SIRAƊIN UƘUBA 2
by @nusybee143
🔥SIRAƊIN UƘUBA🔥
__Free_book_
✍️Nusy bee
Page 2
Ƴan mintuna bayan ta sauke wayar taji sallama,ta ɗauke kai daga kallon da takeyi a ƙatuwar plasma TV ɗin dake luxury parlourn,ta kalli saitin kofar da kulawa,wanda yayi sallamar ya bayyana
Matashin saurayi ne,giant, kyakykyawa wankan tarwaɗa,sanye yake da riga da wando na puma track suit baƙaƙe, kyakykyawan gashin shi da bai taru sosai ba ya sha gyara,yayi murmushi yana kallon ammin nashi da tuntuni murmushi yake kwance akan fuskar ta,ya ƙarasa kusa da ita ya zauna ya rungume ta yana faɗin"I miss you ou lovely mother"
Itama murmushi tayi tana faɗin"SULAIMAN ka dawo?ya aikin?"
Sulaiman ya yatsina fuska yace"aiki kadaran kadahan ammi,yanzun ma na gaji sosai,tun ɗazu na shigo gida amma sai da na fara Branching part ɗina nayi relax sannan nayo nan"
"Weldone son!I hope you are doing good"
Sulaiman yace"absolutely ammi,good evening my ammi"ya ƙarashe yana kwantar da kanshi a kan kafaɗar shi
Hajiya Raheena tayi murmushi tana kallon shi tace"kai fa baka girma ko? ɗaga ni kafin surayya ta shigo taga wannan taɓarar"
Sake maƙalkale ta yayi a shagwaɓe yake faɗin"kai ammi na,kafin ita wa kika fara sani?"
"Yayan ku mana,malam ni ɗaga ni"Sulaiman yayi murmushi sannan ya zauna sosai yana kallon ta,da serious face yake faɗin"ammi gobe da yaushe za'a yi tafiyar nan?"
Hajiya Raheena ta ɗan taɓe baki tace"Abban ku yace wajen goma na safe zamu tashi"
"Kenan ba da yaya AUWAB za'a tafi ba?"
Da sauri ammin nashi ta kalle shi yace"wanne Auwab kake Magana akai? beside,Kai yanzu akace Auwab zai je garin nan sai ka yarda?"
Sulaiman ya ɗan yatsina fuska yana girgiza kai yace"but ammi I see nothing special don Yaya Auwab ya je albasu, don't forget acan aka haifi abban mu,can ne asalin shi"
"Then,so?"ta faɗa tana hararar shi
Murmushi Sulaiman yayi yace"nothing,yaushe zai dawo ne? I'm missing him badly,my brother,my friend,my,my,Kai my everything ma kawai"ya ƙarashe yana murmushi
Hajiya Raheena tayi murmushi tace"ka bi shi mana,ko Boston ɗin baƙon ka ne?"
Sulaiman yayi murmushi ya girgiza kai yace"no!idan na bi shi ni kuma yaya zanyi da nawa aikin kenan? Allah ya dawo mana dashi lafiya kawai"
Hajiya Raheena tace"ameen"daidai nan surayya da Amra sukayi sallama suka shigo da sallama
Suka amsa musu,da girmamawa suka gaishe su,suka amsa, Sulaiman yace"sai yanzu kuke dawowa?"
Surayya ta kyaɓe fuska kamar zatayi kuka tana faɗin"wai ji nayi fa an ce gobe zamu je wancan ƙauyen,da ban so dawowa ba ma,na so booking flight gobe na saci jiki na wuce Maiduguri,kafin a matsa min zuwa wancan ƙauyen"
Sulaiman ya miƙe cike da takaici yana kallon ta,yace"a wancan ƙauyen dai da kike ƙyanƙyami bakya so anan aka haifi uban naki da kike ƙafafa dashi, saboda haka idan kika tashi ƙyamatar ƙauyen sai ki haɗa har da uban ki da shima haifaffen can ɗin ne"yana faɗin haka yace"good night ammie"bai jira amsar su ba ya fice cike da takaicin yadda mahaifiyar tasu take cusa musu aƙidar ƙin dangin mahaifin nasu,duk da ba sosai take nunawa ba
Dukkan su da kallo suka bi shi,Hajiya Raheena taji haushin abinda yayi wa ƙanwar tashi,amma sai ta share bata nuna musu ba,don duk abinda akeyi bata bada ƙofar da karami zai raina babba a yaranta,ta ɗauke kai ta kalle su tace"ku shirya da wuri Please,abban ku ya gaya mana wajen ƙarfe goma na safe zamu tafi"
Amra ta kalli ammin nasu cikin jin takaici tace"to be sincere ammi I dislike zuwa wannan ƙauyen, there is nothing special with that village,I hate it wallahi"ammie ta kalle ta da ɗaurewar fuska tace"yanzun ma zagin da kuka saba janyo min kuke so ku ja min?baki ji abinda yayan ku yace ba?acan aka haifi uban ku?to bana son shiririta,ku shirya zamu je garin ku gobe"surayya cikin sakalci irin na auta cikin shagwaɓa tace"but ammie You know that old woman is so annoying,ki ga fa nan zata zo amma sai tayi ta haɗa mu da abban mu, Aunty beely ma kina ga cewa tayi ta tsani tazo saboda kullum a cikin haɗa ta da daddyn su take,wai taƙi aure"
"Watch your tongue Amra!ita ɗin duk lalacewa mahaifiyar baban ku ce,You have to respect her for the sake of her son which is your father!"ta ƙarashe da ɗan ɗaga murya
Shiru sukayi basu sake magana ba,don sun fuskanci ran mahaifiyar tasu ya ɗan ɓaci,a hankali surayya ta ɗauki ƴar jakar ta,ta miƙe tana faɗin"good night ammie"itama Amra miƙewa tayi ta bi bayan ta,suka nufi ɗakin su dukkan su rai a ɓace
LUGARD ROAD, NASSARAWA GRA, KANO STATE, NIGERIA
"Mum!Wai da gaske ne gobe zamu yi tafiyar nan?"
Ta ɗaga kai tana kallon shi,fuskar shi a ɗaure, da gani yana cikin ɓacin rai,kafin ta kai ga bashi amsa suka ji Muryar beely tana dariya tace"yeah of course Yaya AZAD!that annoying old woman da baka ƙauna gobe dai zaku kwana a waje ɗaya"ta ƙarashe tana dariya
"God forbid!anya daddy yana duba mana kafin yayi abu kuwa?for God sake bana son tension,but that annoying old woman with her villagers' children and grandchildren zasu janyo jinin mutum ya kai matakin ƙarshe, Please mum kiyi wani abu Please"kallon Azad tayi cikin takaici tace"stop begging me nayi abinda kasan bazan iya ba,tun wuri nace ka koma bakin aikin ka amma kaƙi,yanzu shi Auwab da Allah ya taimake shi ya koma bakin aikin shi ba gashi nan ya huta ba?don haka kar ka dame ni,ka bar Ni da abinda yake damu na nima"tana kaiwa nan ta miƙe ta bar parlourn ran ta a ɓace,su kuma suka bi ta da kallo
Beely ce ta kalli Azad cikin kwantar da murya tace"Please yaya Azad Kar kayi Abinda daddy zai ƙullace mu,that woman is his mother,the villagers are his relatives,and he love them,so let's do something that will not hurt him,kwana ɗaya kawai zamu yi,in Sha Allah babu wata matsala,bana son abinda zai janyo mana fushin Daddy"Azad yayi tsaki yace"bilkisu wallahi bana ƙaunar garin nan,bana son haɗa sabga da ƙauyawan nan,ƙazamai ƴan rainin hankali"beely ta yatsina fuska tace"seriously Yaya Azad,amma haka zamu je kawai saboda daddy"
Feena dai na zaune daga gefe tana danne dannen waya,amma hankalin ta da kunnuwan ta suna ga ƴan uwan nata,tana jin haushin yadda suke wulaƙanta dangin mahaifin nasu wai ƴan ƙauye ne,ta girgiza kai cike da takaici,ta miƙe tsaye batare da ta kalli yayyen nata ba da ko kula da ita basuyi ba ta shige ɗakin ta
BOSTON, MASSACHUSETTS,USA
Kyakykyawan matashi ne,fari tas,yake takawa a hankali a gefen titin,kallo ɗaya nayi masa na gano kamannin sulaiman a tare dashi,sai dai shi yafi sulaiman haske,kuma yanayin shi yana gwada rashin son hayaniyar shi, saɓanin sulaiman mai yawan surutu
A nutse ya zare farar p-cap din da ke kanshi,ya zare baƙin glasses da ya kara wa farar kyakykyawar fuskar shi kyau,cikin nutsuwa ya cigaba da takawa zuwa bakin katafaren gate ɗin gidan nashi,hannun shi riƙe da p-cap da baƙin glasses ɗin nashi,ya buɗe ƙaramin gate ya shiga gidan cikin nutsuwar shi da rashin hayaniya kamar koyaushe
Yana shiga ɗakin shi wayar shi tana katsewa,ya ɗan yatsina fuska sannan ya ɗauko ya duba mai kiran, murmushi yayi ganin mai kiran,ya jefar da wayar tashi kan gado ya faɗa toilet ɗin ɗakin nashi
Bai wuce mintuna goma ba ya fito,ya shirya cikin kaya marasa nauyi ya zauna a gefen katafaren gadon shi sannan ya ɗauko wayar shi ya mayar da kiran da akayi masa, ba'a ɗauki lokaci ba aka ɗaga
"Big bruh!sai da kai babban yaya"Muryar Sulaiman ta faɗi haka daga cikin wayar
Murmushi yayi sosai kafin yace"Sulaiman!ya aikin?ya fama da mutane kuma?"sulaiman yace"normal wallahi,Abba ma ya saka na ɗauki hutu tun shekaranjiya,this time dai da shi da daddy sun yi alƙawari zamu je mu ga mahaifar su mu gaida Granny ɗin mu"
"That's good! Amra ta gaya min gobe zaku je ko?"
"Yeah!Amma for sure naga a gidan babu mai son tafiyar,daga ni sai dad"
Auwab ya ɗan yatsina fuska yace"Gaskiya sai dai daga kai sai dad ɗin,don ko Ni ba so nakeyi ba, shiyasa ma da Abba ya fara yi min batun tafiyar na cigaba da zama na anan kawai"
"Haba yaya Auwab! don't forget that anan aka haifi mahaifin mu,nan ne asalin mu,nan ne tushen mu,ka taɓa ganin mutum yaƙi tushen shi?"
Ahto!ko shege yana son tushen shi🥱
#likecommentshare
#Nusy_bee