Chapter 53-54
💫 *RAMIN ƘARYA....* 💫
_WRITING BY AMANAR COOL_✍️
*YOUNG TALENTED WRITER'S ASSOCIATION (YOTA/021)*
Page 53&54
__________"A'isha ke da ki ka ce mini sai gobe za ki zo, sai kuma na ganki yanzu? me ya sa za ki yi tafiyar dare? Bayan kin san hanyar tamu wani lokacin ba ta cika lafiya ba".
"Ka yi haƙuri Yaya ba na son kowa ya san na shigo garin nan, shi ya sa ban sanar da kai cewar yau zan zo ba".
"Kamar ya ba kya son kowa ya san kin shigo? A'isha gidan ne ba za ki je ba? Ke yanzu za ki iya shigowa garin nan ba ke je gida kun gaisa da sauran ƴan uwa ba? Wai ke me yasa abu baya wuce wa ne a gurinki?".
Shiru ta yi ta kasa magana, ba ta son tuna abin da ya faru ko ka ɗan, haka kuma ba ta jin za ta iya zuwa gidan nasu.
Atika ta shinfiɗa mata tabarma ta ce "Zo ki zauna kin yi tsaye, sai ka ce baƙuwa".
Zama ta yi Atika ta kawo mata abinci, sai da ta fara yin sallolin da ake binta kafin ta ci abinci. Bayan ta kammala ne Atika ta ce "Sai mu je ki ga surukar tamu, yau ma ba ta jin daɗi".
Umma ta ce "Ashsha Allah ya ba ta lafiya"
Tashi suka yi Atika ta yi wa Umma jagora da sallama suka shiga ƙofar, Afnan na ɗaki a zaune ta takure guri ɗaya, ta ji muryar Atika na sallama, fitowa ta yi tana amsa sallamar ganinta tare da baƙuwa ya sa Afnan ta duƙa har ƙasa ta gaishesu. Duk da ya na dare na, amma hakan bai hana Umma hango natsuwar da ke tattare da yarinyar ba, nan take ta ji tana mugun son yarinyar, kuma ta yi farin cikin kasancewarta suruka a gareta.
Amsa mata gaisuwar suka yi, sannan ta miƙe ta ɗauko tabarma ta shinfiɗa musu a barandar gurin, zama suka yi. Atika ta ce wa Afnan "A'isha ga surukarki nan ta zo duba ki, mahaifiyar mijinki, ba a nan garin take ba".
Afnan ta yi ƙuri da ido tana kallon Umma duk da ba ta ganin fuskarta sosai, tunani take dama ita wannan matar ba ita ce ta haife shi ba? Ikon Allah, to ita wannan daga ina ta zo kuma?.
"A'isha ya na ji kin yi shiru?" Atika ta yi maganar.
"Babu komai Inna".
Sannan ta mai da dubanta ga Umma ta ce "Barka da zuwa Umma ya hanya?". Haka kawai Afnan ta ji bakin ta ya kama sunan Umma, shi ne ta kira ta da shi.
Umma ta ce "Lafiya ƙalau Alhamdulillah, fatan mun same ku lafiya? Ya ki ke? ya baƙunta?".
Afnan ta ce "Alhamdulillah".
Atika ta kuma cewa "A'isha dama ta zo duba ki ne, kuma tana son idan za ta koma ku wuce tare can in da take, saboda an ɗan samu matsala ne, rashin isowar mijin na ki, ashe juyawa ya yi ya koma can gida, shi ya sa bai ƙaraso ba, kuma yanzu bashi da lafiya, to kin ga bai da ce ki ci gaba da zama a nan ke ka ɗai ba, gara ki na kusa da shi".
Afnan ta ce "To shikenan Inna, Allah ya bashi lafiya".
Da amin Atika ta amsa
Umma ta ce "Ashe dai takwara ta ce? To ni da wane suna zan kira ki?" Ta yi maganar ta na murshishi.
Sunkuyar da kai ta yi, ta ce "A gida Afnan a ke kirana da shi".
Umma ta ce "To shikenan ni ma Afnan ɗin zance. Yawwa sannan ki shirya saboda gobe nake so mu yi sammakon tafiya".
Afnan ta amsa da "To".
Atika ta ce "Gobe kuma A'isha? Nazata sai jibi".
Umma ta ce "A'a goben dai zan wuce".
Tashi suka yi tare da yi mata sallama. Afnan ji ta yi kamar ta ce wa Umma ta zauna su kwana tare.
Ba yadda sarkin fada bai yi da ita ba a kan ta bari har jibi ta koma, amma ta ƙi, kuma ta ƙi yarda da batun zuwa gidansu ta gaishesu, dole ya haƙura ya ƙyaleta, ɗakin da ke kusa da na Atika Umma ta kwanta. Bacci ya kasa ɗaukarta, tunanin rayuwarta ta baya take yi, da irin abubuwan da suka faru da ita a wannan garin. A hankali ta ji ƙwalla na zubuwa da ga idonta, ta sa hannu ta goge. Duk yadda Umma ta so ta rintsa amma bacci ya gagareta, kiran sallan farko a kan kunnenta.
Tana idar da sallan asuba ta fito a lokacin Yayanta bai dawo da ga masallaci ba, ta yi wa Atika ina kwana tare da tambayarta ko Yaya ya dawo masallaci?
Atika ta ce "A'a bai dawo ba, amma A'isha tun yanzu za ki tafi sai ka ce wadda a ke kora? Ai ya kamata ki bari ku karya mana".
Dan babu yadda za ta yi ne ya sa ta tsayawa ta karya, Atika ganin tana son wucewarta ne ya sa ta ɗora abin karin, ko da gari ya yi haske sun karya har Afnan ɗin. Umma ta ce ba sai Afnan ta ɗauki komai na kayanta ba, iya kayan sakawanta za ta ɗauka. Sarkin fada ya so Umma su biya ta gidan mai gari Afnan ta yi musu sallama amma Umma ta ƙi wai ita ba ta son kowa ya ganta ne. Haka suka yi musu sallama suka ta fi.
Afnan sai tunanin take ina kuma za ta koma da zama? Yanzu idan Maryam ta zo ba ta ganta ba fa? Shiru ta yi tana nazarin rayuwa.
Bayan gari ya ƙarayin haske, mai gari ya kira Sanusi gaisawa suka yi, sannan ya nemi da ya kaiwa Gwaggo wayar, tana zaune Sanusi ya kawo mata wayar, ta amsa tana faɗin "Ummaru ne ko? Ai wallahi saina shiga ƙafar wando ɗaya da kai...." Ba ta ƙarasa maganar ba ta ji mai gari ya ce "To uwar fitana bashi ba ne, wai ke Halima a rayuwa idan ba fitana ki ka yi ba kya jin daɗi? Kuma ki rasa waƴanda za ki uzzurawa sai ƴa,ƴanki? Wannan wace irin rayuwace? Ai koma dai masifar za ki yi masa kya bari ku gaisa".
Gwaggo ta ce "Ka bari kawai Yaya yaran ne da abin haushi, ina kwana dai, ya mutan gida?".
Bai amsa gaisuwarta ba, ya ce "Ba wani abin haushi, yara na yi miki biyayya amma ba kya gani, wannan dai ba hali ba ne ki canza". Nan ya shiga yi mata faɗa ta in da ya shiga ba ta nan yake fita ba, sai da ya yi mai isarsa sannan ya ƙyaleta.
Gwaggo ta ce "Allah ya ba ka haƙuri, in sha Allah za a gyara".
Ya ce "Da dai ya fi miki, dama ina son faɗa miki cewar A'isha surukarta ta zo ta tafi da ita can in da take da zama a yau ɗin nan, saboda mijin na ta a can yake zama kuma baya jin daɗi ne".
Gwaggo ba ta tsaya jin ba'a sin komai ba, ko tambayar wane gari ne uwar tashi take ba? ta ce "To Allah ya basu zaman lafiya. Duk in da za su je da ita, su je, ai yanzu nauyinta a kansu yake".
Shi ma bai tsaya yi mata bayanin komai ba suka yi sallama. Miƙawa Sanusi wayar ta yi, tare da faɗa mishi abin da mai gari ya ce. Sannan ta miƙe ta nufin ɓangarensu Mama, dama tana da haushin Maryam ta dawo jiya ba wanda ya bi ta kanta, kuma ta san dole ne sai ta zo da tsaraba, amma a ka hana ta.
Maryam na zaune kusa da Mama suna karyawa, Baba na ɗaki, Gwaggo ta shigo musu kamar an hankaɗota, gaisheta Mama ta yi. Maryam ko ta yi kamar ba ta ganta ba.
Wani banzan kallo Gwaggo ta yi wa Mama sannan ta ce "Ki riƙe gaisuwarki ba na buƙata, ai ni ban kai matsayin da za ki gaisheni ba, kuma ba ni da darajar da za ku zo har ƙofata ku gaishe ni ke da waccan ɗayar marar kunya, wallahi duk Hajara ta fi ku hali. Sanusi ya yi sa'ar mace ta gari. Ɗan ladi da Ummaru kam ina roƙon Allah ka da ya ɗauki raina ba tare da na ga sun a jiye mata na gari ba. Yanzu saboda an ɗauke ne banza, an mai da ni ba kowa ba, har wannan marar kunyar ta dawo ban sani ba? Kuma na san ba za ta zo haka hannu rabbana ba, dole za ta zo da wani abin, amma da yake ke ce uwarta ke ki ka haifeta, ke ka ɗai ki ka ƙwamushe kayanki ba bu wanda ki ka ba wa a gidan nan. To ki ci, idan ma kin ci iya wannan ne, dan wadda za a riƙa fakewa dominta a ce za a je ƙauyen ita ma yanzu ba a nan za ta zauna ba, uwar mijinta ta zo ta tafi da ita can garin da suke da zama, in ya so yanzu sai muga ta tsiya".
Tunda Gwaggo ta fara magana babu wanda ya kulata sai yanzu da ta ce Afnan ba ta nan. Suka ɗago da sauri suna kallonta.
Maryam ta ce "Aunty Afnan ɗin ce ba ta nan? Jiya na baro mata a gidanta yanzu ki ce ba ta nan, hmmmm".
Gwaggo ta ce "Rufe mini baki mara kunyar banza, ko uwarki gata nan zaune na fi ƙarfin na yi mata ƙarya balle ke, shashasha".
Murguɗa mata baki Maryam ta yi tana hautsinarta, nan fa Gwaggo ta ce ina wuta ta saka Maryam a ciki, ta in da take shiga ba ta nan take fita ba, sai da ta yi musu tatasss sannan ta bar gurin.
Abin da ya sa Maryam ta yi wa Gwaggo shiru sannin cewar Baba na ɗaki kwance, da wallahi sai ta yi mata rashin kunya da ma kwana biyu tana ɗaga mata ƙafa. Baba kuwa na jinsu amma ya yi shiru kamar baya nan.
Mama ba ƙaramin tashi hankalinta ya yi ba, ta san tunda Gwaggo ta faɗa to tabbas haka ne, yanzu shikenan ba ta san wace uwa duniyar ƴarta take ba. Duban Maryam ta yi ta ce "Maryam da gaske Afnan ba ta nan? Yanzu ba mu san in da take ba kenan?".
"Mama kar ki damu, in sha Allah duk in da ta je za ta nememu". Maryam ta yi maganar.
Shiru Mama ta yi, ta kasa magana, ita kaɗai ta san me take ji a zuciyarta.
Kawu Sanusi ko ya na zuwa ya gaya wa Hajara abin da ke faruwa, wani irin daɗi ta ji, ta san ko iya haka Amina za ta yi baƙin ciki na rashin sanin in da ƴarta za ta zauna, nan take ta ji Allah ya kawo mata sauƙi, ba ma sai ta yi wahalar kashe kudinta ba, wurin koma wa wajan Malam ba.
********
Turai kuwa iya ƙuluwa ta ƙulu da abin da Mami ta yi mata, sannan ta ɗauke alwashin sai Mami ta yi nadamar da ba ta taɓa yi ba a rayuwarta.
Ta sake kiran Malamin ta ce "Ya ƙara uzzurawa zuciyar Mudan da soyayyar Hasina, a rufe masa idanuwansa da ga ganin kowa sai ita, hatta Mahaifiyarsa, kar ya saurara". Mugunta kala kala ta shiryawa Mami.
Mami kuwa hankalinta ya fara tashi da rashin lafiyar da Huda ke yi, gashi ƙememe ta ce ba za a kaita asibiti ba, kuma ba ta so a kira likita ya zo ya duba ta, ta rame sosai ta yi haske, ga baƙin cikin abin da Mudan ya yi mata na damunta ga wannan ciwon da Huda ke yi.
Sannan a gefe ɗaya tana cikin farin ciki na jin cewar Hajiya Maimunata na nan tafe, ta san ko ba komai Zainab za ta sha hantara da wulaƙanci.
******
Misalin sha ɗaya da rabi, Haidar na zaune ya gama cin abinci Faruk ya shigo ɗakin ya ce "Abokina har yanzu fa ƙofar gidan nan a rufe take, an ya duk in da Umma ta je tafiyar ba ta da alaƙa da wannan ɗan uwan nata da ka ce? Tunda a yadda na yi maka misalin kamanninsa ka ce shi ne wanda ya haɗa auren nan".
Haidar ya ce "Ni ma na fara tunanin hakan, amma dai ya na da matuƙar wahala a ce Umma za ta bisa zuwa ƙyauyen nan, sai dai ko wani abin da ban, Faruk hankalina ya tashi fa, ashe kamar na san wani abu zai faru jiya na ce ka je, ka yi baddasau ka duba halin da take ciki".
Faruk ya ce "Ni ma dai hankalina ya tashi, dan jiya a fusace na ga ya shiga gidan, amma ko da ya fito kuma sai na ga fuskarsa a sake, sai dai abin tambayar ba lokaci ɗaya suka fito ba, da na tambayi mai shagon nan dake kusa da ƙofar gidan ya tabbatar mini da yamma Umma ta fita, da ga gidan".
Haidar ya ce "To ina Umma ta je? Ka ga Faruk saka lambarta a wayarka sai ka kirata, mu ji".
Karɓar lambar Umma ya yi ya saka a wayarsa, ya kira bugu biyu Umma ta ɗauka ganin baƙuwar lamba ce, tana ɗauka ta ji muryar Faruk ya na faɗin "Umma ina kwana".
Dakewa Umma ta yi ta ce "Lafiya ƙalau Alhamdulillah Faruk ya a ka yi na jiku shiru kwana biyu kun ɗaga mini hankali? Ya mai jikin? Da sauƙi".
Faruk ya ce "Umma ki yi haƙuri don Allah garin ne babu newtork, ko da muka je sai Malamin ya ce sai mun ɗan zauna zuwa nan da kwana huɗu daidai ya haɗa maganin sai mu tafi da shi, da yake garin da nisa, mu ma duk hankalinmu a tashe yake, sai yanzu muka ɗan samu newtork ɗin ya dawo, shi ne na ce bari na kira ki dan hankalinki ya kwanta".
Umma ta ce "Allah sarki to Allah ya bashi lafiya, kar ka damu ka yi masa sannu, sai kun dawo".
Faruk ya ce "To Umma ai bacci yake da na baku kun gaisa".
"A'a kar ka tasheshi ina yi masa sannu idan ya farka, Allah ya yi muku albarka, sai anjima". Faruk zai yi magana Umma ta kashe wayar tana mamakin iskanci irin na yaran, amma ba komai zai gane ba shi da wayo. Afnan kallon Umma take tana kallon garin da suka zo, idan ba gizau idonta ke yi ba, garinsu take ganin an dawo da ita cikisa, kenan dama mijin na ta a nan garin yake zama shi da maihaifiyarsa? Ta yi wa kanta tambayar da ba ta da mai ba ta amsa, shiru ta yi ta zubawa sarautar Allah ido.
Faruk ya ce "Haidar Umma fa lafiyanta ƙalau ai ka ji duk yadda muka yi da ita, wato na so na tambayeta ina ta je, to ina gudun kar ta ce ina muka ji ba ta nan".
Haidar ya ce "Haka ne, ka san wani abu Faruk akwai abin da na manta a gidan, mai muhimmanci, ina son yanzu zan je da sauri na ɗauko, tunda ina da makullin ƙofar gidan a hannuna dama rabasu muka yi ni da ita kowa ya riƙe a hannunsa".
Faruk ya ce "Haidar karfa ka je tsautsayi ya sa Umma ta cimmaka a gidan".
"A'a in sha Allah ba za ta cimmi ni ba, bari na tashi na je".
Haidar bai tsaya komai ba, ya bar ɗakin Faruk ya ce bacci yake ji da ya raka shi.
Babu ɓata lokaci Haidar ya ƙaroso gidan ya buɗe ya shiga, baifi minti biyu da shigarsa ba mai napep ya sauke su Umma a ƙofar gidan.
Amanar cool ce ✍️
***