RUFAFFEN DUMA

Chapter 14

by @khairatup01

RUFAFFEN DUMA
Ummulkhair S Panisau.
(khairatup)
Karamci Writers Association.
wattpad:Khairi_Muhd.
Arewabooks:Khairatup01

14

*

Da sauri ta kuma sauka ta ɗauko jakar nan da aka kawo mata ta ajiye a gefenta. Hannun ta har rawa yake yi wajan buɗe kwamfutar ta. Kunnawa tayi ta. Tana ta jijiga jikinta har ta samu wayar ta kunnu. 

Sunaye biyu ta rubuta. *Alhaji Sule Bako da Chief Henry Okoro* tuni aka jero mata jawabai a kan su. 

"Shahararrun ƴan kasuwa  masu hannun jari a masana'antu da kamfanoni daban-daban waɗanda aka kama shekaru huɗu baya bisa zargin safarar yara mata. "
 Maryam ta koma da baya ta sauke ajiyar zuciya. Jakar gefen ta ,ta janyo ta buɗe. Fayil ɗin ta fara zarowa ta kuma ɗauko USB ɗin ta saka a kwamfutar ta jona. Hotunan mutane biyun ne aka ɗauka ba tare da sanin su ba , sai hotunan yara ƙananu ƴan mata da ma manya da yara maza. 

Kenan sune mutanen da Paul yayi bincike a kan su ?  Sun kasance manyan ƴan garkuwa da mutane  suna safarar yara daga ƙauyuka zuwa birane , wasu kuma ana kai su ƙasar waje. Paul ne ya bankaɗo wannan sirrin har ta kai ga aka kama su sunansu ya bazu a ƙasar duk da ana zargin ba su kaɗai ba ne da wasu amma sun ƙi faɗar su da waye. Fayil ɗin ta kuma duba wa, hotunan yaran da aka ceto,da rahotanni na shari'ar. Sai a lokacin ta tuna ta kuma jawo jaridar da aka yanka wani sashi a ciki aka adana. "AN SAMU SHAIDU AKAN WAƊANAN ƳAN KASUWAR NE TA HANYAR WANI WANDA BA A SAN SHI BA." Ta fito da idanuwanta waje tace "Kenan Paul ne a lokacin wanda ya ɓoye kan sa?"

Ta kuma dubawa nan ta ga jerin sunayen da aka rubuta masu sa hannu a lamarin amma ba a wallafa su ba kuma ba ayi shari'a dasu ba bare a kamasu ta tambayi kan ta "Why?"

Cike da tsoro ta ce "Kenan waɗanda ba a kama ba ɗin suna da sa hannu da ɓacewar Paul ko kuma bai haƙura ba ya ci gaba da bincike a kan su? Wataƙila ma sune yau suka aika masu  maharan dan su kashe su.

Ta gama tsayarwa a cikin ranta,dole ne ta ga waɗanan mutanen biyun a gidan yari, zata je ta ji ta bakinsu da kanta.

Amma ta san ba za a bata damar ganinsu kaitsaye ba sai tana da takardar izini daga kotu.Ta hanya ɗaya zata samu. Muhammad zuciyarta ta raya mata. Nan da nan ta ja wayar ta soma nemansa amma bai ɗaga ba. Sai a lokacin ta tuna dare yayi sosai don ita bata yi bacci ba baya nufin wasu ma ba su yi ba. Haka ta haƙura ta tattara komai ta adana ta kwanta cike da tunani kala-kala.

Da safe ta shirya. Idanuwanta sun kumbura saboda rashin bacci. Ko da Mama ta gan ta sai ta kalle ta tana son tayi mata magana sai kuma ta fasa don ta san ko ma tayi mata babu abinda zata ji daga ciki kuma ba zata bari ba,har ma ta fi mahaifinta taurin kai da ƙarfin hali. 

"Barka da safiya Mama."

"Barkanmu Maryamu. An  fito da wuri haka?"

"Mama aiki muhimmi." 

"Ai kullum a haka kike. Zauna ki karya kafin ki tafi"

"Mama in naje zan ci  a cafe."

"Maryam...."

Jakarta ta sura tayi waje tana "Mama in na dawo zan ci." 

Mama ta girgiza kai cike da taƙaici. Ta manta ranar ƙarshe da suka zauna ita da Maryam suka yi hira ko magana mai tsayi. A kullum aikin ta ne prority ɗin ta. A lokuta da dama ma sai ta dinga tunanin anya kuwa bata yi wauta a barin Maryam ta faɗa harkar jarida ba?    

*

Adaidaita sahun bai tsaya a ko ina ba sai a ƙofar gidan The Muhammad Sageer. Ta biya shi kuɗinsa ya tafi.

Wayar ta, ta zaro daga cikin jakarta ta kira layinsa. Kamar zata tsinke sai kuma aka ɗaga.

"Miss!"

"Ina ƙofar gidan ka ,ina da buƙatar taimakon ka da gaggawa."

"Miss ba kya gajiya da janyo fitina? Yau kuma meye?"


"In shigo muyi magana ko in ta tsayawa a nan waje?"

"Oh! Bari a shigo da ke." Ya faɗa yana ajiye wayar.

Bata jima ba aka buɗe mata gate. Bata shiga ciki kaitsaye ba, inda suka zauna rannan ta shiga ta zauna. 

Kusan minti goma tana zaune wuri guda tana ta saƙe-saƙe,bata lura da zuwan sa ba kawai kofin shayi da plate ɗin chips da gashashiyar kaza ta ga an ajiye mata a gaban ta.

Ta ɗaga kai ta kalle shi.

"Eat. Wannan farar safiyar na san baki karya ba kika fito. Fara karyawa tukunna sai muyi magana."

Bata yi masa musu ba daman cikinta na kiran chiroma rabonta da abinci ma ta manta. Haka ta cire fulako ta ci abincin kuma ga mamakinta tas ta cinye ta sha tea ɗin harda gyatsa. 

Ya ɗago kan sa daga danna wayar da yake yi yace "Ko ke fa.Yanzu yaƙi zai fi miki sauƙi."

Tayi murmushi kawai. 


"Ina jin ki me zan miki?"

"So nake ka shigar min gaba. Ina son shaidar izinin zuwa gidan yari don ganin Alhaji Bako da Henry a jail yau."

Gabaɗaya hankalinsa ya tattaro ya maida kan ta. Yayi mata ƙuri da idanuwansa masu kaifi da ladaftar da masu kallonsa. Dole ta ɗauke kallonta daga nasa.

"Miss! Ina kike son jefa kan ki ne? Na ga kin ɗauki abin nan personal?"

"Eh na ɗauke shi personal, saboda mahaifina,saboda ƙasata da kuma talakawan da ake zalinta."

"Humm! Kina burge ni saboda jarumtar ki Miss. "

"Wai ba zaka iya faɗar suna na ba?"

"Miss ya fi miki daɗi. Sunan Mamana gare ki, so ina respecting ɗin mai sunan." 

"Ayya!. Allah Ya jiƙan ta."

"Amin, na gode."

"Muje ko?"

"Eh."

Bai wani sha wuya wurin samun takardar izinin ba.

Tana cikin mota yayi komai ya kai mata. In yana tare da Maryam baya barin securities ɗin sa su raɓe shi a ɓoye ma yake fita ko yau yana da aikin da zai yi mai matuƙar muhimmanci amma ya zaɓi ya zo ya taimakawa Maryam yarinyar na burge shi da jajircewar ta da son gaskiyarta bata karaya. Shi ma yana son ya gano abubuwa da dama waɗanda yake da zargi a kan su. 

"Na gode ,sai na dawo."

"Hey! Wait ke kaɗai za ki je ne?"

"Eh. Da wa zan je da?"

"Ni mana."

"Aa bana son ana ganin mu tare. Kai fa babban mutum ne da duniya ta san ka kar alaƙa da ni ya taɓa maka martabar ka."

"Ban tambaye ki ba.ko ki bari na raka ki ko ke ma ki haƙura don ba zan bari ki je ke kaɗai ba,musanmman ma bayan abinda ya faru da ku jiya, bare kuma yau da kike shirin zuwa gidan yari cikin manyan masu laifi."

Tayi nazari kuma ta gamsu da bayanansa a halin da take ciki yanzu tana da buƙatar garkuwa.

*

Babban gidan yari na Mando suka nufa. Gidan yarin yana daga gefen titi ne a gefen babban titin da ke kai wa filin jirgin sama,yana tsare da katanga mai tsaho da kanti na tsaro.

Jami'ian DSS suka raka su har cikin ɗakin baƙi.Ɗakin yana da gilas a tsakiya,inda ake magana ta waya da waɗanda aka tsare.

Muhammad ya kalle ta yace "Ba zan shiga ba ina nan."

"Na gode." Ta faɗa akan leɓɓanta a hankali.

Tana nan zaune suka shigo. Dukaninsu cike da gajiyawa a tattare da su da rashin kwanciyar hankali. Jikinsu sanye da rigunan gidan yari. Maryam ta daidaita nutsuwarta ta ɗauki wayar ta saka a kunneta tace "Suna na Maryam,ɗaliba ce ni. Ɗalibar jarida na zo ne akan wani project akan wani ɗan jarida da ya ɓata ,mai suna Paul Stone."

Alhaji Bako ya saki murmushi  ya maimaita sunan "Paul Stone... jarumin da ya tarwatsa harkokinmu. Na ji daɗin ganin har yanzu akwai  masu sha'awar abinda ya aikata har ba a manta shi ba, kamar yadda mu ma bamu manta shi ba."

Da wani irin kallo Chief ya kalli Maryam yace "Kin zo neman gaskiya? To ki kula yarinya. Paul ya bi wannan hanyar yanzu yana ina?"

Cike da ƙarfin hali Maryam tace "Na san abinda kuka aikata. Na ga hotunan yara ƙananu da kuke safararsu. So nake na sani yana raye ko ya mutu?"

"Ba mu sani ba, ba mu muka sa aka mai wani abin ba, kamar yadda kike gani mun yarda da hukuncin da aka yi mana. Sai dai ki nemo sauran da suke waje suna rayuwarsu mu muna nan muna girbar abinda muka shuka. Ki tambayi waɗan da suke da iko a gwamnati da kasuwanci. Paul ya bankaɗo sunayensu,amma bai kai ga fallasa su ba."

Zuciyar Maryam ta buga tabbas ta ga sunayen amma bata san su waye su ba.

Henry yace "Yarinya saurare ni da kyau, nan da kika gan mu hasali a killace muke amma muna da labarin komai. Da kin san su waye kike ƙoƙarin shiga gonarsu da kuwa baki yi dalilin da ya sa Smith ya kusan rasa ransa ba,Ki kula da abokanan ki.ki daina wannan binciken kafin ke ma ki zama labarin da za a rubuta gobe."

"To wai me yasa duka wannan ɓoye-ɓoyen?"

"Ki tambayi kan ki.Wanene ya fi jin tsoron abinda Paul ya sani? Ba mu ba ne mu kawai ƴan wasa ne da ake juyawa."

Numfashin Maryam ya tsinke a hankali ta gyara zama tace "Kuna nufin akwai wanda yake waje wanda ya fi ku haɗari?"

Basu ƙara magana ba jami'ai suka shigo suka ce lokacin ta ya ƙare. Aka maida su ciki ita kuma ta fita waje. Tare da Muhammad suka fita.

"Kun gama?"

"Eh mun gama."

"Bari na ɗauko mota."

Motoci take bi da kallo yadda suke wuce su, titin ya rabu biyu akwai wadda zata maida ka sabon titin Rigasa wasu koma na komawa Mando. Iska ke bugata kawai amma ba sanyin take ji ba zuciyarta ta ƙudurci sabon niyya.

"Ba zan tsaya ba." ta furta a hankali. "Inda Paul Stone ya tsorata ya tsaya da wannan gaskiyar ma ba zata fito ba. Zan kamala abinda ya fara." 

Ta kalli titin da zai maida su cikin gari a hankali take tunani a ranta "Waye Mastermind ɗin?"

"Kai ni wurin Smith."

"Miss! Ki yi haƙuri da ganin Smith na tsahon lokaci, na maida shi inda ba wanda ya sani kuma ba zan bari kema ki sani ba."

Maryam ta saki baki kawai. Kamar zata yi mai taurin kai sai kuma ta fasa tace "Kai ni Global Times."

"Zan yi hakan." 

*

"Wai ƙaramar yarinya ta shiga ta fita ta hana mu sakat a garin nan? Kun sa yin komai a kan ta?" Shehu ya faɗa yana kallon sauran abokan harƙallarsa.

"Tana da sa'a ne,amma bata fi ƙarfin mu ba. Ga shi yanzu Muhammad ya take mata baya yana mata aikin gadi koda mun so ba zamu iya yi mata komai a yanzu ba. "

"Ya kamata a ɗau mataki a kanta. Don da alamu wannan wata sabuwar Paul Stone ce ko ma nace ta fi shi naci." 

"Na yarda da hakan. Ni a gani na kawai a yi mata babban sharrin da ba zata iya fita ba."

"Yau fa taje gidan yari wurinsu Bako." Shagari ya faɗa.

Gabaɗaya suka amsa da "What?" 

"Ƙwarai ma taje. Don yarana sun gaya min."

"Me taje yi kenan?"

"Basu sani ba."

"Dole ne a tashi a tsaye in ba haka ba za a samar da matsala."

"Za ayi wani abu a kai in ji Wazeer."

"Na aika a ɗauko ɗaya ɗan jaridan da aka samu aka soka wa wuƙa. Amma an neme shi an rasa ,su kan su ma'aikatan basu san ya aka yi ya ɓace ba."

"Wannan aikin na mutum ɗaya ne. Kuma zamu yi maganinsa shi ma."

"A ajiye maganar maƙiya ma a gefe. Ya batun aikin nan an samo yaran kuwa? "

"An samo su amma gaskiya dai ana buƙatar ƙari sun yi kaɗan. Tun bayan wancan fallasar iyaye suke taka tsan-tsan akan kilace yaransu."

"To me kuke jira? Ai aiwatar da ɗaya aikin ta hanyar  kwamushe su,a rikitar da ƴan gari su  kwaso mana ƴan matan. Babu wanda zai zargemu."

"Daɗina da kai akwai ƙwaƙwalwa mutumina." 

"Wancan harƙar fa an gama?"

"Akwai tsaro a arear amma muna ta tsara yadda zamu yi mu haƙo kayan."

"Ya kamata, DSP, jibi makaman nan da kuɗaɗen zasu shigo a rabawa yara a ci gaba da gashi. Hakin ka ne ka kula da shigowarsu lafiya. "

"An gama Boss."

"Zaku iya tafiya. Taro ya tashi."

Haka duk suka watse daga wurin.