Chapter 69-70
💫 *RAMIN ƘARYA....*💫
_WRITING BY AMANAR COOL_✍️
*YOUNG TALENTED WRITER'S ASSOCIATION (YOTA/021)*
Page 69&70
Assalama alaikum taku hafsat collection take muku sallama ina yan gayu suke uwar gida da amarya harma da yan mata yan kwalisa🥳🥳 hafsat collection ta shirya tsab wajan zakulo ma bambanta hadaddun kaya nagayu tundaga kan kayan kawata gida kitchen nasakawa 💃💃 ado da kwalliya shine cikar macen datasan kanta bata wasa da kayan gayu🥰🥰 musamman da suka kasance na hafsat collection gasaukin farashi ga inganci babu inda bama tura kaya cikin aminci da yardar Allah👏🥰 kudai kukasance da hafsat collection ga kadan daga cikin abinda take kawomuku lace,zip gwns ,jaka,takalmi,mayafi yan yayi ,kayan kitchen masu kyau sauki inganci kai tsaye ku tuntubi ta ta wannan number kamar haka *** ko kuyi join group kai tsaye dan ganin kayan datake kawowa mungode sai munjiku mutanan arziki🥳🥳🥳🥰🥰👏👏
___________Abba ba ƙara min farin ciki ya ke ji ba na dawowar Yayar tasa, Hajiya Maimuna ita kaɗai ta rage masa, ita ce ya ke yi wa kallon uwa tun bayan rasuwar iyayensu, shi ya sa yake mugun sonta da girmamata.
Gaba ɗaya sun baje a katafaren falon gidan ta sai hirar yaushe rabo suke, babbar ƴarta ta ce "Momy wai har yanzu ba a gama girkin nan ba ne? yunwa fa nake ji". Hajiya ta ce "Idan kin matsu sai ki tashi ki shiga kitchen ɗin da kanki ki girka".
"Momy ai dan kin san ban iya girki ba ne".
Dariya suka yi gaba ɗaya, Mami ta ce "Ummie ba ki iya girki ba? Ahh gaskiya ya kamata ki koya kafin ki yi aure, kar a je a riƙa yi wa sirikinmu shirme" . Hajiya ta ce "Ba abin da ta iya dafawa sai indomie".
Dariya Ummie ta yi ta ce "Mami ai tunda na iya dafa indomie ai shikenan, ba sai na koyi wani girkin ba, ko aure na yi duk baƙin da zan yi sai na tarbe su da indomie na haɗa musu da dafaffen ƙwai, da zoɓo mai sanyi".
Dariyar ta suka shiga yi harda Abba.
Mami ta kuma cewa "Ai ke Ummie ba kowa ke son indomie ba"
"Au haba Mami? Ni fa na ɗauka yadda nake sonta kowa ma so yake yi, to duk da haka dai ita zan riƙa yi wa baƙi, idan na yi aure, ciki ko hadda abokan shi, ba an ce suna zuwa cin girkin amarya ba? to zan dafa musu indomie da da faffen ƙwai, na haɗa musu da zoɓo mai sanyi, tunda na iya zoɓo".
Haka suka shiga dariyar Ummie, sai zuba musu shirme take
Abba sun daɗe gidan sannan suka yi mata sallama, suka tafi
Suna isa gida Abba ya tsayar da su a falo ya kalli Mami ya ce "Saratu sake maimaita maganar da ki ka faɗa mini a kan yaran nan".
Mami ta sake faɗa, kafin Abba ya yi magana Mudan ya ce "Wallahi Abba na san na so Huda a baya amma ban da yanzu, gaskiya ba zan iya auren ta ba, Abba don Allah ka ba ta haƙuri".
Ran Mami ba ƙara minin ɓaci ya yi ba, idanuwanta suka yi jajur, ta ji kamar zuciyarta za ta fito.
Abba ya dubi Huda ya ce "Ke daughter ki na son shi ne har yanzu?" Da sauri ta ɗaga kai alamar eh Abba ya ce "To shikenan duk ku tashi ku ba ni guri, na san matakin da za ɗauka". Mudan ya so ya yi magana amma ya kasa, saboda baya iya yi wa Abba rashin kunya.
Suna fita ya ce wa Mami "Na yanke shawarar duka zan aura mishi su ɗin, da Huda da Hasina ɗin".
Mami ta ce "Gaskiya Alhaji ban yarda da auren Hasina ba".
"To shikenan bari na zuba miki ido ki yi duk yadda ki ke so, tunda ni ban isa da su ba".
Ta ce "A'a ba haka nake nufi ba, Allah ya baka haƙuri". Tashi Abba ya yi ya nufi ɗakinsa, ita ma ta shige nata ɗakin.
*******
Bayan an tashe su Maryam daga makaranta, a hanya suka riƙa dariyar Daudu, yadda ya yi wuƙe-wuƙe da ido ya na kallonsu, Feena ta ce "Wai kin ga haƙuransa kamar ba na mutane ba".
Maryam ta ce "Hmmm ai ko iya haka an gama cutar da ni, ni idan wannan zancen ya fita ai sai na ji kunyar fita waje".
Dariya Feena ta yi suka ci gaba da ai bata Daudu
Daudu ko su Maryam na barin gurin ya je ya samu Babansa ya ce masa ya fasa auren Maryam, ba ita yake so ba, ƴar gidan Sanusi yake so Zaliha. Baban ya amsa masa da to ya ce "Zan yi wa Sanusin magana, amma tun farko me yasa ka ce waccan ɗin ka ke so?"
Ya ce "Baba ni fa da ma ba ita na ke so ba, sai bayan da na faɗa maka cewar ita nake so, naga sam ba ta dace da ni ba, saboda yarinyar ba ta da kunya ko kaɗan".
Malam Almu ya ce "To shikenan".
Umma dai da ta gaji da tambayar Afnan me yake damunta, ta zuba mata ido, ta san tabbas akwai abin da ke faruwa, sai dai ba za ta tsaurara bincike ba, koma me ye ne su can su ƙarata, ta yi alwashin ba za ta sake shiga sabgar su ba, saboda ta lura Afnan ɗin ba wadda za ta ba ta haɗin kai ba ce.
Da sallma ya shigo gida jiki a sanyaye ya wuce ɗakinsa, Umma ta bishi da kallo ganin ya shigo cikin wannan yanayin da ba ta saba ganin sa a ciki ba.
Haka kawai sai ta ji ta damu da yanayin da ta ganshin ɗin, ɗakin nasa ta shiga, ta tarar da shi zaune ya yi tagumi.
Ta ce "Haidar lafiya me yake damunka ne? Na ga lafiya ƙalau ka fita a gidan nan?".
Ɗago kai ya yi ya dube ta cikin yanayi na damuwa ya ce "Umma abin da ke damuna kin hana ni yin magana akansa. Duk da wannan karon an zo mini da abu mai rikitarwa da ruɗar wa a ciki".
"Haidar me ya faru ne? Wane abu ne aka zo maka da shi da zai saka shiga wannan damuwar?".
"Umma don Allah ki yi haƙuri da tambayar da za ki ji daga gare ni. Duk da kin hana ni yin zance, amma ya zama dole na san abin da ke faruwa, Umma waye mahaifina? Idan kuma baya raye kamar yadda ki ka faɗa, ina ne danginsa suke?".
Nan take fuskar Umma ta sauya, ɓacin rai ya bayyana ƙarara a fuskarta, idanuwanta suka sauya launi.
Cikin kakkausar murya ta ce "Haidar ban hana ka yi mini wannan maganar ba? Bance maka ba na buƙatar na ji ka sake tambaya ta dangin mahaifinka ba? Ina ce mahaifinka shi be dolenka kuma baya raye, to dole sai kasan inda danginsa suke? Ka da ka sake zuwar mini da wannan maganar, ina son wannan karon ya zama shi ne na ƙarshe da za ka sake yi mini tambayar nan".
"Umma please don Allah ki tsaya ki saurare ni, wallahi ina cikin damuwa ne, ki tsaya ki ji dalilina na koma yi miki wannan maganar".
"Ba abin da zan tsaya ji daga gare ka, ka da ka sake zuwar mini da zancen nan". Daga haka ta tashi rai ɓace ta bar ɗakin na sa.
Dafe kansa ya yi ya rasa me yake yi masa daɗi, maganar da dattijon nan ya gaya masa ce take dawo masa ɗaya bayan ɗaya. "Ka je gida ka tambayi mahaifiyarka ta gaya maka waye kai? Ina mahaifinka yake? Ka sani mahaifinka na raye, kuma yana nan ya na rayuwa cikin farin ciki da kwanciyar hankali".
Sake dafe kansa ya yi, ya ce "Haba Umma me yasa za ki yi mini haka? Don Allah ki fitar da ni daga cikin wannan ruɗanin da zuciyata take ciki".
Mama suna zaune suka ji ɓaɓatun Hajara, cikin masifa da ɗaga murya take bala'in babu wanda ya isa ya aurawa ɗiyarta wannan barbaɗaɗɗen yaron, "Wato ni za a yi wa munafunci? Ai tun farko ba ita ya ce ya na so ba, yanzu za a zo mini da wannan maganar, to wallahi ban yarda ba".
Tashi Maryam ta yi ta zuba da gudu ta yi waje, Mama na kiranta amma ta ƙi tsayawa, Hajara na tsaye a gefen iccen dake tsakar gidan, sai masifa take yi da kumfar baki, tunda Kawu ya zo mata da maganar ga abin da Malam Almu ya ce masa, ta fito ta nufi ƙofar ɗakin Gwaggo sai dai Gwaggon ba ta nan, shi ya sa ta zo nan tana masifa.
Maryam tsaye ta yi ta shiga tuntsurar dariya, ta ce "Allah na gode ma, aniyar muɗa ta bi randa, Allah ya gwada muku shi a sarki, to me ye abin ta da jijiyar wuya? Naga ai Daudun yaron kirki ne, bashi da matsala".
Ana haka sai ga Gwaggo ta shigo tana faɗin "Me yake faruwa ne? Tun daga ƙofar gida nake jin hayaniya?".
Hajara ta ce "Wannan ɗan iskan yaron ne, ya aiko wai ba Maryam yake so ba Zaliha, kuma wallahi ba zan yarda ba".
Zaliha da ita ma shigowarta kenan, ta ji abin da Hajara ke faɗa, fashewa ta yi da kuka ta ce "Ni kuma? Allah ba zan auri wannan ɓarawo ba".
Gwaggo ta ce "Ai wannan maganar banza ce, ita ɗin da ya ce ya na so tun farko ita ɗin za a bashi, shakuruminki shalelena ba wanda zai aura miki shi, tunda ba ke ya ce ya na so ba, wannan duk makircin Amina ne, kuma zan yi maganin ta".
"Au saboda ni ce maƙiyiyarku? To wallahi ni ma ba wanda ya isa, ya aura mini shi, ita da yake ƴar gwalce ai ba za a so ranta da na uwarta ya ɓaci ba, sai mu, to muma Allah ne gatanmu, kuma ki sani Gwaggo duk abin da ki ke yi mana dan ki baƙanta mana rai, bamu be ba kya so ba ɗanki ne ba kya so, sannan yadda ake son a gane mu a wulaƙance da izinin Allah ba zamu wulaƙanta ba, sai dai ƴan baƙin ciki su mutu". Nan Maryam ta shiga amayar musu da abin ke ranta, sai da ta yi mai isarta sannan ta bar wajan.
Hajara ta ja Zaliha tana ci gaba da masifa.
Gwaggo barin gurin ta yi.
Afnan ta ɗauki wayar Umma ta kira layin Mama, Mama na ɗauka ta ji Afnan ce, cikin farin ciki suka gaisa, Afnan ta ce "Mama ina Baba? Ina so mu gaisa da shi".
Mama ta ce "Ya fita, sai dai in ya dawo".
Ta ce "To ina Maryam? Mama don Allah ta zo yanzu ina son ganin ta".
Ta ce "Lafiya dai Afnan?"
"Babu komai Mama kawai dai ina son ganin ta ne yanzu".
Ta ce "To shikenan zan gaya mata, in sha Allah za ta zo, ina sirikar taki?"
Afnan ta ce gata nan kwance ina ga bacci take yi".
Sallama suka yi, Mama na ajiye wayar Maryam ta shigo, Mama ta ce "Yanzu Maryam duk kiran da na yi miki sai da ki ka je gurin nan?".
"Wai Mama haka za a zuba musu idon ne? Ni fa ba zan iya wannan haƙurin naki ba, idan ka fiye haƙuri cutar da kai ake yi".
Mama ta ce "Allah ya shirye ki, sai ki shirya Afnan ta kira tana son ganin ki".
Da murna ta shirya tana zumuɗi, bayan ta gama shirin tana ƙoƙarin fita, babu za to sai ga Sharifa ta zo gidan, bayan sun gaisa da Mama ne Maryam ta ce mata "Gashi kin zo ni kuma fita zan yi".
Sharifa ta ce "Ba damuwa muje na sauke ki inda za ki ɗin, ni ma ina sauri ne, kawai dai na ce bari na biyo mu gaisa, ina Aunty Afnan take ne?"
Maryam ta ce "Ai gidan ne za ni"
"Gidan aure ta yi shi ne ba ki gayyace ni ba?".
"Yi haƙuri auren ne ya zo a bazata".
Sallama suka yi wa Mama suka fita.
Basu ɗauki lokaci ba suka ƙaraso ƙofar gidan, da sallama suka shiga gidan, fitowar Umma kenan daga ɗaki ta yi tozali da Sharifa, cikin razani ta ce "Innalillahi wa'inna ilaihim raji'un". Luuu ta yi baya za ta faɗi da sauri Haidar ya ƙaraso ta faɗa jikinsa.
Amanar cool ce ✍️
***