Fatima Zahra By Rukayya Yusuf Ibrahim (A. Y. M Palace Nova)
Chapter 02
Fatima Zahra🧕🏻🌹
📚📖
Mallakar
*_Rukayya Yusuf Ibrahim
(A. Y. M Palace Nova✍️)_*
Taurarin Marubuta Writer's Association 🤝✍️
*Free Page*
Bismillah....✍️
Shafi na biyu 02
Dariya tayi mai ciwo ta dube shi ta ce" Mujahid a yanzu na rasa kowa duk acikin waɗanda ka ambata ".
Cikin tsoro yace" kinga ya kamata kiyi mana bayanin abinda yake faruwa, ni nasan ke me gata ce Zahra, gaba da baya , ina Innan ki? Da gwaggonki ina Baffa? Zahra ina Minal ko Nusaiba? Ina Husna ina Amira? Zahra ina su Sajid duk suka barki cikin wannan halin ?".
Mama ta dubeta tace" Zahra kinga ni Uwa ce a gare ki, tunda ko ba Mujahid da yake abokin karatun ki, ni Malama ce a gare ki.
Malamai kuma suna zama a gurbin iyaye, ki daure; ki bani labarinki tun daga farko har zuwa yau Zahra ".
Shiru tayi na wasu mintuna tace " Mama dan Allah kafin na faɗa miki labarina , zan rantse miki da Allah ban taɓa aikata zina ba ko makamancin ta ba, idan har ƙarya zan fadamiki to Allah shine shaida ta".
Mama ta ƙara dafa tace" na yarda dake Zahra tun ba yanzu ba, a ɗalibaina ke ta daban ce Zahra dan haka ina jinki".
Ajiyar zuciya tayi idonta na zubar hawaye ta fara da cewa " kamar yadda ku ka sani sunana Fatima Yusuf T. Arɗo waca aka fi sani da Zahra.
Ni ƴar dangi ce gaba da baya kuma masu matuƙar haɗin kai.
Na taso acikin farin ciki tare da Mahaifiyata da Mahaifina da Yayyena maza guda shida.
Asalin mu ƴan jahar Burda ne , gidan mu ; gida ne na manyan mutane da suka gina so da kaunar junan su tun sal-sala, domin suna riko da zumunci sosai .
Alhaji Muhammad asalin sa ɗan cikin garin Burda ne , bafilatani ne gaba da baya.
Ya taso cikin soyayya da kulawa ta iyayyansa domin shi kadai Allah ya mallaka musu.
Saboda haka duk wani jin daɗin rayuwa sun nuna masa, tunkan karatun boko yayi suna a garin Burda, Iyayyansa suka sashi , tare da ta Mahammadiyya.
Wannan ilimi da ya samu ya kuma hankaltar dashi da nutsuwa domin duk son da Iyayyansa suke masa , sun jajurce akan tarbiyar sa.
A haka Allah cikin ikonsa , ya taso da fasahar kiyo , wato sana'ar Babansa amma kuma sai ya shigo da ilimi acikin harkar na zamani.
Inda da taimakonsa Mahaifinsa ya buɗe katuwar gona ta kiyo daban-ban da noma.
Kuma aka buɗe gurin siyar da nonon shanu na gaske da madararsu .
Da wannan Allah ya rufa musu asiri bayan kiwo suka shigo cikin burni suna sarar kayan sawa kamar su: atamfa ,shadda, da sauransu.
Ƙarshe ma dai Gwani ardo ya bar rugar su can Burda ya dawo birnin Dima.
Burda sai ziyara ko duba gonakinsa na can.
Alhaji Muhammad Tilan , yana da shekara ashirin da uku Babansa ya aura masa ƴar kanwar Mahaifinsa Hadiza.
Duk da ba santa yake ba, yayi biyayya ya karɓa har suka samu rabon ɗa na miji mai suna Abdullahi.
Bayan haihuwar Abdullahi da shekara daya Alhaji Muhammad yazo wa da Mahaifinsa zancan ya samo wata yana so a can cikin garin Hulwan.
Mahaifiyarsa ta tisashi da faɗa akan ya janye , yaushe ya auri Hadiza balle yace zai ƙara aure.
Nan aka sha fama kafin ta yarda Alhaji Muhammad ya auri Kubura itama Hadiza ce amma Kubura ake ce mata, kyakkyawar bafulatana ta gaske.
Cikin ikon Allah zaman Kubura da Hadiza baizo da matsala ba, domin Kubura yarince mai hankali ba ruwanta, ita kuma Hadiza tana jan girmanta .
Ta haka suka taso cikin ƙauna da soyayya ga mijinsu suna girmamashi yana girmama su.
A yanzu haka haihuwa tayi nisa inda Hadiza ke da yara biyar uku mata biyu maza, yayinda kubura keda takwas duk maza ɗaya ce mace.
Yaran sun taso cikin so da ƙaunar junansu kamar yadda iyayyansu da Kakaninsu suke buri, domin bazaka taba ban-bance waye dan Kubura ba ko na Hadiza ba.
Cikin ikon Allah yaran Alhaji Muhammad Tilan , guda goma sha uku suka kafa babbar zuriyar da yake matukar alfahari da ita.
Mahaifin Alhaji Muhammad sun rasu tare da bar masa wasiyar hada iyalan gidansa , kar ya sake ya raba kawunan su.
Kuma ya cika burin iyayyansa inda ya dinga hada yaransa aure da ƴan uwansa na Burda .
To a haka ya dinga hada aurataya da yaran ƴan uwansa ko da ; yaran ƴan uwan matansa, domin zumunci ya ƙara yaɗuwa .
Haka rayuwa ta cigaba, wani auran yayi daɗi; wani sai hakuri cikin ikon Allah babu wanda dai aka rabu.
Yanzu haka iyalansa sun rarrabu kashi -kashi inda Allah ya kara buɗawa kowa, shi kuma girma ya cimmasa.
Kuma har yanzu yana garin Dima tare da yaransa biyar Abdullahi wanda yara ke ce masa Papa kuma shine babba ɗan gurin Hadiza wato gwaggo.
Sai Aminu shima shine babba amma gurin Inna wato Kubura shi kuma yara na ce masa Dadi.
Sai Nasiru wanda yara ke cema Baffa karami , sai BaffaYusuf ,sai kuma Gwaggo Rahana da take aure ita ma a Diman.
Sauran kuma wanda suka hada Hajiya Binta ita ƴar gwaggo ce ,da gwaggo Hannatu da Hadiza wacca ita ce ƴa daya tilo gurin Inna, wacca suke kira da Gwaggo hajja duk a Burda suke aure da mazajansu.
Sauran mazan kuma Isma'il yana Hulwan da yaransa shi da Kawu Mustapha.
Akwai Abubakar yana Gohar da nasa iyalin ,sai Aliyu shima yana da nasa iyalan a Burda, sai kuma Umar shima kuma a Burda yake da zama da nasa iyalan sai dai kuma yanayin aiki yanzu yana kasar waje sai lokaci bayan lokaci suke zuwa tare da yaransa.
Murnar shagalin hidimar karamar salla ake kamar yadda kowa na irin gari da nasu al'adar, suma kowa na ziyartar ƴan uwa da abokan arziki.
A yau gidan Alhaji Muhammad Tilan Ardo, cike yake fal da jikokinsa musaman wanda suke cikin garin Dima.
Ana ta hadadar sallah, ƙa'idar gidan ce duk sallah mata da maza haɗuwa ake a tafi sallar idi, idan andawo kuma a gidan Alhaji Muhammad wanda muke kira da Baffa nan za aci a sha a ɗauki hotunan tarihi.
Kamar kowace shekara yau gashi an haɗu ana ta hira amma iyaka cin yaran da suke Dima sauran garin wannan karon kowa na cikin garinsu.
Kamar yadda na faɗa muku ni ƴa ce ga Baffa Yusuf da sauran ƴan uwana Minal, Nusaiba da Husn harda mu acikin masu taya iyayanmu girki da rabawa ƴan uwa.
Kowa na zaune suna ci ana farin ciki aka gama aka ɗauki hotunan tarihi, dare yayi kowa ya watse ya tafi gidan su.
Gidajan yaran Baffa duk suna kusa dashi ;duk baki dayan su kowa da nasa.
Kamar Papa yaransa su 19 ne matansa biyu , Shi kuma Baffa Nasir yaransa sha biyu shima matansa biyu, sai Abbana ke da bakwai matarsa daya , sai Baffa Aminu da ke da sha bakwai matansa uku amma daya ta rasu.
Gwaggo Rahana itace take can unguwar sarki mai yara bakwai .
Dukkan waɗɗan nan yaran sun taso da shakuwa sosai da san junansu makaranta tare boko da Islamiyya, musaman mazan domin sun fi yawa , don Baffa Yusuf (Abban mu kenan ) yaransa duk maza ne ni kaɗai ce mace.
Rayuwar alhalin Baffa abun burgewa ce, musman waɗanda mu da muke kusa dashi .
Domin duk yaran kowa na girmama iyayyansu babu bambanci tsakanin Baffa wane da ;Baffa wane duk mun dauke su ɗaya .
Matsala ɗaya ake samu ta ɓangaran matansu , domin sha'anin yau da gobe musamman zaman mata .
Rayuwa ce waca aka gina ta cikin tsantsar san juna da gaskiya ɗaya ba ya gaba da ɗan uwansa acikin yaransa ko faɗa ko kuma mummunan kalami.
Abbana Baffa Yusuf shi kaɗai ne ya auri bare, ma'ana waca bata da alaƙa da ahalinsu , sauran kuwa sai dai bayan auran dangi su ƙara da ta biyu da bare.
Baffansa yaso Abbana( Baffa Yusuf ) ya auri ƴar dangi , amma fafur yaƙi saboda Khadija ƴar maƙocinsu da yake santa tun tana yarinyar.
Dole Baffa ya hakura domin Khadija da ahalinta ana zaman mutunci sosai dasu.
Zahra, Husna,Minal da Nusaiba kanmu a haɗe yake, kuma mun taso tare, komai kusan iri daya ake mana.
Minal ƴar Baffa Abdullahi ce sai Nusaiba ƴar gidan baffa Aminu, san nan Husna ƴar Baffa Nasir.
Mune a lokacin ƴan mata masu tasowa domin duk anyiwa Yayyan mu mata aure sai Yaya A'isha kuma ita ma saura lokaci kaɗan ake jira.
Duk da kasancewar auran zumunci aka fiyi a dangin arɗo , amma kuma Yayyan mu da suka wuce anbawa kowace dama ta fida miji a dangi ko a waje.
Hakan yasa muka saki jikinmu muna buga soyayyarmu da samarin mu na waje ba a dangi ba.
Haka zalika muna san karatun mu yayi nisa kafin ayi mana aure, amma dole mun sani a dangin mu mata basa nisa a karatu sai a gidan miji, in ya amince a ɗauki nauyinki ko in zai iya ya ɗau nauyinki .
Acikin mu ni ce ƙadai nake da saurayi a dangi wato Yaya Munir, amma kuma akwai wanda yake mugun sona Faisal ɗan bayan layin mu.
Bama shi kaɗai ba, kuma ba wai batun alfahari ba ina da samari sosai duk da ƙankantar shekaruna domin a yanzu ma nake shirin shiga sha takwas.
Faisal shine zabina domin so yake min irin na mutuwa da zai iya komai a kaina, tun bana kulashi har zuciya ta rinjaye ni, domin ance zuciya nasan mai kyautata mata.
Faisal kuwa bayan ɗumbin soyayya ta ido ko kunne da kowa yake gani kuma yaji, mutum ne mai kyautatawa ;kuma ba iya ni ba,har ƴan uwana da ƙawayena suna morarsa saboda da dalili na.
Gafe guda ga Munir da yake masifar sona da kishina, dan babu wanda ya tsana a duniya kamar Faisal.
Matsalar da aka samu daya ce, shi Munir a can Burda yake gidan Baffa Umar kuma yawanci basa ƙasar, lokaci zuwa lokaci yake zuwa hutu gidansu , saboda haka na fi shaƙuwa da Faisal .
Haka rayuwar mu ta kasance cikin jin daɗi da kuma kalubalan yau da gobe .
Tsakanin mu da kakanin mu kuwa sai san barka musamman ni da kullum sune abokan hirata, sona da shaƙuwata ya sami gurin zama a zuciyar Inna da gwaggo har ma da Baffa.
Dan haka irin wasa da dariya da muke abun sai ya bawa mutum mamaki.
An sallace azumi anzo bayan salla, wanda muke da bikin Yaya A'isha , muna ta murna daman ita kaɗai ta rage a Yayyanmu sai kuma mu da sauran mazan.
Takanas Baffa ya aikawa mutanan Burda, Hulwan da Gohar akan lalle -lalle kowa ya hallaci bikin nan , domin yawancin bukukuwan da akayi sai dai wane ya wakilci wane basa zuwa gaba ɗaya balle kuma su taho da yaransu baki ɗaya.
Amma a wannan karon Baffa yace " kowa ya taho da iyalansa domin bayan biki yana da babban taro domin ƙara zumunci".
Aikuwa suka fara shiri Munir ya riga dawo wa saboda ƙanwarsa ce, kuma a wannan karon yana so ya faɗawa Baffa yana sona kuma dole wannan wawan da yake zuwa ya hakura da ni.
Kamar wasa Yaya Munir ya dawo cikin Dima sati biyu kafin bikin Yaya A'isha.
Ya danno da ƙarfinsa akan dole sai ya tunkuɗe gwamnatin Faisal a gurin Zahra.
Soyayya ta ban mamaki ya fara nuna min, ya kasa ya tsare akan dakatar da Faisal .
Acikin ƴan uwanmu mata da maza wasu na goyan bayansa; wasu kuma sunfi goyan bayan Faisal.
A ɓangare na kuwa baza ace bana san Yaya Munir ba, domin duk irin siffar mutanan kirki ta bayyana akansa , kuma shima Faisal haka, hakuri da juriya kuwa zan iya cewa Yaya Munir yafi Faisal, dan sau tari in mukai faɗa bai iya fushi ba, amma kuma gani nake Faisal shine daidai da ni.
Akwai kuma abinda nake hangowa ga Yaya Munir ta ɓan garan Mahaifiyarsa, don kwata -kwata Maman sa basa jituwa da Momina.
Domin har cewa Momin mu take ta mallake Abban mu, dan dai ita Momin mu bata da hayaniya ,kuma Momi bata biye mata, sun ma fi mu'amala da Ummi mahaifiyar su Nusaiba kishiyarta kenan .
To har da wannan dalilin nake tsoro akan Yaya Munir.
Haka Munir ya dage sai ya kori saurayina Faisal , Mahaifiyarsa da taga da gaske yake ta ce" bai isa ba" bazai yiyu a mallake mata ɗa ba kamar yadda aka mallake Baffa Yusuf ba.
Magana ta fara tashi domin acikin mutane ta ƙare masa zagi ta ce" yaje ya nemi ƴar kanwarta".
Har magana taje gurin Baffa, amma baice komai ba .
Da wannan na tattara hankalina kan Faisal, mukai ta zuba soyayyarmu.
Soyayyar da kowa ya shaida , wasu ma kwaikwayon mu suke, saboda mun so junan mu , don a kaf unguwar mu da kewaye sai da kowa ya shaida soyayyarmu da Faisal.
Munir kuncin duniya duk ya ishe shi , yana ji yana kallo zan ci ado na tafi gurin Faisal in yazo zance.
Kamar yayi kuka wani lokacin, daman ya taɓa faɗa min cewa babban abinda yasa yake so na shine kwalliya.
Domin babu ƙarya ni mace ce da tasan darajar ado , jan lalle da baki basa wuce ni, kullum cikin sabunta kitson kaina nake, bana zama da datti ko a dakina ne kuwa, kuma duk wannan tarbiyyar Mahaifiyata ne domin ita ma ƴar ado ce , shiyasa da yawa facalolinta ke kishi da ita.
Ranar da ta zama mafarin sabuwar rayuwa gare ni ita ce, bayan ƴan uwa ta kowane ɓangare sun hallaci bikin Yaya A'isha an kaita gidan mijinta da kwana biyu, Baffa ya tara gagarumin taro.
Ya dubi yaransa kaf , a wannan lokacin kowa yana nan har baffa Umar dake wata ƙasar yazo.
Ya fara buɗe taro da addu'a san nan ya ɗora da cewa" babban burina haɗa kan zuriyata waca ko bayan raina zakuyi alfahari da ita, shiyasa nake haɗa a aure domin ƙarfafa zumunci a tsakanin ku, na haɗa aure ganin idanku ba adadi ,wanda sai tarin alkairai masu yawa.
kuma cikin ikon Allah zan a haɗa a yanzu kamar yadda na saba".
Cikin tsoro duk wanda yake saurayi ko budurwa a cikin jikokin Baffa ya ɗago yana kallonsa.
*_Mai son complete book din nan ₦500
Account:8148563513
Rukayya Yusuf Ibrahim
Opay bank
A tura shaidar biya ta ***.
*_