin daɗin yanayin, tunawa da ta dauki kusan mintina arba'in cikin wannan ɓakar jijen yasa nan take fara'a fuskarta daukewa a hankali ta sauke kanta ƙasa ta mayar da dubanta ga daya daga cikin samarin ta ce ''we will vanished in the next 10 minutes in har bai zo ba'' wanda ta yi wa magana ya ce ''yadda ki ka ce hakan za'a yi leader Neelam''


Sawun mutane ta fara ji yadda suke taka busassun ganye hakan yasa ta fahimci sun Æ™araso,tabar wiwi dake maÆ™ale jikin rigarta ta ciro daya daga cikin samarin ya taho da sauri tare da Æ™itsta mata ashana,nan take warin tabar wiwi ya gwaraye wajen 




Cike da Æ™asaita ya karaso wajen sanye yake cikin doguwar riga jallabiya kansa dauke da hular taÉ“a ka ji hadisi yadda ya naÉ—e hirami hannunsa riÆ™e da taba sai ka Æ™ure masa ido za ka iya ganin fuskarsa saboda yadda yake fitar da hayaÆ™i daga bakinsa da hancinsa kamar salansar mota wasu samari biyu na biye da shi daya hannunsa riÆ™e da bindiga ta toka irin wanda ake amfani da ita a wancan zamanin daya kuma hannusa riÆ™e da wata jakar fata mai madaidaiciyar girma,wata iriyar murmushi Vigas ya sakar mata har sannan fuskarta haÉ—e harda ba ya iya ganin fuskarta amma ya fahimci ranta ya É“aci hakan yasa ya tako har inda take zaune ya sunkuyo daidai fuskarta ya ce 

''A yi min afuwa Neelam L'' haka ya ke kiranta banza ta yi masa ba ta ci komai ba har sannan fuskarsa dap da tata hakan yasa ta matsa kadan kafin daga bisani ta tashi tsaye tana nuna mai akwatin da ta tashi a kai ta ce 


''ga kaya nan na kowa maka kamar yadda ka buÆ™ata buÉ—e wannan ka fara duba'' murmushin da bai kai ciki ba Vigas ya yi a hankali ya miÆ™e tsaye yana Æ™arewa Neelam kallo ya ce 

''cheek the goes'' daya daga cikin samarin da ya zo da su ya je inda akwatin ya ke daya daga cikin samarin da ke tare da Neelam ne ya buÉ—e masu akwatin bindigoge ne kala daban daban shaÆ™e cikin akwatin bayan sun gama duba wannan sun sake buÉ—e daya akwatin shima dai bindigoge ne cike ciki,bayan sun gama dubawa ne daya daga cikinsu ya ce 

''Komai ya yi oga'' alama Vigas ya yiwa yaran gidansa da su biya Æ™udin daya daga cikin yaran gidansa sa dake riÆ™e da jakar fata ne ya miÆ™owa yaran gidan Neelam jakar,daya daga cikinsu ya Æ™arÉ“a wanda daman shi ke Æ™arÉ“ar kuÉ—in duk sanda leader su ta siyar da kaya,in kuma siya zata yi to shi ke biyan Æ™udin,buÉ—ar jakar ya yi yaga silallu ne cike cikin jakar sai rafar naira biyar guda biyu da kuma rafar naira goma kwara daya,hannu ya sa ya É—iÉ“e silallu yana duba ingancin su bayan ya tabbatar da ingancin kuÉ—aÉ—en ya ce 

''Sun cika leader'' Neelam dake tsaye Vigas ya tsareta da ido tun É—azu ta kalle Vigas ta ce 

''in ka cigaba da haka zan yanke duk wata harƙalla dake tsakaninmu,na sha faɗa maka cewar ni matar aure ce ka fita harka ta amma baka ji''...ɗan jim ta yi sai ta ce ''you know what...today will be the last day da zan haɗu da ke becous l will report you to chief'' tana gama faɗin haka ta bi gefinsa ta wuce runtse idanunsa ya yi yayinda ta zo wuce shi har cikin zuciyarsa yake son Neelam har mamakin kansa yake da irin son da yake mata,bai taɓa ganin fuskarta ba bama shi kaɗai ba duk wanda take harkar bindigoge da su babu wanda ya taɓa ganin fuskarta sai chief ƙadai wanda shine oganta



Ƙarɓar jakar ƙudin ta yi ta manna shi da ƙirginta kallon yaran gidanta ta yi ta ɗan ɗaga murya ta ce ''VANISHED'' tana gama faɗin haka sun ji motsin motan ƴan sanda, hakan yasa cikin sauri ta ciro layarta dake maƙale cikin rigarta ta matse layar,nan take ta ɓace ɓatt yaran gidanta kuwa kowa ya kama gabansa haka ma Vigas da yaransa cikin sauri suka dauko akwatunan bindigoge suka tsire




Cikin sauri expecter Sanusi tare da sauran polisawa suka shigo jijin ganin babu kowa cikin jijin yasa expecter Sanusi rarraba sauran polisawa ko Allah zai sa su yi nasara kamo Æ´an ta'addan amma haka suka yi ta dube-dubensu suka Æ™are basu kamo ko É—aya daga cikin Æ´an ta'addan ba cike da É“acin rai Expecter Sanusi ya bar jijin tare da sauran polisawa 






Karfe 9:15am daidai Expecter Sanusi ne tsaye cikin rumfar dabbobi inda yake share masu ɗaki,kallo daya za ki masa ka gane yana cikin damuwa,tunanin yadda zai kamo Neelam shahararriyar me dilar bindigoge yake,Neelam ta gagari gwamnati tsawon watanni takwas kenan ana ta fafutukar yadda za'a kamota amma abin ya ci tura gwamnati ta sa ƙuɗaɗe masu yawan gaske ga duk wanda ya kamo Neelam a raye ko a mace,shi ba ƙudin bane damuwarsa,Expecter Sanusi ya kasance ɗan sanda ne me tsananin ƙishin ƙasarsa hakan yasa yake son kawo karshen Neelam



 Mahaifinsa Mallam Ubaidullahi babban Malami ne wanda ake ji da shi a Æ™auyen kullum cikin niman laÆ™ani yake wajen babansa dan ganin y kawo karshen Neelam,Mallam Ubaidullahi dake zaune kan tafurmar kara yana sauraron labaran karfe tara cikin labaran ne aka faÉ—a yadda daren jiya yan sanda sun yi kokarin kamo Neelam amma ba su yi nasara ba,wata iriyar murmushin manya Mallam Ubaidullahi ya yi kafin ya mayar da dubansa ga É—ansa sai a sannan ya fahimci dalilin É“acin ran Expecter Sanusi,kallonsa Mallam Ubaidullahi ya yi na wasu Æ´an mintina kafin ya yi magana cikin É—an É—aga murya ya ce 

''Sanusi da ka gama ka zo za mu yi magana''

''To baba''cewar Expecter 

Wata Æ´ar budurwa ce mai kimanin shekaru sha tara ta fito daga cikin É—aki ginin Æ™asa ta nufi Mallam Ubaidullahi fuskarta dauki da murmushi shima murmushi ya yi mata,a hankali ta tako har zuwa inda Mallam Ubaidullahi ya yi shimfida ta yi zaman ta kan tafurmar kara tare da yiwa mahaifinta sallama amsar sallamar ya yi fuskarsa dauke da murmushi,sanye take cikin wasu riga da zani na saÆ™i kalar Æ™asa kanta daure da wata Æ™atuwar É—ankwali yadda ta naÉ—e shi a kanta kamar rawani,cike da nitsuwa da kuma sanyin yanayi ta buÉ—e dan karamin bakinta,laÉ“e bakinta ja jawaur kamar ta shafa jambaki ta ce 
 

''Barka da safiya Baba'' ta faÉ—a tare da sunkuyar da kanta Æ™asa alamar girmama 

Amsa gaisuwar mahaifinta ya yi ya ce 

''kina lafiya Æ´ar ba?" ta amsa da ''lafiya klau baba''

Mahaifiyarta mai suna Zainab da yaranta ke kiranta da lnno zaune take cikin wata rumfar zana duk hayaÆ™i ya tunnuÆ™eta ta jin muryar Zuwaira yasa ta joyu tana mayar da dubanta inda Mallam ke zaune,kamar zata yi magana sai kuma ta shiga gyara kirare da ke cikin wuta da alama girki zata daura cikin Æ´an mintina wutan ya tashi hakan yasa ta dauki tunkunyar Æ™asa da ke cike da ruwa ta daura bisa kan murhu,tashi ta yi daga kan dutsen da take zaune a kai ta nufi inda Mallam ke zaune yana sauraran rediyo tun kafin ta karaso wajen ta fara yiwa Zuwaira magana ta ce 


''yanzu ke saboda Allah gari ya waye ba ki san ki share tsakar gida ba,kullum sai na gaya maki ki share gida duɓi ko ina kashen kaji ga ganyayyakin bishiyar lemon duk sun ɓata gida,ba ki da aiki kullum sai dai ki manne da mahaifinki kina zuba masa shagwaɓa'' ta karasa magana tare da zama kusa da Mallam turo baki gaba Zuwaira ta yi,kafin ta tashi cikin yanayin nan nata na sanyin jiki


Har sannan idon lnno a kanta kwafa ta yi ta ce ''yanzu dai ki dauki tulu maza ki je rafi ki É—ibu mana ruwa dan bamu da ruwa a gidan'' murmushi Mallam ya yi ya ce ''duk waÉ—anan ayyukan uwata za ta yi aiy sun mata yawa''

Cikin kwantar da muryar lnno ta ce 

''A'a Mallam Æ´a mace ce fa wata rana gidan wani zata je''...shiru lnno ta yi na wasu yan sakkani kafin cike da É—a'a ta ce 

''dan ma ka kafi kan maganar wannan boÆ™o ne amma ayi da tuni tana É—akin miji a ce yarinya shekara sha tara bata yi aure ba'' tana gama faÉ—in haka ta ja bakinta ta yi shiru,a hankali lnno ta É—ago ta dalla wa Zuwaira harara da har sannan tana tsaye bayan bishiyar lemo sai wani tuttura baki ta ke,hararar da lnno ta banko mata ne yasa babu shiri ta wuce can kofar É—akin lnno inda aka jero tulu ta dauki daya ta kama hanyar fita daga gidan,ta zo giftawa kusa da Expecter Sanusi yayanta murya can Æ™asa ta ce 

''Barka da safiya yaya'' ko kallo bata ishe ba ya cigaba da aikin da yake 



Mallam ya dauki a ƙalla mintina uku yana nazarin maganganu lnno kafin ya ce

''Maganar ki gaskiya ne kamata ya yi a ce uwata (haka yake kiran Zuwaira sunan Mahaifiyarsa ce da ita)ta na É—akin miji,amma akwai abinda nake son ki fahimta wannan boko bata da wata illa kawai dai wasu daga cikinmu ne basu fahimci ta ba''

Numfasawa lnno ta yi ta ce 

"To Mallam haka ne amma ina jin tsoron wanan boko kaga dai Sanusi har yau ba'a sama masa mata ba dalilin boko da ya yi gaba daya mutanen wannan Æ™arkarar ganinsa suke kamar ba musulmi ba kasancewarsa É—an sanda kaima da Mallam kullum cikin aibata ake a kauyen nan kawai dan Æ´aÆ´anka sun je makarantar boko''...lnno ta É—an jinkirta zancenta kafin ta ce ''duk faÉ—in Æ™auyen babu Mallamin da ya kai ka sani amma an waye gari sama da rabin mutanen kauye sun daina binka sallah'' zuwa yanzu muryar lnno ya fara rawa ta ce 

''Saboda boko mai gari ya gina sabuwar masallacin juma'a duka-duka mutanen da ke binka sallah basu fi hamsin ba''


Wata ƙawatatciyar murmushi Mallam Ubaidullahi ya sake da ya ƙara fitar masa da kyauwunsa na bafulanin asali ya ce ''ki daina ɗaga hankali duk za su fahimci amfanin ilimin boko nan gaba kaɗan ki kwantar da hankalin ki''

Daga nan lnno bata kuma cewa komai ba sai kawai ta ce ''to Allah ya nuna mana wannan ranar, Allah kuma ya kawo wa Æ´aÆ´anmu mafita ya haÉ—a su da abokan zama na gari''


Sosai Mallam ya ji É—aÉ—in addu'ar da lnno ta yi zuciyarsa fess ya ce 
''Ameen Allah ya yi maki albarka''
Ita ma ta amsa da ''Ameen''

lnno na shirin barin wajen ne Mallam Ubaidullahi ya dakatar da ita ya ce 

''magana akan Sanusi na sama masa mata za'a daura aure wannan satin''

Nan take damuwar da ke cike cikin zuciyar lnno ya gudu fuskarta dauke da tsananin farin ciki ta ce

''Alhamdulillah Allah na gode maka kai Masha Allah abu ya yi kyau..wace matar? Æ´ar gidan waye?" Mallam ya bata amsa da ''Æ´ar gidan aminina Mallam Saminu na sabuwar anguwa''

Har sannan fuskar lnno dauke da tsantsar murna ta ce

''lklima take da suna ko,nasan ita kadai ya haifa''

Mallam ya ce ''eh ita''

''To Allah mun gode maka kai Alhamdulillah..kaga Mallam zama bata sami ni ba bara nayi maza na shiga rumbu na duba kayan hatsi nan naga me da me zamu buÆ™ata na bikin'' tana gama faÉ—in haka ta tashi ta nufi hanyar bayan gida can inda rumbun kayan abinci yake 


Shi dai Mallam ya bi bayanta da ido fuskarsa dauke da murmushi cikin zuciyarsa kuwa cewa yake mata da maganar bikin basa wasa tun ma aka ce na Æ´aÆ´ansu,mayar da dubansa ya yi ga Sanusi da ke ta faman aikin kwashe kashin shanu cikin rumfar da shanu suke,cikin É—an daga murya ya ce 

''Sanusi'' cike da ladabi Sanusi ya amsa ''na'am baba'' Mallam ya ce 
''da ka gama ina son magana da kai''

''To baba'' cewar Sanusi



Bayan fitar Zuwaira can hanyar rafi ta haÉ—u da Æ´an mata da duk cikin su babu sa'arta duk sa'aninta sunyi aure daga masu Æ´aÆ´a uku sai masu Æ´aÆ´a hudu,yawancin Æ´an matan kauyen iyayensu na aurar da su ne a shekaru sha uku zuwa sha huÉ—u 


Cikin yanayinta na sanyi jiki take tafiya kamar wacce take tausayin ƙasa haka take taka ƙasa ƴar siririya da ita tana tafiya kamar iska ya ƙade ta tsabar rashin ƙiɓa,fara ce sosai duk gidansu cikin iyayenta da ƴanuwanta babu mai haskenta duk ta fiso haske, kyakkyawa ce ta ƙarshe tana da hanci mai tsawo da ɗan kauri irin hancin shuwa arab idanunta kullum kamar me jin barci gasu da girma amma ba girma can-can ba ɗan karamin bakinta mai dauke da jajayen luɓa ne ya ƙarawa fuskarta kyau,lokacin da ta fara girma kusan gaba daya samarin kauyen son nuna suna son aurenta har ɗan sarki amma Mallam Ubaidullahi ya ce karatu za ta yi,sun buga nacin su sun haƙura duk cikin samarin mutum daya ne ya kwantawa Zuwaira a rai tana masa wata iriyar mugun so da ita kanta take tsoron irin son da take masa saboda ji take za ta iya koma mene a kansa ji take za ta iya kashe koma waye a kansa son da take masa ya wuce tunanin mai tunani wannan ba kuwa bane face Bilyaminu( Dady) shima kuma yana sonta sosai amma son da take masa ya fi wanda yake mata





***


Shuukran