Episode 4
by @zahraroyal
*MUGUN ICCE*
*©Zahra Royal Star*
*ROYAL STAR WRITER'S ASSO.........*
PAGE 4
*Ƙauyen Karaɗuwa, Kankia LGA, Katsina state Nigeria*
Zama Inna tayi tana kallon ƙofar waje tana ta mita a ranta.
A fili ta furta.
"Ohh'ni har yanzu Sadiya shiru, ita bata gudun duk abunda za'a ce mata"
Miƙewa Inna tayi tana surutu ita ɗaya tana ƙarawa.
Jin sallamar Sule ya shigo gidan yana nufar wata buta dake a tsakar gidan domin zuwa ya ɗauro alwala ya dubi Inna dake tsaye tana ce masa.
"Wai Sule baka ci ƙaro da yarinyar nan ba Sadiya ne a waje?"
"A'a Inna na ɗauka ai tun ɗazu tayo gida?"
"Hmm kamar baka san wacece Sadiya ba?, ka riga kasan sai ta ɓata ma mutum rai kamin ta dawo, yanzu haka yau ma sai an kawo ƙararta gidan nan ta taɓa wani"
"To Inna mi yasa baza'a haƙura da sa mata tallar nan bane?"
"Uhum to nima ina tunanin hakan, amma dai kasan wannan ƴar tallar tana taimakawa mana sosai"
"Haka ne kam ba laifi tana rage wasu hidindimon"
"To ka gani ko banza sana'a tana da daɗi, kawai dai sai dai na sake wata sana'ar wacce za'a rinƙa saya a cikin gida kawai, inaga hakan zanyi. Ni so nake ma na kira Yayanku Umar shiru kwanaki biyu banjisa ba Allah yasa lafiya dai"
"Inna Sadiya ko an bar ɗora mata talla nan bafa daina yawo zatai ba, idan har taga damar fita saita fatan. Ya Umar kuma kowanne lokaci ma zaki iya ganinsa a garin nan"
"Ai wannan yarinya Allah dai ya shirya ta kawai"
Da Amin ya amsa yana ɗaura alwala yana fita haɗe da cewa zai duba ta idan sun idar da sallah.
Sadiya ko sai da ta saida gyaɗar ta tass harta kamo hanyar gida ta ci karo da wata ƙawarta Hasiya.
"Ke Hasiya waye na kama?"
Hasiya ta ja ta tsaya tana haɗe wani miyau tana duban Sadiya ta ce.
"Kamar ya wa kika kama kuma?"
"Ke dalla karki rainan wayo, ba ke ba ce jiya munje makaranta, an dake ni na makara shine kuka kama min dariya?, kuka biyo hanya kuna gulmata ba? ko ba haka bane iyee?"
Tsoro ne ya kama Hasiya taya akai ta san duk wannan?, iya saninta dai tasan daga ita sai Hansai ƙawarta wacce suke makwaftan juna da gidansu. Dama kuma sun daɗe sun jin haushin Sadiyar shine an dake ta a makaranta suka taho suna dariya suna zaginta da mata Allah ya ƙara.
"Nifa wallahi kinga babu ruwa na"
"Tabɗi jam ai wallahi yau sai na gurji bakin rashin kunyar nan naki, gobe ma idan an dake ni a makarantar kin ƙara saka bakin nan naki"
Sadiya ta faɗa haɗe da sauke teran gyaɗarta tana ƙara ɗaure ƙugunta.
Hasiya harta saka ƙafa zata zura da gudu taga kamar walƙiya Sadiya tasha gabanta tana kamo hannunta guda ɗaya ta murɗesa ta baya har sai da yayi ƙara ƙissss.
Wani ihu Hasiya ta saki haɗe da rufe idonta da masifar ƙarfi jin wata azaba na ratsata.
Kuka take tana cewa.
"Dan girman Allah kiyi hakuri"
"Ke ce kenan kunyi gulmar tawa?"
"Eh...e..eh... wall... wallahi munyi, amma ba wani abu muka ce bafa"
"Zaki ma faɗi gaskiya ne yarinya"
Sadiya ta faɗa tana saka ɗayan hannunta ta kamo ɗayan hannun Hasiya ta ƙara murɗewa, Daddawa da kukar da Hasiya ta sayo ma Innarta suka zube a ƙasa, nan take ƙasa ta buɗe su.
Sai da Sadiya taga Hasiya ta jigata harda sakin fitsari a wando tsabar yadda take jin azabar murɗe mata hannuwa da Sadiya tayi. Har zata sakar mata hannu ta wuce taji saukar maganar wani mutum ya tsaya a kansu yana cewa.
"Ke Sadiya sakar mata hannunta mana, wannan ai mugunta ce, dama ke bakya jin bari kuma bakya jin maganar kowa"
Taɓe baki Sadiya tayi tana sakin hannun Hasiya, tana sakinta ko Hasiya ta zura da mugun gudu tana kuka ta nufi gida har tana neman faɗuwa a ƙasa.
Tana kallonsa ta ƙara taɓe baki ta ɗauki teran gyaɗarta ta ɗora akai tana tafiya tana ƙara binsa da wani kallo kamin ta ce.
"Mutum dai ya rinƙa shiga abunda babu ruwansa, wata rana shima ya sake ya shigo gona ta haka zanma ƴarsa ko kuma abun ya ƙare kansa"
"Marar kunyar banza marar kunyar wofi, a haka zaki ƙare sai shegiyar rashin kunya cike da ciki"
Hararara ta zafga masa kamar idonta zasu faɗo, shi kam ganin wannan uwar hararara kamar wacce ake juyarma ido, yadda take juya su kamar aljana ya bashi tsoro da mamaki, da sauri ya bar mata wajan, dan yasan ta tsaf zata aikata abunda ta ce ɗin, ba wadda bai san Sadiya a garin ba. Idan ka taɓa ta saita rama, idan baka shiga gonarta ba bazata taɓa ka ba, amma muddun ka taɓa to sai fa anjika da ita, bata barin saita kwana wannan halinta ne.
Tana shiga gidan ba sallama ta faɗa.
Inna na zaune tana ta duban hanya, ga Sule shima shiru bai dawo ba.
"Koma kiyi sallama"
Inna ta faɗa tana ƙare mata kallo.
Turo baki tayi tana aje teran dake kanta zata ƙara magana Inna ta ƙara nuna mata hanyar waje tana cewa.
"Zaki koma kiyi sallamar ne ko sai na zo kanki yanzun nan?"
Bubbuga ƙafa ta kamayi tana ƙara ɓata fuska ta koma kamar zata saki kuka.
Sallamar a ciki-ciki tayo ta ta shigo gidan, tana miƙa ma Inna kuɗin gyaɗarta da wasu duk suka zube a ƙasa wajan faɗan data tsaya.
Amsa Inna tayi tana kallon kuɗin ta jujjuya su tana ƙirga su, nan take ta gane ta zubar da wasu, girgirza kanta kawai Inna tayi tana cewa.
"Wai ke baza ki taɓa hankali bane wai Sadiya?, kinfa fara girma haba Sadiya"
"To ni Inna...
"Kinga ina kika tsaya ma tukunna?"
"Ni Inna babu ina na tsaya"
"Ƙarya kike wallahi. Su wa'innan sauran kuɗin da kike je kika zubar fa suna ina?"
"Allah kuwan Inna ni...."
"Ni rufe mini baki, waye bai san halinki ba, Allah yasa ba tsayawa ki kai mugun jan faɗan nan naki ba in...
Maganar Inna ce ta katse jin tashin maganar wata mata da tayo sallama a tsakar gidan.
Tsabar faɗan data shigo dashi ko sallamar bata idasa ba ta faɗo gidan riƙe da Hasiya a hannunta.
"Wallahi yau ba sai gobe ba sai ta rama murɗe mata hannu da wannan aljanar jikar ƴar taki tayi ma ƴata ba zai yiwu ba wannan ai tsabar mugunta ne"
Innar su Hasiya ta faɗan tana tsayawa akan Inna tana harare-harare.
"Innar su Hasiya lafiya dai ko?"
"Ai ita ce zata kawo haka ko?, ai kinfi kowa sanin hatsabibancin wannan jikar taki. To kama min ƴa tayi ta tare a hanya ta murɗe mata hannuwa har suka fara banɗarewa, a haka ta dawo min gida, sana tasa ta tayi min asarar aiken da nayi mata, ta zubar min da kuka da daddawar da ta sayo min, dan haka wallahi sai an biya ni kuɗin aiken da nayi mata, sana ta tabbatar ta gyara mata hannuwa su dawo dai-dai"
"Subhallahi, dan Allah kiyi hakuri"
"Babu fa wani maganar haƙuri yawwa, kawai ayi abunda na ce shine kawai"
Innar su Hasiya ta faɗa tana ɗaga ma Inna hannu alamar ba maganar tayi haƙurin nan.
Inna ta kai dubanta inda Sadiya take tsaye tana jefa mata wani mugun kallo. A mamakin Inna gani tayi tana kallon Hasiya kallo irin na zamu haɗu ne nan gaba.
"Zo nan Sadiya na ce"
Maƙe kafaɗa Sadiya tayi alamar bazata zo ɗin ba, tana komawa baya kaɗan kamar mai shirin rugawa da gudu tabar gidan.
Sule ne yayo sallama hakan yasa Inna saurin cewa.
"Yawwa kamo min yarinyar nan dan Allah Sule"
"Inna mike faruwa ne?"
"Kasan Allah idan ka bari ta fice a kanka zan huce haushi na da maganar da kullum take jawo min"
"Amma Inna...
Maganarsa ce ta maƙale jin ihun Sadiya data saki tana kallon ƙofar waje.
Wata hamdala Inna ta saki tana cewa.
"Kai Alhamdulillah gara da Ubangiji yasa ka dawo yanzu a dai-dai wallahi Umar, kaganta nan bata da aiki kullum sai jan faɗa, ai ga wadda kike tsoro nan ya dawo dole zaki nutsu ne yanzu"
Rugawa da gudu Sadiya tayi ta ɓoya a bayan Sule jikinta na ɗaukar rawa, dan idan akwai wadda take mugun tsoro baya wuce Ya Umar. Tunda yasa ƙafa ya tafi birni karatu basu sake ganinsa ba sai idan yayo masu aike ko kiran waya, sai yau da Allah yasa ya dawo a dai-dai da lokacin data tafka laifi, tasan waye shi, tasan abunda zai iya mata, shi yasa take mugun shakkarsa da tsoronsa.
Daka kallesa zaka san ya banbanta da mutanen dake zama a ƙauyen, saboda shi ɗan gayu ne kuma akwai wayewa sosai a tattare dashi.
Sosai Sule ke murmushi na jin daɗin ganin ɗan uwansa ɗaya tilo daga shi sai shi sai kuma auta Sadiya iyayensu suka haifa.
"Mike faruwa ne baiwar Allah?"
Ya tabbaya da muryar nan tasa mai cike da wata irin natsuwa da zurfi.
Ita kanta matar dole ta sassauta Muryarta dan baƙaramin kwarjini taga yayi mata ba, ta shiga gaya masa duk abunda ke faruwa.
Kuɗi kawai ya zaro ya miƙa mata da bai san adadin nawa bane ma, ta amsa hannu na rawa, ta kamo Hasiya suka fice daga gidan.
Ko kallon inda Sadiya take baiyi ba, amma ita tasan ba wai ya kyale ta bane, wallahi tasan akwai abunda ya taka ne.
Sosai Inna ke murnar ganinsa sai nan-nan take dashi shida Sule, ita kuwa raɓe ta koma can nesa dasu tana jin yadda ƙirjinta ke dukan uku-uku gaba ɗaya sai taji tana ma jin haushi su Inna har Ya Sule ɗin, ji dan Allah yadda suka wani mance da ita, ta wannan mugun mai baƙar zuciya suke yi ma kawai.......