Chapter 12
by @khairatup01
RUFAFFEN DUMA
Ummulkhair S Paisau.
(khairatup)
Wattpad:khairi_muhd
arewabooks:khairatup01
12
*
Cafe ɗin cikin ofishin ta shiga ta zauna dama ta turawa Smith saƙon ya same ta a nan. Ta buɗe littafin rubutun ta amma ta kasa rubuta ko da kalma guda a ciki sai wasa take yi da biron hannunta kamar yadda zuciyarta ke kai komo.
Smith ya sa hannunsa biyu ya tafa a kan fuskarta, a dan firgice ta juyo tana kallon sa. "Ka bani tsoro Smith."
Zaunawa yayi yana dariya . "Wasa nake miki naga kin nutsa can kina tunani. Me kike nazari ne?
"Paul Stone!"
Ya kalle ta da kyau kafin yace "Wai baki haƙura ba Maryam?"
"Kai ma ka san ba zan haƙura ba ai."
"Maryam why sai ni?"
"Saboda wannan fuskar taka tana gaya min akwai sauran bayanin da baka gama gaya mini ba."
"Maryam a halin yanzu bacci ya kamata kiyi don da ganin cikin ƙwayar idanuwanki baki bacci ba kwana biyu."
"Ban rufe su ba,kuma ba zan rufe ba sai ka gaya min abinda nake son ji."
"Maryam bamu da komai sai inuwa kawai."
"Smith abokina,ba zamu ci gaba da bin inuwa kawai ba. In har mu na son sanin ainihin abinda ya faru da Paul dole ne sai mun je wurin da za mu samu amsar tambayoyin mu."
Ya ɗaga gira ya kallon ta. "Wanne wuri kenan?"
"Gidansa."ta faɗa tana kallon cikin idanuwansa. "Ina son ka kai ni can gidansa. Ina son na ga kayan aikinsa,kwamfutarsa,teburinsa,takardunsa...."
"Maryam kin haukace? Kina gaya mana mu kai kan mu gidan zaki ne. Ba kya tsoron masu bibiyarmu su samu galaba a kan mu?"
"Ban damu ba. Na shigo aikin nan ba don ina tsoro ba sai don ina son na bayyana gaskiya."
"Maryam..."
"Smith don Allah. Ina ji a jikina akwai abinda zamu samu."
"Ina tsoro."
"Ba komai ina tare da kai."
"Yaushe?"
"Cikin dare."
Ajiyar zuciya ya sauke ya na kallonta ya kuma ɗauke kan sa ya ce ban san gidansa ba amma akwai abokinsa Godwin zan same shi ya gaya min kwatancen sai na gaya miki muje amma ba yau ba."
"Kana ganin zamu iya yarda da wani bayan kan mu?"
"Zamu iya ɗaukar risk."
"Alright zamu yi. Ina son na shiga rayuwarsa kamar yadda ya bari. Paul yana kan wani babban abu ne kafin ya ɓata. Idan kuma mun ce zamu bibiyi rahotannin hukuma ba zamu samu komai ba don a ko ina akwai azzalumai."
*
Smith ya lullube fuskarsa da facemask baƙi ,ya sanya baƙin gilashi ya rufe idanuwansa. Wayarsa ya zaro daga aljihunsa ƴar ƙaramar keypad ya danna wata lamba ya kira ana dagawa yace "Ina bakin shagon."
Ban san me aka ce masa ba dai ya shiga shagon. Ya tarar da wanda ya je gani kan kujerar roba ,yana shan sigari,yana wasa da wayarsa.
"Good afternon" smith ya faɗa cikin nutsuwa,ya zauna ya zame gilashinsa ya ajiye a gefe kan teburin.
Godwin ya ɗago a hankali,yana kallon Smith daga ƙasa zuwa sama yana tantance shi. Sannan yace "Afternoon. Waye kai?"
"Smith.ina neman wani ne da ake kira paul Stone. An gaya min kai da shi aminai ne."
Wani murmushi mai cike da raini Godwin ya saki. Ya maimaita sunan "Paul Stone? Hmm..tsohon abokin ne amma me yasa kake tambaya?"
Smith ya jinjina kan sa,ya ciro littafin sa na rubutu ya yi rubutu ya kalli Godwin yace "Ina son ka bani adireshin sa ne kawai."
Godwin ya kwantar da sigarinsa,ya jingina da kujera yana shafa gemunsa yace "kai ɗan sanda ne?"
"Aa." Smith ya amsa da sauri. "Ni ɗan jarida ne. Ina bincike ne a kan Paul ne saboda gudunmowar da ya bawa jarida ina son mutane su san shi."
Godwin yayi shiru na ƴan daƙiƙu,sai ya yi murmushi wanda bai kai zuci ba. "Paul baya son baƙi....amma... sai ya lumshe ido sai kuma ya ce "For a little token,zan iya gaya maka inda yake da zama a wancan lokacin."
Tuntuni dama Smith ya gane Godwin ba aminin arziƙi ba ne don akwai ma'anoni a cikin maganganunsa. Yana jin akwai almar tambaya akan Godwin.
"Baka da matsala,zamu baka ko nawa kake so." Ya faɗa cikin dabara.
Cikin magana irin ta area boys ya kalli Smith da turanci yace masa "look my friend be careful where you dig. Paul's enemies are not the kind you want to meet. Even me." Yayi dariyar mugunta ya ci gaba "i dey protect myself."
Smith ya gane ya shigo cikin wata cakwakiya shi ma. Yana cikin yanayin da zai iya kawo mai haɗari. Amma haka ya kalli Godwin cikin ido yace "I'll take my chances . Kawai ka gaya min adireshin."
Godwin ya ɗaga kafaɗa yace masa "Rubuta." Ya gaya masa adireshin shi kuma ya rubuta a cikin littafin na sa. Godwin ya ce da shi "Gashi nan na baka. Amma kar kace ban gaya maka ba."
Smith ya miƙe zuciyarsa na bugawa . Yana jin wannan adireshin zai kai su ga wata gaskiyar da suke nema ko kuma cikin haɗarin da basu taba zata ba.Ya bashi kuɗi kamar yadda ya buƙata.
DARE
10:00PM
Smith da Maryam na daga gefe a tsaye daga can ɗaya ɓarin na titi suna kallon ƙofar gidan Smith. Dare ne baka jin komai sai kukan karnuka da kuma hasken fitilu unguwar ma babu mutane sosai shiru layin.
Smith ya kalli Maryam yace "Maryam kin shirya?"
Ta gyaɗa mai kai tace "Muje."
"Da zarar fa mun shiga ba gudu ba ja da baya."
Duk da zuciyarta na bugawa kamar ana buga ganga sai da tace da shi "Na shirya."
Smith ya fitar da maɓallin kwaɗo ya ɓalle ƙofar. Ƙarar buɗe ƙofar tayi wani irin ƙara mai sanyi da ya sanya suka ji ɗan tsoro kaɗan suka kalli juna.
Suna shiga ciki Maryam ta kunna fitilar wayar ta ganin cikin da duhu. Gidan a cike yake da ƙura ga yana ta ko ina. Tari ta yi ta sa hannu ta toshe bakinta tana kallon bagon falon. A hankali ta isa kusa da teburin Paul akwai laptop a kai wadda ta sha ƙura.
"Anya kuwa Smith sun san da wannan laptop ɗin kuwa?,Murya na rawa ta ce Smith ka kunna mu gani.
Smith ya matsa ya kunna laptop ɗin. Tana gama kamowa ya ga hakan nan ana rubutu a jiki an sa masa "WHO ARE YOU?"
Maryam ta yi baya da sauri ,zuciyarta tayi wani ɗan tsalle . Smith...wannan...waye ya rubu..."
"Calm down ba wani abu ba ne. Laptop ɗin is hacked suna yin haka hackers ana kallonmu. Bamu da isashen lokaci muyi sauri muyi abinda zamu iya mu tafi kafin a zo a same mu.
"Haka ne." Nan suka dinga tonu takardu tsofaffi fila-fila suka yi wa ma'ajiyar Paul har ta sare sai kuma ta buɗe dirowa ta hango wata takarda da wani hoto. Ta jawo ta riƙe a hannunta tace "Smith zo ka gani wannan hoton tsofaffin manyan ƴan kasuwan nan ne kamar da kuma Sana...." tayi shiru jin kamar motsi bayan nasu a ciki gidan.
Smith ya tsaya cak ya na kallon inda suka ji ƙarar ya kalli Maryam da tuni idanuwanta sun firfito waje tana kallonsa a tsorace.
Hannunsa ya saka ya sa a kan bakin sa alamar tayi shiru kar ta yi magana.
Takardar da hoton ta nannaɗe ta cusa a cikin rigarta da sauri.
"Smith."
"Ki tsaya a nan."
"Aa kar ka bar ni a nan ni kaɗai Smith mu je tare..." wani ƙarar sautin ta kuma ji sai gata a gaban Smith da sauri ta riƙe hannunsa gam-gam.
Smith ɗin ma a tsorace yake amma haka ya dake ya sa hannunsa biyu kan bakinsa alamar kar ta kuma magana.
Inuwa suka gani ta bayyana a cikin ɗakin, ba a ganin fuskar amma mutum ne a tsaye kakkaura da shi.
Maryam ta saki wayarta a ƙasa don tsoro ta saki ihu.
Smith ya ce "Maryam!"
Tsugunnawa tayi ƙasa ta ɗauki wayar hannunta na rawa ta kuma kunna ftilar amma bata ga kowa ba suka kuma haskawa.
"Smith mu tafi don Allah."
Smith yace "Maryam tsaya ba kya jin warin gas na tashi?"
Idanuwanta ta kwalalo waje tace "Am sorry Smith ni na jawo maka."
"Maryam mu fita daga nan."
Basu kai ga fita ba aka kashe fitilar dake haska ragowar wurin tuni duhu ya lullube ko ina. Maryam na iya jiyo bugun zuciyarta a kunnen ta. Sai kawai ta ji ihu daga sama. Smith ya yi tsalle ya kare ta,yayi da wani abu mai kaifi ya bugi bango.
Wani mutum ne ya fito daga wani ɓari na gidan ya tsaya a gabansu tsam fsuskarsa a rufe take da wani baƙin kyalle . Bai yi wata magana ba kawai ya janyo wuƙa a ƙugunsa ya kai wa Maryam hari.
Smith ya yi saurin dakatar da shi ,suka fara kokawa a cikin duhu,ƙarar ƙarfe na buguwa da bango ko ƙasa.Tuni Maryam ta takure a gefe guda tana neman lambar wayar Muhamamd shi ne kaɗai ya faɗo mata a ranta.
Aikuwa cikin sa'a ta same shi nan tace mai "kai taimaka mana muna cikin matsala zasu kashe mu. "
"Kina ina Maryam ke da waye?"
A firgice ta gaya mai adireshin ta kashe wayar. Fitilar wayar ta haska nan ta ga Smith na riƙe da hannun maharin,amma bai yi aune ba ya wafce hannunsa cikin azama ya soka wuƙar a gefen cikin Smith.
"Smith" Maryam ta faɗa da ƙarfi." Da gudu tayi wurin shi amma maharin yayi tsalle ya fice ta taga.
Smith ya durƙasa ƙasa hannunsa riƙe da wurin da aka soka mai wuƙar jini na zuba kamar an yanka kaza.
"Maryam.." ya faɗa da ƙyar cikin ƙarfin hali ki tafi ,ki gudu zasu dawo na ji kamar an sa gas yana likin Maryam go save yourself."
"No! No! Smith ba zan bar ka ba. Tare muka zo tare zamu tafi." Ɗan kwalinta ta saka ta danne wurin da jinin ke zuba tana hawaye. "Ba zan bar ka ka mutu ba Smith."
Tashi tayi da ƙyar ta samu ta lallaba ta ja Smith ta soma fita da shi daga gidan ya mata nauyi amma haka take jan sa tana kuka tana jan numfashi kafin su ƙarasa fita ya suma.
Suna fita gidan ya tashi ji kake boom ƙara mai rikitarwa. Faɗuwa tayi a ƙasa ita da Smith ɗin duka tuni jikinta ya soma karkkarwa tayi kaca-kaca da jinin Smith. Da tuni suma yanzu sun ƙone a cikin wannan gidan? Tuno hakan kawai na sa ruhinta ya soma rawa.
Ji tayi kamar magana a bayansu haka ana "Ku nemo su kamar fa sun fito basu ƙone ba boss ba zai bari ba." Tana jin haka kuwa ta zare takalmanta a hankali ta dinga jan Smith daga tsallake suka raɓe a bayan wata bishiya mai yalwar ganyayyaki. Daga nan tana kallan yadda tiƙa-tiƙan mazan ke nemansu a cikin duhu. Kawo yanzu tana cike da da na sanin kin bin shawarar Smith ga shi yanzu ta yi sanadin da aka soka masa wuƙa. Da sauri ta kama pulse ɗinsa taji tana harbawa suma yayi. A tsorace take sosai.
Ta gama karaya cewa yau kam ba iya Smith ba ita kanta ba zata fita daga wannan wurin da ran ta ba.
Sai dai ƙarar mota ce ta shigo layin ta kasa kunne tana jin yadda motar ke antaya gudu.
Maharin kuwa juyawa yayi ya kalli ɗaya abokin nasa yace "Kai waye yake shigowa nan?"
Motar kuwa tsayawa tayi cak a gaban gidan Paul da ke kamawa da wuta.
Muhammad ya fito daga cikin motar da baƙar jacket a jikinsa ,hannunsa riƙe da ƙaramar bindiga yana kallon yadda wutar ke ƙara girmama. Tuni ya ji zuciyarsa ta tsinke a tunaninsa Maryam ta ƙone a ciki.
Juyawa yayi a fusace ya kalli maharan guda biyu yace "Ina Maryam? Me kuka yi mata azzalumai?" Ya nuna musu bindigar hannunsa.
Ɗayan ya gane shi ya yi tsit. Ɗayan kuma yana ƙoƙarin yayi magana sai kuma ɗayan ya riƙo hannunsa yace masa "Mu gudu wannan ba sa'anmu ba ne."
"Amma waye shi ɗin?"
Muhammad ya saki harbi a iska. Maryam ta kiɗime ta saki ihu cike da tsoro.
Da Muhamamd da maharan inda suka ji ihun suka kalla bayan bishiya.
Tuni suka soma musayar wuta a junansu. Wata mota ta kuma shigowa ita ma. Bouncers ne a ciki da bindigu. Ba sa son harbin Muhamamd su abinda suke so Maryam ce.
Muhammad ya lura suna da yawa kuma suna da makamai kawai ya yanke shawarar komawa cikin mota harinsa shi ne ya je inda Maryam take.
Yana shiga ya yi ribas kamar zai fita ne. A nan suka daina harbin dukansu suka tsaya kallonsa. Basu yi aune ba ya ci wani burki ya afka ciki da gudu daidai bishiyar ya tsaya ya fito ya tsaya a gaban motar ya ga Maryam duk tayi hurjajjan ta fita daga hayyacinta.
"Maryam ku shiga ciki."
"Ya suma."
"Waye?"
"Smith,abokin aikina tare muka zo yana ƙoƙarin ceto na suka soka mai wuƙa a ciki."
"Maryam sau nawa na gaya miki ki bar wannan taurin kan."
"Muhammad mu kai shi asibiti don Allah"
Zo ki kama bindigar nan.
Ta zaro ido ta girgiza mai kai tace "Ba zan iya ba."
"Maryam...." ya kira sunanta da wani irin tsawa.
Tashi tayi ta amsa bindigar ta na kallon maharan guda uku suma da bindigu a hannunsu suna kallonta suka bushe da dariya.
Ta haɗiyi yawu makwat ta na kallon su ita ma.
Muhammada ya ciciɓi Smith ya saka a bayan mota.
"Shiga cikin mota."
Da gudu ta zagaya ta shiga.
Shi ma ya shiga yana kallonsu suna kallonsa.
Yana jan taku ɗaya suka sa harbi sun kuma tare hanya.
Ya gama yanke shawarar ta kansu zai bi ya wuce.
Ya bawa motar wuta ya fige motar da gudu. Ganin da gaske kan su zai bi ya sa suka dare gefe ya fice daga layin.
Na cikin motar yace "Ku shigo mu bi su ku shigo."
Suka shiga sai dai ko mai irin motar Muhammmd ba su gani ba. Dole suka kama hanya suka koma.
Muhamamd kuwa na ganinsu. Dan laɓewa yayi a wani lungu don ya san zasu biyo shi ɗin.