Chapter 8
by @khairatup01
RUFAFFEN DUMA.
Ummulkhair S Panisau.
(Khairatup)
Wattpad:Khairi_Muhd.
Arewabooks:Khairatup01.
Pg8.
"Ban yi tsamanin haka kake ba Wallahi!" Ta faɗa kaifin idanuwanta a kan shi.
Ya juyo da kan sa yana tattare girarsa cike da mamakinta yace "Me kika zata to? Mugun attajiri ? Mai kuɗi masifaffe ko marar zuciya?" Ya tambaye ta kaitsaye.
Dariya tayi ta ce "ku san haka ne. Ni fa tun ran da na fara ganin ka nake mamakin halin ka. Na ɗauka dan a gaban kyamara ne ko kuma don muna interview ne amma sai ka bani mamaki jiya zuwa yau."
Ya maida kansa kan Tab ɗin hannunsa yayi murmushin gefen baki kawai. Yace "kuma yanzu me kika gani?"
Ta yi shiru kawai, zuciyarta na bugawa. Ita fa ƴar jarida ce,aikin ta shi ne ta rubuta, ba ta faɗaɗa zuciyarta ba.
"Yanzu na ga wani babban mutumin da ya bani mamaki."
Daidai nan dereba ya tsayar da mota. A hankali ta ɗaga kai ta kalli ƙofar gidansu lokaci guda ta sauke ajiyar zuciya kuma. Har ta sa hannu zata buɗe ƙofar motar sai ta ji yace da ita "Za ki iya cin abincin daren gobe da ni?"
Ta juya ta kalle shi idauwasu cikin na juna. Bata ji tambayar kamar ta neman yarda ba ta ɗauki tambayar kamar umarni ne yake bata.
Ta ɗauke kai haɗe da buɗe bakinta tana son tayi masa gardama ,sai kuma ta tuna da iyaka tsakaninta da rayuwarta. Sai kuma zuciyarta ta riga ta, bakinta ya buɗe tace "Abinci kawai?"
Ya kalli cikin idanuwanta,bai kawar da kallonsa ba. "Ba yanzu ba,gobe zan aiko direba ya zo ya ɗauke ki."
Daga nan ya yi wa direba alama da ya ja su tafi. Nan suka bar ta da mamaki. Tunani ta soma yi. "Cikin shiru mai cike da nauyi ta fahimci cewa haka soyayya kan fara ba tare da tsawa ko kuma wuta ba,sai dai da tambaya,kallo,da kuma alƙawarin cewa labarin bai ƙare ba tukuna akwai sauran al'amari a gaba." Haka ta ja ƙafar ta zuwa cikin gida.
Tana shiga ta hango Mama zaune kan kujera ta yi zugum!
"Mama.....Mama!"
Mama ta juyo ta ɗago kanta tana kallon fuskar ƴar ta ta. Miƙewa tayi tsaye ta baza mata hannunta biyu tace "Maryama!"
A hankali ta ƙarasa ta shiga cikin hannun ta. Mama ta sa hannu biyu ta rufe ta ruf. Tare suka saki kuka. Aka rasa mai rarrashin ɗan uwansa.
"Mama kiyi haƙuri ,ki yafe min Mama. Ni ce na janyo miki. Ba zan kuma shiga abinda zai saka ki shiga matsala makanmaciyar wannan ba."
"Aa Maryama. Ba laifi ki ba ne. Allah Ya tsara hakan. Alhamdulillahi na dawo cikin kwanciyar hankali da lafiyata. Basu yi min komai ba cikin hukuncin ubangiji."
Maryam ta sauke ajiyar zuciya ta saki Mama. Nan suka zauna suna bawa juna labarin daren jiya.
"Mama baki gane komai ba a wurin da aka ajiye ki?"
"Ban ga komai ba. Hasali ma idanuwana a rufe suke da baƙin ƙyalle. Babu abinda na gani."
"Mama ki tuna ko za ki tuno wani abin da zai iya taimaka min."
"Maryam ina ƙara gaya miki don Allah ki rabu da wannan aikin. Ni gwara ki dinga ɗauko labarai muna ganin ki a akwatin talabijin ba wai ki dinga yin rubutu a kan masu laifi ba. Bani da ƙarfin zuciyar da zai saka na jure rashin ki bayan rashin babanku da yayanki ba."
"Mama kece ƙwarin guiwa ta, in na rasa ki ba zan jidaɗin rayuwata ba. So nake ki zame min ƙarfi ba hanyar karaya ta ba. Mahaifina ya rasa rayuwarsa akan faɗa da ƙarya da kuma son gaskiya. Abin kunya ne a gareni na koma gefe nayi kallo kawai ba alhalin ƙasata na buƙatar gudunmowata. Mama ina jin a jikina akwai wani babban al'amari da yake shirin faruwa ko kuma yake faruwa."
Hannun Mama ta ɗora akan Maryam tace "Allah Ya miki albarka ,Ya baki ikon kawo ƙarshen su amin."
"Amin Mama.Yanzu na samu ƙwarin guiwa."
*
Bayan saukarta ya ajiye tab ɗin hannunsa a gefe. He was like me yayi ne haka wai? Ya rasa wane irin abu ne yake jan sa ga Miss Maryam. Jingina yayi da kujerar ya kwanta ya kulle idanuwansa. Abubuwa da dama suna damun sa a cikin ran sa, ya rasa ta ina zai ƙulla ma. Fuskar mahaifiyarsa yake hangowa yadda idanuwanta suka firfito waje suka ƙara girma, bakinta a buɗe tana kokawa da numfashin ta. Da sauri ya buɗe idanuwansa yana jin wani abu na taso masa a rai. Tuni idanuwansa suka sauya kala ma. Ba ya bacci yadda ya kamata kullum hoton da ke yi masa yawo a idanuwansa kenan. Wayarsa ce ta soma ƙara a hankali ya danna abin amsa kira yace "Hello" bai ma san me kiran nasa ba don bai duba ba.
"Yaya Muhammad!"
A hankali ya haɗi yawu yace "Uhm ,Ayra."
"Yaya an kama Aayan!"
"What?"
"An kama shi a nan ya yi tuƙin ganganci har ya ɓata wa wasu shago na bakin hanya, an ci tarar kuɗaɗe yana hannun ƴan sanda yanzu haka. Ina ta kiran Daddy amma bai ɗaga ba wai yaje campagain. Mummy kuma na kasa gaya mata an kama shi."
"Calm down ! Zan zo amma kar ki bari hawayenki su zuba akan Aayan. Baya jin magana ko kaɗan."
"Tam Yaya."
"Kin tabbata iya ɓarnar ce ba a kama shi da ƙwaya ba ko shi ya sha ta ba?"
"Yaya....ban..."
"Na fahimta baya cikin hayyacinsa."
"Eh Yaya."
"Zan zo amma ba yau ba yanzu haka zan yi wata taiyar ne. Daga can zan wuto, zan yi magana da wani abokina a can ya samar masa lawyer kafin na iso. And kamar yadda na faɗa bana son kukan ki akan wancan stuid twin ɗin naki mai kunnen ƙashi."
"Ba zan yi ba Yaya."
"Good!"
Yana ajiye wayar ya sauke glass ɗin,yana kallon waje. Daga baya kuma ya maida glass ɗin
ya ɗauko wayarsa ya cigaba da dannawa.
Ya gaji da ɗabi'u da hallayen Aayan. Yaron baya jin magana. Komai da ruwan shi. Iya cases ɗin da yake shiga na sa yana ɓarnar da kuɗinsa ko ubansu Alh.Barau baya yi. Saboda shi Alh. Barau mutum ne mai mamaƙon masifa. Yana da son abin duniya sosai. Cairon ma da ya kai su saboda kar Aayan yayi wani abu marar kyau a nan ya shafi takararsa. "Slefish man." Ya faɗa a hankali yana murza yatsunsa. "Saura minti nawa mu isa ne?"
"Yallabai mun kusa in sha Allah!."
Tsaki yayi a hankali ya kuma zaro wata wayar ya nemo wata lamba. Bugu biyu aka ɗaga wayar bai tsaya wani gaisuwa ba yace "Zan turo maka da wata lamba ka yi magana da su ina son a shiga case ɗin ƙanina ne Aayan Barau a can Cairo."
"ok sir!."
Yana gama faɗa ya kashe wayar ya ajiye a gefe kawai. A kan idonsa ya ga kiran Nimra na shigowa amma ya ƙi ɗagawa. Kawai munanan hotuansu na baya ke masa gizo a idanuwansa. Tsaki ya saki tuno abinda ya faru tsakainsu wattanin baya kawai yake yi. Ya tsane ta sosai baya son ganinta ma. Amma ta kasa ganewa ta dame shi ta shigar mai cikin rayuwa da yawa.
Da ya gaji da kiran da take mai ya ɗaga a fusace yace "In kika kira sau biyu ba a ɗaga ba ba zai sa ki gane ba a son ɗaga wayar ki ba ne?"
"Muhammad wai me yasa duk ka canja bayan wancan abinda ya faru na ga da ba iya laifi na ba ne hadda na ka and besides ma abin nan ya wuce babu wanda ya san ayi fa."
"Are you dumb or what ? Kin san me kike faɗa kuwa? Kin san ko girman abinda kike ganin ba wani abu ba ne? Look Nimra ki shiga sabgar ki ki kyale ni."
"Muha...." kit ta ji ya kashe wayar. Ta bi wayar ta da kallo a hannunta bakinta a buɗe. "Waya ya kashe min wai?" Ta tambayi kanta. Bata da amsa cikin fushi tayi jifa da wayar hannunta ta bugu da bango wayar ta tarwatse.
Yana ajiye wayar ya sa hannu ya dafa goshinsa ya murza yana jin wani irin ciwon kai. Matsaltsalu basa ƙarewa wa ɗan'adam a duniya. Shi kam ya gaji ya far kai wa maƙura kansa zai fashe zuciyarsa zata tarwatse. Gani yake kamar shi kaɗai ne mai matsala a duniya.
*
Miss Maryam muna yi miki fatan alkairi da kuma murnar dawowa bakin aiki cikin ƙoshin lafiya.
Na gode!
Kan kujerar ta zauna. Ta kunna laptop ɗinta sai taga ma kamar an yi mata amfani da ita. Murmushi tayi tana nazari.Cikin ranta kuwa cewa tayi "A banza babu abinda zaku samu a kan laptop ɗina in kuna ganin kuna da wayo to ni ta fi ku wayo. A kafta."
Kofin shayi ya tura mata gabanta. Ɗaga kai tayi ta ce "Thank you."
"You are welcome. Ya kike jin jikin na ki?"
"Alhamdu lillahi. Da sauƙi. Yaya kwana biyu?"
"Gamu fa muna ta aiki."
"Ah! Ko zan iya tambayar ka Smith?"
Ya kurɓi ruwan shayin yace "Uhm ina jin ki."
"Waye Paul Stone?"
Yayi saurin sa hannunsa akan lebbansa ya kalli hagu da damansa ya kuma juyowa ya kalle ta da sauri yace "Miss Maryam , me yasa kike da taurin kai ne?"
"Ban gane ba?"
"Ki bar maganar nan ba a nan zamu yi ta ba.Yin maganar a nan zai iya janyo mana gagarumar matsala."
"Amma..."
"Ki yi haƙuri ki bar maganar zamu yi ta amma ba a nan ba kuma ba yanzu ba."
"To ina sauraron ka."
"Maryam Yallabai na kiran ki." Faith ta faɗa tana kallonsu duka su biyun.
Tashi tayi ta shiga ofis ɗin Yallabai ɗin.
*
Ɗakin yayi shiru na wasu sakanni. Ba abinda ke shiga ido ko ɗaukar hankali kamar wata fitila guda ɗaya mai walƙiya. Bayan ya gama taron siyasa ya tafi don zama da aminttacensa Alh. Waziri. Yana ɗaya daga cikin masu ba shi shawara. Alh. Barau ya zare babbar rigarsa,ya buɗe wata jaka a gefensa,y fito da wasu takardun kwangila da kuɗaɗe. "Waziri,yau da gobe idan jama'a suka bani mulki,sai ƙofoffin kasuwancinmu sun bunƙasa Wannan siyasar ba komai bace face garkuwa. Idan na hau kujerar mulki,babu wanda zai iya bincikar dukiyar da na mallaka."
Waziri yayi dariyar ƙeta yace "Haka ne. Amma akwai matsalar wasu gidan jaridu da suke son saka mana ido. Suna ƙoƙarin bincikar tashar jirgin ruwan nan da ka mallaka a ɓoye."
Dariya ya saki. Ya ci gaba "Ɗan jarida ai sambaɗe shi ba abu ba ne mai wahala a wurina. Ba sa gabana kafinsu anyi wasu a baya kuma sun ƙarbi sakamakonsu."
"Haka ne."
"Waziri bara na gaya maka abinda baka sani ba. Duk wanda ya yi ƙoƙarin tona asirinmu, ko ya shiga kabari kafin lokacinsa,ko ya bar ƙasar da ƙafafunsa. Ka tuna fa ba ni ƙaɗai nake buga wasan ba,bani ne shegen ba akwai manya a baya na masu ruwa da tsaki. Kaga kuwa idan na faɗi to bani kaɗai zan faɗi ba da yawa zasu faɗi tare da ni. Wannan kuma ita ce asalin ainihin siyasa. "
Miƙewa yayi ya ɗauko wani kofin gilashi ya zuba giyarsa a ciki ya tsaya cak kuma yana kallon mudubi, idanuwansa suka ƙanƙance ya saki wani makirin murmushi ,ya shafa gemumsa yace "Hhh!Mai ceton jama'a. Su fa jama'a abinda suke gani daban ne. Suna min kallon mai cetonsu,alhalin ni kuma ni ne silar halakarsu."
Ya kalli Waziri shi ma Waziri ya kalle shi a tare suka ɗaga kofin giyar suka ɗaga sama alamar yabawa.
*
"Yaya aka yi ne Abdurrahman?"
"Yallabai sai fa ka zo."
"Sai na zo kamar yaya? Mai amfanin ka in har sai na zo?"
"Afuwa Yallabai ba laifina ba ne."
Sauke ajiar zuciya, Yayi siririn tsaki yace "Bana nan amma zanyi ƙoƙarin ganin gobe na shigo ya ƙara haƙuri kawai. Illar rashin jin magana kenan."
Abdurrahman yace "Yallabai,haƙuri zaka yi yaro ne. Ya samu wasu abokai ne suke ruɗarsa."
"Ku jira kawai kamar yadda na faɗa,ina gamawa da meeting ɗin zan taho."
"Allah Ya kawo ka Yallaɓai."
Mutane na masa kallon hamshakin ɗan kasuwa kuma mai kuɗi,hakan bai hana ya baranta ga sauran mutane ba.Babban burinsa ya kafa tarhi a kasuwanci,ya kai ko ina
ana zancen shi.
Zauren taron a cike yake maƙil da manyan ƴan kasuwa da attajirai daga ƙasashe daban-daban kamar yadda suka saba zaman. Muhammad ya gyara zamansa cikin shigarsa ta rai da rai ,kwarjininsa ya kuma bayyana. Numfashi ya sauke ,ya kalle su ido cikin ido sannan ya soma magana.
"Ina miƙo gaisuwa ta gare ku abokan cinikkaya. Na tsaya a gaban ku don samar mana da mafita a kan matsalar jigilar kaya ta duniya.Ina son mu ƙiƙiri Smart Logistics Alliance.Dadalin da zai haɗa kamfanonin sufuri,masu kaya,da kwastamomi a waje ɗaya. Al zai yi mana hasashe na buƙatu,blockchain zai tabbatar da gaskiya a farashin,kuma za a mu gina ɗakunan ajiya a matsayin birane na duniya misali a Dubai,Singaphore,Lagos da shanghai."
Wani ɗan ƙasar Dubai yace "Wannan ra'ayin naka zai iya juyar da harkar sufuri gabaɗaya. Amma kana son ka riƙe kaso nawa a ciki?"
Kaitsaye Muhammad yace "50%"
Mutumin yayi murmushi yace "Kana nufin kana da daidaito da mu wurin yanke shawara."
Muhammad ya gyaɗa masa kai don ba da tabbaci. "Hakan shi ne tunanina. Na shafe shekaru ina tunani akan hakan ,ka ga kuwa dole ne na riƙe kaso mai tsoka. Wanann ba ƙaramin aiki ba ne,amma idan kun amince da hakan ,amma ku tuna cewa ba iya ribar zamu samu ba,za mu sauya rayuwar ƙanan ƙasuwanci a faɗin duniya."
Shiru ya ratsa ɗakin. Suka kalli juna.
Shugaban kwamiti daga China yace "Mun amince da shirin ,amma ba za mu baka 50% ba sai dai 40% zamu riƙe 60%. Za ka samu kujerar yanke shawara a majalisar gudanarwa, amma rinjayen ra'ayi zai kasance a hannunmu yake."
Muhammad ya san dama za ayi hakan, kuma hakan yake son ayin saboda samu cikar na shi burin.
Leo yace "Me ka ce Muhammad Deal on?"
Muhammad Ya kalle shi yace "Na ji. In har 40% zai ba ni ikon kare wannan shirin,na amince amma ina da sharaɗi."
"Meye sharaɗin?"
"Sharaɗin shi ne za ku sanya hannun jari wajen gina ɗakunan ajiya a ƙasata musanmman a Lagos da Kano. A karo na farko Najeriya za ta zama cibiyar farko,kafin na ku su biyo baya. Idan kun amince da hakan shi kenan deal on."
Gabaɗaya manyan attajiran suka sa dariya haɗe da tafawa Muhammad. Basirasa da wayonsa suke ƙara cusa shi a cikin su.
Shugaban kwamitin Amuruka yace "Ka yi magana kamar zakin da ya san abincinsa. Mun yarda muna tare da kai ,Muhammad Sageer." Ya kira sunan cike da gwaranci.
A nan suka sanya hannu,aka rufe yarjejeniyar. Muhammad ya san wannan rana ce da za ta canja hanyar kasuwanci a duniya kuma ya yi farinciki da Najeriya zata fara anfanuwa.
Daga nan ya nufi airport don zuwa Cairo wurin Aayan.