SIRAƊIN UƘUBA

SIRAƊIN UƘUBA 4

by @nusybee143

🔥 SIRAƊIN UƘUBA 🔥

__Free_book_

✍️Nusy bee

Page 4

Ummiyo Kam ba wajen aikin abincin baƙi ta nufa ba kai tsaye,sauran masu ɗora mata talla ta shiga bi ɗaki ɗaki suna ce mata babu talla,har dai ta kawo ɗakin inna haleema, fuskar nan a murtuke ta tura mata farantin gyaɗar da ta ƙulla jiya tare da faɗin

"Ta dubu ɗaya da ɗari takwas da hamsin ce,saura kuma ki ɓatar min da kuɗi ki gane kuren ki"ita dai Ummiyo ta ɗauki gyaɗa batare da tace uffan ba,dama ita ba mai yawan magana bace

Tana fita ƙofar gida suka kusan cin karo da baffan ta Aliko baban Nadiya,bai kwana a gida ba jiya,ya kwana a ƙauyen kusa dasu inda yake sana'ar shi ta dafa mazarƙwaila,da sauri ta zube tana gaishe shi gami da yi masa Barka da dawowa

Ƙare mata kallo yayi yana amsawa,sannan yace

"Waye ya baki wannan tallan?"

"Karɓowa nayi a wajen inna haleema, su baba Hari sun ce babu talla yau"

"To itama haleeman bazaki je mata tallan ba,mayar mata da kayan ta ki wuce ki kamawa ƴan uwan ki ayyukan da sukeyi na cikin gida"babu musu ta juya ta koma cikin gidan,don ta san baban Nadiya yafi dukkan ƙannen mahaifin ta zafi,tana zuwa ɗakin inna haleema tayi sallama,ko amsawa Inna haleema batayi ba ta hau surfa masifa ta inda take shiga bata nan take fita ba,tun tana yi a ɗaki har ta fito tsakar gida,ita dai Ummiyo tuni ta bar wajen ta shige ɗaya daga cikin ɗakunan da ake gyarawa baƙin

Tana shiga sameera da lubabatu sukayi hanzarin toshe hanci, lubabatu faɗi takeyi"kai don Allah Ummiyo!don Allah ki fita kar ki saka Ni amai,har hanjin ciki na ya fara juyawa,wanne irin wulaƙanci ne wannan don Allah?"

Ta ɗaga kai ta kalle ta,gaba ɗayan su huɗu da ke ɗakin ruƙayya ce kawai ta girme ta da ƴan watanni,amma dukkan su ƙannen ta ne,sai dai hakan bai saka ta damu ba,don ta saba ganin abinda yafi haka, bata ce uffan ba ta cigaba da aikin ta

Sameera ce ta buga tsaki tana faɗin"to gaskiya idan bazaki fita ba mu ba baƙin zafi bane sai mu fita, fisabilillahi sai kiyi tsiya ayi miki Magana ki yiwa mutane banza don wulaƙanci, saboda mugun halin da kika gada daga uwar ki?don naji ance itama nuƙufurcin tsiya gare ta, gaskiya idan baki fita ba zan fita"

Ba yau aka saba ciwa mahaifiyar ta mutunci a gidan ba,ba ga manya ba Baga yara ba,sai dai bata ga laifin su ba,don da bata bar ta bayan rasuwar mahaifinta ba da bata hau wannan SIRAƊIN UƘUBAr ba, ballantana har ta kai ga wannan matakin da ko kare ƙyamar ta yakeyi ballantana mutanen garin nasu,tunanin ta ya yanke sanda taji zaliha na faɗin"to ke sameera da kike maganar a bar ta a ɗakin a fita,bakya tunanin ɗakin zai kama hamamin jikin ta?kinga daga nan sai ƴan birnin su kamu da wani ciwon ko?sanadin shaƙar mummunan wari,kinsan dama mun fi su ƙwari,to a bar mu da abar mu,don haka itace ya kamata ta fita"

"Gaskiya dai,ke Ummiyo fita tun muna gane juna"a cewar lubabatu

Ko kallon banza basu ishe ta ba,duk irin zagi da cin mutunci da wulaƙancin da sukayi mata babu wadda ta cewa uffan, kuma gashi itace ƙarfin aikin

Tsayin awanni biyu da ƴan mintuna ya ɗauke su kafin su gama gyaran,suna fitowa kuma taga inna haleema a zaune a bakin ƙofar ɗakin ta fuska a cunkushe,sai ya da habaici takeyi,ashe wai agololin nata Madina da Zubaida ta bawa tallan gyaɗar,shine take ta habaice-habaicen ai tana da yaran,ƴan mutunci ƴaƴan gata,ba irin wadda aka hana ta bawa tallan ba

Wata muguwar harara ta makawa Ummiyo, Ummiyo ta ɗauke kai ta shige ɗakin ta batare da ta nuna ta san da halittar wata inna haleema ba

Bata juma a ɗakin ba ta fito ta nufi ɗakin baba Hari ta amshi kokon ta na karyawa,tana gama sha ta shige wanka kamar yadda taga kowa yanayi,sai dai ita saɓanin sauran da ruwa kawai tayi nata wankan, lokacin har an fara sauke girke girken da akeyiwa waɗannan manyan baƙi da ake ta kambamawa,ita kuwa a gare ta da zuwan su da rashin zuwan su duk ɗaya a wajen ta

Bayan ta fito daga wanka ta shafa man alayyadin da ƙawar ta saude ta ɗan tsiyaya mata a kwalba,bata sake bin ta kan komai ba tayi kwanciyar ta akan matacciyar tabarmar ta,don a gajiye take,ga wankan da tayi banda tayar da dauɗa babu abinda yayi mata,sai tsamin dauɗa takeyi,amma ko a jikin ta,tayi kwanciyar ta,har bacci ya sake yin awon gaba da ita

Bata sake sanin me takeyi ba sai da taji Nadiya na tashin ta cikin farin ciki,tana farkawa tace"Ummiyo ki fito, baƙin sun ƙaraso,baki ga motocin su ba wallahi,kamar a landan,sai ƙamshi sukeyi kamar furen aljanna,ke dai kawai zo ki gani"babu musu Ummiyo ta miƙe ta bi Nadiya don ganin baƙin da Nadiyar take ta kurarawa

MALUMFASHI,KATSINA STATE, NIGERIA

"Auta!auta!!auta wai bakya ji na ne?"

Wata mace ce wadda aƙalla zata kai shekaru talatin zuwa da biyar tayi firgigit kamar mai bacci gami da ture kwanon ɗan waken da ke gaban ta,wanda tuni ya daɗe da sandarewa saboda rashin kula shi da akayi tsawon lokacin da aka zuba shi

Wata dattijuwa ce,wadda aƙalla zata kai shekaru saba'in,amma kamala ta ɓoye tsufar ta,fes take cikin shigar mutunci,ta ƙaraso ta zauna gefen ta ta kalle ta cikin kulawa tana faɗin

"Auta tun ɗazu kika zubo abinci,ina ta jiran ki kare cin abincin kizo ki je kiran da Hajiya Hadiza take miki amma naga ko taɓa abincin bakiyi ba,ina zuwa kuma sai naga kin faɗa tunani, tunanin me kikeyi haka?"

Murmushin ƙarfin hali auta tayi tace"ba dai tunani ba ko inna?bacci ne ya fara ɗauka ta,kin san jiya hidimar bikin Abida bai bar Ni na kwanta da wuri ba, gashi na tashi saboda sauran aikace-aikace da suka rage"

Kallon tsaf inna tayi mata kafin tace"to shikenan, Allah ya kyauta,ki gama cin abincin sai ki je ki kwanta"auta bata sake magana ba ta kama cusa ɗan waken da take jin shi kamar magani, lokaci lokaci kuma tana goge hawayen da suke taruwa a idanun ta,don ita kaɗai ta san irin suyar da takeji a ranta

Inna bata juma da tafiya auta taji sallama,ta ɗaga kai da murmushi a fuskar ta tana amsawa,ya shigo ya zauna shima yana murmushi,ta gaishe da girmamawa"yaya aƙilu ina kwana!"

Da murmushi shima ya amsa mata gaisuwar kafin ya tambaye ta ya gajiyar bikin Abida,wadda ta kasance ƴar yayar ta ce da take bi zuwaira,shi kuma ƙanwar shi ce, mahaifiyar tata ta rasu shekaru goma sha biyu baya,yanzu shine yake riƙe da yarinyar

Bayan sun gama gaisuwa a nutse ya dube ta,cikin kwantar da murya ya kira ta

"HABEE"

"Na'am yaya"ta faɗa tana daidaita nutsuwar ta

"Habee menene matsalar ki?kar ki damu ki gaya min,nayi miki alƙawarin in dai ina da dama sai na magance miki matsalar ki ko ta mecece in sha Allahu"

Ƙwalla suka ciko idanun habee,ta goge sannan ta kalle shi cikin karayar zuciya tace"yaya aƙilu ina cikin damuwa,a ƴan kwanakin nan ina yawan yin mafarkin ta,ban taɓa ganin ta cikin farin ciki ba,sai dai naga tana kuka tana kira na nazo gare ta,to jiya kuma nayi mafarkin wai gata tana tafiya a cikin wata duhuwa, cikin wata ƴar siririyar hanya tana kuka,ga ababen tsoro a wajen,yaya aƙilu idan nace bana jin zafin rabuwa da ita nayi ƙarya"ta ƙarashe cikin kuka mara sauti

Duk da cewa yaya aƙilu yaji damuwar abinda ya gaya masa amma sai ya basar yana murmushin ƙarfin hali,ya dube ta yana faɗin"auta har yanzu da sauran ki,banda abin ki kin manta cewa mafarki ba gaskiya bane?kuma ma masu fassarar mafarki sun tabbatar da cewa mafarkin kuka alkhairi ne,na dariya shine sharri,sannan sauran abubuwan da kike gani shaiɗan ne kawai yake son yayi wasa da tunanin ki

Kuma ko da ace gaskiya ne idan kika riƙe addu'a inaga sai tafi yi mata amfani fiye da wannan hawayen da kike zubar mata ko?"

Kalaman Alhaji aƙilu sun ɗan sassauta zuciyar Habee,ta ja ajiyar zuciya ta sauke sannan tace"in Sha Allahu zan ƙara dagewa akan addu'a, Allah ya tsare ta a duk inda take"

Ameen ameen,yanzu dai kin san me nake so dake?"Habee ta girgiza kai batare da tace komai ba tana kallon yayan nata

Alhaji aƙilu ya cigaba"kin san dama zamu koma garin Sokoto da zama baki ɗaya, dalilin bikin Abida ne muka tsayar da tariyar sai an gama,amma yanzu in Sha Allah nan da ƙasa da wata guda zamu bar garin nan zuwa garin Sokoto,idan kin amince ki bi mu can,idan yaso sai ki koma makaranta abinki,ki manta duk wani ƙunci da kike fama dashi,amma shawara tana gare ki"

Murmushi ya faɗaɗa a fuskar Habee,tana matuƙar jin daɗin yadda yayyen nata suka damu da damuwar ta, basa ƙaunar ganin ta cikin ɓacin rai ko kaɗan,dama haka Allah yake tsara lamuran shi,sai ya buɗa maka ta wani ɓarin amma ya jarabce ka ta wani ɓarin,ita kam ɓangaren yayyen ta alhamdulillah,babu kalar tarairayar da basayi mata tunda ta dawo gida

GIDAN SA'IDU MANOMI, ƘAUYEN ALBASU, KANO STATE

Gida kam ya ɗau harama sosai na saukar waɗannan manyan baƙi masu daraja a wajen waɗanda suka kawowa ziyara, yaran gidan manyan su da ƙanana sun kewaye motocin nasu sai kallo sukeyi,masu rawar kan cikin su har da shafawa,sam basu kula da irin kallon wulaƙanci da yawancin baƙin suke bin su dashi ba

Daga bakin ƙofar gidan Ummiyo ta tsaya tana bin komai da kowa da kallo a tsanake,ita kuwa Nadiya da gudu ta ƙarasa kusa da motar kamar zata kifa haka take duƙawa don gaida baƙin,shi kanshi Sulaiman sai da abin yaso bashi dariya ganin ɗabiar mutanen,amma sai ya ayyana hakan itace yanayin rayuwar su,wadda kowa da irin tashi,don haka shi dai yabi sahun iyayen nasu masa wajen amsa musu gaisuwar cikin fara'a

Ita kam Ummiyo batayi cikakkun sakwanni biyar a bakin ƙofar ba ta juya ta koma cikin gidan,kai tsaye ɗakin ta ta nufa,ta kwanta tana kallon ramukan ɓeraye da kyankyasan da suke taya ta hira a ɗakin duk dare

A ɗakin iya Sabuwa aka sauke su,ita kanta tayi farin ciki sosai na ganin ƴaƴan nata,don kai tsaye ta nuna da su ta damu,sai wasu daga cikin jikokin nata da take so,kamar Amra da Nusra,waɗanda aka sakawa sunan ta,sai Sulaiman,a cewar ta shi ba mutumin banza bane,baya gudun asalin shi,amma ragowar dama ba shiri suke ba, musamman Azad,beely da Auwab,a cewar ta basu da tarbiyya basu da ɗa'a,wannan shaidar tana yi musu zafi, musamman Hajiya Raheena da ta san Auwab bai san yadda zai raina babba ba,asalima ita bata taɓa bari babba ya raina ƙarami,ko mijinta yana matuƙar yaba mata ta fuskar tarbiyya

Hajiya ke kika san haka😁innarmu dai bata sani ba🫣

#likecommentshare

#Nusy_bee