Episode 1
by @zahraroyal
*MUGUN ICCE*
*©Zahra Royal Star*
*ROYAL STAR WRITER'S ASSO......*
*Tsokaci*
A rayuwa, ba zaka taɓa gane wanda yake sonka ko ƙinka gaskiya ba — sai wani abu mai girma ya riske ka. A irin wannan lokaci ne zaka gane matsayinka a zuciyar mutane. Wannan labari yana fito da gaskiyar da ke cikin zuciyar ɗan adam: *mutum mugun icce ne.*
Koda makusantanka ne, koda jininka ne, kowa na iya cutar da kai. Zuciya bata da ƙashi, kuma amana tana da rauni mai sauƙin karyewa. Wannan littafi ya cika da cin amana — ba irin ta nesa ba, ta kusa, ta jini, ta aboki, ta masoyi — cin amanar da ke ragargaza zuciya.
**Zaka karanta mamaki mai ban tsoro.
Zaka ji raɗaɗin amana da ba za a iya mantawa da ita ba.
Zaka gane cewa wanda ka ɗauka tamkar garkuwa…
Shi ne ya jefa ka cikin ƙunci.
Haka rayuwa take… *mutum mugun icce ne.*
PAGE 1
*House No 26, Gadon ƙaya, Kano State Nigeria*
A hankali ta shiga buɗe idonta daya tara ruwan hawaye. A hankali hawayen suka shiga silalo mata akan fuskarta.
"Wai bazaki fito ba?, kina jina ina magana, kin mayar dani ƴar iska?"
Daga can waje tsakar gidan nasu taji maganar Aunty Murja.
Jikinta na ɗan rawa ta dafa bakin gadon da take zaune ta miƙe, tana jin wani irin jiri na ɗibarta, saboda kwana da tayi tana zazzaɓi, ga aman dake wahalar da ita.
Tana sauke lumfashi mai zafi ta idasa fitowa daga cikin ɗakin.
Tana fitowa Aunty Murja ta watsa mata wani mugun kallo tana ƙara nunata da yatsa ta ce.
"Ai wallahi Salma ni da ke ne a gidan nan, kuma tabbas sai munje asibiti ko kyamis anyi miki awon ciki, yaya za'ai ace tun daran jiya kike kwara amai kamar zaki amayar da duniya, da an kalle ki an san akwai wani abu a ƙasa tattare da ke".
Wani irin kuka ne ya turnuƙe Salma ta sake shi tana jin wani irin baƙin ciki ya rufe mata zuciya.
"Munafaka ai dole zaki fashe da kukan munafurci mana, saboda asirinki zai tuno. Yo dama ya za'ai Mlm ya bari ƴaƴansa suyi wani karatu, gaku gandama-gandama kun kasa auruwa, ai dole a fake da karatu ana yawon iskanci tunda an rasa na aure har yanzu, ace duk yawan samarin ki kin kasa samin na auri sai dai na holewa ko?. Ai kawai tsabar ya baku lasisin iskanci ne kawai shi Mlm ɗin, amma ba abunda kuke yi sai yawan iskanci ba wata makarantar da kuke zuwa yawwa"
"Wallahi Umma Salma baza ta taɓa yin abunda kike ƙoƙarin cewa ba"
"Rufe min baki, shashasha marar zuciya kawai, ko na zo na ci ub*anki yanzun nan"
Turo baki Yusura tayi tana kamo hannun Salma dake neman zubewa ƙasa tsabar yadda jikinta da babu ƙarfi kwata-kwata.
"Sake ta dalla can asibiti zamuje wallahi yau ba sai gobe ba, dole ne asan abunda taje ta kwaso ma mutane, uban naku ya zo yaji abunda take aikatawa"
"A'afa Umma kar aje aji kuny....
"Kunyar buh*un ubanki Yusura?, wai shin ko kema uwar Salma ta shanye min ke ne?, ko kuma ita ta haifar min ke ban sani ba?"
"To ai Umma abunda kike kwata-kwata bai dace ba wallahi, dan kawai Salma ta zo gidan nan a matsayin karatu ta zauna na ɗan lokaci ne fa kawai, ta gama ta tafi"
"Zaki rufe min baki ko sai na zo na fasa miki shi?"
Shiru tayi ganin yadda Salma tayi saurin girgiza mata kai. Haɗe sauran maganar kawai tayi, ba dan wai Ummar ta ce zata fasa mata bakin tayi shiru ba, sai dan kawai Salmar data nuna mata.
"Ungo nan sanya maza"
Kallon hijab ɗin tayi. Hannunta na ɗan rawa ta amsa ta sanya. Da sauri Yusura ta ƙara kama mata hannu. Aunty Murja kuma tayi gaba tana mitar suyi sauri.
Bin bayanta kawai suke har suka isa wani ƙaramin kyamis dake a cikin unguwar tasu.
"Yawwa zauna. Kai bawan Allah ana awon ciki a nan?"
Wani matashi dake tsaron kyamis ɗin ya kalleta sosai ya amsa da eh ana yi.
Salma najin lokacin da take hamdala sai ka ce an faɗi wani abun jin daɗi, sosai take mamakin matar nan ainun.
"Yanzu fisbilillahi Umma miye abun hamdala a nan ciki?, wai.....
"Dalla gafara can, rufe min baki na ce, kifa kiyaye ni Yusura, ub*an wani ya ce ma ki biyo mu ne wai?"
Zata sake magana Salma ta sake matse mata hannu alamar tayi shiru dan Allah.
Suna nan Yaron kyamis ɗin yayi awon da yake ya iya komai akwai kayan aiki dama.
Sun ɗauki lokaci kamin yaron ya kalle su ya ce.
"Yawwa hajiya a nan dai ya nuna cewar...
Katse sa tana cewa da sauri.
"Ya nuna cikin ne hala ko?"
"Noo Hajiya gaskiya a iya bancike na babu wani ciki gaskiya, ga abunda ya nuna bata da shigar ciki"
Salma bata san lokacin data runtse idonta a hankali wasu hawaye na sake zubo mata, tana sauke ajiyar zuciya a hankali.
Tana jin yadda Aunty Murja ke ƙara cewa.
"Kai Yaro anya kuwa ka san aikin ka?, ka duba da kyau ma kuwa?"
"Hajiya iya gaskiya nake faɗa miki, amma idan baki yarda ba zaku iya zuwa babban asibiti sai a sake mata wani awon"
"Dole ne ma sai munje asibitin, domin gaskiya ban yarda ba ni"
"Amma tsakani da Allah Umma wannan abun fa yayi yawa da kike yi wallahi, wannan wacce irin ƙiyayya ce ne wai?"
Saukar marin da Yusura taji ne akan ƙuncinta ne yasa ta fiddo ido waje tana duban Umma data ɗaga hannu ta zafga mata tafi, tana huci ta nunata da yatsa ta ce.
"Idan ina magana akan wannan baƙar ƙaddarar kika sake kika ƙara katse ni ko gwalashe ni, na rantse da Allah zan nuna miki cewar ni ce na haife ki ba wai ke ce kika haife ne ba, tunda naga ke baki da tunani shashasha ce ke"
"Haba Hajiya ayi haƙuri dai"
Yaron kyamis ɗin ya faɗa yana ƙoƙarin sallamarsu.
Sosai Yusura ke hawayen baƙin cikin halin Umma.
A haka suka taso suka dawo gida har lokacin Umma na mita tana faɗa ta inda take shiga bata nan take fita ba.
Tana shiga ɗaki ta ɗauki wayarta ta danna wata number tana ɗauka ta fara magana.
"Ke dai bari A'i wannan yarinyar Yusura ke shirin ɓata min rai"
"Mi yake faruwa ne Murja?, yi min baya ni"
A'i ta faɗa daga cikin wayar.
Gyara zama Aunty Murja tayi ta ce.
"Hmm bari A'i, kinga yarinyar nan ko miye zanyi na ma wannan yarinyar Salma sai ta ce ban iya ba, yarinyar kamar ba ni ce na haife ta ba?"
"Uhmm ai sai da na ce miki Murja kiyi duk mai yiwuwa ki datse karatun nan da yarinyar nan take. Taya za'ai iyayenta na can ƙauye daga zuwanki za'a kawo miki ƴar wata wai da sunan ta zauna karatu take, salon azo a ɗora miki hawan jini, ko azo miki da mugun abu"
"Abunda da nake zargi kenan, ko kuma so ake tazo birni ta samu miji ɗan birni, tunda a a can sun gagara su sami mijin, ƙannan-ƙannansu ma sai aure suke suna barin su, su kuwa daga ita har shegiyar ƴar uwar nan tata Ummi marar kunya mai ido a tsakar ka ai sunyi kwantai babu ɗan iskan dake zuwa masu da maganar aure, dama kuma wannan shegen ƙauye nasu idan suna ciki ai ba samun mijin zasu yi ba, shine aka fake da karatu. Nifa zargina ma kar taje tayo mana abun kunya, kin san ƴan ƙauye basu iya wayewa bafa. Ni so nake kawai nayi maganin Yusura ta daina jin tausayinta dan ub*anta, so nake nayi mata gata amma ita bata gani. Yanzu dan Allah A'i idan ana ganin Salma tare da Yusura ya za'ai har wani ya ce yana son Yusura?, nesa ba kusa ba ƴar iskar yarinyar nan Salma ta fita komai, kowanne shege sai kika ga ya zo da sunan wai Salma yake so"
"Tabɗi jam ai ko sai kin miƙe tsaye wallahi. Amma koda yake ai nake ganin ba wai aure yake kawo su ba, tunda kinga har zuwa yanzu babu wadda ya fito da sunan aure ne ya kawo sa"
"Yo ƴar iska ce ni A'i na bari ta auri wani, ina ai sai dai idan bata zaune gidan nan wallahi, zasu san illar turota karatu da saukai. Sana kuma ruwan ido ne irin nasu, wai fa basu ga wadda ya dace dasu bane, inaga mai abun hannu ake so ya fito, kwaɗayayyu kawai. Nanfa kina gani sai ubansu yayi sati har biyu ban gansa garin nan ba, yana can wajan tsofaffin Matan nan nashi, da ba abunda yake ci a wajansu sai wahala"
"To ai Murja ki ce kika zauna, ai wallahi da yanzu sai kinga dama ki barshi yaje inda suke ma, ita kuma Yusura itama da an miƙe tsaye kanta zata daina shiga al'amarin Salma"
"Nifa A'i bana so ya rinƙa zama a nan ɗin ai, nasan mi nake shiryawa ai, ke dai akwai lokacin da ni da kaina zan zo na ce ki raka ni inda za'a min maganin shegu su dukansu. Ita kuma Yusura akwai wani abu da nake jira, ba boka ba Mlm zan sa dole sai ta tsani ƴar uwar tata, zanga ƙarshen tausayi ai........