Fatima Zahra By Rukayya Yusuf Ibrahim (A. Y. M Palace Nova)

Chapter 03

by @aymcreatives

Fatima Zahra🧕🏻🌹

📚📖

Free Page

Na

*_Rukayya Yusuf Ibrahim

(A. Y. M Palace Nova✍️)_*

Taurarin Marubuta Writer's Association 🤝✍️

Bismillah....✍️

Shafi na Uku 03

Ya cigaba da cewa "zan haɗa Nusaiba ƴar Gurin Aminu da Khalid ɗan isma'l, san nan Husna ƴar gurin Nasir da Sadiq ɗan gurin Mustafa, akwai Na'ima ƴar gidan Umar da Munir ɗan gidan Aminu, akwai ƴar gidan Abdullahi Minal da Abdulkarim ɗan gurin Aliyu, sai Salim ɗan gurin Abubakar da Amira ƴar gurin Rahanatu, amma ita zamu tun-tuɓi ubanta muji tunda mu dangin uwa ne kafin nasu haɗin ya tabbata.

Akwai Mahmud ɗan gurin Umar da Fatima Zahra ta gurin Yusuf, akwai Nafisa ƴar gurin Aliyu da da Khalil na gurin Yusuf.

Kuma inshAllah auran nan duk bazai ɗauki lokaci mai tsayi ba, zan bawa duk wanda baida gurin zama muhalli ya zauna kan ya mallaki nasa , na bada wata biyu kuje ku fahimci juna , akwai aurarankin da zan haɗa bayan naku InshaAllah ".

Ya sake cewa"akwai wanda yake da magana?".

Duk kan mu tun da ya fara maga jikin mu yake rawa musamman mu matan wasu ma acikin mu kuka suke mara sauti.

Kafin mugama tunani ko ince hankalin mu ya dawo jikin mu baffa Abdullahi yace " babu mai magana Baffa, ai duk hukuncin da ka yanke shine daidai fatan mu Allah ya ƙara haɗa kanmu, kuma Allah ya sa wannan haɗin mutuwa ce zata raba" .

Aka amsa da amin kowa ya tashi jiki a saɓule.

Babban tashin hankalin shine duk haɗin da yayi babu mai yiwa wani kallon arziki ,duk da kasancewar mu ƴan uwa, kowa haɗin yazo masa a bai-bai.

Ta gurina da Minal da Amira kuwa abin yafi muni, domin muna da masoya wanda muke mutuwar so , gashi an haɗa auran da waɗɗan da wannan ne karon farko da zamu iya cewa mun gansu da wayan mu domin duk a waje sukai karatu da Yaya Mahmud da Yaya Abdulkarim da Yaya Salim .

Sauran kuwa duk mun sansu sai dai babu shaƙuwa mai ƙarfi .

Ɓangaran Yaya Munir kuwa ji yayi kamar yayi hauka domin an bada ni ga wanda yake matuƙar ganin mutunci kuma ƙanwarsa ce zaɓin da baffa yayi masa gashi mahaifinsu shike riƙe da shi kamar ɗan sa a Burda.

Duk waɗɗan haɗin ansha kuka , wani ma harda masu cewa basu yarda ba ciki kuwa harda ni, domin tunanina ya zanyi da Faisal?".

Ta dubi Mujahid tace" in baka manta ba a wannan lokacin har makaranta muka daina zuwa" ya ɗaga kai alamar eh.

Ta cigaba da cewa" haka muka sha rarrashi da lallabawa daga ɓangaran iyayyan mu da Yayyan mu, suma kuma mazan yadda ake dannar kirjin mu haka aike dannar nasu tunda kowa ba so yake ba.

Daddy wato Baffa Aminu da Baffa Abdullahi sune sukaje har gidan su Faisal sukai musu bayani, kuma suka gamsu suka basu hakuri; kuma aka kira Faisal aka bashi hakuri .

A wannan ranar duk imanin ka, in ka dubi Faisal sai ya baka tausayi, domin kuka wiwi-wiwi ya dinga yi da idonsa, yana roƙon su amince masa ya aure ni.

Amma Baffa baya magana biyu dole aka bawa Faisal hakuri domin Baffa cewa ma yayi shi kansa Faisal bazai iya bashi aure a jinin sa ba , saboda bai yi masa ba.

Momina ta jajurce da ita da ƴan uwanta wajan kwantar min da hankali sosai, har naji zan iya zama da Yaya Mahmud ko da kuwa yana da mugun hali.

Haka shirye-shirye ya kankama na bikin mu , waɗɗan da basu zana jarabawar sakandiri ba irina aka ƙara lokaci domin muyi, bayan mun gama da wata biyu baffa ya tsaida lokaci , akayi biki iya biki wanda ba a taɓa yinsa ba acikin dangi ba , domin kuwa ya shafi kowana bangare na ahalin.

Dukkan mu gida Baffa ya bayar kowa da nasa wasu kuma suna dashi kuma duk a cikin Dima.

Yawanci gidajen mu babu nisa dana juna, kuma daga gidan mu zuwa gidan mazajan mu babu nisa.

Kowacce a cikin mu ta ɗauki ƙaddararta na rayuwa da abokan zamanta, mun fara rayuwar auranmu babu kushe bare hassada.

Mijina wato Yaya Mahmud mutumin kirki ne, mutum ne wanda bai fiya san hayaniya ba, mutum ne mai kauda kai da hakuri , za a iya kiransa cikin mutane nan da ake kiransu da miskilai, yasan ba auran soyayya bane tsakanin mu, amma ya koyar da ni yadda zan so shi kamar yadda nayi kokarin koya masa sona, ta hanyoyin da Momina ta fadamin wato biyayya kan duk abinda ya umarce ni, girmama mahaifiyarsa da ƴan uwansa, bashi hakuri lokacin da nayi masa kuskure, kada na dinga fushi dashi , na kasance mai hakuri a kowana yanayi na tsinci kaina.

Duk waɗannan abubuwan zan iya cewa sun zo min da sauƙi domin cikin ƙankanin lokaci muka shaƙu , muka zama abu guda, yana nuna min soyayyar da ta mantar dani auran haɗi mukayi.

Dangi kowa ya lura da hakan domin auran mu yafi na kowa daɗi abunda wasu basu taɓa zato ba.

Takaduna na makaranta suka fito ya amince min akan cigaban karatuna , har ya fara min shirye-shirye kwa tsam sai ga ciki ya bayyana, sai ya ce na bari na haihuwa sai na koma in yaso muyi tsarin iyali yadda zan jima kafin na ƙara wata domin na samu nutsuwar karatu.

Matsaloli sun fara afkuwa ne lokacin da wata Suhaila ƴar gidan baffa Aliyu tazo daga Burda ta tare a gidan Baffa .

Amma kullum tana gidan mu, tun abun baya damuna tazo ta dinga bin ƙwaƙwafin duk abinda nake, ta yini har Yaya dawo san nan ta tafi, duk da na fahimci baya sake mata amma ya ɗan fara damuna kasan ance in daso da kishi .

To abu dai kamar wasa tazo tai ta kwarkwasa a gaban sa ,ni kuma na kufula nace karta ƙara zuwa min gidan miji .

A nan naga tujara, taita min rashin kunya , karshe dai ta daina zuwa.

Sai daga baya naji ashe tun asali ita take sansa har iyayan su na can sun amince za a haɗa auransu sai baffa ya zaɓa masa ni .

Da ya dawo bayan na hana Suhaila zuwa gidan mijina da wajan kwana biyu yazo yake min faɗa akan meyasa nai mata haka, ya dinga min faɗa abinda bai taɓa yimin ba , na bashi hakuri aka wuce gun.

Bayan satitika ban san me ya faru ba Momina ta kirani zuwa gida , da kansa ya kaini a zuwan da daddare zai zo mu tafi.

A nan Momi ta dubeni tace" Zahra kiyi hakuri da duk wata ƙaddara da ta sameki, kisa a ranki wata babba jarabawar zaki cinye" .

Na dube ta nace" Momi lafiya?" Zuciyata na bugawa

Ta ce" Zahra mijinki zai ƙara aure!" Atake naji wata mummunan faɗuwar gaba ina kallon Momina waca ta cigaba da cewa" Yarinyar nan Suhaila ƴar Baffan ku Aliyu ce zai aura, daman tun farko tana san sa kuma iyayanku na can Burda sun so haɗa auran, hukuncin Baffa ne yasa suka haƙura, sai yanzu da yarinyar ke neman illata kanta shine suka faɗawa Baffa,kuma ya amince nan da wata shekarar lokacin kin haihu lafiya sai a ɗaura musu aure, ance a faɗa miki ne domin ki sani karki ji a wani gurin domin dole zai dinga zuwa gurinta zance su ƙara fahimtar juna".

Cikin kuka nace "Momi wannan ai cin amana ne , daga auran namu , me yasa za ai min haka ? Me yasa ni ba a barni da wanda nake so ba?".

Tsawa daga bakin kofa ta Abbana naji, ya fara min faɗa yana cewa" mijinki yana da damar auran mata uku in yana da hali a rana ɗaya, dan haka ko kina so; ko baƙa so dole ayi wannan auran".

Ban san sanda bakina yace" wannan ai zalunci ne ba" ai kuwa ya kwaɗa min mari.

Babu yadda na iya nayi shiru da bakina, ya gama min faɗa Momi ma tayi nata san nan akace naje gurin Baffa.

Shima kuma zancan yayi min da fadan nayi hakuri ƴar uwata ce, zamuyi zaman mutunci.

Haka ya ƙara ci maganarsa ko tari banyi ba, bayan ya gama na mike ko su gywago banyiwa magana ba na tafi gidan mu.

Da dare Yaya yazo ɗauka ta nace bazan bishi ba.

Momi ta fara bani baki amma naƙi fafur har sai da Abba yazo ya marmare ni na biyo shi ina huci.

Tun daga wannan lokacin na daina sakewa da shi, zan dafa abinci amma babu wata alaƙa da zata haɗani dashi , tun yana jurewa har ya kai ga ya fara min magana, ni kuwa na buɗe baki nai masa rashin kunyar anci amanata kuma an zalunce ni.

Ni kaina wani zubin ina mamakin fushi da zafin zuciyata ko kuma dan ina da ciki ne tunda ance masu ciki na da saurin fushi.

Yaya Mahmud tun yana jurewa har ya kai ga ya samu babban Yayana Hafiz, yazo yayi min faɗa amma ban ji ba.

Yaya Hafiz ya samu Abban mu da zancan shima yazo ya min faɗa, shima taurun kaina yaƙi sawa na hakura musamman a kwanakin Suhaila ta dawo zuwa ta kawo masa abinci har gida , shi kuma dan ya kunsa min na gyara halina ya zaunar da ita suyi ta hira a gabana.

A haka wata rana na kamata nai mata ɗan bazan duka shi kuma na kwaɗa masa abu goshinsa ya kumbura.

Lamari ya kai har gaban Baffa kowa ya ban laifi, ƴan uwanmu kowa haushi na yake ji suka daina kula ni wasu ma.

Rana ta zame min zafi inuwa ƙunna, na fara dawowa tunanina na bawa mijina hakuri.

Muka fara dawowa kamar da, anan yake cemin nayi hakuri auran Suhaila wata kaddarace shi ba santa yake ba, amma halin da zata shiga yake dubawa da kuma mutuncin mahaifinta amma shi nice matarsa abar ƙaunarsa .

Da haka na fauwalawa Allah lamarina, domin cikina a lokacin ya shiga wata na shida ,haka na kira Abba da Momi na basu haƙuri, haka Baffa ma, na dai bawa kowa hakuri .

Duk suka haƙura, suna samun albarka da addu'ar zaman lafiya.

Amma wannan hakurin banyi sati acikin sa ba wata masifar ta same ni".

Sai ta fashe da kuka ta cigaba da cewa" safiyar asabar ce Yaya ya fita muna wasa da dariya wajan mintinan talatin , na shiga bayi da niyar yin bayan gida , kawai sai naji zafi ya dame ni nayi wanka baki ɗaya na, na fito daga ni sai tawul ina tsane jikina, kawai nayi arba da abinda ya rukita tunani na".

Kuka ya kufce mata ta cigaba da cewa" naga mutum akan gadon aure na , kuma ba kowa ne illah Faisal tsohon saurayina, tuni na kiɗime na fara ƙoƙarin komawa bayi amma sai naji an turo ƙofa , ina kallon gurin naga Yaya Mahmud ne ya dawo , jikina ya kama rawa ina girgiza masa kai, amma ina yaja kofar ya fita harda sa mukulli .

Free Page ya kare ga mai buƙatar wannan littafin zai iya yin magana ta wannan lambar:

***