SIRAƊIN UƘUBA 5
by @nusybee143
🔥 SIRAƊIN UƘUBA 🔥
__Free_book_
✍️Nusy bee
Page 5
Basu juma sosai a ɗakin inna sabuwa ba suka wuce ƙaton ɗakin da aka tanadar musu don cin abinci,an kai musu komai an jere,Beely da surayya ana fara serving ɗin su suka ce baza su ci ba,a ƙoshe suke
Hajiya Raheena cikin kufula ta juya shuwa ta rufe surayya da faɗa, kasancewar kaf yaran nata suna jin Yaren ta,ta nuna mata ɓacin rai sosai kan ƙoƙarin ƙara ɓata mata suna da take shirin yi a tsakiyar dangin miji,Hajiya Salma tayi saurin katse ta da faɗin"a'a Hajiya,ƙyale ta tayi ra'ayin ta,kawai don tace bazata ci abinci ba sai ki kama yi mata faɗa?ki ƙyale ta taji da damuwar dake ranta"
Shiru Hajiya Raheena tayi batare da ta sake magana ba,ta daɗe da gane salma tafi ta tsageranci da rashin kunya, shiyasa basa taɓa daidaitawa da uwar mijin nasu
Bayan awa ɗaya sun kammala komai,sun sake dawowa ɗakin inna sabuwa,ita dai Hajiya salma har ma da yaran ta ji sukeyi kamar a kan ƙaya suke
Barrister Umar ne ya kalli mahaifiyar tasu yace"Ni kuwa Inna har yanzu banga yarinyar wajen yaya Garba ba"
"Ai kuwa tana nan,ina Nadiya?ke Nadiya?"kusan ƴan mata biyar ne suka shigo suna tambayar"inna me za'ayi miki yanzu?"
Inna ta galla musu harara tace "ku fice ku bani waje, Nadiya nake Kira"lieutenant general Usman yana murmushi yace"inna bar su su gaisa da ƴan uwan su su san juna,ku shigo ku zauna,ke,je ki kira Nadiya da Ummul khairi ƴar gidan marigayi yaya Garba"lubabatu da aka aika ta amsa cikin girmamawa sannan ta fice da sauri don isar da saƙon da aka bata
Ƴan mintuna sai ga Nadiya ta shigo da sallama,ta durƙusa ta gaida su a girmame, waɗanda suka ga dama suka amsa,sauran kuma a yatsine suka kalle ta suka ɗauke kai
Barrister Umar ne ya fara tambayar su game da karatu,babu laifi duk cikin su babu wadda bata gama primary ba,kuma ba laifi suna ɗan ganewa ko da babu yawa,ya yaba musu sosai,babu jumawa Ummiyo ta shigo tana sallama da sanyin Muryar ta
Ɗakin ya ɗauki shiru da shigowar ta,sai bin ta akeyi da kallo,bata ko sake ɗaga kai ta kalle su ba ta rissina ta gaishe su, waɗanda sukayi niyya suka amsa,sauran dai sai kallon ta sukeyi a yatsine kamar sun ga kashi
Da ƙarfi Beely tace"wai tabɗijam! gaskiya an cuci ƙauye"
Barrister Umar ya daka mata tsawa,a firgice ta nutsu,cikin ɓacin rai yace"wannan ƙauyen da kika raina anan aka haifi uban naki da kike taƙama dashi"kafin ya sake magana ma sameera tace"ai bama yanayin mu ƙauyawa bane,yanayin ta ne,bata wanki bata wanka"Hajiya Raheena sai kallon su take tana jinjinawa,ita kam Hajiya Salma tuni ta ɗauke kanta
Feena ce ta miƙe tsaye ta kama hannun Ummiyo suka fice daga ɗakin,da kayan wankan ta ta taimakawa Ummiyo tayi wanka,ta wanke mata gashin ta mai bala'in cika da tsawo amma ya danƙare,don sanda ta wanke mata kan sai da aka zuba kumfa wajen sau shida sannan tayi haske,zuwa lokacin tayi kuka har ta rasa hawayen zubarwa saboda zafi,bayan ta gama yi mata wankan ta saka ta a gaba suka nufi ɗakin ta don duba mata kaya
Gaba ɗaya babu kayan arziƙi,kayan ma sai wari wari sukeyi,gasu duk a yayyage,wasu an ɗinke da zare da allura,feena ta kira Sulaiman,ƙasa ƙasa ta roƙe shi ya je kasuwa,ta gaya masa abubuwan da zai siyo mata
Tana kashe wayar ɓera yazo zai wuce da gudu,ta ƙwala ihu tayi waje,sai daga baya ta leƙo taga Ummiyo a zaune a takure,tace"ki fito don ni tsoron ɓera nakeji,ki zo muje ɗakin inna sabuwa ki shirya"da sauri Ummiyo ta girgiza kai tace"na gode anti,zan shirya anan"
"C'mon ki taso,kizo mu wuce ɗakin inna sabuwa"
"To zan iya zuwa ɗakin baba Hari?"ta tambaya da sanyin murya,feena tace "eh mu je,ni waɗannan ƙwarukan ne bana so,ki fito mu wuce"babu musu Ummiyo ta miƙe tabi bayan ta suka nufi ɗakin baba Hari don ta chanja kayan da feena ta saka Sulaiman ya siyo mata
Wata doguwar riga ta bata ta sanya,ba ƙaramin kyau Ummiyo tayi ba,feena tayi ta koɗa ta,ta bata hijabin da Sulaiman ya haɗo mata dashi,ta saka sannan suka nufi ɗakin inna sabuwa
Da sallama suka shiga, duk da cewa da farko Ummiyo ta so cogewa a bakin ƙofar,amma feena ta ja hannun ta suka faɗa ɗakin
Gaba ɗaya occupants ɗin ɗakin mayar da hankali sukayi gare su,Hajiya Salma mamaki da baƙin ciki ya hana ta magana ganin abinda feena tayiwa Ummiyo,ga waɗannan ƙauyawan da suka cika ɗakin suna ta damun su da hayaniya a cewar ta,da fara'a sosai Barrister Umar yake faɗin"Weldone feena!zo nan Ummul khairi"babu musu Ummiyo ta ƙarasa kusa dashi ta rissina ta sake gaishe su,da yawan mazauna ɗakin sai kallon ta sukeyi ganin yadda ta chanja tashi ɗaya
Sulaiman ne ya kalle ta da murmushi yana faɗin"Ummul khairi ba gaisuwa?"ta ɗaga kai cikin sanyin murya ta gaishe shi,ya amsa yana murmushi,ta gaida Azad da ya kalle ta sau ɗaya ya ɗauke kanshi ya mayar ga waya,bai amsa ba,sai ɗan kallon ta da yayi ya sake ɗauke kanshi yana danna waya yana taɓe baki, ruƙayya ce da taji a duniya babu wanda ya burge ta irin Azad, cikin karya murya tace"Yaya Azad da Kai Ummiyo take fa"
Shi karairayar da takeyi ma dariya ta bashi,ya kalle ta yana faɗin"wacece Ummiyo?"
Cikin jin daɗin ya kula ta ta nuna masa Ummiyo da ke gefe,tunda ta gaishe shi bai amsa ba ta ɗauke kai gefe
Sulaiman ne ya yatsina fuska yana faɗin"menene kuma Ummiyo?"wani banzan kallo Ummiyo ta jefa masa ta ɗauke kai,ita a ganin ta ya raina mata wayo ma,bai jira amsar ta ba yace"menene school name ɗin ki in full?"
Bata san ma da ita yake ba,sai da taji su lubabatu suna ta dariyar shaƙiyanci, ruƙayya cikin dariya tace"ai bata san me kace ba ma,bata taɓa zuwa makaranta ba, kullum aikin kenan talla"
"Talla kuma?"a cewar Beely"dama har yanzu ana wannan yayin?"
"Kin san ƙauye kuma,meye bazaki gani a ciki ba?"a cewar Hajiya Salma tana kallon Ummiyo a yatsine
Ba Sulaiman da su Barrister ba,hatta Hajiya Raheena sai da tayi saurin kallon salma, Barrister Umar ya girgiza kai cike da takaici, Salma bazata chanja ba,harshen ta bazai taɓa saituwa ba,ya kalli Ummiyo cikin tausayawa yace
"Ummul khairi kema kina son zuwa makaranta?"
Tunda suka zo basu ga fara'a a fuskar ta ba sai Yanzu, don tana jin sunan makaranta ta fara murmushi tana gyaɗa kai,cike da tausayawa da jin nadamar banzatar da rayuwar ƴar marainiyar da sukayi lieutenant general Usman yace"kar ki damu kinji, Ummul khairi,da ke zamu tafi mu saka ki a makaranta in Sha Allah,kiyi karatu,gaya min,me kike son zama idan kinyi karatu?"sam bai kula da kallon da matar shi,Hajiya Salma,da yaran su suke bin shi dashi ba,banda Sulaiman,feena,sai haidar da hankalin shi yana kan waya ma,sai Nusra
Murmushin nan bai bar fuskar Ummiyo ba ta amsa da faɗin"likita nake son zama"
An gaida likita ummiyo 😁
#likecommentshare
#Nusy_bee