RAMIN 茦ARYA...

Chapter 57-58

by @amanarcool323

馃挮 *RAMIN 茦ARYA....* 馃挮



_WRITING BY AMANAR COOL_鉁嶏笍



*YOUNG TALENTED WRITER'S ASSOCIATION (YOTA/021)*



Page 57&58


___________茦arasowa Haidar ya yi ya nemi guri ya zauna, Umma ta dube shi ta ce "Ina ka je tun 蓷azu? Na je kai ma abinci ban tarar da kai ba? Kai da na bari kwance".

Babu kunya Haidar ya ce "Umma na 蓷an fara jin sau茩i ne, shi ya sa na 蓷an fita waje".

Umma kallonsa kawai ta yi, gani take kamar an canza mata shi, kamar ba Haidar 蓷in da ta sani ba ne. Da ga jin zancen auren nan gaba 蓷aya ya canza ya ari halin da ba nashi ba ya a 蓷orawa kansa.

Afnan kam sunkuyar da kai ta yi, ta kasa 蓷agowa ganin Haidar da ta yi ya sakata cikin wani yanayi. To me ya kawo shi wannan gidan? Ko dai 蓷an uwansu ne? Tunda ta ji ya ce Umma, kuma ana maganar a jiye masa abinci, to me hakan yake nufi? ta yi tambayar a zuciyarta. Alla Alla take ya yi abin da ya kawo shi ya fita da ga gidan, ta dai na ganin shi a kusa da ita. Saboda ba 茩aramin tashin hankali take shiga ba.

Haidar kuwa tsare Afnan ya yi da ido ko 茩iftawa ba ya yi, shi ma tunanin ya ke me Afnan ta zo yi a gidan nan? Dama Umma ta santa ne? to amma ai Afnan ta yi aure, to ko dai Umma ta san mijin da ta aura ne? Ganin ya na 茩o茩arin rikicewa ne, ya ka sa fahimtar komai ya sa shi cewa "Umma dama kin san Afnan ne? Na ga ban ta蓳a ganinta a gidan nan ba sai yau".

Murmushi Umma ta yi, sannan ta ce "瞥ata ce".

Haidar ya ce "To ai ni ban sani ba, Umma ita ce fa yarinyar da na zo da maganarta".

Umma ta ce "Allah sarki". Daga haka ta yi masa shiru

Sake cewa ya yi "Amma Umma ai na ga kamar an yi mata aure ko sati 蓷aya ma ba a yi da yin auren ba? ya aka yi kuma na ganta a nan? Sannan Umma me ye ala茩arki da ita?".


Gajiya ta yi da tambayoyin da yake yi mata. Duk da ba ta so ya sani yanzu ba, tana son ta ga shin zai ne mi ganin matarsa 蓷in ko har yanzu ya na nan a kan bakarsa, amma sai ta yi wani tunani, ta 茩are masa kallo sannan ta ce "Haidar Afnan 拼ata ce, kuma ita ce matar da a ka aura maka". 

Da wani irin sauri Afnan ta 蓷ago da kanta, ta kalli Umma sannan ta dubi Haidar da yake kallon Umma ya kasa magana, ji yake kamar ba dai-dai kunnuwansa ke jiyo masa ba.


"Umma ki ka ce Afnan ce matar da a ka 蓷aura mini aure da ita?".

Ummu ta ce "Kwarai kuwa shakka babu. Afnan ce matarka".

Wani irin farin ciki ne ya mamaye zuciyar Haidar ban da hamdala babu abin da yake yi a zuciyarsa, yanzu da ma duk wannan abin da yake yi ashe da ita a ka 蓷aura masa aure? Kai amma ya cuci kansa, da ya sani tun ranar da a ka 蓷aura auren ya je. Nadama da danasi ne suka mamaye zuciyarsa, ya yi Allawadarai da abin da ya aikata.

Wani sanyi ne wanda tunda ta zo duniya ba ta ji irinsa ba yake shiga cikin zuciyarta, ya na huda duk wata kusurwa dake jikinta, ya na shiga 蓳argo da tsokarta. Haidar ne mijin da aka aura mata? Da ma shi ne? Lallai babu abin da ya gagari Ubangiji, "Alhamdulillah Alhamdulillah Alhamdulillah" shi ne take ta nanatawa a zuciyarta. Ta ji wata nutsuwa da kwanciyar hankali sun shige. Farin ciki take ji sosai a zuciyarta wanda ta rasa dalilin hakan.

Gaba 蓷aya kunya ta kama Haidar ya na son koma yi wa Umma magana, amma idan ya tuna irin abin da ya yi sai ya kasa magana.

Umma ta ce masa "Ka tashi ka je ga abincinka can tun 蓷azu na a jiye ma, ba na son wasan zama da yunwar nan da ka ke yi, ga shi yanzu ba lafiya ce da kai ba".

"Umma ai na ji dama fa sosai" ya yi maganar ya na mi茩ewa ya je ya 蓷akko abincin ya dawo, ya zo zai zauna kusa da Afnan Umma ta ce "Me ye haka? Ke Afnan tashi bashi guri, dawo nan ki zauna".

Kallo ya bi Umma da shi, to me take nufi da hakan? Matarsa ce fa? "A'a Umma ta yi zamanta, ni 蓷aki ma zan koma". Da ga haka ya tashi ya shige 蓷akinsa, zama ya yi ya na jin farin ciki marar misaltuwa a cikin ransa, wai yanzu Afnan ce matarsa, mallakinsa, bai sani ba?.

Faruk ya kira 

Ya na 蓷auka Haidar ya ce "Allawadaran Halina Faruk, wallahi na kwafsa"

Faruk ya ce "Me ya faru? Wace kwafsawar ka yi?".


"Faruk ka san wacece matar da aka aura mini kuwa?"

"Haidar kenan ya za a yi na sani"

"Afnan ce fa"

"Afnan wace Afnan 蓷in?".

Haidar ya ce "Wadda dai ka sani, Afnan tawa, wai ashe ita ce, a ka aura mini. Faruk na cuci kaina, da nasani tun ranar auren na je, kai ma dai Faruk da laifinka me yasa ba ka ba ni shawarar na je ba, ka biye wa shirmena, da shiririta".

Faruk ya ce "A'a Haidar kar ka yi mini sharri, kai ma ka san na baka ha茩uri ka 茩i yi".

"To me yasa baka takura mini ba? gaskiya Faruk ba ka kyauta mini ba. Duk kunya ta dame ni, na rasa me zancewa Umma, ko 蓷azu ai na gaya maka abin da na yi ta fa蓷a".


"Wai ya ka na 茩o茩arin 蓷ora mini laifi ne Haidar? Kawai dai kuskure ne an yi shi, sai a kiyaye gaba, yanzu Afnan 蓷in na nan gidan?".

"Eh ta na nan"

Faruk ya ce "Ah ka ce dai yau ka cikin alkhairi dumu-dumu abokina, za ka shiga da ga ciki". 

"Hmmm Faruk kenan ban ga alamun hakan ba, a yadda na ga yanayin Umma, kai zama fa na zo yi kusa da yarinyar ta hana ni".

Dariya Faruk ya yi ya ce "Kai haba dai, to Allah ya gyara kar Umma ta hana ka cin amarci yau, shawara 蓷aya zan baka, ka yi 茩o茩arin ba ta ha茩uri da nuna mata cewar komai ya wuce, sannan ka na son kamar yadda ta ce Afnan 蓷in za ta dawo 蓷akin ka da zama, ka yarda, kuma ka amince da hakan, sannan ka bata ha茩uri akan abin da ka fa蓷a mata, tunda dai shi 茩aryar rashin lafiyar da ka yi bata san shiri ne ba".


Haidar ya ce "To shikenan, ka ta ya ni da addu'a"

Dariya Faruk yake yi sosai ganin yadda duk Haidar ya susuce.

Jin Faruk ya dame shi da dariya ne ya sa shi kashe wayar


Bayan Haidar ya bar gurin, Umma ta dubi Afnan ta ce "Afnan kin san abin da na ke so dake? Ko da wasa kar in ga kin kula Haidar a gidan nan, ko ya kira ki 蓷akinsa ki je. Duk da cewar mijinki ne, amma ban yarda ki kula shi a yanzu ba, kar ki yi tunanin wani abu ko akwai wata matsala ne, a'a wannan tsakanina da shi ne, ya ta蓳a ni ne, kuma ta haka ka蓷ai zai sa ya gane kuskurensa, ina fatan kin fahimci ne".


Cikin jin kunya Afnan ta ce "To Umma in sha Allah, duk yadda ki ka ce hakan za a yi".


"Yawwa yarinyar kirki Allah ya yi miki albarka, ya baku zuri'a ta gari, masu yi muku biyayya kamar yadda ki ka yi".

Da Amin ta amsa

Umma ta kuma cewa "Ni ko Afnan ya a ka yi Haidar ya sanki bayan ke ba 拼ar nan garin ba ce? Ko dai kuna shigowa garin nan siyayya ne ko makamancin hakan?".

Afnan ta ce "A'a ni 拼ar garin nan ce, uwayena duk suna nan garin"

Cikin mamaki Umma ta ce "Amma a ka ce mini a 茩auye ki ke, ke 蓷in jikar mai gari ce"

Afnan ta ce "A'a mai gari Yayan kakata ne, ni da ita da iyayena duk nan garin muke zama".

Umma ta ce "Allah sarki, kuma a ka yi miki aure a 茩auye?"

Afnan ta ce "Kakar tawa ce ta bu茩aci a yi hakan".

Shiru Umma ta yi, kafin ta ce "Ta ko kyauta ai Allah ya sanya albarka a cikin wannan auren". Da ga haka Umma ba ta kuma magana ba, dan ba ta son ta cika ta da dogon surutu.


*******

Mudan kuwa tunda ya bar gidan bai sake dawowa ba, ya na can gidan Turai ya nani 茩e a 茩ugun Hasina, ya na zuba mata kalamai kala-kala tare da yi mata alwashin ba wanda ya isa ya hana shi aurenta, ya shaidawa Turai cewar zai fa蓷awa Abba a zo nema masa auren Hasina ko da Mami ba ta amince ba. 茦warin gwiwa ta bashi tare da 茩ara ziga shi, bai dawo gida ba sai yamma. A lambun gidan ya tarar da Abba da Ammi zauna suna shan iska gaishesu ya yi, sannan ya ce 

"Abba 蓷azu na zo gurinka ban tarar da kai a falo ba".

Abba ya ce "To me yasa baka kira ni a waya ba? Ina fatan dai ba wata matsala ba ce?"

"Abba dama magana ce na ke son yi da kai a kan yarinyar da na ke son aure. Amma Mami ta ce ba ta yarda ba, ba zan aureta ba, ni kuma gaskiya Abba ita na ke son aura".

Abba ya ce "Dan me za ta ce ba za ka auri yarinyar da ka ke so ba? Tukuna kai wace yarinya ce? Sannan 拼ar gidan waye?".


"Abba ba fa wata ba ce. Hasina ce 蓷iyar Momy Turai, ita ce fa, amma Mami ta ce sam ba ta yarda ba".

"Mudan ka fa蓷a mata yarinyar da ka ke son aure kuwa?".

"Eh Abba na fa蓷a mata"

"Ita da bakinta ta ce maka ba ta amince ka auri yarinyar ba? To me take nufi? Hajiya na ga ai 蓷iyar aminiyarta ce, tamkar 蓷iya take a wurinta dan me za ta ce haka?" Abba ya 茩arasa maganar ya na kallon Ammi.

Ammi ta ce "Ina ga akwai abin da ya sa ta ce hakan 蓷in, ka bincike ta ka ji"


Abba ya ce "Ba na jin tana da wani dalilin, kawai dai rashin tunani ne wannan, kai Mudan tashi ka je zan yi magana da ita, matu茩ar na ji ba ta da wani 茩wa茩waran dalili, ni zan shige maka gaba na ne ma maka auranta".

Godiya Mudan ya yi sannan ya mi茩e ya bar gurin, mita Abba ya shiga yi, Ammi na tausarsa, a kan ya bi komai a hankali.

Mami tunda ta kulle kanta a 蓷aki ba ta fito ba, gaba 蓷aya hankalinta a tashe yake, wannan abin kunyar da me ya yi kama? Yanzu idan wannan maganar ta fito me za ta cewa jama'a? Da wane idon za ta kalli 拼ar uwarta, a ce 蓷an cikinta ne ya yi wa 蓷iyar 茩anwarta wannan aikin, yarinyar da tun daga yaye take a hannunta, idan ba fa蓷a ta yi ba wasu 蓷auka suke yi 拼ar cikinta ce, amma yau ita ce Mudan ya iya rufe ido ya yi mata wannan aika aikar. To yanzu ita ya za ta yi? Wace mafita ya kamata ta nema cikin sau茩i ba tare da maganar ta fita ba.


Huda ma na 蓷aki ta yi kuka har idanuwanta sun kumbura, gaba 蓷aya ta ji ta tsani kanta, duniya ta yi mata zafi, nadamar biyewa Mudan da ta yi suka aikata wannan ta'asar take. Ko da 茩awarta Nusee ta kirata, 蓷auka ta yi tana kuka, Nusee jin Hida na kuka ya sa ta tambayar me ya faru? ba ta 蓳oye mata komai ba ta gaya mata abin da ke faruwa.


Ha茩uri ta shiga ba ta tare da rarrashinta, ta tabbatar mata da za ta shigo gobe.

*******

Bayan sallan isha Haidar ya shigo gidan da sallamarsa, hannunsa ri茩e da leda Umma ya tarar tsaye ta gama zuba ruwan wanka, ganin Haidar ya shigo ya sa ta koma kan shimfi蓷a ta zauna, Afnan na 蓷aki, zama ya yi ya gaishe da Umma. 

Amsa masa ta yi

Ya ce "Umma ina Afnan ne?"

"Me za ta yi maka?" Umma ta tambaye shi tana kallonsa.

"A'a ba komai kawai dai ban ganta ba ne"

Umma ta ce "Tana 蓷aki"

Tashi ya yi babu kunya zai shiga 蓷akin, da sauri Umma ta ce "Haidar ina za ka? Me za ka yi mini a 蓷aki yanzu?"

Dawowa ya yi ya zauna, sannan ya ce "Umma don girman Allah ki yi ha茩uri da abin da na fa蓷a 蓷azun wallahi su蓳utar baki ne, na san na yi kuskure ki yi ha茩uri don Allah ki yi ha茩uri".

"Ah ni babu abin da ka yi mini, ai dama da farko auren ne ka ce baka so, kuma ka turo Faruk ya ba ni ha茩uri ka kar蓳i auren, yanzu fatana guda shi ne Allah ya ba ka lafiya".

Da sauri ya kalli Umma har zai yi magana sai kuma ya yi shiru, sai can ya ce "Yawwa Umma maganar gyaran mini 蓷akin da ki ka ce za ta yi, an gyara 蓷akin ne?".


"Haba Haidar kai da ka ce baka bu茩ata, ko ganinta ba ka son yi".

"Don Allah Umma ki yi ha茩uri, ta zo ta gyara mini ina so, sannan ta kwaso kayan na ta, ta dawo 蓷akin, na yarda wallahi".

"Ai wallahi 茩arya ka ke yi baka isa ba Haidar, sai dai ka zauna kai 蓷aya a 蓷akin nan, ita kuma muci gaba da zama a nawa 蓷akin, dama ba lafiya ce da kai ba, idan ta ga ji da zama, ta ji ba za ta iya ci gaba da zama da kai a haka ba, sai ka sallami 拼ar mutane ta yi tafiyarta gidansu. zan taya ta da addu'ar Allah ya ha蓷a ta da wani mijin lafiyayye". Da 茩yar Umma ta gama maganar dan ba 茩aramar kunya ta ji ba, ba ta ta蓳a irin wannan zancen da Haidar ba, ko makamancinsa.

Magiya Haidar ya shiga yi wa Umma ya na son fa蓷a mata gaskiya, sai dai ya na gudun 茩ara yin wani laifin.

Da Umma ta ga zai dame ta da surutu, tashi ta yi ta 蓷auki ruwan wankanta ta shiga ban 蓷akin, ta bar shi nan zaune.

Ganin haka ya sa Haidar da sauri ya tashi ya fa蓷a 蓷akin Umma Afnan na kwance a kan kujera, bacci ya fara 蓷aukarta, sai dai baccin bai yi wani nisa ba, alamun shigowar mutum ta ji, a tunaninta Umma ce, shi ya sa ba ta wani damu ba. Haidar ya 茩arewa Afnan kallo da ke kwance babu hijabi a jikinta, ya ga yadda 茩irjinta ya ciko ma sha Allah, sai tsokale masa ido suke yi, wasu yawu ya ha蓷iye, ganin 蓷akin da haske sosai kasancewar a kwai wuta, ya sa shi kashe wutar 蓷akin, ya bu蓷e tagar 蓷akin hasken 茩wan da ke tsakar gidan ,ya hasko ta cikin 蓷akin. A hankali ya taka ya isa kusa da ita. 

Zama ya yi cikin wata lan茩wasashshiyar muryar da bai san ya na da ita ba ya ce "Afnan"

Shiru ba ta amsa ba, ya kuma cewa

"Bab. Afnan" ya yi maganar tare da kai hannunsa ya ta蓳a na ta hannun. 

Bu蓷e ido ta yi, ai tana ganin Haidar zaune kusa da ita, da sauri ta tashi tana lalubin inda hijabinta yake, garin ta mi茩e tsaye ne ta tafi luuu za ta fa蓷i da sauri Haidar ya taro ta ta fa蓷a jikinsa.Ya rungumeta.

"Afnan kashe wutar 蓷akin ki ka yi?" Umma ta yi maganar tana kunna wutar 蓷akin, salati ta yi tare da kashe wutar 蓷akin da sauri.


Amanar cool ce 鉁嶏笍 
***