RAMIN ƘARYA...

Chapter 67-68

by @amanarcool323

💫 *RAMIN ƘARYA....*💫



_WRITING BY AMANAR COOL_✍️



*YOUNG TALENTED WRITER'S ASSOCIATION (YOTA/021)*



Page 67&68



Assalama alaikum taku hafsat collection take muku sallama ina yan gayu suke uwar gida da amarya harma da yan mata yan kwalisa🥳🥳 hafsat collection ta shirya tsab wajan zakulo ma bambanta hadaddun kaya nagayu tundaga kan kayan kawata gida kitchen nasakawa 💃💃 ado da kwalliya shine cikar macen datasan kanta bata wasa da kayan gayu🥰🥰 musamman da suka kasance na hafsat collection gasaukin farashi ga inganci babu inda bama tura kaya cikin aminci da yardar Allah👏🥰 kudai kukasance da hafsat collection ga kadan daga cikin abinda take kawomuku lace,zip gwns ,jaka,takalmi,mayafi yan yayi ,kayan kitchen masu kyau sauki inganci kai tsaye ku tuntubi ta ta wannan number kamar haka *** ko kuyi join group kai tsaye dan ganin kayan datake kawowa mungode sai munjiku mutanan arziki🥳🥳🥳🥰🥰👏👏



__________Wani kalan tsotsa yake yi wa bakinta, hakan ya ƙara tsananta tsoro da farga a cikin zuciyar Afnan, ga wani baƙon yanayi da ta tsinci kanta a ciki.

A hankali Haidar ya ja ta zuwa kan katifar ba tare da ya raba bakinsu ba.

Afnan mutsutsun ƙwatar kanta take yi amma ta kasa, jin ya kai hannunsa saman ƙirjinta, ya sa ta zabura da ƙarfi ta ƙwace bakinta, cikin tsoro da rawar murya ta ce "Don Allah Ya Haidar ka yi, ka yi mini afuwa na tuba, kar Umma ta duba ba ta ganni ba" .

Ai kamar ƙara tun zura shi ta yi, sannan a yadda yake ji yanzu bai ji zai iya ɗaga mata ƙafa ba, saboda gaba ki ɗaya ya fita hayyacinsa, babu in da baya kai hannunsa a jikinta, tun Afnan na yi masa magiyya da basa haƙuri har ta yi shiru, tana ci gaba da kuka, sai da ya ga ma lalubeta son ranshi, da yi mata abin da duk wata ɗiya mace mai cikakkiyar lafiyar da a ka yi wa, za ta ji tana son kasancewa cikin wannan yanayin.

Afnan jin Haidar na ƙoƙarin ɗaukar hanyar sa ta zuwa birnin Lagos ya sa ta zabura da ƙarfi ta ririƙe shi, bakinta na son yi magana sai dai babu hali.

Haidar kuwa wanda ya yi nisa baya jin kira, duk abin da Afnan ke yi, bai hana shi yin abin da ya yi niyyar yi ba.

Umma kam na can tana tiƙar baccinta kamar wadda a ka yi wa wani abin domin ta yi baccin.

Afnan ta yi kuka, ta yi magiyar a banza, domin Haidar bai barta ba, sai da ya tabbatar da su a matsayin miji da mata, sannan ya sarara mata, mirginawa gefe ya yi, ya na jin wani irin farin ciki a zuciyarsa marar misaltuwa, godiya yake wa Allah da ya nuna masa wannan ranar, da bai yi zato ko tsammanin zuwanta nan kusa ba, ga farin cikin samun matarsa da ya yi a matsayin cikakkiyar budurwa, wannan abin farin ciki da alfahari a gare shi.

Jin kukan Afnan na tashi ƙasa-ƙasa ya sa shi koma janyota jikinsa ya rungumeta ya na rarrashinta.

"Shhhhh Beb stop crying, am so sorry, ni ne ko? Ba zan kuma ba, ki yi haƙuri, wannan shi ne cikar kamalar aurenmu, bai kamata muna matsayin mata da miji ba kuma amma mu kasa tabbatar wa da kanmu hakan. Beb haƙiƙa ban irin godiyar da zan yi ba, da Allah ya mallaka mini ke a matsayin mata ba. Afnan na yi matuƙar farin cikin da jin yadda na same ki, thank you appreciate it sweetheart, haƙiƙa ke ce hasken da ta shigo rayuwa ta donmin ta ya yi mini duk wani duhun da ke cikin ta, farkon rayuwar da na yo a baya dariya nake ga waɗan da suke soyayya har nake ganin cewa shirme suke yi, saboda ban yarda da siddabarun dake cikin ta ba. Amma a yau na samu damar gaya miki cewar kin canza kowa ne wani motsi na rayuwata, har nake jin zan iya ɗaukar nauyin kowa ne mai yin soyayya domin ya samu cikar muradin shi, yanzu na yarda in dai har akwai soyayya a duniya to sanadin ki ne Beb, ina miki son da bakina ba zai iya faɗar adadin sa ba, ina so ki ba ni dama domin mu gina rayuwar aurenmu cikin farin ciki da kwanciyar hankali, mu tara wa su Umma da Mama jikoki masu albarka". 

Haka dai Haidar ya shiga yi wa Afnan da ɗaɗab kalamai masu sanyi da ratsa zuciyar wanda a ke yi wa, har ya samu ta yi shiru ta dai na kukan. Afnan kuka kuma ba ƙara min daɗi kalaman na Haidar suka yi mata ba, tarihin rayuwata babu wanda ya taɓa gaya mata cewar ya na yi mata wannan soyayyar sai shi. 

Haidar ya lallaɓata ya taimaka mata ta shiga toilet ɗin dake ɗakin, ta tsarkake jikinta, tana fitowa ba ta zauna ba, ta saka hijabinta. 

Ganin ta yi tsaye ya sa Haidar ya ce "Ina za ki? Ba kwanciya za ki yi ba?".

Da ƙyar ta ce masa "Ɗakin Umma na yi".

Haidar baya son takura mata ne, ya sa shi buɗe ɗakin. A hankali take tafiya ya na kallonta har ta fita a ɗakin, bayan ta ya bi, sai da ta kai ƙofar ɗakin Umma sannan ya juyawar shi, har lokacin Umma bacci take yi ba ta farka ba.

Kwanciya Afnan ta yi, tana tunanin abin da ya shiga tsakanin ta da Haidar, ganin abin take yi kamar a mafarki, wai yau ita ce ta tsinci kanta a irin wannan yanayin. Hawaye ta ji suna bin kuncenta wanda ta rasa ko na me ye.

Haidar yau sakayau yake jin sa, haka ya yi baccinsa cikin farin ciki da nishaɗi.

Da asuba sai da Umma ta tashi Afnan ta yi sallah, da ƙyar ta tashi tana ɗingishi ta yo alwala tana idar da salla ta kwanta a gurin.

Umma ta ce "Afnan lafiya ki ke kuwa? Ko dai ba kya jin daɗi ne?".

Ta ce "Lafiya ƙalau nake Umma, bacci ne nake ji".

Ta ce "To shikenan"

Haidar bayan ya dawo da ga masallaci, ya shigo gaishe da Umma, Afnan na jinsa amma ta yi kamar baccin gaske take yi, dan ko Umma ba ta san idonta biyu ba. 

Umma ta amsa masa gaisuwar, Haidar sai kallon Afnan yake, ya na jin wata nutsuwa na shigarsa, ya yi tunanin ko Umma za ta yi masa magana, sai dai alamu sun nuna ba ta fahimci komai ba, tashi ya yi ya fice a ɗakin.

*****

"Sanusi ya kuka yi da Almu da ka yi masa zancen cewar ya turo a yi maganar?" 

Kawu ya ce "Eh Gwaggo na gaya masa, ya ce za su ɗan shirya ne, saboda da sadakin su za su zo, in da halima auren suke so a yi da wuri".

Gwaggo ta ce "Ma sha Allah hakan ya yi, kai kuma ka yi wa mutane shiru ba ka ce komai ba, ko ba ka yi murna da wannan maganar ba? Ko kuma nuna mini za ka yi ko yanzu ka na goyon bayan matar ka ne?" Ta ƙarasa maganar tana kallon Baba.

Baba ya ce "Gwaggo ai ba ni da abin faɗa. Duk hukuncin da kuka yanke ya yi".

Ta ce "To ai shikenan, sannan ina son ka ja wa matar ka da ƴarka kunne, ka da su ce zasu ja dani akan wannan maganar".

Ya ce "In sha Allah Gwaggo zan yi musu magana".

Bayan Baba ya bar wajan Gwaggo, ko da ya zo Maryam na shirin tafiya islamiyya. Ta ji Baba na yi wa Mama maganar, ashar Maryam ta yi a zuciyarta, ta ƙuduri aniyar sai ta ƙartawa Daudu rashin mutuncin da sai ya yi da ya sanin cewar da ya yi ya na sonta. Ko sallama ba ta tsaya yi wa Mama ba ta fita, tana fitowa a ƙofar gida ta ci karo da Feena suka wuce, Feena ta lura kamar ran Maryam a ɓace yake.

Ta ce "Ƙawata ya a ka yi ne? Waya taɓa mini ke? Na lura kamar ranki a ɓace yake".


Maryam ta ce "Ki bari kawai wannan banzan ne, mai hanci kamar an yi dakon goriba ni zai ce wa ya na so, ita kuma waccan jarabar da Allah ya haɗa mu zama da ita wai ya zo an bashi ni, sai ka ce wata kaza".

Feena ta ce "Ikon Allah wai waye ya ce ya na sonki ɗin?".

Cikin taikaci ta ce "Waye ban da wannan wawan Daudu, dan ya na ɗan kutumar uba, wallahi sai ya gane Allah ɗaya ne".

Feena ta ce "Wa ki ka ce? Daudu? Amma wannan yaron ya cika tantirin ɗan iska, shi yanzu saboda ya raina mutane ke ɗin zai ce ya na so? Lallai ya ɗebo ruwan dafa kansa, wallahi ba ke ba, ni ma ba zan bar shi ba". Mita suka shiga yi.

Kamar daga sama za su karya kwana, idon Feena ya sauka a kan Daudu dake zaune a kan wani dakali shi da abokanensa, ai da sauri ta nuna wa Maryam shi, ta ce "Ji tsoron munafukin Allah can, mu je mu same shi.

Suma Maryam na ƙaraso a dai-dai nan Dauda ya ɓaɓɓaka wata uwar dariya mai kama da gunjin Jaki, gashi wa hangame bakinsa gaba ɗaya, haƙuransa da suka yi shan zuma. Duk sun baya na. 

Wani taikaci ne ya ƙara turniƙe zuciyar Maryam wai yanzu wannan ne a ke son haɗa ta da shi.

Daudu na ganin Maryam ya ƙara washe baki ya ce "Ahh ka ga gimbiyar mata Meramuna, amarya a gurin Daudu, ke ce da kanki? Kin ga ban zo ba har yanzu ko? Wallahi ina shirya miki tsaraba ne..." Bai ƙarasa ba Maryam ta katse shi da faɗin "Kai don Allah dakata hakan, shin na tambaye ka, kai wane irin dabba ne wawa mara hankali? Kai yanzu saboda bauɗewar tunani ni za ka kalla ka ce ka na sona? To wallahi a hir ɗinka, aljanunka su kiyaye tsamiyata, ni na fi ƙarfin mutum shashasha irinka, sannan ina gargaɗinka da ka je ka samu tsohon uban naka mai son zuciya kamar ka, ku janye batun neman auren nan, wallahi wallahi wallahi kaji na rantse maka har sau uku, idan ba ka janye ba, sai ka gwammace uwarka Lami ba ta kawo ka duniya ba. Duk gidanmu babu yarinyar da ka isa ka aura, dan haka ka kama kanka".

Feena ta dube shi ta ce "Kai ma Daudu ban da kai ɗin kamar haihuwar taɓaɓu ka ke, ina kai ina Maryam fisabilillah? Yanzu ka dubi kanka ka dube ta, Daudu duk unguwar nan waye bai san halin ka ba? Yanzu a haka ɗin ka ke tunanin Maryam za ta soka, wallahi kai ma kasan ƙwayar da ka ke sha ta gaya maka ba dai-dai ba".

Cikin zafin rai Daudu ya ce "Ke ke kam zance ubanki yanzu a gurin nan, ita ma na ragama mata ne kawai, amma ke yanzu zan yi maganin ki a gurin nan, ki bar ganin ta ci mini mutunci ina da ya ƙi nin na fiki matsayi a gurin ta".

Maryam ta ce "Wa ka fiya matsayi? To bari ka ji silifas ɗin da take shiga da shi banɗaki ya fi ka daraja da matsayi a gurina, wallahi ka kama kanka da ni". Sai da suka zazzaga masa cin mutuncin son ransu sannan suka bar gurin.

Suna tafiya abokansa suka ce masa ya rabuda ita kawai, ko ƴar gwalce ya haƙura da ita.

Ɗaya daga cikin su ya ce "Ba ta yi iƙirarin duk ƴan gidan sun fi ƙarfin ka ba? To ka nuna mata ƙarya take yi, ai akwai ƴar gidan Sanusi wannan yarinyar Zaliha, sai ka ce ka fasa ba ita ka ke so ba Zaliha ka ke so, wallahi ina mai tabbatar maka da sai ta ji baƙin ciki". Nan sauran abokan suka yi na'am da wannan shawarar, Daudu kuwa ya koma jin haushin da ya ƙyale su Maryam.

****

Har kusan ƙarfe tara Afnan na kwance a ɗaki, har Haidar ya zo yi wa Umma sallama, ya fita tana kwance, sai ya ji duk ya damu, ya san duk dalilin abin da ya faru jiya ne take wannan kwanciyar, haka dai ya fita.

Umma ta ce "Afnan"

A hankali ta buɗe idonta ta kalli Umma 

Umma ta ce "Afnan wai lafiyar ki kuwa? Me yake damunki ne wai?".

Tashi zaune ta yi ta ce "Umma babu komai fa, kawai bacci ne" 

Umma ta ce "To ai baccin ne naki kamar ba na lafiya ba, tun ɗazu nake cewa ki tashi ki karya amma kin yi shiru".

Tashi tsaye Afnan ta yi, a hankali ta fara tafiya tana ɗan ɗin gisa ƙafa, da kallo Umma ke binta, har ta fita toilet ta shiga bayan ta fito ta dawo ɗakin. Umma na nan zaune, zama ta yi .

"Afnan me ya same ki ne? Ni dai na san jiya har na kwanata lafiya ƙalau ki ke, amma yanzu naga kamar tafiyar ki ta sauya, me ya samu ƙafar taki ne?".
 
Shiru ta yi ta rasa me za ta cewa Umma ɗin.

"Afnan tambayarki na ke yi".

"Ƙafa ta ce ke ciwo"

"Me ya samu ƙafar, garin yaya?".

Sunkuyar da kai ta yi ta kasa magana 

"Afnan Haidar ne ko?".

Da sauri ta girgiza mata kai alamar a'a 

"Hmmm" shi ne abin da Umma ta ce, tabbas akwai abin da ke faruwa, jiya ba ta san dawowar Haidar ba, sannan ba ta san lokacin da Afnan ta shigo ɗaki ta kwanta ba, ta dai rabar da za ta yi wanka. Kar dai Haidar taɓa yarinyar nan ya yi? Jikinta ya ba ta ba banza ba.


Yau jirginsu Hajiya Maimunatu ya sauka, gaba ɗaya familyn Abba suka je tarbo ta, tun a hanya take wani shan ƙamshi da Ammi. Mami kuwa sai wani iyayi take yi, kai tsaye gidansu a ka wuce da ita. Ammi kuwa ta ce wa Abba ba ta jin daɗi ita direba ya wuce da ita gida, hakan ba ƙaramin ɓatawa Maimuna rai ya yi ba, ta ga Ammi ta raina ta ne shi ya sa ba za ta raka ta har gida ba, nan ta ci alwashin a wannan karon sai ta raba ƙaninta da wannan matar.


Amanar cool ce ✍️
***