Chapter 13
by @khairatup01
RUFAFFEN DUMA
Ummulkhair S Panisau.
(khairatup)
Karamci writers Association.
Wattpad:khairi_muhd.
13.
"Za mu kai shi asibiti mafi kusa. Miss ki daina kuka ki rufe wurin da kyau jini ya daina zuba."
Daman ta sa ɗankwalinta haka ta kuma dannawa tana share hawayenta ."Don Allah ka yi sauri,numfashinsa yana sauri."
Motar ta kuma ketare titi cikin gudu,fitulun titin suna wucewa kamar walƙiya.Har sai da suka isa cikin asibitin.Muhammad ya taka birki,ya fito daga motar cikin hanzari.
Da sauri ya shiga ciki yace "Emergency!"
Ma'aikatan lafiya suka fito da gado mai taya ,suka ɗauko Smith suka saka shi a kai.Marayam ta bi bayansu da gaggawa ,tana kuka da addu'a a cikin ran ta.
"Ya Allah ka cece shi." Ta faɗa da murya mai rauni da karaya.
Muhammad ya tsaya a bakin ƙofa,zufa na keto masa duk da sanyin da ake yi.
Kallon Miss yayi yace "Maryam...kar ki damu in sha Allahu za a ceto shi. Ki yi imani."
Kallonsa tayi idanuwanta cike da hawaye. "Na gode da ka zo ka taimaka mana."
Wayarta ta ji tana ringing ta manta ma da wayar a cikin aljihunta , zaro wayar tayi daga cikin aljihu. Sai dai kiran ya katse. Sai kuma saƙo ya shigo.
"WANNAN GARGAƊI NE KAWAI. IN KUMA BA KI BAR BINCIKEN BA GARGAƊI NA GABA SAI YA FI WANNAN."
Jikin Maryam yayi sanyi. Ta juya ta kalli Muhammad.
Maryam ta zauna a kujerar bakin ɗakin Tiyatar. Hannunta har yanzu akwai jini a jiki. Zuciyarta na rawa,idan tana kallon ƙofar ɗakin da aka rufe. Muhammad ya tsaya a tsaye daga gefe kamar mai gadin ɗakin. Hannunsa cikin aljihun wandon sa,idanuwansa na bin ko wanne motsi kamar mai shirin duk wani haɗari.
Bayan awa ɗaya aka buɗe ƙofar ɗakin, likitan ya fito yana cire safar hannu ya ce "Ku ne kuka kawo shi?"
"Eh." Maryam ta faɗa da sauri tana miƙewa. "Yaya yake?"
Likitan yace "Mun dakatar da zubar jinin. Wuƙar ta kusa taɓa masa zuciya amma bata kai nan ba. Yanzu mun maida shi ICU ,amma har yanzu bi farfaɗo ba. Yana buƙatar kulawa sosai da hutu."
Maryam ta ji wani nauyi ya sauka daga zuciyarta. Ta dafe ƙirjin ta tace "Alhamdu lillahi."
"Duk wannan abin saboda ni ya faru da Smith. Da ban ce muje ba da ƙila yana gidansa a kan gadonsa yana bacci."
Muhammad ya gigrgiza kai yace "Kar ki ɗora laifin hakan a kan ki. Duk wanda ya ke son ganin gaskiya ta bayyana, dole ya fuskanci haɗararruka a hanya. Amma wannan ba zai sa ki karaya ba. Ya zame miki wani tsani da kwarin guiwa wurin ganin kin cimma nasara shi ne ramuwar da za ki yi wa Smith."
Maryam ta kalle shi tace "sun ce min na daina wannan binciken."
Wannan yana nufun sun tsorata da ke ,kuma tabbas binciken ki yana kan hanya akwai wata manakisa da ake ɓoyewa."
"Nima na gamsu da hakan."
"Maryam,na tabbata akwai wanda ke ɓoye wani abu babba. Kuma ba za su yi ƙasa a guiwa ba, don ganin ba mu gano komai akan ku ba. Dole ne mu yi gaggawa kafin su kuma kawo miki wani harin."
Miƙewa tayi tsaye ta tsaya bakin ƙofar ICU. Idanuwanta cike da hawaye,amma ta daure ,lokaci guda kuma ta juya tace "To me za mu fara yi?"
"Zo ki zauna." Ya nuna mata wuri.
"Gaya min komai me ya faru a gidan Paul ɗin?"
"Kwanfutar sa muka samu muna buɗewa kuma anyi hacking ɗinta bamu samu komai a ciki ba. Sai wasu takardu su ma sun tsufa ba masu amfani ba ne ba sai....." sai kuma ta zaɓi da tayi shiru bata son ta faɗawa kowa komai yanzu ta sa a ranta ba zata dinga gaywa kowa komai ba."
"Sai me kuma?"
"Ba komai iya su kenan kuma sun ƙone a gidan Paul."
Wata ma'aikaciyar jinya ce ta tsaya a gabansu tace "Kece Maryam?"
Maryam ta ɗaga kai ta kalleta tace "Ni ce."
"Ok. Wani a waje yana son ganin ki."
"Wanne ne zai zo gani na a asibiti a wannan lokacin?"
"Ban sani na bai gaya min sunan sa ba. Yace akwai saƙon da zai baki."
Maryam ta kalli Muhammad ta kalli Nas. Muhammad ya ɗaga mata kai alamar taje.
"Ba matasala?"
"Zan biyo bayan ki na baki kariya."
Hanyar da Nas ɗin ta bi nan suka bi. A harabar asibitin suka tsaya.Wani mutum suka gani a tsaye sanye da hula mai rufe fuska da facemask.Ta matsa kusa, mutumin ya ajiye wata ƙaramar jaka a ƙasa sannan ya juya ya bar wurin ba tare da yace uffan ba.
Maryam ta kalli jakar zuciyarta na bugawa.Ta bi bayan sa da kallo har ya ɓace
Sai kuma ta juya ta kalli
Muhammad tace "Me yake nufi?"
Muhammad ya sa hannu ya ɗauki jakar. Buɗewa yayi ya ga wani fayil ne a ciki da kuma takardu da wani USB drive da aka ɗora akan wata takarda.
"NA YARDA DA KE SHI YA SA NA BAKI WANNAN SHAIDAR."
Muhammad ya kalli Maryam ,idonsa na bayyana cewa lamarin ya fi yadda suke tunani.
"Maryam muje na kai ki gida kiyi wanka ki huta."
"Uhm'uhm , ba zan tafi na bar shi ba. Tsoro nake ji kar naje a kashe shi."
"Maryam in kin tsaya ma ba za ki iya yi masa komai ba. Zan saka yarana su zauna in na gama shirina ma zan saka a dauke shi daga nan a kai shi wuri mai tsaro."
"Amma..."
"Ki yarda da ni."
Dole haka ta haƙura ya kai ta gidan amma ranta cike da fargaba da zulumin mai gobe zata haifar.
Yana sauke ta ya juya. Tun kan yayi nisa ya danna wayarsa ya kira wata lamba.
"Yallabai."
"Akwai aiki. Ina son a sauyawa Smith wurin zama a yau a daren nan ko Miss bana son ta san an sauya mai wuri. Ka gane abinda nake nufi dai ko?"
"Na fahimta Yallabai yanzu zan yi yadda kake so."
Kit ya kashe wayar. Kaitsaye gida ya nufa a gajiye yake wanka yayi da ruwa mai ɗumi. Yana saukowa zai ci abinci a kan dinning mai aikin sa ya shigo da wata envelope ya ba shi.
"Daga ina?"
"Yallabai afuwa, na sha'afa ne ban baka ba. An kwana biyu da kawo wa baka nan yau kuma da na yi niyan baka sai ka fita."
Karɓa yayi ya ajiye ta a gefe. Sai dai ƙamshin turaren da ya ji a jiki ya ɗan ja hankalinsa ya san turaren amma ya kasa tuno na waye.
Yana gama cin abincin ya sha shayi,Ya koma falo. Dama a gajiye yake sosai,bai taɓa artabu irin na yau ba shi yasa duk kan sa sai ciwo yake yi masa.
Envelope ɗin ya buɗe nan ya ci karo da hotonsa da Maryam a hotel ɗin nan da suka je cin abinci. Da takarda a ciki.
"International Business man yana holewa da ƴar jarida. Wannan baban labari ne da in aka wallafa duniya zata yi Allah wadai da kai. Saboda haka kayi hattara ka fita daga harkarta."
Yana gama karantawa ya saki murmushi ko dogon nazari ba zai yi ba wannan Nimra Wazir ce. Ƙamshin turaren da ya ji ma na ta ne sai da ya karanta saƙon ya gane.
"Mata! Ba su da hankali."
A fili kuwa cewa yayi "Hoton nan yayi kyau,dama bamu yi hoto da ita ba."
Ya so ya kira ta kuma sai ya ga dare yayi. Saƙo kawai ya tura mata a taƙaice.
"Nimra wannan wasan ya fi ƙarfin ƙaramin kan ki. In kin ga dama ki wallafa a shafin farko a jaridar gobe ina jira."
Yana aika mata ya ajiye wayar ya haura sama don bacci yake ji.
Ya so ya kira Miss amma sai ya ga dare yayi sosai gara ya bar ta ita ma ta huta don a tsorace take ga kuma harin da aka kai wa Smith a gaban ta.Abu ɗaya ne ya ba shi mamaki kuma ya dame shi,meye dalilin da ya saka maharan suka ƙi yi masa komai? Me yasa suka koma da baya da ganin shi? a iya tunaninsa bai da haɗi da su bai ma taɓa ganinsu ba. Tambayoyi ne rututu a kan sa amma bai da amsar su bare mai ba shi amsar. Dole ya koma ya kwanta, addu'a ya fara yi kafin ya shafa ya kashe fitila ya kwanta.
*
Zaune take a kan wata ƴar ƙaramar kujera da ke cikin ɗakinta. Ta cure ta dunƙule a wuri guda tana zukar sigari. Launin idanuwanta sun sauya kala sun koma jajir da su saboda zuƙe-zuƙe. Ta gama kai wa linter lokacin da saƙon Muhammad ya iso mata. Tashi tayi da sauri cike da mamaki da fusata tayi wulli da wayar gefe guda tana sakin ihu. Irin ihun da sai da ya jawo hankalin masu aikin gidan da su kan su iyayen nata. Tuni baccin kowa ya ƙaurace yau Hajiyar gidan ta botsare jujunta sun tashi.
Har ƴar tseren shiga ɗakin ake tsakanin Daddy da Mummyn.
Aka bar masu aiki a ƙasa da leƙe da ɗage wuya.
Fitilar ɗakin Daddy ya kunna yana salati.
"My daughter! meye haka me aka yi miki me ya faru?"
"Me ya sa kike ihu Nimra?" Mummy ta tambaye ta.
Nimra kuwa da ta barbaza gashinta da hannu sai ta koma kamar wata sabon kamu. Tana share hanci tace "Daddy ko na mutu ko na kashe Muhammad ko na kashe yarinyar da ke son shiga tsakanina da masoyina. Wallahi Daddy da gaske nake yi in Muhammad bai zama nawa ba nima ba zan bari ya zama na wata ba, ba zan taɓa bari ba."
"Ya isa, shhhhh! Ya isa nutsu,nutsu Baby ba wanda zai raba ki da Muhammad." Daddy ya faɗa yana shafa kanta.
A hankali da wayo da dabara suka lallabata suka kai ta kan gado. Mummy abin duniya ya ishe ta, ta zauna a gefen Nimra tana shafa kan ta kamar zata yi kuka ita ma.Daddy da kan sa yayi mata allurar bacci.Suna nan har baccin ya ɗauke ta. Tashi suka yi suka kashe mata fitilar suka fita.
Kowa yayi cirko-cirko a tsaye. Mummy ta takarkare ta sakar musu wata iriyar tsawa tace "Munafukai ku koma inda kuka fito kun wani tsaya gulma." Ai ƙafa mai na ci ban baki ba tuni suka yi ta kan su don sun san ba ƙaramin aikinsu ba ne su koresu ko a gana musu wata azabar.
A cikin ɗaki kuwa Mummy ta kalli mijinta Waziri cike da damuwa tace "Waziri , wannan abin fa ya fara isa ta hakan nan. Ko ka ɗauki mataki ko na biyo ta bayan gida."
"Zuwaira ki bi a hankali. Nan da kika gan ni ina sane da komai ba wai na naɗe hannu na tsaya a gefe ba ne. Akwai lokacin da nake jira. Shi Sanata da kuke gani bai isa ya hana Muhammad ko saka shi ba hasalima ba sa magana ko shi Sanata bai san ranar ƙarshe da ya ga Muhammad ba. Yanzu kuma siyasar nan ta sako mu a gaba in ba gamawa aka yi ba ,ba zamu samu sauƙi ba. Ina son hankalinmu ya kwanta ne na san yadda zan mai ya aure ta."
Ajiyar zuciya ta sauke ta sa hannu ta kulle fuskarta kamar zata yi kuka don tausayin ƴar ta tilo mafi soyuwa a gare su.
*
Da sauri na shige ɗakina saboda bana son Mama ta san ma na dawo bare ta ga jinin da ya ɓata min jiki hankalinta ya tashi. Sosai na dirje jikina saboda yadda jini ya kama jikina sai ƙarnin jini nake yi ƙyanƙyamin kaina na dinga ji.
Na jima kafin na fito na sauya kaya. Tunani na faɗa kan halin da Smith ya ke ciki. Gabaɗaya na koma tunanin shin waye ya sanar musu da zuwan mu gidan? Ko daman dai ana bibiyarmu ko kuma suna waje dama suna jiran isowar mu? Ba wai arashi ba ne zuwan na su dama sun shirya kashe mu ne. Wai ma shi wannan Paul Stone ɗin wanne sirri ya gano ake bibiyar case ɗin sa haka?
Tonowa tayi da hoton da ta ɗauko kuwa ta tashi da sauri ta janyo dirowa ta ɗauko hoton. Kulle ɗakin tayi da sakata ta koma kan gado ta zauna a tsakiyar gadon ta ajiye hoton. Hoton ta ƙura wa ido da kyau tabbas manyan ƴan kasuwa ne a wancan lokacin wanda duniya ta san su sosai. Amma ta kasa tuna sunansu. Wayarta ta janyo amma sai ta ga ta mutu sai a lokacin ta tuna bata da carji. Sauka ta kuma yi ta saka wayar a caji ta koma ta zauna, ta juya bayan hoton nan ta ga sunansu da kuma shekarar da aka yi hoton. Ta tuna a shekarar aka yi wata babbar fallasa a kan wasu manyan mutane a jihar masu aikata manyan laifuka da sunan su ƴan kasuwa ne har ma aka yi nasarar kama su.... zuciyarta na ƙara ingizata akan ta nemo laifin da suka yi daga lokacin ne zata fara warware zaren.