Fatima Zahra By Rukayya Yusuf Ibrahim (A. Y. M Palace Nova)
Chapter 01
Fatima Zahra🧕🏻🌹
*📚📖💻*
Mallakar
*_Rukayya Yusuf Ibrahim
(A. Y. M Palace Nova ✍️)_*
Sanarwa
Wannan littafin ƙirƙiraran labarine , idan wani/wata sunyi yayi kamanceceniya da rayuwarka to armashi ne👏.
Sadaukarwa
Na sadaukar da wannan littafi ga masoya da abokan arziki a faɗin duniya.
Bismillahi Rahmani Rahim
SHAFI NA ƊAYA 01
Sama ta haɗe sosai gari ya fara duhu alamar ruwa a kowane lokaci zai iya sauka iska na kaɗawa irin mai sanyi-sanyin nan.
Tafe take da akwatinta babba tana tafiya tana kuka ga kuma ciki ajikinta cikin tashin hankai, a haka dai cikin kamar zai wata bakwai.
Mace ce fara tas , amma kuma da alama yarinyar mace ce.
Domin fuskarta, ta yarinta ce da badan cikin da yake jikin ta ba, tsab zaka ce budurwa ce, irin waca bata isar aure ba ma.
Tafiya take tana ɗaga kafufawanta da ƙyar tsabar wahala, ga kuma hawaye na zuba a idon ta, ko kallan gabanta bata yi , ƙarshe ma da tayi tafiyar ta gaji sai ta samu guri ta zauna ta haɗa kai da gwiwa ta fara raira kuka mai ciwo .
Layin da take tafiya shiru-shiru , babu yalwar mutane sai jefi-jefi dake wucewa.
Wata mota ce ta tsaya dai-dai inda take, wanda ke ciki ya fito da alamun motar ce ta tsaya saboda wata matsala, gashi babu mutane da yawa a hanyar, kasancewar irin guraran masu kudin nan ne ga kuma yanayin garin na damina.
Juye-juye yake bayan fitowar sa, domin samun mafita , ya buɗa wajan injin motar ya ga alamun ɗaukan zafi tayi.
Ya duba duk shagunan wajan, da yake tsakar rana ce duk a kulle suke, a daidai nan ita kuma baiwar Allah nan ta ɗago ta zuge jakarta ta fito da gorar ruwan da tayi guziri ta kafa a bakinta tana sha .
Shi kuma ya juya kamar ance juyo inda take ya juyo, ai da saurin sa ya nufo ta da niyyar ta taimaka masa.
Amma yana zuwa ya zaro ido cikin mamaki , yana nuna ta bakin sa na rawa yace "Zah..Zahra me kike yi a nan?".
Cikin sauri ta ɗago tana kallon sa, sai tayi saurin ɗaukar kayanta tayi gaba ko magana bata yi masa ba.
Da gudu ya bita ya riƙe jakar yana cewa "Zahra dan Allah ki tsaya kiyi min bayani, me akai miki? Kukan me kike ? Ko baki gane waye ba ? Mujahid ne fa Zahra?" .
Ta juyo cikin kuka tace" Mujahid ka ƙyalleni na tafi , a yanzu ba Zahran da ka sani ba ce.
Wannan ta gabanka rayuwarta a lalace take , duniya ta fito domin tazama ƴar cikin duniyar , saboda a yanzu duniya ce gata na, dan haka ka nisanta daga gare ni, dan Allah ka manta ma wai ka taɓa sani na Mujahid" .
Cikin mamaki yake kalonta yadda take kuka tana magana.
San nan ya lura ba acikin nutsuwarta take ba, sai ya sassauta murya ya ƙara dubanta.
" Shikenan zo ki samun ruwa na zuba a mota sai na kaiki duk inda za ki je kinga bake ƙadai bace".
Miƙo masa tayi, dan ko bakomai ta gaji da tafiyar wajan awanta biyu ko uku tana tafiya.
Ya zuba yace" shiga mota " .
Ba musu ta ɗauko jakar ya taimaka mata suka sa a mota.
Bayan sunyi tafiya mai nisa yaji kamar numfar-fashi take, ya juyo yaga idon ta na neman kafewa , cikin tashin hankali ya ƙara ƙarfin gudun motar ya nufi hanyar asibiti .
Cikin mintina ƙalilan yazo wani asibitin kuɗi jikinsa na rawa , ma'aikatan jinya suka turo gadon ɗaukar marasa lafiya; suka ɗauketa ; suka shige da ita ɗakin taimakon gaggawa.
Haka ya dinga kaikawo a farfajiyar asibitin zuciyarsa na dukan uku-uku daga ƙarshe dai ya ɗaga waya ya kira Mahaifiyarsa ya shaida mata yana asibiti ga abinda ke faruwa.
Ba a fi mintuna ishirin ba Mahaifiyarsa ta iso gurin tana sauri da tambayarsa an fito da ita.
Yace" a'a".
Haka suka zauna wajan ƙarin mintuna ashirin kusan awanta ɗaya, san nan aka fito da ita.
Kana dubanta zaka san ta jigata sosai amma cikin ikon Allah, juna biyun dake jikinta yana nan lafiya lau.
Hajiya Salwa Mahaifiyar Mujahid ta dube shi tace " daman Zahra Yusuf T. Arɗo ce?" Ya ɗaga kai yace" eh Mama" .
Haka aka kai su ɗakin kwanciya ;aka kuma yi mata allurai acikin ruwan da aka sa mata.
Likita sawa yayi Mujahid da Mama suka zo.
Cikin ɓaccin rai ya fara yi musu faɗa akan halin da yarinyar ke ciki, a tunaninsa iyayyanta ne.
Kuma yace "duk abinda yake sa ta acikin damuwar nan ya kamata ayi maganisa da domin za a iya rasa ta a rasa abinda ke cikinta" .
Dole Mama da Mujahid sukai shiru suka bishi da "to".
Bayan fitar su Mama ta kalli Mujajid cikin damu ta ce" ina ka samu Zahra?".
Ya ce" Mama a hanya muka hadu ".
"To ya kamata muje mu sanar da iyayyanta gaskiya ".
"A'a Mama Zahra ta ce bata son ganin su, ina tunanin akwai wata matsalar Ni kaina daƙyar ta yarda na taimaka mata".
Shiru Mama tayi kafin kada kai su wuce dakin da Zahra take.
Har sun zauna sai koma gida ta ɗako kayanta da abinci tazo asibitin, domin ta kwana da ita.
Tunda dole itace zata zauna da ita, Mujahid namiji ne kuma bata da wadda zata zauna.
Haka Mama ta zauna da Zahra kwana uku harta ɗan murmure, bayan an faɗa musu jininta ne ya hau, da tsautsayi ma cikin jikinta da sai ya fitar da kansa,aka ce ta rage damuwa da kuruciyarta.
Tunda Mama taji haka ta dage da kula da Zahra , kuma ta fahimci Zahra ba tasan a tambaye ta komai a yanzu, sai tayi mata shiru har aka sallame suka ta tafi da ita gidan su .
Sai da Zahra ta ƙara jin sauki , wata rana lahadi Mama tana zaune kusa da Zahra.
Mujahid na gefe sunyi karin kumalon safe ta kalli Zahra ta ce" Zahra yau kusan kwanan ki sha huɗu a tare damu, kuma na lura bakya san ayi miki zancan gida, amma ya kanata kiyi mana bayani kar iyayanki suga laifin mu".
Hawaye ne ya kufce mata , ta shiga raira kuka mai tsuma zuciya wanda yasa Mama dafata , amma kafin Mama ta ƙara magana Zahra ta share fuskarta tace" Mama na gode Allah ya saka da alkairi da irin karamcinku gareni , kun min hallaci ba tare da alakar jini a tsakanin mu ba , abunda na sani a yanzu ko iyayena baza su min ba, sai dai na mutu" . Ta sake fashe da kuka mai ciwo.
Ta ci gaba da cewa" Mama duk sanda kuke so in tafi zan tafi, domin ni yanzu bani da kowa sai Allah da ya hallice ni , dan haka na gode sosai Allah ya biyaku da abinda kukai min".
Mujahid ne yace"wai me kike nufi da baki da kowa Zahra ? Ina Momi ina Abba? Ina su Yaya? Ina kuma mijinki ? San nan menene abinda ya rabaki dasu ga ciki jikinki? Ko dai ba a sani ba kika fito?".
__________
_*FATIMA ZAHRA 🌹
Mai son complete dinsa zai tura ₦500
Account:8148563513
Rukayya Yusuf Ibrahim
Opay bank.
Shaidar biya ta ****_