Chapter 7
by @khairatup01
RUFAFFEN DUMA.
Ummulkhair S Panisau.
(Khairatup)
Wattpad:khairi_Muhd.
Arewabooks:Khairatup01
pg07
Hajiya Mujiba ɗawisu kenan sarkin ado. Ba a banza kika sace zuciyata ba.
Haj.Mujibat ta saki wani irin murmushi cike da gadara da kuma iyayi. "Nawan ni kaɗai,barka da fitowa annurin zuciyata gabaɗaya."
Alh.Barau da ƙaton tumbinsa ya samu wuri ya zauna kusa da Mujibat. Hannunta ya kamo yana murzawa sannan yace "An ɗauki tsahon shekaru bamu zaga ƙasashe ba matata. Abubuwa da dama sun sha min kai na. In har ba samun kujerar nan nayi ba ,hankalina ba zai kwanta ba nutsuwata ma ba zata dawo ba."
Hannunta ita ma ta ɗora kan nasa ta lumshe masa ido tayi alamar tabbacin ya kwantar da hankalinsa.
"Alhaji ai bana jin wannan lamari. Ni na sani da yardar Allah sai ka yi sai kuma ka je. Duk maƙiyanka sai dai su zama fadawan ka. Ai ba yau aka fara dama siyasar da kai ba wannan kafirar ƙwawalwar taka ai bata harbawar banza."
Ya kuma sakin wata iriyar dariya sannan yace "Bayan ke babu wanda ya san halina Mujiba. Shi ya sa nake ƙaunar ki,bainu ba kya tsufa."
A hankali ta jefa masa tambayar da take son jefa mai a siyasance.
"Ɗazu Ayan ya bugo mini waya ,yace ya kira ka baka ɗaga ba.Kamar dai akwai abinda ya faru yake son kuyi magana."
"Ban ga kiran nasa ba kuma. Dake hankalina na kan yaron nan Muhammad."
Tuni yanayin fuskarta ya sauya ta gyara zama tana muskutawa kaɗan tace "Shi ma ina da magana a kan sa ai. Yanzu haka zaka zuba masa ido yayi ta yin yadda yake so? Shekarunsa fa sun kai matakina ajiye iyali. Kuma ka kyale shi yana zaune can wani gida daban a wata unguwar,ba ka ganin cewa akwai wani abun da yake aikatawa? Sannan hakan fa zai iya zama illa ga siyasar ka."
Ya fitas da wani irin numfashi ya gyara zama yace "Kin fa san waye Muhammad! Kin kuma san halinsa tsab. Na rasa yadda zan yi da shi kuma na kasa lanƙwasa shi yadda nake so."
"Wai shin ma meya haɗa ku ne?"
Shiru yayi tsawon wasu lokuta kafin ya kalle ta yana murza zoben hannunta yace "Hajiya wasu labaran ba a tono su,idan aka tono su za a samu gagarumar matsala. Ki bar maganar kawai."
"Alhaji ai na ɗauka ni da kai babu ƴar wannan a tsakanin mu?"
"Haka ne,amma wannan ba zan iya faɗarsa ba. Ina fata za ki yi min uzuri kamar yadda kike mini a baya?"
"Haka ne. Amma dai ka same shi ka yi masa maganar auren sa da Nimra. Hajiya ta kira ni ina ganin kamar ma zuwa zata yi ne muyi maganar."
Alj. Barau ya miƙe tsaye yace "Kai haba! Ku bari a bi shi a hankula ni dai kun san haifar sa nayi kawai amma ban isa na saka shi ko na hana shi ba."
Hajiya ta buɗe baki cike da mamakin abinda ya faɗa.
"Kar kiyi mamakin hakan don hakan ba ɓoyyyen abu ba ne a wurin ki. Sunana ma don bai isa ya sauya ba ne da zai iya da kuma an yarda to tabbas sunan uwarsa zai saka "Maryam!"
Ambatar sunan Maryam kaɗai da aka yi sai da taji kamar an kwaɗa mata guduma a tsakar ka.
Har ga Allah ta tsani sunan matar ma. Duk da bata same ta a gidan ba kuma bata san ya akai Barau ya rayu da ita ba. A yadda ta ji kawai an wayi gari da rasuwarta ta kwanta lafiya amma aka tashi da rashin ta. An kuma ce wai zuciyar ta ce ta buga a cewar likitoci. Sai dai bayan matuwarta aka samu rashin jituwa da rabuwar kai tsakanin Muhammad da shi da Barau ɗin.Da kan sa ya nemi kuɗinsa da faɗi tashi da yana ma ɗan zama a gidan shekarun baya kuma ya kwashe komai na sa ya bar gidan ko da leƙe baya zuwa gidan. Yaranta biyu da Barau ƴan biyu ne ma da Ayaan da Ayra suna can Cairo suna karatu....tafi yayi mata a kan fuskarta yace "Ina kuma kika tafi Hajiya?"
Ta yi yaƙe tace "Ina nan kawai ina tuna baya ne."
"To a tuna lafiya sai na dawo ina da meeting da jama'a."
"Wai yau ne dama campgain din na ku ko?"
"Yau ne mana."
"Ai na sha'afa. To a dawo lafiya Allah Ya bada sa'a."
"Amin."
*
Yau Asabar ,garin Kaduna cike take da hayaniya. Murtala Square ta yi kaca-kaca da tutocin jam'iyya,da pastoci masu rubuce da kalmonin yabo,da kiɗe-kiɗen waƙoƙi masu ɗauke da taken "Barau ne sabon hasken Kaduna..." jama'a ana sowa ana tafi ana bin waƙar. Jama'a sai tururuwan taruwa suke yi daga kowanne loko da sako. Wasu da rawanin jam'iyya,wasu da riguna masu ɗauke da hoton Alhaji.Barau.
Cikin shiga ta farar shadda ɗinkin babbar riga mai ɗauke da adon sirfani mai ɗaukar ado. Tafiya yake cike da nutsuwa da fara'a a kan fuskar sa. Tafiya yake irin ta jarumi wanda jama'a ke jiran fitowarsa na tsawon shekaru.Sautin ganga da kaho suna ta ɗaukar hankalin mahalarta taron.
Kan kujera ya zauna a saman dandalin da zasu yi taron. Bayan ƴan jawabe-jawabe aka gabatar da shi. Miƙewa yayi tsayi ya ɗaga hannunsa sama . Tuni aka saki wani irin ihu da guɗa daga mata. Bakinsa ya ƙara girma saboda yadda ya ga jama'a sun fito duk don shi hakan ya faranta masa rai sossai.
Hannun dai ya kuma ɗagawa sama duka biyu. Sai kowa yayi tsit baka jin ko tari sai irin kukan yara daga nesa kamar ta jarirai da kuma na yaran da basu fi wattani biyar haka zuwa shidda ba.
"Ƴan uwana jama'ar jihar Kaduna" Ya faɗa muryarsa cike da kwarjini.
"Yau gani a gaban ku a matsayin ɗan takara ,amma fiye da haka na zo muku ne a matsayin ɗan uwa,ɗan ƙasa,ɗan gari,wanda yake son tsaya muku yake kuma son ganin ci gabanmu gabaɗaya daga ni har ku."
Sai jama'a suka amsa da ihu da sowa ana kiran "Barau ! Barau ! Barau!"
Dogon numfashi ya ja,sannan ya fara lissafa alƙawarrukansa cike da salo mai kama da labari ko jan hankali.
"Nan da kuka gan ni kafin na zama Alhaji.Barau. Asalina ɗan talakawa ne,na taso daga cikin talakawa, na san raɗaɗin rashin makaranta. Wallahi idan kuka bani dama,Kaduna za ta zama garin ilimi. Zan gina makarantu a karkara,za mu ɗauki nauyin ƴa'ƴan talakawa,kuma ba wani yaro da zai tsaya a titi yana bara a maimakon karatu." Ya ɗan dakata ya tsaya ya kalli wajen da wasu dattawa ke zaune,ya cigaba da magana.
"Na san da batun rashin lafiya. Na san yadda ake kwana a asibiti babu magani. Na rantse,idan Allah Ya bamu nasara a wannan tafiyar ,babu wata uwa da za ta sake kukan rashin magani saboda rashin abin siyan maganin. Za mu gina asibitoci,za mu kawo likitoci ƙwararru, za mu samar da magunguna kyauta."
Taro ya ɗauki ihu da sowa. Wani matashi daga gefe ya ɗaga hannu yace "Ina da magana."
"Ina sauraron ka samari."
"Batun aikin yi fa ga matasa?"
Alh. Barau ya juya gefe,ya juya hagu,ya juya dama ya kalli matasan nan kaf na cikin taron ,ya ɗaga hannunsa sama yace "Matasa ku sani ku ne garkuwar jihar nan. Za mu buɗe masana'antu,za mu ba ku horo,ku zama masu kasuwanci ba masu jiran aikin gwamnati kawai ba.Matasa za su zama ƙarfin tattalin arziƙin Kaduna!."
Tuni aka koma magana ƙasa-ƙasa cike da ƙus-ƙus. Maganganu suka zama kamar ruwan sama da ya daɗe yana jiran ya zubo.
Ya ci gaba ganin kamar alƙawarukansa na samun ƙarbuwa a zukatan mutane.
"Ku bani dama,ku bani goyon baya,mu kawo ƙarshen yunwa,mu gina Kaduna da hannuwanmu. Talaka shi ne ginshiƙin ƙasa ,kuma ni zan kasance tare da ku daga farko har ƙarshe."
Ganguna suka soma bugu,tururuwar jama'a suka mamaye wajen,mata da maza,dattawa da matasa,suna ɗaga hannayensu suna rera waƙar "Barau 2012! Sabon hasken Kaduna!"
Alhj. Barau da farinciki da walwala ya shiga motarsa yana ta ɓaɓaka dariya. Ya kalli P.A ɗin sa yace "Wato su mutane har yau ba zasu waye su yi tunani mai kyau ba. Kullum da sabon abin da muke cin su da yaƙi su kuma yarda da mu su dangwala mana ƙuri'a. Da ka yi harbi a daidai inda yake musu ciwo shi kenan magana ta ƙare."
Ai Alhaji bana jin ka na san zaka lashe ƙuri'un nan da yardar Allah! Dama ga shi Oga Muhammadu ma yana taimakawa talakawa da matasa sosai ,ko don shi ma zaka samu yadda kake so. Ka yi bacci kayi milo ka ɗaga lemo mai sanyi ka kora babu ja babu haufi Kaduna taka ce wannan karon.
Shi yasa nake son ka P.A ,ka san daidai ka san kuma ta kan siyasa zaka yi albarka mutumin nan.
Suka kyakyata da dariya duka.
*
Ban daga ina ko ta ya aka kawo mini wannan baƙar abayar ba mai cike da ado na duwatsu tana walwali tamkar wanda aka shirya mata tarin duwatsun nan na swarvoski!
Ɗaga rigar nayi na karata da jikina Ya subahanallah! Ta yi nasarar hawa kan farar fatata.
"Tsayin yayi miki?"
Ta juya da sauri ta kalle shi. Bata san yana wurin ba. Ƙasa tayi da kanta tace "Tayi kyau. Na gode!"
Lumshe idanuwansa kawai yayi ya juya sai kuma ya tsaya yace "Abuja zan tafi. Ki yi sauri sai mu sauke ki a gida."
"Babu kowa a gidanmu...."
"Kar ki damu mahifiyar ki an dawo da ita, kuma an gyara dukanin ɓarnar da aka yi muku, sannan na saka muku mai gadi mai kyau. Babu abinda zai faru in sha Allah! Kawai ki kula ki maida hankalinki ki san irin takun da za ki na yi ,ba a kowanne wasa ne ake samun nasara ba."
"Na gode!"
Yayi gaba kawai abin sa.
A gurguje ta shiga tayi wanka ta shirya. Wani flat ɗin takalmi ta gani baƙi shi ma ta saka. Ba tare da ɓata lokaci ba ta fita daga ɗakin ta ja ƙofar ɗakin tayi waje.
Komai tsaf-tsaf.
A bakin mota ta ga direba a tsaye, yana ganinta ya buɗe mata gidan baya ta ɓarin dama ta shiga ta zauna. Ƙamshin turaren sa kawai ta ji ta gano tare zasu yi tafiyar dai kamar yadda ya sanar mata. Tashin motar yayi suka fara tafiya.
Ta wutsiyar ido take kallonsa yadda yayi kyau cikin suits baƙaƙe da farar t-shirt a ciki mai dogon hannu. Agogon hannunsa ma Rolex ne.
Cikin ranta tace "Wai ma mutumin nan baya saka kowanne kaya sai wannan baƙar suit ɗin ne?"
"Kika ce?"
Da sauri ta juya ta kalle shi tana zare idanuwa "Ba dai ya ji ni ba?" Ta tambayi kanta.
Cikin i'ina tace "Ban ce komai ba, ba komai."
"Oh!" Kawai ya faɗa. Ita kuma ta runtse idanuwanta biyu ta ciji leɓɓanta na ƙasa a rai tace "ki nutsu mana Maryam."