Episode 3
by @zahraroyal
*MUGUN ICCE*
*©Zahra Royal Star*
*ROYAL STAR WRITER'S ASSO.......*
PAGE 3
*SALMA POV*
Ɗan dubanta tayi tana sadda kanta ƙasa tana wasa da yatsun hannunta ta ƙara ɗagowa ta dubeta ta ce.
"Aunty Murja, nifa babu abunda ke damuna, zazzaɓi ne kawai fa"
Wata uwar hararara data ɓalla mata yasa Salma ƙara sadda kanta ƙasa tana jin zuciyarta babu daɗi.
"Munafurci kawai, ai dole kiyi ƙasa da kanki man, kuma wallahi dole ne ayi awon cikin nan kinji na gaya miki"
Akan layi suke na ganin likita, wasu na shiga wasu na fita.
Jiki a mugun sanyayye Salma take zaune wajan, duk da hankalinta kaso ɗari a kwance yake, tunda a iya saninta ita dai tasan bata da wani ciki, amma zargin Aunty Murja da take mata ne yayi tsauri da yawa, abun na taɓa mata zuciya ainun.
Kiran sunan su da akai ne yasa Aunty Murja kamo hannunta da ƙarfi ta jata zuwa office ɗin Doctor, sosai take binta da kallon wannan ƙarfin hali da take mata da son alama dole saita ƙaƙaba mata abunda bashi kenan ba.
Suna shiga suka zauna ya fara mata tabbayoyi tana basa amsa, kai tsaye Doctor ya gano zazzaɓin cizon sauro ne kawai ke damunta.
"And ba sai anyi wani awon ciki ba, zazzaɓi ne na cizon sauro ke damunta"
Doctor ya faɗa yana wasu rubuce-rubuce akan wata farar takarda.
Ai Aunty Murja najin hakan tayi tsalle ta dare tana cewa.
"Kaga Doctor nifa ba wannan ne ya kawo ni ba yawwa, so nake kawai a tabbatar min da zargi na"
"Zargi kuma bawar Allah?"
"Eh zargi man, duk ga alamar ciki nan a tare da ita sana kuma ka ce wani zazzaɓin cizon sauro ne ke damunta, nifa gaskiya ko ban wani yarda da abunda ka ce ba yawwa, kawai ayi mata awon cikin a tabbatar idan da gaske kake babu cikin"
Ɗan tsayawa yayi yana kallon Aunty Murja na wasu saƙonni kamin ya sauke lumfashi, yana dawo da dubansa inda Salma take, kanta a ƙasa yake amma yana ganin hawayen dake mata zuba tana saka hannunta a hankali tana sharewa.
Kai tsaye yayi fara zargin akwai wani abu tattare da Matar nan.
"Amma ina shi Mijin nata?, kamata yayi yana a nan ai"
Taɓe baki Aunty Murja tayi haɗe da saurin cewa.
"Inafa taga miji, to babu shi"
Zare gilas ɗin idonsa yayi yana mamaki zaiyi magana Aunty Murja ta katse shi da cewar.
"Kaga Doctor kayi mana abunda ya kawo mu kawa shine, ba sai ka tsaya jin ba'asin labari ba"
Kamar yadda ta ce bai wani ja da ita ba, ya kira wata Doctor suka je da Salma aka ɗibi fitsarinta da jininta da duk abunda ya kamata.
Da kansa Doctor ɗin ya ce su jira shi minti kaɗan zai zo da sakamakon gwajin.
A nan Office ɗin ya barsu.
Ƙara gyara zama Aunty Murja tayi tana kallon Salma haɗe da sakin murmurshi mai sauti tana girgirza ƙafa ta ce.
"Ai yarinyar kima gama kukan munafurcin ki gaskiya dai ta kusa halinta, dan yau ba sai gobe ba zaki gane kuranki, hmmm wai karatu, ai shi Mlm ɗin shi kuka maida shashasha maloho da har ya yarda wai karatu kike a nan"
Salma bata jin zata ƙara magana, idan ta ce zata ce wani abun to tabbas kuka ne kawai zata ƙara fashewa dashi, ko kuma ta gaya mata magana marar daɗi, azo kuma ta ƙara ƙulla mata wani shirrin.
Shigowar Doctor yasa Aunty Murja sakin murmurshi ganinsa ya shigo da farar takarda a hannunsa yana jujjuyata. Samun waje yayi ya zauna yana dubansu gaba ɗaya, zaiyi magana Aunty Murja ta katse sa da faɗin.
"Doctor ai dama na gaya maka abunda nake zargi shine dai ya tabbata akanta ko?"
Sauke ajiyar zuciya yayi tana kallon Aunty Murja sosai kamin ya girgiza kansa ya ce.
"Baiwar Allah bafa haka bane, kin tsaya ai nayi miki bayanin sakamakon da muka gani ai ko?"
Shiru Aunty Murja tayi fuskarta na sauyawa sosai.
"Ina jinka Doctor kufa faɗi gaskiya, domin a cikin aikin ku babu cin amana"
Murmushi ya saki yana mamakin ƙarfin hali irin na wannan Matar, ita ala dole yadda ya fahimta sai ance yarinyar nada ciki.
"To gaskiya a iya bancike bata da wani ciki, zazzaɓi ne kamar yadda na ce miki ɗazu, shine dama kuma da alama haka take zazzabinta kamar mai laulayin ciki hakane ko?"
Ya faɗa yana sake duban Salma, da yanzu ta ɗago suka haɗa ido dashi ya sakar mata murmurshi kaɗan.
Sauke idonta tayi ƙasa ta ce.
"Eh Likita sometimes haka nake yawan zazzaɓi na wallahi, shi yasa ma yake wahalar dani. Itama Aunty Murja ɗin dan yau ne ta fara ganin kalar zazzaɓin nawa, taƙi tsayawa nayi mata bayani ne shine yasa"
"Yeah na lura da hakan. Amma da alama kina daɗewa bakiyi ciwo ba?"
"Haka ne Doctor, wani lokacin ma gaskiya ina mantawa da rabo na da yin ciwo irin haka, shi yasa idan ya kama ni baya min ta daɗi"
"To yanzu dai za'a sa mata ƙarin ruwa ne da wasu allurori da za'a mata kamin a sallame ku ku tafi"
Gani sukai Aunty Murja ta wani miƙe haɗe da ɗaukar jakarta tana cewa.
"Ƙaryar banza ƙaryar wofi, idan ma ba cikin ne da ita ba, shima ai yana nan tafe, domin babu yacce za'ai zandamemiyar budurwa kamarki mai shekaru ace har zuwa yanzu bata san ɗa namiji ba, kuma kina zaune ƙalau babu uwar data sha miki kai, ai dole akwai inda kuke maƙalewa kuna rage zafi. Kuma ni dai kinga tafiyata domin bazan tsaya nayi jinyar ƙatuwar budurwa ba irinki, idan kin gama daga can kyayo gida, idan kuma yawon da aka saba za'a je ne to sai sadda Allah yayi miki dawowa zance"
Tana faɗar haka ta wani ja kai ta fice tana sakin maganganu masu zafi da ɗaci a zuciya.
Rufe idonta kawai Salma tayi tana jin yadda ƙirjinta ke mata soya sosai.
"Am so sorry fa bawar Allah, zan shiga maganarku, amma wannan ɗin ba ita ce ta haife ki ba ko?"
Ɗaga masa kai kawai tayi haɗe da furta.
"Matar Babanmu ce"
"Hmm haba no wonder naga alamar hakan. Wai mi yasa mata kishi ke sawa suna kauce hanya ne? But ina wannan da alama banda kishi da akwai cutar hassada dake damunta, kuma na ce haukan kishin da ban taɓa cin karo dashi ba sai a wajanta. But amma fa kayi hakurii please"
Girgiza kai kawai tayi tana murmushin yaƙe dan jikinta ƙara sanyi yake ga zazzaɓin da take fama dashi.
Gani yayi ta miƙe tana neman hanyar fita yayi saurin dakatar da ita da cewa.
"Ina zaki je ne?"
"Zan bita ne"
"Noo ki tsaya sai an miki taimako gaskiya na asibiti saboda jikinki babu ƙarfi"
"Noo Doctor na gode, banda abunda zan iya badawa koda an saka min ruwan, babu kuɗi a hannu na, suna wajanta kuma ta wuce dasu, koda ma tana nan bazata taɓa badawa ba na sani"
Tausayi kawai ta basa tunda ta fara maganar. Ya sami kansa da tasowa har inda take yana cewa.
"Please karki tafi sai an miki duk taimakon da ya dace, ni zan ɗauki nauyin komai please"
Wata ajiyar zuciya Salma ta sauke tana ɗan satar kallonsa. Nitsatstsan mutum ne mai kamala da tausayi, gashi da kwantar da hankali, haka kawai ta samu kanta da sakar masa murmushi kaɗan shima ya mayar mata, kanta ta sadda ƙasa tana jin yadda gabanta ke faɗuwa.
"Please koma ki zauna kinji"
Zatai magana ya ce.
"Pleaseee"
Komawa tayi kawai ta zauna tana wasa da yatsun hannunta ya ɗan matso kusa da ita ya ce.
"But sorry ya sunan Malamar tawa?"
Wani irin banbarakwai taji maganar tasa, kai kuji bawan Allah, daga ganin sarkin fawa sai miya tayi zaƙi kuma?.
"Noo noo noo karfa ki ɗauka wani abu ne na tabbaya ne kawai"
"Salmaaa"
Ta faɗa kamar bata so.
"Wow so nice name"
Ya faɗa yana jifanta da murmushin nan nasa da taga alamar ma'abocinsa ne, kuma abunda bai sani ba yana yi masa wani irin kyau haɗe da ƙara masa kwarjini a wajan mai kallonsa.
A takure take a nan Office ɗin ya kira wata Doctor mace ta kawo duk abunda ya dace ya katse komai ya fara dubata ya saka mata ƙarin ruwan haɗe da mata allurorin a cikin ƙarin ruwan, da yake akwai gadon duba marar lafiya a Office ɗin nashi a nan aka kwantar da Salma. Doctor ɗin da ya kira Mace tayi mamakin yadda Doctor Farouk ɗin ke ta nan da wannan baiwar Allahn da take gani, tayi mamaki ba kowanne mutum yake sakar ma fuska ba kamar haka dai yadda taga yana ma Salmar kamar wacce ya daɗe da sani......