Chapter 41-42
💫 *RAMIN ƘARYA....* 💫
_WRITING BY AMANAR COOL_✍️
*YOUNG TALENTED WRITER'S ASSOCIATION (YOTA/021)*
Page 41&42
___________Mama kuwa kuka take yi sosai, irin kukan nan mai taɓa zuciya, tunda Gwaggo ta ja Afnan ta fita da ita, gaba ɗaya ta rasa me yake yi mata daɗi. Baba ne ya shigo ya tarar da ita cikin wannan ya na yin.
Zama ya yi, ya rasa me zai ce mata, domin shima abin na damunsa a zuciyarsa.
Kallon Mama ya yi da ta ke kuka ba tare da ta kula shi ba, tabbas tunda har Amina ta kasa danne kukanta ya san wannan al'amarin ba ƙara min taɓata ya yi ba. Duk haƙurin ta amma yau ita ce ke wannan kukan.
Ya na so ya bata haƙuri amma ya kasa, gashi dai kukan na ta ba ƙaramin ɓata masa rai yake yi ba. Ganin ba daina kukan za ta yi ba, shi kuma ya na son bata haƙuri amma kamar an ɗaure masa baki ya kasa magana
Ya sa ya miƙe ya bar mata ɗakin.
Ƙara fashewa tayi da kuka, ta ce "Ya Allah ka dube ni, Ubangiji ka shiga lamurrana da na ƴa,ƴana. Ya Allah ka kula mini da ƴata. Allah kashiga lamarin ta, ka kare ta daga dukkan sharri na mutum da aljan".
Ta ƙare addu'ar ta na kuka ba na wasa ba.
Ikon Allah ne ya kai Haidar gida, da ƙyar ya fito da ga cikin napep ɗin ya shiga gida, babu kowa a tsakar gidan Umma na ɗaki, kai tsaye ɗakinsa ya buɗe ya shiga kwanciyar rub da ciki ya yi, ba abin da ke yi masa yawo a idanuwansa sai fitowar da ya ga an yi da Afnan ta na kuka an sakata a mota, kenan da gaske an yi mata aure? Ji ya yi gaba ɗaya dubiyar na juya masa, ya rasa inda zai saka ransa, ya ji sauƙi da raɗaɗin da yake ji, ƙirjinsa zafi yake yi masa ba na wasa ba, zuciyasa na bugawa da ƙarfi, wata irin fitinaniyar soyayyar Afnan yake jin ta na barazanar tafiya da numfashinsa.
Umma jin motsi ya sa ta fitowa
Ɗakin Haidar ta gani a buɗe, da mamaki ta ke bin ɗakin da kallo, ta na tunanin me ya dawo da shi gida a irin wannan lokacin, kuma bai nemeta ba.
Ɗakin ta nufa da sallama ta shiga, a kwance ta ganshi, ta daɗe tsaye ta na ƙare masa kallo, da ta ga alamar bai ji shigowar ta ba, dan ko sallamar da ta yi bai amsa ba, ya ta ce
"Haidar"
Shiru bai amsa, kuma bai motsa ba.
Ta kuma ce wa
"Haidar" nan ma Shiru
Ƙarasawa tayi ta bubbugi ƙafan shi, ta ce
"Haidar" da ɗan ƙarfi, sai a lokacin ya motsa da ƙyar.
A hankali ya juyo, tare da buɗe idon shi ya sauke su akan Umma da ta tsare shi da ido, ta na nazarinsa.
"Haidar lafiya ka ke kuwa? Me yake damunka na ga ka dawo gida yanzu? Bayan ba lokacin dawowarka ba ne".
Haidar ya furzar da iska mai zafi sannan ya ce "Umma ba na jin daɗi ne"
"Ashsha subhanallah, me yake damunka? Kuma shi ne zaka shigo baka neme ni ba?"
"Ki yi haƙuri Umma ba na son ɗaga miki hankali ne".
"To kasha magani ne?"
"Eh nasha shi ya sa na dawo gida na ɗan kwanta ko zan samu yin bacci". Da ido kawai Umma ke binsa. Ta mugun tausayin ɗan na ta, ta na son yin magana da shi amma ganin ba shi da lafiya yasa ta ƙyale shi. Ta ce "To Allah ya baka lafiya, ka samu ka yi bacci ɗin, in sha Allah ciwon kan zai ragu". Tashi tayi ta fita, ta na fita Haidar ya sauke a jiyar zuciya. "Ya Allah kai ka saka mini son wannan yarinyar a zuciyata, Ubangiji ka kawo mini sauƙi da salama, Allah ka kawo mini mafita.
Sai bayan la'asar motar su Afnan ta isa, a ƙofar gidan mai gari ta tsaya. Har lokacin Afnan ba ta daina zubar da hawaye ba.
Kawu Sanusi ya fara fitowa, ya na gaisawa da mutanen da ke gurin.
Sauran matan fitowa suka yi, Aunty Murja ta ja hannun suka nufi cikin gidan, da murna aka tarbesu, kai tsaye ɗakin Asabe uwar gidan mai gari aka wuce da Afnan. Saura matan kuwa shimfiɗa a ka yi musu, sannan aka a jiye musu abinci shinkafa da wake, aka haɗo musu da fura tasha nono.
Aka zubawa direba shima aka kai masa
Afnan ma an kai mata na ta, sai dai ko kallon shi ba ta yi ba, daga ƙarshe ma tura fuskarta tayi cikin hijabi ta ci gaba da kuka.
Kawu Sanusi ko fada ya wuce ya gaisheda mai gari, suka gaisa da sauran jama'ar wurin
Mai gari ya ce "Sanusi ya hanya? Sannuku da ƙoƙari kun sha tafiya, ita amaryar tawa an shiga da ita cikin gida? Ko da yake mijinta ya yi mini ƙwace" ya yi maganar ya na murmushi
Kawu ya yi dariya ya ce "Eh an shiga da ita ciki"
Mai gari ya ce "To ma sha Allah, Allah ya sanya alkhairi a cikin wannan auren, ya kauda fita, sarkin fada ga amana nan an kawo muku Allah ya taya ku riƙo, za ta zauna a gidana zuwa jibi in kun kammala gyaran sai ta tare a ɗakin ta".
Da Amin aka amsa, sarkin fada ya ƙara yi wa kawu godiya
Sannan mai gari ya tashi domin shiga cikin gida su gaisa da mutanen. Shiga ya yi suka gaisa cikin girmamawa.
Ya ce "Ina amaryar tawa ne?"
Asabe ta ce "Ta na ɗakina".
Ya ce "To shikenan bari na ƙyaleta yanzu zuwa anjima ma gaisa".
Kawu Sanusi ya ce idan sun kammala su tashi kar dare ya yi musu a hanya.
Aunty Murja da Bilki suka shiga ɗakin da Afnan take, nan suka tarar da Maryam da ita suna kuka, zama suka yi suna rarrashinta tare da ba ta haƙuri, Aunty Murja ta ce "Afnan ki yi haƙuri, ki ci gaba da addu'a in sha Allah za ki ji daɗin haƙurin da ki ka yi, ki rungume mijinki, ki yi masa biyayya, domin aljannarki ta na ƙarƙashin ƙafarsa, ina son ki rungume ƙaddararki Afnan, haka Allah ya ƙaddara auren ki zai kasance, dan Allah ka da ki saka damuwa a ranki, gudun jawowa kanki wata matsalar, ki zauna da kowa lafiya, ki yi wa iyayen mijinki biyayya, sannan ka da ki walaƙanta danginki na nan".
Kuka sosai Afnan ke yi kamar ranta zai fita, haƙuri ina Bilki ta cigaba da bata, sannan suka ce Maryam ta tashi su wuce ana jiransu, jin hakan ya ƙara ɗaga hankalin Afnan ta rirriƙe Maryam ta na kuka
Asabe ta shigo ɗakin ta ce "Wai ku fito ana jiranku, sauran matan har sun fita waje"
Aunty Murja ta ce "To shikenan mun tsaya bata haƙuri ne, gata nan sai ku cigaba da bata haƙuri da rarrashinta, sannan idan aka ji tayi ba dai-dai ba dan Allah ku tsawatar mata".
Asabe ta ce "In sha Allah zamu yi iya ƙoƙarin mu".
Miƙewa suka za su fita Afnan ta miƙe ita ma
Kallonta suka yi Bilki ta ce "Ina kuma za ki je Afnan?"
Cikin kuka ta ce "Biyar ku zan yi Inna, dan Allah ku koma da ni". Tayi maganar ta na ci gaba da kuka.
"Haba Afnan ina kuma aka taɓa yin haka? Ki dai yi haƙuri, in sha Allah nan da kwana biyu zamu dawo".
Ƙememe Afnan ta ce ba za zauna ba, sai da aka kira kawu Sanusi ya ce su wuce, dan ubanta ko ƙofar ɗakin nan ta ƙaraso sai ya saɓa mata.
Riƙe Maryam tayi ta na kuka sosai ta ce "Dan Allah Maryam ke kar ki ta fi ki bar ni".
Maryam ma riƙe ta tayi ta ce ba inda za ta je ta bar ta, takaici ne yasa kawu ya ce "Ku zo mutafi idan ta iya ita ma ta tabbata a nan ɗin".
Ba yadda ba a yi da Maryam amma ta ce ba za bisu ba, mai gari ya ce "Su yi tafiyar su zuwa gobe ko jibi dai-dai sun samu nutsuwa sai ta koma, haka aka yi su kawu suka kama hanyar komawa gida.
Afnan ganin Maryam a kusa da ita ya ɗan kwantar mata da hankali, ta ɗan saki jiki har suka samu cin abinci.
*********
Gaba ɗaya Mudan ya rasa suku ni a zuciyarsa, soyayyar Hasina ce tayi masa babakere a zuciya, baya ganin kowace mace face ita, komai yake yi tunanin ta ne a zuciyarsa, ge ɗaya ga fitanar Huda kullun da sabuwar fitana da tijarar da take zo masa da ita, ya rasa yadda zai da ita, gashi ya na kokwanto akan cikin da take iƙirarin ta na da shi, shi fa baya jin idan ma gaskiya ne ta na ɗauke da cikin ya kasance nasa ne. Dan baya jin iya shi kaɗai take bi.
Tashi ya yi ya shiga toilet wanka ya yi a gurguje, ya shirya, makullin motar shi ya ɗauka ya fito, in da motar shi take ya nufa, ya ja ya bar gidan. Kai tsaye gidan Turai ya nufa.
Turai na zaune a falo, ita da wata dillaliya, sai Hasina dake saman kujera ta ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya ta na taunar cingam.
Mudan ya yi sallama ya tare da afkowa cikin falon kamar wanda aka je ho.
Turai ta ce "A'a Mudan yau kaine a gidan namu babu sanarwa?"
"Eh Momy ni ne, fatan na same ku lafiya?".
Ya yi maganar ya na ƙuwara Hasina ido, da tayi kamar ba ta ganshi ba. Alhalin hankalinta na kansa kawai mazewa ne tayi.
"To ma sha Allah, ka ce yau zumuncin ne ya motsa? To ya ka baro mini Mamin taku da Huda fatan su na lafiya?"
"Lafiya ƙalau suke, sunce ma a gaisheki".
Murmushi Turai tayi jin abin da Mudan ya ce, ta sallami dillaliya sannan ta dubi Hasina ta ce
"Ke Hasina baki ga yayankin ba ne? Na ga ba ki gaishe shi ba".
Sai a lokacin ta ɗago ta dube ta ce
"Barka da wannan lokacin Ya Mudan"
"Yawwa ƙanwata barka ya ki ke?"
"Alhamdulillah" ta bashi amsa .
Turai ta kuma cewa "To ki kawowa Yayan na ki ruwa mana"
Miƙewa tayi ta je ta ɗakko masa ruwa da kofi sannan ta zuba mishi ta miƙa masa.
Karɓa ya yi ya sha ruwan kaɗan
Turai "Mudan jira ni zan ɗan shiga ciki".
"To Momy ba damuwa, sai kin fito". Tashi tayi ta bar falon ta shige bedroom ɗin ta. Ya maida dubansa ga Hasina ya ce "Ƙanwata hutawa ɗai ake yi?".
"Eh" ta bashi amsa ta na ɗan basarwa
Ƙare mata kallo ya yi ya ce "Ƙanwata wai ko na yi miki wani laifi ne? Ina magana ana amsa mini sama sama". "A'a, ni kuwa me za ka yi mini kai da ba guri ɗaya muke ba". "To ai na ga ina magana ne ana basarwa".
"No ba komai kar ka damu, ya Huda?"
"Ta na nan ƙalau".
"Ok"
Mudan ya yi gyaran murya ya ce "Hasina wurinki fa na zo"
"Wurina kuma? To Allah yasa ba wani laifin na yi ba?"
"Ina ai ke ba kya laifi, komai ki ka yi dai-dai ne, Hasina magana nake so muyi mai muhimmanci, wato a gaskiya ba zan tsaya yi miki ɓoyon komai ba, sonki nake yi, kuma so na aure".
Da sauri ta kalle shi ta ce "So kuma ni ɗin?"
"Eh mana ko akwai haramcin auren mu ne?"
"A'a ko ɗaya kawai dai ina mamaki ne"
"Me yasa za ki yi mamaki dan na ce ina sonki da aure?".
"No ba komai". "To shikenan Hasina ba na son ɓata lokaci ko jan aji irin wanda ku ke yi idan an ce ana sonku, amsa nake buƙata, shin ki na ga za ki iya aurena?"
"To ka bani nan da kwana biyu zan yi shawara". Mudan na son musa mata amma ya kasa yi mata musun, ya ce "To shikenan, ina jiranki" suka yi musayar lambar, har zai wuce ta ce ya bari ta kira masa Momy suyi sallama. Kafin ya tafi, ya amsa mata da "To".
Ta miƙe ta kira masa Turai suka yi sallama sannan ya bar gidan.
*********
Sai bayan isha su Bilki suka isa gida kowa a gajiye yake, Gwaggo da ta samu labarin Maryam na can ba ta dawa ba, masifa ta shiga yi, ta in da ta shi ba ta nan take fita ba, ta ce dan kawai dare ya yi da sai ta je ta dawo da ita. Mama kuwa da ta samu labarin Maryam na can kasa magana tayi sannan kuma ta ɗan ji daɗin zaman Maryam ɗin ko ba komai Afnan za ta ji sanyi idan ta ga ƴar uwarta a kusa da ita.
Da dare mai gari ya shigo gidan ya na faɗin "Ina amaryar take ne, ta so ga angonki nan ya zo zai duba ki"
Gaban Afnan ya buga da ƙarfi jin an ambaci angonta, ka sa tashi tayi, sai da mai gari ya sake magana sannan ta miƙe a hankali tayi waje.
_A yi haƙuri da in da aka ga typing errors_
Amanar cool ce ✍️
***