RAMIN ƘARYA...

Chapter 51-52

by @amanarcool323

💫 *RAMIN ƘARYA....* 💫



_WRITING BY AMANAR COOL_✍️



*YOUNG TALENTED WRITER'S ASSOCIATION (YOTA/021)*



Page 51&52




__________Hankalin Umma ba ƙaramin tashi ya yi ba, na rashin sanin halin da su Haidar suke ciki, tun jiya take kiran wayar sa a kashe, gefe ɗaya tana tunanin me za ta cewa Yaya Sa'adu? Tunda ta ga bai kuma kiran ta ba, ta san ya yi fushi ne, zai ɗauka tana yi masa yawo da hankali ne, sake kiran wayar tayi har yanzu wayar a kashe, ita gashi ba lambar Faruk ce da ita ba, balle ta jaraba kiran shi ko Allah zai sa tashi wayar ta shiga.

Haka ta zauna jiki ba ƙwari, aikin gidan ma ta kasa yi, gaba ɗaya ta rasa me za ta yi.

Tana nan zaune ta ji ana sallama a ƙofar gida. 

Tashi tayi ta saka hijabin ta, fita tayi domin ta duba mai sallamar, uban gidan Haidar ne, duk da sau ɗaya ta taɓa ganin shi a lokacin da ta je yi masa godiyar babur ɗin da ya saya wa Haidar, gaisawa suka yi cikin mutunci.

Sannan ya ce "Lafiya dai duk jiya ban ji Haidar ba? Kuma na kira wayar shi a kashe?".

Umma ta ce "Nima tun jiya nake kiran wayar shi a kashe, bashi da lafiya ne, ya je karɓar magani shi da abokin shi tun jiya ban ƙara jin ɗuriyar su ba".


"Subhanallah ai ban san bashi da lafiya ba, to ina suka je karɓar maganin?" .

Ta ce "Ni dai sunce gurin wani malami ne za su, to bayan sun tafi sai na sake kiran su nan suke faɗa mini basu tarar da malamin da suka je gurin shi ba, amma zasu wuce gurin wani malamin, kuma shi ba a nan garin yake ba, tunda muka yi wannan maganar ban sake jin su ba".

"Ikon Allah, to Allah yasa lafiya, bari na je na bincika, kar ki damu in sha Allah babu wata matsala".

Godiya tayi masa, sannan suka yi sallama ta koma ciki.


Maryam tana komawa gidan mai gari, ba ta tsaya komai ba ta ce ita gida tayi, ba yadda ba su yi da ita ba akan ta bari ta ƙara kwana biyu ta ƙi, haka suka shirya mata tsaraba, aka yi mata rakiya. 

Afnan kuwa tayi kuka har ta gode Allah, wani irin zazzafan zazzaɓi ne ya rufe ta, nan take ta fara rawar sanyi, ya ye zanin dake shinfiɗe a kan katifar tayi, ta duƙunƙune a ciki. Tunanin Haidar ne ya zo mata a rai ta ce "Allah sarki ya Haidar ko a wane hali yake ciki? Ina roƙon Allah ya baka haƙuri da juriya my Haidar". Ta ƙarasa maganar tana dasa sabon kuka.

Misalin sha biyu Umma na zaune, kamar daga sama ta ji sallamar Yayanta, ƙirjinta ne ya buga da ƙarfi, rabon sa da gidan nan an daɗe, tun wani zuwa da ya yi, ya ce ta shirya zu je ƙauye ta ƙi, jin haushin hakan yasa shi cewa ba zai sake zuwa inda take ba.

Cikin sanyi jiki ta miƙe fitowa tayi tana amsa masa sallamar. Kallo ɗaya tayi masa ta san yana cikin tsananin fushi da ɓacin rai.


"Yaya kai ne da kan ka? Sannu da zuwa, ya hanya? Shigo ciki mana ka tsaya a waje".


"Ba zama na zo yi ba, A'isha kin ba ni mamaki, kuma kin yi mini abin da ban zata daga gare ki ba, kin nuna mini ban isa da ke ba, ban isa na yanke hukuncin dana ga dama akan ki da zuri'arki ba, shikenan babu komai, dama abin da dangi ke jira kenan, kuma gashi kin yi mini, sai su yi dariyar su son ransu, abu ɗaya nake so dake yanzu ina Haidar ɗin yake? Ya zo ya bani takardar sakin ƴar mutane, na je na bawa iyayen ta Haƙuri".


"Yaya dan Allah ka yi haƙuri, wallahi kai ma ka san ka isa da ni, kuma kana da damar da zaka yanke duk hukuncin da kaga dama a kan mu, kuma dole mu yi maka biyayya akan shi, ko da kuwa bai yi mana daɗi ba. Yaya Haidar ne ba lafiya yanzu haka baya nan ban san halin da yake ciki ba, tun jiya da ya ce na bari zai karɓo magani, sannan ya zo ya wuce ban ƙara ji daga gare shi ba, na yi kiran wayar shi ba ta shiga".

Shiru sarkin fada ya yi yana nazarin maganar sannan ya ce "Bashi da lafiya to me yake damunsa?".

Ta ce "Nima dai ban sani ba, jiya ne yake gaya wa abokin shi, shi ne abokin na sa ya ke gaya mini, ban san wace irin rashin lafiya ce ke damunsa ba".


Duban ta ya yi da kyau ya ce "A'isha kin san wani abu? Ina ji a jikina ba abin da ke damun yaron nan, kawai dai akwai abin da yake shiryawa ne, Haidar ba yaro ba ne, ba ta yadda za a yi a ce tun jiya wayar shi a kashe, idan ma wata matsala aka samu ko wayar ce ta samu matsla, ai zai iya a ron waya ya kira ki, ko ya kira ki da wayar abokin na shi, tunda ya san hankalin ki ba kwanciya zai yi ba".


Umma tsayawa tayi tana kallon yayanta sannan tana nazarin maganganunsa, tabbas maganarsa abin dubawa ce, to amma me yasa Haidar zai yi mata haka? Kenan guduwa ne ya yi? Shi ya sa ya yi ƙaryar bashi da lafiya, lallai Haidar ya shayar da ita ruwan mamaki, ko da yake ba zata yi mamaki ba. 

"A'isha ki yi tunani akan magana ta, ko baki yarda da abin da na faɗa ba ne?"

"A'a Yaya na yarda mana kawai dai ina mamakin abin ne, wallahi Yaya kana yin wannan maganar na ji kwata kwata ban yarda da ciwon na sa ba, amma ba komai ya je, tunda haka yaga tafi masa, ba zan ɗaga hankalina gurin neman sa ba. Duk in da ya je zai dawo ne, yanzu Yaya meye abin yi?".

"A'isha kin kuru, a yadda na shigo gidan nan banzo miki da daɗi ba, sai dai da na fahimci ba laifin ki ba ne, yasa na sassauta fushina, abin yi ɗaya shi ne, zan bawa iyayen ta haƙuri, ta koma gidansu kafin shi wannan yaron ya dawo ya bani takardar sakin ta, saboda idan ta ci gaba da zama a gidan wani abin surutu ne a gare ni, a ce na a jiye ƴar mutane a gida, sannan ina son ki sani daga yanzu in dai abin da ya shafi Haidar ne na zare hannuna a ciki, dama dai ni ne nake shiga harkar shi, to tunda na ga bai san mai son shi ba, ni ma na zare hannuna daga lamarin shi".


Cikin kuka Umma ta ce "Dan Allah Yaya ka yi haƙuri ka da a raba auren nan, wallahi har cikin zuciyata na ji ina son auren kuma na gamsu da shi, ka yi haƙuri ba sai ta koma gidan iyayen ta ba, idan ma surutun mutane ka ke gudu nayi maka alƙawalin zan je da kaina har ƙauyen na dakko ta na zo da ita nan gidan. Duk da nayi wa kaina alƙawalin ba zan koma ƙauye ba, amma matuƙar hakan zai saka farin ciki zan yi".


"A'isha da kin bari an raba auren nan tunda baya so, ka da yazo ya wulaƙanta ƴar mutane, kin ga ya zubar mini da mutunci, sannan mai gari ma ba zai ji daɗi ba, ina ga a haƙura kawai". Ya yi maganar cikin ɗaure fuska duk da ya yi mamaki sosai da ya ji ta ce za ta je ƙauye, kuma ya yarda abin bai yi mata daɗi ba.

"Ni dai Yaya ina neman wannan alfarmar dan Allah ka yi haƙuri, ka bari na ɗakkota sai mu zauna a nan ɗin".

Da ƙyar tasamu ya amince da hakan, sannan ta lalaɓa shi ya shiga ɗaki ta kawo masa ruwa da abinci ya ce, bai wani jima ba ya yi mata sallama, tare da jaddada mata cewar duk bata zo goben ba sai dai a warware auren nan.


Haidar kuwa ya na ɗakin Faruk hankalin shi kwance, sai dai idan ya tuna Umman shi yana shiga damuwa, saboda ya san hankalinta a tashe yake, sai dai baya jin zai iya komawa gidan yanzu, ko maganar baya so ana yi masa, gaba ɗaya damuwa tayi wa zuciyar shi yawa, tunanin Afnan ya hana shi sukuni, gashi kamar ƙara rura wutar soyayyata ake yi a zuciyarsa.


Atika ta zo kawo wa Afnan abinci, sallama tayi ta ji shiru, ta daɗe tsaye tana sallama ba a amsa ba, shiga tayi ɗakin a kwance ta tarar da Afnan tana rawar sanyi da sauri ta ƙarasa gareta ta ce

"Subhanallah A'isha baki da lafiya ne?"

Kasa magana Afnan tayi.

Hankalin Atika ya tashi a lokacin da ta ya ye zanin da ta rufa da shi, shi kansa zanin ya ɗau zafi, jikinta kamar garwashi.

Ta ce "Innalillahi wa'inna ilaihim raji'un, ya zan yi ni Atika? Ga mai gidan baya nan".

Ƙoƙarin tashin ta zaune tayi da ƙyar ta iya tashi zaune ɗin, ta jingina da jikin gini ɗakin.

Atika ta ce "Sannu A'isha me yake damunki ne?" Tayi tambayar tana kallon Afnan dake rufe da idanuwanta hawaye na bin fuskarta.

Kasa bude idonta tayi, kuma bata yi magana ba

Atika ta kuma cewa "Ki yi haƙuri A'isha kin ji, ga abinci na kawo ki yi ƙoƙari ki ci, kafin mai gida ya dawo ya karɓo miki maganin zazzaɓi". Rarrashin Afnan ta shiga yi, sannan ta samu ta ci abincin ka ɗan, ta kuma kwanciya.


Mama na ɗaki kwance ta ji sallama kamar muryar Maryam ta ji, zubur ta miƙe ta fito aikuwa Maryam ɗin ta gani, da gudu Maryam ta saki kayan hannun ta ta rungume Mama cikin murnar ganin ta.

Mama ma murna take na ganin Maryam ɗin, a hankali Mama ta ce "Maryam ina Afnan? Tana can ko? In ji dai tana lafiya?".


"Mama tana can lafiya ƙalau take, sai dai ko da na barota kuka take yi, Mama wai sai na zauna".

Mama ta haɗeye wani abu mai ɗaci ta ce "Dama nasan hakan zata faru ai, Allah sarki Afnan Allah ya baki haƙuri da juriya, ya baki ikon yin biyayyar aure".

Da Amin Maryam ta amsa sannan ta ce "Mama bari na yi wanka zafi nake ji".

Ta ce "To".

Har Maryam zata shiga ɗaki ta kuma cewa "Mama wai kin san wani abu kuwa? Har na dawo banga mijin Aunty Afnan ba, an ce baya gari, tun ranar da ta tare aka ce zai dawo, amma har yau bai dawo ba, kwanan ta biyu a gidan. Duk tsoron Aunty haka take kwana a ɗakin ita ka ɗai". Ta ƙare maganar cikin yanayin damuwa.

Mama ta ce "Ikon Allah yanzu ita ka ɗai take bacci a ɗakin? To ke me yasa ba zaki taya ta baccin ba?".

"Mama cewa fa aka yi yana hanya zai zo, taya zan tsaya wurin ta".

"Allah ya kyauta" shi ne abin da Mama ta faɗa sannan.

******

Abba na falonsa tare da Ammi suna hira, wayar sa ce ta fara ringing ɗauka ya yi tare da yin sallama, cikin girmamawa ya ce "Barka da wannan lokacin Hajiya, ya gida? Ya iyali?".


Tunda ya ambaci Hajiya gaban Ammi ya faɗi. Addu'a ta shiga karantowa, domin samun nutsuwa a zuciyarta, ji tayi ya ce "To shikenan Hajiya Allah ya kawo ku lafiya. Zan gaya musu in sha Allah". Daga haka ya kashe wayar.

Ya dubi Ammi ya ce "Hajiya ce ta ce a saka ƴan aiki su gyara mata gidan ta jibi tana tafe".

Ammi ta ce "Ma sha Allah, Allah ya kawo ta lafiya" tayi maganar tana murmushin ya ƙe, dan ta san wannan zuwa idan zai yi wa kowa farin ciki ban da ita.

*******


Sai yamma sarkin fada ya isa gida, kai tsaye fada ya wuce.

Mai gari ya ce "Sarkin fada ina ka shiga duk yau baka zo fada ba? Na aika gida a dubo ko lafiya aka ce baka nan".

Sarkin fada ya ce "Ranka ya daɗe a yi mini afuwa na rashin fada da ban yi ba, yau na yi sammako ne na je gurin A'isha akan maganar yaron nan da bai zo ba, ashe lafiya ce bashi ne". Ya yi maganar ba tare da ya faɗi ai nahin abin da ke faruwa ba.

Mai gari ya ce"Subhanallah Allah ya bashi lafiya, amma me yasa baka faɗa mini cewar yaron bai zo ba? Sai ɗazu nake samun labari".

"A gafarce ni ranka ya daɗe ina jin kunyar sanar da kai ne, shi ya sa yau na yi sammakon zuwa".

"To yanzu ya aka yi?".

"Eh to ita A'ishan ta ce zata zo gobe ta tafi da yarinyar can wurin ta kafin ya samu sauƙi".

Mai gari ya ce "Ah to ma sha Allah, ai hakan ma babu laifi, yarinya dai zata koma garinsu da zama kenan? To Allah ya taimaka ya basu zaman lafiya da zuri'ar ɗayyiba".

Da Amin sarkin fada ya amsa, sannan ya ce wa mai gari zai je gida dan dawowarsa kenan".


Da yamma haka Umma ta shirya dan zuwa ƙauyen, dama taƙi faɗa wa Yayan nata ne cewar yau zata zo, dan kar ya hana ta tafiyar dare, da yake ƙauyen in dai ba magariba aka kira ba to ana samun motar zuwa, bata son kowa ya gane ta har ta je ta dawo shi ya sa zata yi shigar dare, ta yo sammakon fitowa da safe, dan ba yadda zata yi ne, shi ya sa zata kwana a garin nan, amma da tana samun mota ba abin da zai sa ta kwana a wannan garin. Allah ya taimake ta tana zuwa saura mutum ɗaya mota ta cika, dan haka babu ɓata lokaci suka kama hanya.


Ko da sarkin fada ya isa gida bayan ya huta ne yake bawa Atika labarin abin da ke faruwa, tayi mamakin ƙarfin halin Haidar idan ka ganshi kamar ba zai yi taurin kai ba, nan take faɗa masa ma yarinya ba ta da lafiya.


Ya ce "Subhanallah me yake damunta?".

Atika ta ce "Zazzaɓi ne ya rufe ta ɗazun, amma dai yanzu jikin nata da sauƙi ko da na je duba ta ɗazun naga ta ji sauƙi".

Ya ce "To Allah ya bata lafiya"

Ta amsa da Amin.


Sai wajan tara da rabi na dare Umma ta iso garin kai tsaye gidan sarkin fada ta wuce, ya na zaune bai daɗe da dawowa daga fada ba, suka ji sallamar Umma, amsawa Atika tayi da mamaki ta ce "A'isha ki ce a daren nan?".



Amanar cool ce ✍️ 
***